Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 4

RAYUWAR MACE*
Hafsat Rano
Free Page (4)

***Zazzaune suke da kawayenta su biyar wanda sai da Umma tayi mata fad’a sannan ta sanar da su da maganar bikin,sai gasu kuwa washegari da aka yi kafi. Lefe suka kalla suke cin abincin da Umma ta saka aka kawo musu sannan suka me kushin da Nadeeya ta turo ta shiga aikin yi musu kunshin wanda ita dai asma’u kawai bin su take da kallo ta sallama komai musamman da taga an soma yi mata lallen sai ta fad’a kogin tunanin yadda rayuwar ta zata kasance idan ta auri Adam. Duk hayaniyar da suke da tsokanar ta, bata kula sh ba, dan ba ma gane musu take ba. Ana gama mata jan lallen sai kawai ta zame a wajen ta kwanta ta rufe idon ta, tana fatan ace tayi bacci ta farka taga an ce ai mafarki ne babu maganar auren ta da Adam din. Sai dai sam baccin yaki daukar ta, duk abinda suke fad’a na shakiyanci tana jin su.
   Sai bayan magriba sannan aka gama musu,  suka tafi anan ta samu ta shige daki ganin gidan ya cika sosai da yan uwa, gobe za’a yi kamu dan haka makusantan umman duk sun zo da su Yaya Hadiza da yaran su, dangin Abba kuwa kusan rabin su suna gidan Hajiya Mama, sai gobe zasu taho nan din daga nan kuma sai su raba kansu gida biyu wasu su zauna anan wasu a gidan Hajiya Maman.
   Tana kwance Rauda da Hidaya suka shigo, suka zauna suka shiga yi mata hira, sai ta mike ta dan ware a cikin su har tana kyalkyala dariya tamkar bata da sauran damuwa, su kansu sun yi mamaki sai suka ki yarda su bar ta ko na dan lokaci ne suka raba dare suna hira irin ta yan uwa, da tuna rayuwar baya da yarintar su. Sai chan dare suka kwanta suka tashi da asubah daga nan kuma aka shiga shirye shiryen kamu da za’a yi a kangon Abban dake jikin gidan nasu ta baya.
   Bata fito ba ta sake gyara kwanciyar ta dan dama ba sallah take ba, ta dai kama ruwa ta wanke jikinta sannan ta sauya kayanta ta koma ta kwanta dan bata san idan ta tashin me zatayi ba, kayan da zata saka a kamun da komai duk su Rauda sun hada mata waje daya, dama tun farko tace musu ba zatayi make-up ba, wanda dama shine yake cinye dukka lokacin shiyasa kawai ta cigaba da mikewa tana jin hayaniyar na tashi ana dora tukunya ana saukewa alamun dai da gaske bikin ake, babu kuma wani abu da zai hana sai dai mutuwa.
   Ji tayi ta nemi guntun hawayen da take dashi ta rasa, tana tunanin ma ko sun kafe ne tun yanzu dan ta san akwai sauran kuka a gabanta. Sai kawai ta dinga sauke ajiyar zuciya a hankali tana karanto duk addu’ar da tazo bakin ta.
   Breakfast su Rauda suka shigo dashi, kosai ne da kunu sai farfesu da akayi mata daban sai ruwan tea game bukata, bata shan kunu da dangogin sa tun da chan, shiyasa sai Rauda ta hada mata tea ta dinga hadawa da kosan da bread kuma sai taci sosai dan kwana biyu bata samun isasshen cin abinci saboda zulumi. Umma ce ta shigo rik’e da wata Leda a hannun ta, ta ajiye a dakin ta kalle ta, tace

“Ku koma chan gidan Safiyya sai ku shirya a chan nayi mata magana, za’a aiko muku da abincin rana idan an gama nan dakin ma wasu bakin ne zasuyi amfani dashi.”

“Dama yanzu muke shirin tafiya.” Cewar Rauda tana tattare kayan wajen.

” Kizo daki na.”

