SALON SO COMPLETE NOVEL

SALON SO COMPLETE NOVEL

SALON SO!
NA:
HADEEZA SALISU SHAREEF
POSTED BY:
SULAIMAN BOMBOY.
.
PART 1 TO 6
.
Kyakkyawar yarinya ce ‘yar kimanin shekara goma sha bakwai, direbanta ya yi parking da mota ya zagayo ya bude mata ta fito ta shiga cikin wani hadadden gida kerarre, ke da kallon tsarin ginin kin san hoto ne daga kasar waje aka yi irin sa. A kofar falon ta yi sallama ta shiga. Matar da take hakimce akan kujera cikin tsantsararriyar kwalliya ta kece raini, tana ta girgiza kafa da wayar sadarwa a hannunta da take hira. Tana ganin shigowar yarinyar ta dire wayar cikin fara’a ta tare ta, tare da cewa, “A’a Jawahir ‘yar Dady yau a gari? Ko dai batan kai kika yi ne?” Jawahir ta yi murmushi yayin da ta durkusa gabanta ta ce, “Aunty ina yini?” “Lafiya lau Jawahir, amma dai a nan za ki kwanar min ko.? Tun da gobe ba ku da makaranta.” Jawahir ta yi dariya tare da cewa, Tafiya zan yi Aunty yau Dady zai dawo daga saudiya, da kuma ya dira a kasar nan ni zai fara tambaya, kuma ni ma ba zan so ya dawo ba mu hadu ba. Aunty ta yi murmushi ta ce Jawahir gidan Daddy ke dai kullum kina like a gida kamar daddawar daka ba kya son zuwa ko ina ko?” Amma zan je na samu mommy dinki na ji ko ita take hana ki zuwa.” Jawahir ta yi murmushi, “Wallahi Aunty babu rawan mommy Daddy na ne baya son na rinka fita. Sallamar da ta ji ce ta sa ta yin shiru, sai da aka amsa masa sannan ya shigo. Ya zauna a kan kafet tare da rissinawa ya gaisar da Aunty. Aunty ta amsa cikin kulawa ta musamman ta kalle shi ta ce, Ba dai har ka dawo daga office din ba?” “Wallahi Aunty vacci nake ji shi ya sa na taho gida don na kwanta na huta.” Aunty ta girgiza kai tare da cewar, “Ba ka kula da bakuwa ba ne?” Sai sannan ya kalle ta ya ce, “Wallahi ai kamar jawahir ko.?” Au ka mance ma? To ita ce, Jawahir ta dan rissina ta ce, “Yaya Haidar ina wuni?” Ya amsa cikin kulawa sannan ya ce, “Ya su Dady?” “Daddy ba ya kasar, yau dai muke sa ran dawowarsa.” “To Allah ya dawo da shi lafiya, Abin da Haidar ya ce kenan ya mike ya nufi sashensa. Jawahir ta mike Aunty zan tafi” “Haba jawahir har tafiya zaki yi.?” “Wallahi Aunty tafiya zan yi doki nake yi ne na je na fara shirin tafiya taryar Daddy. “To ‘yar Daddy ki gaishe min da shi, kafin na zo gobe yi masa sannu da zuwa. “Ta fito da sauri, direbanta ya karbi kayan da yake hannunta ya zuba a but ya bude motar ya shiga ya tayar suka miki hanyar gida +++++++++++++++++++++ Alhaji Ibrahim shine mahaifin Jawahir, mutumin kirki ne, akwai shi da son jama’a ga yawan kyautatawa na kasa da shi, sam ba shi da kyamar talaka. Yana da dadin zama idan ka kiyaye abubuwan da ba ya so, na farko ba ya son raini, kuma shi kaifi daya ne, in dai ya ce, “I, ko “A’a” to ba wanda ya isa ya tankwara shi sai uwarsa. Su uku ne a wajen iyayensu, shi ne babba sai Aisha wato Aunty babar Haidar sai Aminu, wanda shi ne autansu. Ubansu da suke kira da Baffa ya dade da rasuwa sai mahaifiyarsu Rahmatu da suke kiranta da Inna. Inna mace ce mai kirki da hakuri ga ta da son zumunci, duk inda aka ce ga dan uwa ko ta yaya suka hadu ta jawo shi a jiki ita bare ma jawo shi take yi don ya zo ya ci arzikinta. Tana zaune a unguwar sabon tatin mandawari. Tana matukar son jawahir don a cikin jikokinta babu wanda ya kama kafar son da Inna take yi wa jawahir. Alhaji