WA ZAI FURTA 2

???? WA ZAI FURTA??????
0⃣2⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( maman Ibrahim) Allah ya shirya Miki zuri’a ya Kara arziki*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD KO DA YAUSHE*
*DOMIN KU AUREN FARI FANS ANA MUGUN TARE*
*Federal University dutsinma*
Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Bilkisu bata Sami sakewa ba, karatun Yana mata mugun wahala, ahankali take bin su chinyere suna nuna mata abubuwa duk Wanda ta fahimci Yana da kokari zataje don Kara fahimtar abinda ya shige mata.
Su Anwar sune Yan baya ga komai, ya biye wa mashiririta yaki nuna ma kowa Shi din Mai kokari ne, masu karyar suna da kokari sai ya kwantar da kanshi Yana Jin yanda suke kwabar bayani musamman idan akazo gun lissafi.
Hankalin sa a kwance duk C.A din da akayi shine overall, Yana amsa sunan Anwar a zahiri ba Wanda yasan Shi da Hamza Yusuf a badini.
Fahimtar halin Bilkisu na rashin girman Kai yasa Shi suke gaisawa da ita sama-sama Yana son kulla mu’amula da ita Amma Yana ganin hakan a gareshi zai zubda mishi aji. Ita kuwa a gareta Sam bai ma gabanta ko kadan idan an hadu a gaisa idan ba a hadu ba Bata ko tunanin sa. Shine ma sau da yawa take Dan takura tunanin sa kadan kadan.
Ta Dan Fara sakewa da su chinyere saboda ta lura sune masu kokarin ajin, takan zauna tayi tunanin akwai department din da yakai Economics barin wuta duk makarantar? Sau da yawa tana tunanin Anya ba hausa ko Islamic zata koma ba?
Ta gama tsorata da makarantar musamman yanda taji ana bada carry over, probation da Kuma withdraw. Takan yi tunanin ai ita abun kunya ne gareta ta sami Koda carry over din ne ma hakan yasa ta Kara dagewa tana Kara naci cikin karatun ta musamman da jarabawa ta karato kullum tana library ko Kuma tare da su chinyere tana Kara koyon karatu.
Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class tana faman karatu yazo wucewa kunnensa like da air piece har ya gitta said yaga kamar ita, yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko gizo idanun sa keyi Masa kamar kullum?
Kamar kada ya dawo sai Kuma dai ya koma don tabbatarwa …..ita din daice tana ta faman Mimi da baki ya kyalkyace da dariya lokacin daya kunna Kai ajin hankalinta naga littafi har yazo ya zauna kusa da ita….tayi firgigi cike da tsoro ko da taga shine bata San lokacin da ta balla mishi harara ba…..yayi murmushi afuwan matsoraciya duk wadannan mutanen meye zai kamaki da rana gatse gatse haka? Ya karasa maganar Yana janyo littafin ta gaban sa, meye kike karantawa ayi mun bayani.
Haushi ya turnuketa domin karatun ya Fara shigar ta sosai gashi yazo zai rikita ta, Tasha mur tare da janyo littafin Dan Allah karatu nake zaka rikitani ka tashi ka bani wuri…..bazaki koya mun ba?
Nima Yanzu ai nake karantawa ta fada cikin fada fada, yayi murmushi it’s alright go ahead and read ya sunkuyar dakai kawai bisa desk din. Ta ci gaba da karatun ta ba tare da ta Kara bi ta kansa ba.
Idan ta karanta sai that bude can karshen littafin ta rubuta haka haka Yana ta lura da ita duk ta dage bakin Rai bakin fama Nan da nan ya gane hadda ce takeyi. Yana so ya mata bayani Amma ya rasa ta inda zai Fara……
Tana son kamshin turaren sa ainun Anwar Dan gayu ne matuka Yana daukar wanka gashi kyakkyawa. Kamar ta karanci zuciyar say ta Dan karkato Dan Alalh wannan kalmar me take nufi? Ta sungo mishi littafin a gaban sa. Daman tun zaman sa kusa da ita ya kashe music din hakanan wayar ke jikin kunnen sa………yayi kamar baiji me tace ba har sai da ta kalleshi sannan ya Dan zare wayar daga kunne Shi ala dole baiji me tace ba ya dan kalleta Shima kina magana ne?