Tace wa Asma’un tayi gaba, tashi tayi tabi bayanta tana fita akayi mata cha, amarya amarya, ta dinga yake kawai tana gaishe su har suka dangana da dakin Umman inda duk kannen umman suke cike. Gefen gadon ta zauna tana gaishe su, suna amsawa wasu suna tsokanar ta, Aunty hauwa ce ta tabo ta, tace ta dawo ciki sosai, ta matsa wajensu, ta soma mata magana a hankali yadda ba kowa zai ji ba, sai ita da take fadawan, har ta gama bata ce komai ba, tayi godiya idon ta na cikowa da kwalla dan maganganun sun shige ta sosai kasancewar Aunty Hauwan babbar malama ce ta san addini kwarai, duk abinda ta fad’a mata gaskiya ne sai dai bata san ta Ina zata fara ba, ta Ina zatayi yiwa Adam irin biyayyar da Aunty Hauwan take fad’a. Ta dan jima a dakin har sai da su Rauda suka leko sannan ta tashi suka dunguma zuwa gidan Safiyya, amarya ce bata jima sosai a unguwar tasu ba, suna da alaka ta bangaren Umma shiyasa ma umman ta zabi su je chan su zauna saboda gidan zai cika da mutane sosai.

   Wajen karfe hudu ta gama shiryawa da taimakon su Rauda da wasu kawayen ta da suka zo tun dazu, kuma suka tursasata dole aka dan mata makeup duk da light ne amma tayi kyau, ta dinga hararar su suna mata dariya dan ita har ga Allah bata son duk abinda ya shafi kwalliya irin wannan ita dai barta da yar powder da kwalli sai lipstick shikenan.
   Abbati ne yazo daukar su a motar Abba duk da ba wani nisa bane duk cikin layi daya ne amma ita kunyar fita take a haka shiyasa kawai ta kirashi yazo ya dauke ta da kawarta daya su kuma sauran suka yi gaba wajen kamun suka jira a wajen dan su shiga da ita.
   Wajen ya cika sosai, an tsara komai yadda ya kamata, Hajiya Mama da Jama’arta suna bangare daya sun sha kwalliya, su Nadeeya ma sun iso sun sha kwalliya sun yi kyau sosai, kallo daya zaka musu kaga banbancin wayewa fiye da mutane da yawa a wajen, idon su a bude yake sosai sai suka zama daban a wajen.
  Amarya na zuwa aka soma abinda ya tara mutane a wajen, nan fa su Hajiya Mama da mukarrabanta suka bud’e bakin aljihu suka dinga zazzaga kudi, baka jin komai sai sunan su da MC ke ambata saboda ya ga ruwan kudi, ita kanta Ummaa uwar bikin gefe ta koma ta zubawa sarautar Allah ido, sun kankane komai hatta wajen Amaryar su Nadeeya ne suna ta aikin daukar hoto, sauki daya da umma take hangowa Asma’un shine ta wajen su Nadeeya din da Hajiya Maman, kamar suna son ta, kamar zata samu sauki a wajen su, ko dan alaka me karfi da take tsakanin su, sai dai kash!

   Wajen takwas aka gama, shima da an daka ta tasu ba za’a tashi ba, basu shiga gidan Abban ba, suka hau motocin su suka tafi. Sauri take ta isa daki ta cire kayan dake jikinta dan ba karamin takura mata sukayi ba, tana zuwa dakin su taga mutane ne tsofaffi a cike duk sun kwakkwanta,juyawa tayi zuwa dakin su Abbati, tasan babu kowa kuma basu dawo ba, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya ta hau kokarin zuge zip din rigar da ta kamata sosai dan ma ta saka wadataccen mayafi amma da babu abinda zai sakata, jin hannu tayi a gadon bayanta, ta juyo a razane suka yi ido biyu dashi, ta daddage zata kwalla kara ya rufe mata bakin da karfin sa. Kici-kicin fuzge kanta take ya saka dayan hannu ya rike mata kan sosai, sai kawai ta fashe da kuka me cin rai. Sakin ta yayi da sauri yana mata wani irin kallo. Da sauri ta juya ta fice daga dakin jikin ta sai rawa yake kamar mazari, dakin Umma ta shiga ta wuce da sauri wardrobe din Umman ta dauki hijab ta saka sannan ta fito da sauri, a tsakar gida sukayi kicibis da Abbaty,ya tare ta da sauri

“Dama ke nake nema, Adam yana dakin mu tun dazu yana jiranki.”

” Dan Allah kace ya tafi, ni ba zan iya zuwa ba.”

Zaro ido yayi

” Abba ne fa yace na zo na gaya miki, babu ruwana wallahi.”

“Abba!? Ya dawo ne?”

” Tun dazu ai yana nan, shima Adam din tun kuna wajen kamun yazo Abba yace ya jira shine yayi magana aka tashi ai daga kamun. “

Wani abu ne ya tokare mata a wuya, bata masa magana ba kawai ta bi hanyar dakin nasu, ta tura ta shiga, yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin. Gefe ta samu ta makale ya matso yana kallon hannun ta da kafarta da akayi mata lalle.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button