ibrahim matarsa daya Hajiya Hafsatu, ita ce mahaifiyarsu Jawahir, suna ce mata Mommy. Mommy tana da ‘ya’ya shida biyar maza daya mace. Akwai Abba me sunan kakansu sai Abdullahi, sai Nasir, sai Jawahir da Auwal da Sani. Jawahir ita ka dai ce mace a gidan, kowa ji yake da ita ba ma kamar Alhaji ibrahim da yayyanta. Suna son ta suna shagwabata amma duk da haka ba ta sangarce ba don tana tsoronsu tana kuma jin maganarsu. Jawahir yarinya ce kyakkyawa tana da hankali da nutsuwa akwai ta da biyayya ba ta da rowa. Sai dai miskila ce ba kowa take iya sakewa da shi ba, ba ta fiya son magana sosao ba, in kinji hirarta ce ne da Daddynta ne ko yayyanta sai mommynta, to shi ne za ki ji har da dariya. Amma shagwababbiya ce ta kin karawa don ita har kannanta Auwal da Sani shagwaba take yi musu bare kuma su Yaya Abba da uwa uba Daddynta. Bayan Auwal ne ya dauke min babban turarena da ya fi kowanne tsada. Shi ne kike kuka? Rabu da shi zai gamu da ni ne je ki cikin dakina kan mudubi ki zabi wanda kike so share hawayenki ki yi dariya. Ta fada dakin Dady da gudu tana murmushi yaya Abba ya ce, Su jawahir sarkin rigima. Shi kuwa Haidar a zuciyarsa cewa ya yi, Kai wannan yarinyar tafi ya shagaba shi ya sa take ba ni haushi sai na ga kamar na doke ta in ana lallabata. Yarinya sai shagwabar tsiya sai ka ce ita ce Auta.” Tunaninsa ya katse ne a dai dai lokacin da jawahir ta fito daga dakin, hannunta rike da sunkumemen turare. Ta nunawa Dady ta ce, Dady ga shi na dauka. Yace, “To ‘yar Dady ya yi miki wannan din?” Ta daga kai, “To maza ki je ki boye abunki ki ta fesawa. Ta durkusa fuskarta cike da murmushi ta ce,Na gode Dad Allah ya kara girma, Ya shafa kanta yana murmushi ta yi waje a guje. Takaici ya cika Haidar a zuciyarsa ya ce, Ya za a yi ma wannan ‘yar yarinyar a ba ta wannan turaren? Ya za ta yi da shi? don kudinsa wajen dubu goma sha biyar ne,to ita ta san darajar kamshin ne ma. Yanzu haka wasanta za ta yi da shi kawai. Yaya Abba ya girgiza shi tare da fadin, Haidar me kake tunani ne? ko ka tuno America ne? da yake tare suka yi karatu a can shi da Haidar din. Dariya suka yi suka tafa. Kiran sallar da aka yi ne ya sa su tashi don zuwa su ba da farali. To irin wannan halayyar ta Haidar ita ce take bawa jawahir haushi don haka ko gidansu ya zo ba ta kula shi karkari ta ce masa ina wuni ta wuce shi ba tare da ta jira amsarsa ba. Dan mulki kenan. Ita jawahir duk da miskilancinta ba ta da daukan kai kuma akwai ta da yi wa mutum murmushi tana da halin kyauta duk inda ta ga talaka ko kaskantacce in dai ta san mai bukata ne, to za ta gayawa Daddy ya taimaka musu. wannan halayya tata ita take kara sa kaunarta a zuciyar Daddynta. Kamar yau da safe jawahir ta gama baccinta ta fada toilet a yi wanka ta fito ta tsaya gaban mudubi aka shiga kalailayar jiki, a shafe nan a goge can, ta tsara kwalliyarta cikin boyal shudi rigar fitet da zane ta sa hadadden fashion dinta yari da sarka da abin hannu me shudin dutse, Daddynta ne ya siyo mata daga london. Ta hadu iyakar haduwa fuskar tata sai sheki take yi ta feshe jikinta da turaruka ta fito ta nufi sashen Dady. Ta kwankwasa ya yi mata izini ta bude ta shiga. “A’a ‘yar Dady kwalliyar ta yi miki kyau, Ta yi murmushi ta durkusa ta gaishe shi, “Don Allah Dady ina so yau zan je gidan Inna. “Kin sani jawahir ba na so ki rinka