Cewa nayi me wannan kalmar ke nufi? Ta nuna mishi da yatsa ….yabi hannun nata da kallo Yana kallon Zara zaran yatsun ta ya ce bari muji sentence din, Ya fada mata ma’anar kafin yace kin gane course din nan ne? Ta Dan bata rai to gashi dai Ina karantawa…… Ya Kara janyo littafin gaban sa ya budo shafin farko…… Kin San fa abun duk labari ne Kinga…….ya Fara mata bayani a hankali ahankali Nan da nan ta Fara fahimta sosai saboda bayanin nasa duk da hausa yake mata. Haka haka har ya gama mata littafin. Taji dadi sosai da sosai ta fadada fara’ar ta ohhhhh Ashe ka Gama covering komai ko???…….a’a fa nima kawai na gane darasin ne lokacin da yake bayani a class…..Amma wallahi ka iya bayani saboda har kafi malamin ma iyawa….ya danyi dariya tinda na Miki bayani da hausa ko? Ta kyalkyace da dariya yabi fuskar ta ta Yana Kara kallo ta bude jakar ta to Dan Allah ka gane wannan math din? Ta fiddo littafin. Dariya kawai yake cikin Rai Amma a zahiri yadan basar…….ya kalli littafin, gaskiya ban iya Shi ba Amma ki bari yau sanje dakin wani dan aji hudu ya koya mun gobe sai mu hadu in nuna Miki……da karfe nawa? Ta katse shi, Yayi murmushi duk lokacin da kike so goben……. 8:00am Zan jiraka anan.
Ya zaro ido 8? Gaskiya sai dai 4 saboda barci bazai barni na fito da wuri ba.
Kamar zatayi magana sai Kuma ta fasa ta ce Allah ya kaimu lafiya tare da janye littafin yabi Dan karamin bakin ta da kallo har ta sunkuya.
Ta Mike tana kokarin sagala jaka ta kalleshi tana murmushi Dan Allah ka koya da kyau Zan jiraka anan din goben in shaa Allah.
Yace ba damuwa…..see you then. Ta wuce.
Yabi ta da kallo kamar ya rufa mata baya amma Shi kansa yasan bazai iya hakan ba ( saboda gadara ).
Zuciyarta Fara fes! Ta isa daki taji dadin bayanin Anwar matuka.
Washe gari tana fitowa masallaci ta wuce class din kamar yanda sukayi alkawari, ta fiddo wani course theory ta Fara karantawa kafin ya iso. Ta nayi tana Dan kallon taga tare da duba agogon wayarta har kusan hudu da arba’in.
*Anwar* kuwa Yana can Yana shakar barci abinsa sammm ya manta da maganar su.
Allah ya taimaketa kawai sai ga su chinyere sun shigo karatu Suma Kuma cikin sa’a statistics din zasuyi solving sai kawai tayi joining suka Fara.
Tana yi tana tunanin watakila Anwar bai iya bane Yana Jin kunyar zuwa….ta tabe baki to meye na karyar zaije ya koya bayan yasan bashi da wani kokari….mtsew taja guntun tsoki.
Bai farka ba sai shidda saura ya tashi a hargitse ga takaicin lokacin sallah ya shige ga Kuma tunanin sabawa Bilkisu alkawari da yayi.
A gurguje ya watsa ruwa yayi sallah ya fito da sauri.
Ya shawo kwana ita Kuma ta fito ajin zata tafi. Tana hango Shi tayi sauri bi ta dayan side din tabayan azuzuwa tayi hanyar fita gate sauri sauri…..tana tunanin watakila Yana can Yana faman koyo don yazo ya birgeta..tayi tsoki to karya tame ne?
A hargitse ya shiga ajin sai wurge wurgen ido yakeyi girman Kai da nuna Isa sun Hana ya tambayi su chinyere ko sun ganta. Rai bace ya fita Nan ya Fara bin azuzuwa neman ta.
Helen ta tabe baki I don’t like this Anwar honestly…. Mtsew don’t mind idiot abeg inji chinyere Nan gulma ta tashi.
Ya cika girman Kai da nuna Shi wani ne, baya yi ma kowa magana sai abokansa uku. Surutai kala kala saboda Shi din Daman baida farin jini a class din tun zuwansu Wai ya cika fadin Rai da gadara.
Tunda ga ranar bai Kara Sanya Bilkisu a ido ba yayi neman har ya gaji gashi baida no. Ta bai Kuma San Wanda zai tambaya ya bashi ba haka Kuma baisan accommodation dinta ba hostel take ko off campus. Wasa wasa abun ya Dan dameshi.
Ranar da zasu Fara jarabawa da yake ta karfe uku ce tun biyu saura yake hall din Yana so ya ganta, ita kuwa tun 8 tana library sai biyu da Rabi ta fito bayan tayo sallah. Kansa sunkuye baiga shigowar taba har ta zauna bayansa.
Lallai Anwar ka kyauta shine ka shanya ni rannan ko? To kayi dai dai ta fada tana faman hararar sa .
