RAYUWAR MACE 5
“Ina kayan da na bawa Abbati ya kawo miki?”
Shiru tayi, ya sake maimaitawa bata amsa ba, sai da ya daka mata tsawa me karfi sannan tace a kidime.
“Suna wajen Hidaya.”
“Ok.” Yace yana matsowa daf da ita, ya daga ta gami da fizge mayafin da tayi lullubi dashi, ya rage daga ita sai tsuran kayan jikinta, riga ce fitted da skirt da yayi daidai da jikinta, bin ta ya dinga yi da wani shu’umin kallo, ya lashe lips dinsa na k’asa yana kallon saman kirjinta, hannu ta sa da nufin karewa ya sa karfi ya murde hannun har sai da tayi kara.
“Baki isa ki hanani abinda na saka kudi na siya ba, karki sake idan ba haka ba, zaki fuskanci hukunci me tsananin.”
Yawo maganar ta shiga yi mata akai, siya? Kenan ba auren ta yayi ba ma, siyan ta yayi, da lefen kenan ya siye ta ko da sadaki? Bata gama tunani ba sai jin hannun mutum tayi a jikinta, ta firgice tana kokarin guduwa, hannu daya ya saka ya matse ta kam, ya shiga taba ta duk in da yaga dama, kuka take sosai ta rasa yadda zatayi dan ya hana mata ko da kwakkwaran motsi ne, sai da ya ga dama dan kansa, sannan ya ture ta da karfi tayi baya saura kad’an ta fadi Allah ya taimaka ta tsaya a kafarta, be ko kalleta ba ya juya ya fice yana maida numfashi, ba zai iya resisting ba idan ya tsaya, komai zai iya faruwa.
Durkushewa tayi a wajen ta saki kuka me cin rai, bata taba ganin aure irin nata ba, duk wata amarya a wannan ranar tana cikin farin ciki mara misaltuwa saboda auren wanda take so yake son ta. Sai dai ita akasin haka ne a gareta, babu digon soyayyar ta a tattare da adam, tun tana yarinya Adam be tana kaunar ta ba, be taba tausayin ta ba, illa ma duk sanda suka hadu ko a gida ko a wani waje sai yayi dwewrieiririwroieoei e pie I i a little more Ta yaya zata iya? Me yasa babu wanda yake hango mata abinda take hangowa a gaba, me yasa? Ko kuma dai suna hango matan kawai babu yadda zasu yi ne, musamman Umma da tafi kowa saninta, ita ya kamata tafi kowa tausaya mata, amma sai taga kamar itama bata damu ba. Cigaba da zama tayi a dakin har sai da yamma tayi likis, sai da Abbati yazo sannan aka san tana dakin, dan har hankali ya fara tashi abna tunanin in da taje, idonta ya yi luhu luhu saboda tsabagen kuka, haka dai aka babbata baki sannan ta wuce dakin Abba, kasancewar daga wajen dinner din za’a wuce da ita ba zata dawo ba, nasiha sosai yayi mata wadda ta sake kashe mata jiki, ta kara volume din kukan ta dan kukan ne kadai yake rage mata radadin da take ji a ranta. Shi kansa Abban duk dauriyar da yake sai da yaji ya karaya, hawayen da ita suka tsaya masa a rai, ya nemi dan guntun farin cikin da yayi saura ya rasa, ya dinga ganin baiken sa, da ya barta zuwa lokacin ta, da be yi gaggawa ba. Shi da kansa ya dinga bata hakuri, tayi shiru tana sauraren sa cikin yanayin karaya, umma kuwa kasa cewa komai tayi, har Ya Hadiza ta shigo ta taimaka mata zuwa dakin ta, sannan ta sakata shiryawa saboda dinner din, bata musa ba, dan musun bashi da amfani tunda aikin gama ya riga ya gama, sai dai tana wanka tana kuka sosai, hakan ya jawo mata dadewa sosai a ciki, sai da Rauda ta kwankwasa mata sannan ta fito, suka taimaka mata ta shirya a cikin gown din da ya kawo, gown din da bata da maraba da ta arna sai dogon hannun net da ke jiki, mayafi fari ta dora akai da ya rufe mata duk wajen da yake a bude a rigar, kirjinta da sangalalin hannun ta, takalmin ne dai ba zata iya sak’awa ba saboda ya mata tsayi da yawa, bata ma iya tafiya dashi ba.
Duk abubuwan bukatuwar ta sun yi gaba kafin ta iso, hatta kayan sawarta da komai rankatataf an kai mata su, yadda ana gamawa zasu wuce chan gidan, dama duk wanda suke da bukatar ganin gidan Amarya sun gani tuni, shiyasa kawai aka yanke shawarar musamman ganin dare zai yi kuma shi kansa Adam din ya fadawa Mama yau yake so a kawota, har su Nadeeya na tsokanar da yayi rashin kunya, yayi kuwa mirsisi yana jin su yayi gaba abin sa. Ita kuwa Mama farin cikin da take ciki ba zai fadu ba, ta hasaso shiryuwar danta, tunda duk alamun sa sun nuna yana son Asma’un, a kalla zatayi galaba a kansa a wasu abubuwan da yawa.
Tuni wajen ya cika da jama’ar Adam da kawayen Mama sai su Nadeeya kowa da jama’ar ta, sai bangaren su Asma’un suka tashi yan kad’an, duk suka koma suka darare dan babu ma wanda ya nuna jin dadin ganin su, dama basu da yawa dududu su goma ne kawai, sai Asma’un da Rauda da Hidaya, sai kawarta guda daya, zuwan su ne ma wajen ya saka su Nadeeya nuna sun gansu, aka raka amarya wajenta duk kunya ta isheta, kamar ta tsaga kasa ta shige dan ita ire-iren abubuwan nan tun da ma ba zuwa take ba. Tana zama suna isowa cikin zugar su guda, sun sa suit bakake sai uban gayyar da ya saka fara tayi masifar karbar sa kasancewar shi fari sosai. Nan da nan wajen ya kachame. Baka jin komai sai tashin kida me masifar kara da ya saka haifar mata da matsanancin ciwon kai. Zama yayi a gefenta, daf da ita har tana jin jikinsa a gefen nata, kafarta ya take mata bayan ya zauna, ta kalle shi da sauri ya watsa mata harara, tayi saurin tun k’asa da kanta. Tana jin shi ya lalubo hannun ta, ya matse shi sosai har sai da tayi kwalla, ya sakar mata murmushi yana matsowa daf da ita kamar zai fad’a mata wani abu, ta runtse idon ta da sauri, tana jin sanda ya furta.
“Kinyi kyau matar Adam!” Ya saki murmushin gefen nan, wanda shi kadai yasan manufarsa sai ita da take hasashe!
Rayuwar Mace labari ne daya tamkar da dubu, akwai kalubale a rayuwar asma’u, a rayuwar da yawa yawan mata! Amma sai dai me?
Me zai faru? Wanne irin zama ne zai kasance tsakanin ta da shi? Mata da yawa suna zaune da mazaje masu halin Adam ko fiye, amma kullum magana daya ce, muyi hakuri!
Akwai haske tattare da RAYUWAR ta a gaba, hasken da zai yaye mata dukkan damuwar ta!
Soyayya me tsafta, soyayya me tsayawa a kalbi! Ku biyo zafafa biyar dan ganin yadda zata kasance a RAYUWAR Mace! Rayuwar Asma’u