yawan fita amma tun da gidan Innata za ki je ba komai sai ki je. To me za kaiwa Innan? Jawahir ta dube shi tana murmushi ta ce, Dady duk abin da ka ba ni. To shi ke nan ‘yar gidan Dady, daman ke ake jira tashi mu je a yi brek. Mominta ta fito daga cikin dakin Dadyn cikin rantsatsiyar kwalliya kamar me shirin zuwa fati. Jawahir ta yi saurin zubewa ta gaishe ta, mommy Daddy ya bar ni zan je gidan Inna Ta ce, “Yauwa koke fa, ai gwanda ki je kusan kullum Inna sai ta yo miki waya ta ce ba ta jin dadi idan ta dau lokaci ba ta ganki ba. Suka fito babban falo suka hau tabir inda ‘yan samarin suke jiransu. Jawahir ta gaida Yayyanta inda ita kuma kannenta suka gaishe ta, al’adar gidan ke nan kowa sai ya gaisar da wanda ya girme shi. Ta kalli Nasir ta ce, “Yaya Nasir za ka kai ni gidan Inna? Ya harare ta, Ni direbanki ne ina amfanin Idi direban da aka ajiye muku?” Yaya Abba ya ce, Wai kai me ya sa kake haka ne? duk yanda direba zai kula da ita ai ba kamar dan uwanta ba ko? Ki bari mu gama break sai na kai ki. Ta ce, “Yauwa Babban Yaya na gode Iyayen dai suna jinsu ba su tanka musu ba. Bayan gama break dinsu jawahir tanufi dakinta ta kara gyara fuskarta ta sako shudin takalmi da shudin mayafi ta fito, Dady za mu tafi,” To me za ki kaiwa Innarki? shiga sito ki jido mata abin da kika ga za ki kai mata Nasir ya ce, Wallahi Dady sito din Inna cike yake da kayan abinci da na masarufi. ka manta shekaranjiya ka ba ni kayan abinci da na amfani mota guda na kai mata? kuma da muke zuba mata a sito din ma akwai wasu a ciki. Abba ya ce, To sai a kai kudi kawai. Momy ta ce, Ki je wajen Rahane me aiki ini ta gama gasa kaji dana sa ta da akwai cake da samosa da na bayar akayi mata, sai soyayyiyar miyar zabi dana yi mata tun jiya. Alhaji ya ce, Wallahi dalilin da ya sa kenan kullum Hafsa nake kara son ki, kike dada shiga rai na don duk hanyar da za ki faranta min kin san ta, ga yanda kike kula da mahaifiyata, ni kuwa me za ki nema a wajena na kasa yi miki. Ta yi murmushi, Ba komai Alhaji Inna ai uwatace, ba abin da ba zan iya yi mata ba, don albarkarsu muke nema. Auwal da sani su ma suka ce, Dady mu ma za mu je gidan Inna. Jawahir ta turo baki, Gaskiya Dady ba za su bi ni ba, damuna za su yi ta yi da hayaniya sun fiya surutu. Dady ya ce, Ku yi hakuri Auwal ma je da ku da daddare, kun ga islamiyya za ku je in karfe biyu ta yi ku kyale ta ta tafi. Yaya Abba da jawahir suka fita suka nufi gidan Inna Yana tsayawa da motar ta fito a guje za ta shiga cikin gidan Abba ya kira ta, Zo ki debi wasu kayan mana. Ta ce, To suka kwashi kayan suka yi ciki. Salamu alaikum ‘yar tsohuwa, kina nan?” “A’a wa nake jin magana kamar bera?” Kai Inna ki ga zankadediyar budurwa ki ce mata bera.?” Inji yaya Abba. Inna ta ce, Ai lallai kuwa ‘Yar dady ta girma don ko yanzu ma a ka yi mata aure ai zama za ta yi. Jawahir ta rufe fuskarta da hannuwanta ta ce, Haba Inna yarinya ta da ni ni da ko saurayin ma ba ni da shi.” Inna ta ce, “A’a ba kya dai kula su ga Hafizu abokin Abba nan duk nacin da yake yi kin ki kula shi.” Jawahir ta ce, Ai ke kuma yanzu kin ga za mu bata. Abba ya duba agogo ya ce, Inna ni zan wuce office. To maigidana sai ka dawo. Yaya Abba ya tafi. Jawahir tana cinyar Inna tana yagar cinyar gasasshiyar kaza suna ta zuba hira. A hankali aka yi sallama a kofar falon aka