Da sauri ya dago Kai zaiyi magana kenan invigilators suka shigo tare da fadin everybody out..ta rigashi fita, ko da aka Fara shiga ma tayi saurin fadawa don Zama gaba gaba.
Alhamdulillah jarabawar ta mata dadi ainun domin duk abinda ta karanta suka fito.
Ita ce ta biyar din bayarwa ( submitting ) bata jira kowa ba tayi masallaci don gabatar da la’asar saboda lokacin biyar da kusan ashirin.
G
Haka semester din ta kare ba tare da sun Kara haduwa da Anwar ba, ko kadan Bata yarda su hadu tasan karya zai shirga mata don kare kansa.
Shi Dan garin Kano ne ita Kuma Abuja mahaifinta ke aiki Amma asalin su Yan katsina ne.
Washegarin da suka Gama jarabawa tabar garin Anwar kuwa karfe biyar na ranar yabar dutsinma.
Hutun baida tsawo sati biyu akayi aka dawo. Sun dawo da sati daya aka saki result a *portal* Murna tsalle ga Bilkisu saboda ta cinye ko wane Bata da carry over ko daya ga point dinta 4.33
Hakan ba karamin dadi yayiwa Yan gidan su da iyayenta ba.
Anwar kuwa 5:00 dai dai ya samu saboda duka courses din da sukayi goma Sha daya ko wane *A* yaci. Yaja bakin sa ya tsuke.
A cikin ajin kowa nata fadin result din sa daga Mai 4 point sai masu 3 point da abubuwa. Duk Wanda ya tambayi Bilkisu sai ta ce lafiya Lau ne ni Daman carry over ke bani so to ban samu ba. Bata yarda ta fada ma kowa result dinta ba. Tana zaune an gama lecture din wani mugun malami ta kura ma dan rubutun da tayi ido tana nazarin ya zata ci jarabawa da Dan wannan rubutun? Suleiman ya mata sallama.
Suleiman matashi ne Shima a cikin ajin Mai natsuwa da son addini babancin say da Anwar yafi Anwar saukin Kai da yarinta. Ya zauna kusa da ita bayan ta amsa sallamar Dan Allah Hajiya Bilkisu na kasa bude portal dina ya akeyi ne?
Tayi murmushi Ina wayar taka in nuna maka?
Wallahi daki na barta ki nuna mun da taki…….hankalin Anwar na kansu haka kawai sai yaji ya tsani Suleiman karon farko a rayuwar sa.
Ta fiddo wayar tare da tambayar sa password da matric number.
Portal din na budewa ta Mika mishi wayar kaga inda zaka Danna….. Ya danyi dariya to bude Mana ai ba komai don kin gani. Ta kalleshi tana mamaki saboda tasan Portal sirrin dalibi ne ba kowa kake yarda ka nuna mawa ba. Ya Kara Yar dariya ki bude ba komi. Ki gane mun Ina da carry over?
Ta ce to a sanyaye tana mamakin irin warda da yayi mata farat daya zuciyar ta cike da Jin dadi tare da ganin kimar say da mutunci.
Kaiiii….ta fada tare da zaro ido ka Fadi accounting. Sai kawai yayi murmushi nasan za’a rina sai wane? Ka Fadi GST English Shikenan. Nawa ne point dina? Ta duba can kasa tana warware ido….. Okay gashi Nan 2.65. Ta kalleshi, amma Suleiman me yasa ka yarda dani haka?……Au kin San sunana kenan? Ya fada Yana kallonta cike da mamaki, tayi murmushi eh Mana nasan sunan ka Suleiman.
Ina fatan ke dai lafiya lau ko? Sai kawai ta budo mishi portal din ta tace kaga nawa.
Ya zaro ido kaiiiiiii…… Ta danyi murmushi Amma bana son Dan Allah ka fadawa kowa result dina.
Ya Jin jina Kai in shaa Allah Zaki sameni Mai rike sirrin ki, amma Bilkisu kinyi wuta da yawa fa!
Ta yi Yar dariya kawai.
Allah yasa albarka. Kiban no. Ki dan Allah ko da wani Abu Yana tasowa Kuma idan bazaki damu ba Zan ringa matsowa kina tasar Dani inda ban ganewa.
Ba matsala ga number rubuta……..
A harzuke Anwar yabar class din tunda ga ranar sai kawai yayi baya da ita ko gaisuwa baya son suyi cikin kankanin lokaci ta Saba da Suleiman ta fahimci Yana da saukin Kai bashi da girman Kai sannan Yana da addini tare da daratta mutane.
