NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 6

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*

   *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_

                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[6……]_*



    
…………..Da k’yar ya iya tashi da asubar farko, dan kansa ciwo yake masa, bayi yashiga ya d’aura alwala kafin ya fito ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya ruwan madara, yad’an fesa turare sannan ya fice.
          Tunda ya dawo shike kiran sallar farko a masallacin, yauma kamar kullum zazzak’ar muryarsa mai cikeda sanyi ta karad’e anguwar. Koda ya kammala kiran salla ba zama yayiba, saida ya gabatar da nafila raka’a biyu kafin yay zaman karanta littafi mai tsarki. Ahankali mutane d’ai-d’ai suka fara fitowa, ciki harda malam.

          Bayan an idar da sallar Asubahi Aliyu bai fitaba, zaman yin azkar na safe yay, saida ya kammala sannan yafito a massalacin. Shiga yay suka gaisa da Malam.
     Kallo d’aya malam yayi masa ya karanci damuwa mai tsanani a fuskar d’an nasa, har zai mik’e ya tsaidashi ta hanyar kiran sunansa,
     “Aliyu!”.
 “Na’am baba” ya amsa yana waiwayowa ga malam.
        “Dawo ka zauna”.
 Bai musaba ya dawo ya sake zama kansa a k’asa.
       “Mike faruwane? ko bakada lafiya?”. Malam ya tambayeshi cikeda kulawa.
        Ajiyar zuciya M. Aliyu ya sauke, cikin sark’ewar murya yace, “Lafiyata k’yalau baba, kawai dai wani abune da ban ya girgiza dukkan kuzarina”. Shiru yad’anyi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya, yayinda malam ya kafeshi da Ido 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button