shigo cikin takama da isa. Jawahir sanin me shigowar ne ya hana ta amsa sallamar bare ta dago kai ta kalle shi. Inna ta kama washe baki, “A’a yau saraki ne a gidan tsohuwa? Lallai kam batan kai aka yi. Yayi kasaitaccen murmushi ya durkusa gaban Inna ya gaisheta, ta ce, Bature ba a ganinka sai an cike form ko? Yayi kasaitaccen murmushi ya ce, Inna sai dai idan ba a so ganin namu ba. Ta ce, Wai yaushe za ka yi aure ne? ko so kake yi ka za ma tuzuru? Ya ce, Inna me kike ci na baka na zuba, kwanan nan zan kawo miki dakakkiyar yarinya ‘yar jami’a me cikakken ilimin boko wayayyiya. Inna ta ce, Ba dai cikakkiya ba sai ka kwaso min kwaila. Ya ce, Haba Inna me za ayi da kwailar mace, duk yarinyar da ba ta je jami’a ba ai ba ta waye ba namijin ya sha wuyar zama da ita, don hauka za ta yi ta yi masa.” Jawahir ta san duk da ita yake wannan habaicin maganar ita kuwa ko kallo be ishe ta ba. Inna ta ce, Jawahir kina kallon Yayanki ba za ki gaishe shi ba.? Jawahir ta yamutsa fuska tare da kau da kai gefe daya ta ce, Ai ban gane shi ba ne, Maganar ta yi masa ciwo amma da yake ba da shi ake maganar ba sai ya yi shiru yana jin su. Inna ta ce, Kin ci gidanku, in.. ban da iya shege yaya za ayi ke da dan uwanki ki ce baki gane shi ba?” Jawahir ta ce, To in ban da abinki Inna ai sai kana yawan ganin mutum za ka san shi ko.? Inna ta ce, Ba na son dogon surutu, ni dai ina horonku da ku rike zumunci, don zumunci ba abin wasa ba ne, don Allah Subhanahu wata’ala ya ce, Duk wanda ya yanke zumunci ba shi ba rahamar Ubabgiji. Jawahir ta ce, Inna ni fa ba yanke zumunci zan yi ba, gane shi ne kawai ban yi ba, to ba sai a yi min bayani ba. Ya mike, “Inna bari na karasa office.” To Haidar ba a abin da za kaci a gidan tsohuwa,. Ya girgiza kai tare da yamutsa fuska, Inna ba zan iya cin komai ba a nan don zuciyata tashi take yi. Ya bawa inna kudi ta yi masa godiya tare da sa masa albarka. Ya yi gaba jawahir ta mike ta ce wa Inna bari na raka shi bakin motarsa. Inna tace, Yauwa ko ke fa, ai gwanda ku rinka karfafa zumunci, don bi so nake kullum na ga kanku a hade. Jawahir ta same shi a harabar gidan yana kokarin bude motarsa ya shiga, Jawahir ta ce, A dai taka a hankali a daina jin kai da wulakanci, don duniyar ba matabbaciya ba ce, wata rana a karkashin kasa za a saka mutum. Ya kalle ta ya yatsuna fuska tare da zuba mata harara ya tofar da yawu gefe daya ya sa hannu ya toshe hanci wai doyi take yi. Ta yi shigewarta ciki ta bar shi a wajen yana kokarin shiga motarsa. A zuciyarsa ya ce, Lallai yarinyar nan ba ta da kunya amma zan yi maganinta ne,. Jawahir sun zana jarabawar fita daga Secondary har sun hada fatin gama secondry. Duk yawancin samarin da suke kawo kansu gare ta ba ta kula kowa sai wani Faruk da jininsu ha hadu daga mutunci suka zarce da soyayya. To suna son junansu don duk yanda jawahir take kin samari da an ce Faruk zai zo kaga rawar kai da girin girinkidishin yin tsararriyar kwalliya ta taron masoyi. Sannu sannu soyayya mai zurfi ta shiga zuciyarsu. ** Aunty tana zaune a falo Abvan Haidar ya fito daga toilet ya zauna kusa da ita ya ce, Kin sani ne, Wallahi tun satin da muka je saukarsu Jawahir zuciyata ta matsu da sha’awar halayyar yarinyar nan. Tana da hankali da nutsuwa ga girmama nagaba da ita. Abin da ya fi bani sha’awa da ita yanda take karatun