Ko da ya gane Bilkisu nada kokari sai ya like mata ko C.A zasuyi Yana manne kusa da ita baya yarda tayi mishi nisa.
Ko kadan Bata da mugunta duk amsar da ta kakare mishi zata bashi ya kwashe tsaf!.
Akwai wani course Mai matukar wahala gashi three credit unit ne Kuma calculation Mai rikitarwa kowa Yana Jin course din. Anwar yayi burus da ita Yana Jin kowa na kokawa Amma ya ki nuna ya iya. Kwana takeyi karatu da salloli, Ranar jarabawar course din ana ta jera layi kawai malamin yace ta zauna can, hankalin ta ya tashi ganin ya cillata gaba don yau baya take son Zama saboda ta Sami taimakon wani.
Tana Zama sai taga Anwar ne a gaban ta, ita dai kawai sai addu’a takeyi tasan yau sai Allah da malaman gari. Tambayoyi bakwai be a amsa biyar tambaya ta farko dole ce gata da ‘ya’ya har goma.
Saura kadan ta kurma ihu saboda duka tambayoyin guda daya ne kawai ta sani itama theory ne ba calculation ba.
Idanun ta suka kawo ruwa, taga tunda Anwar ya duke bai dago ba, hall din yayi tsit! Ta yi zugummm, zuwa can kawai ta Fara amsa wacce ta sani.
Mafi yawancin malaman dake tsaron nasu duk sun maida hankali wurin Yan baya. Haka ta dunga rubutu Dan Allah yasa ta Sami Koda *E* ne a course din ta wuce wurin.
Tana gamawa tayi zugummm kawai tana fargaba.
Yadan waigo kadan ganin malaman basa kusa yace kin iya question one naga tana da wahala fa.
Tayi kasa da murya wallahi question 4 kadai na iya cikin bakwai din nan ga Shi ta farkon naga 30marks ne.
Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa.
Habaaaaa…..ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart. Duba daya sai ta kwaso layi biyu. Cikin sauri ta gama shafin tace juya….Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi shirme. Wallahi na gama ka juya kawai.
Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba.
Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi.
Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi.
Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido.
Kije kiyi submitting…ya fada kasa kasa ta ce toh.
Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa. Suleiman kawai take jira ya fito sai kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu….. Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran.
Tabbb….wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba….hada question one?
Eh Mana.
Wai da gaske kike?
Wallahi kuwa.
To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane ba…….Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar *Gate* Yana ta faman sauri.
Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu.
Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya.
Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku. Na gode na gode Allah ya Kara ilimi……Daman ka iya course din sosai haka? Naga yanda ake ta kuka dashi Kai komai ka amsa…..hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ).
Murmushi kawai yayi yace ba damuwa.
Ya wuce kawai. Ta bishi da ido. Anwar…ta Kara kwada mishi Kira…..ya juyo wallahi na gode kaji?
Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa.
Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan semester din.
Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry over daya.
Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first class da over all.
Bata halarci wurin ba. Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba. Hakan yasa Anwar zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama.
Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin su ko wani Wanda ya sanshi. Ashe Suleiman yana wurin.
Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu……………..
*************
*KADUNA RIGASA*
Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba.
Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar kullum ta shigo tana ta faman Bata rai .
Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye……Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad ( Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi Yana ci.
Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam.
Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal….
Kamar Yaya?, Ya bukata.
Kamar yanda kaji.
Kamar yanda naji?
Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa duka wurin ta…..me ke faruwa ne ummi?
Tayi shiru!
Dake nake magana…me ya faru?
Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa Aunty Amira ta koma……. Ke ya daka mata tsawa.
Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini?
Gabanta ya fadi tayi tsuru tsuru, kinji? Munyi dake Ina Miki gini?
Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa? Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba.
Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra’ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to wallahi zakiji ba dadi.
Mtsew ya buga tsaki ya wuce…….ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba.
Kwallah suka zubo Mata. Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta …..salati ta kamayi ubanwa ya aike ki? Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi.
Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe.
Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba. Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai.
Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi’a ba Dan komai ba kada ma akirkiri partyn Amira taji ba dadi.
Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota.
Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa. Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi sanarwa.
Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai…………
Ko ajikin sa. Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna.
Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba. Nan suka Kara hure Mata kunnen wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci.
Kuka takeyi wuiwui.
Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi.
Ana gama sallar isha’i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba…….
*Ayi hakuri da typing error please yanayin typing din ne saboda kawai ta WhatsApp nake yi Kuma gaskiya bana bi idan na Gama kawai nake turawa.
*Daga zainab wowo*????????????????✍???????? WA ZAI FURTA??????

*Daga zainab wowo*????????????????✍????