Alkur’ani a wajen saukar nan tasu, ta iya fitar da harafi ga zakin murya da bawa kowanne baki hakkinsa. Ni yanzu shawarar dana yanke zan je na samu Alhaji ibrahim da ya tallafa ya bawa Haidar auren jawahir. Aunty ta yi ajiyar xuciya ta ce, Wallahi da hakan za ta faru da na fi kowa farin ciki, amma abin da nake tunani Alhaji anya kuwa hakan za ta yiwu ka san halin miskilancin danka kada ya ki a zo zumincinmu yana baci a banza, gaskiya Alhaji ka duba ka gani.” Ya ce, Karki damu Aisha, Allah ya ga niyarmu ta kara donkon zumunci ce a tsakaninmu, insha Allahu ba za su bamu kunya ba. Ta ce, To shi kenan Allah ya taimaka, Ubangiji ya sa a yi a sa’a amin Da magariba Abban Haidar ya nufi gidan amininsa Alhaji ibrahim. Suka karbi junansu da murna da farin ciki. Suna sitting room dinsa. suna yin sallar insha’i a masallacin gidan suka dawo sitting room din suka ci abinci. Daga nan Abban Haidar ya zayyanawa Alhaji ibrahim shawarar da ya yanke na game da hada ‘ya’yansu aure jawahir da Haidar. Alhaji ibrahim ya yi dariya ya ce, Amma na ji dadi. Gaskiya wannan ai shawarace me kyau. Allah ya tabbatar mana da alherinsa, to amin. Allah ya sa ayi da mu.” Ko da Abvan Haidar ya tafi Dady ya shiga gida ya gayawa mommynsu jawahir komai. ita ma addu’ar ta yi tare da sawa abin albarka. Da safe bayan sun kammala break dinsu. Alhaji ibrahim ya kalli jawahir ya ce, To jawahir a yau nake son sheda miki lokacin aurenki fa ya yi, zan aurar dake don cika unarnin Allah subhanahu wata ala. Ta dafe kirji. Dady shekarata goma sha bakwai fa.” Ya ce, To menene, ai kin isa ko ba ki da saurayi ne?” Ta boye fuskarta a cikin hannuwanta ta ce, Daddy akwai Faruk, amma ce masa nayi ya dakata sai na fara zuwa jami’a tukunna na yi masa magana ya fito. Alhaji ta ce, Uhm jawahir ki kyale maganar Faruk ki ba shi hakuri kawai don ni na riga na yi miki miji. Ta dafe kirji cikin kwalalo ido ta ce, Na shiga uku sai kuma kuka don Allah Dady ka yi hakuri ka bar ni na auri Faruk shi zuciyata take so.” Alhaji ya girgiza kai, Kada muyi haka da ke, ki yi hakuri ki bi umarnina ki auri mijin dana zaba miki, insha Allahu ba za ki taba da na sani a rayuwarki ba, kin ji. Ta dafa kanta. Ta amsa da To Dady Allah ya zaba mana mafi alheri, Ta mike ta yi dakin mommy tana kuka. Momy ta ce, Lafiya ke kuma kike kuka? Ke da wa? Me aka yi miki? Mommy ki taimake ni Dady zai yi min auren dole, Ta kwashe komai ta gaya mata. To ke tun dsya ce yayi miki miji to ki hskura da Faruk din mana. Jawahir ta kuma fashewa da kuka, Don Allah momy ki taimaka min ya bar ni na auri Faruk. Momy ta ce, Kin ga kawai hakura ki bi zabin mahaifinki ni ba ruwana ina zaman lafiya ba za ki jawo min tashin hankali ba. Ki bari zan yi nafila da addu’0’i zan miki istihara don neman zabin Ubangiji, amma ba na so ki tayar da hsnkali, don komai mukaddari ne daga Allah, kin ji,ki share hawayenki kar ya gane har yanxu kuka kike yi. Ta ce,,To momy ta mike ta nufi dakinta. ** A gidan Haidar kuwa Alhaji ya gama gayawa Aunty yanda suka yi da yayanta. Aunty ta ce Nina san yaya zai amince ni dai tsorona yaron nan ka san jin kansa kar a yi auren ya zo yana wulakanta min ‘ya.” Alhaji ya ce, Kirawo min shi mu ji ta bakinsa, ta daga waya ta danna lambobinsa ta yi ringin ya fi sau nawa kafin a daga sai can ya daga. Hello wallahi ban san ke ba ce sai da na kalli wayar sai na ga lambarki lafiya Aunty.?” Lafiya kalau ka zo falo Abbanka yana son magana da kai yanxu” To Aunty ga ni nan zuwa Suka ajiye kan wayar. ya yi sallama tare da tura kofar ya shiga bayan sun amsa masa, Ya zauna gaban Abbanshi a kan kafet, Abba ga ni. Ya ce, Yauwa Haidar na kirawo ka ne daman don na ji ko ka tsayar da matar da zaka aura? Haidar ya ce, Wallahi Abba ni ba ni da lokacin kallon matan ma bare na ga wacce ta yi min. Alhaji ya ce, Ni kuwa ka ga ina da lokacin kallon su, don har na samo maka matar da za ka aura, don nasan za ta yi maka yar uwarka ce Jawahir.” A firgice ya daga kai ya kalli Aunty ya ga karatunta ma take yi ya juya ya kalli Abbansa ya ce, Abba jawahir fa ka ce, Haba Abba me zan yi da wannan kwailar yarinyar, yarinyar karama zan aura? Haba ‘yar da ko kilewa ba ta yi ba, kwanan nan fa ta gama secondary. Alhaji ya daga masa tsawa, Kai ba ma son zancen banza, ni ita na zaba maka kuma ita nake so ka aura ta zamo uwar ‘ya ‘yanka. Haidar ya marairaice kamar zai yi kuka, Wallahi Abba jinina bai hadu da yarinyar ba ta da kunya shi ya sa na tsane ta. Aunty ta zaburo ta rufe shi da fada, Yar tawa kake cewa marar kunya ka tsane ta? To bari ka ji na gaya maka ko kana so ko baka so aure bsbu fashi, munyi niyyar hada ku kuma sai mun yi, in ya so ranar da aka kai ta dakinka ka yanka ta gunduwa gunduwa ka kawo mana namanta, wannan shi ne maganin kiyayya marar kunya wanda bai san mutunci ba. Abba ya dakatar da ita, To fadan ya isa haka, na san bai yi dai dai ba amma ki yi hakuri. Ya kalli Haidar, Ka tashi ka tafi amma ka sani jawahir ita ce zabinmu ba gudu ba ja da baya, sai ka je ka yi tuananin abin daka ya fi dacewa da rayuwarka. Haidar ya taso cikin bakin ciki, zuciyarsa tana kuna ya yo dakinsa yana magana a zuciyarsa yana zagaye falon nasa maganar har ta fito fili. Haka kawai a rasa yarinyar da za a ce na aura sai wannan figaggiyar yarinyar ‘yar karama, yarinyar da muka yi rainonta? me zan ji a jikin wannan kwailar, yarinyar da kyar ma in ta fara kirgar dangi? Haba ai an cuce ni, yanda nake ji da kaina nake so na auri katuwar mace wadda ta gama jami’a me hankali wadda za ta fuskanci halina ta bi ni yanda nake so mu zauna lafiya yaushe za a hada ni da wannan faratun? Yarinyar da ba ta fi ta tsaya min iya ciki ba, gaskiya a canja shawara, don in har yarinyar ta yarda ta aure ni sai ta gane kurenta.
.
SALON SO.
PART 7 TO 10.
.
Da Alhaji ibrahim ya gayawa inna shawarar da suka yanke na hada Haidar da jawahir aure, Inna ta yi murna ta yi godiya ga Allah ta sa wa abin albarka burinta zai cika ke nan na hade kan zuri’arta. Bayan Alhaji ya dawo yana cikin iyalinsa suna hira ya kalli jawahir ya ce mata, Jawahir dan uwanki fa na zaba miki wanda za ki aura, wato Haidar Cikin fargaba da tashin hankali ta wuntsilo daga kan kujerar da take zaune ta dirkushe a gaban Uban tana kuka ta rike kafafuwansa tana rokonshi, Don Allah Dady ka yi min rai kayi hakuri kada ka aura min yaya Haidar, wallahi ba ya so na ba ya kaunata, ba ma shiri da shi. Dady kada ya je ya shake ni namutu Dady ku yi asarata. Ba abin da zai faru jawahir yana son ki ba zai yi miki komai ba, ki yi biyayya a gare mu insha Allahu za ki ga kyan abin kin ji.?” Ta daga kai ta mike ta yi dakinta tana kuka mai ban tausayi ga mai sauraro. Momy ta kalle shi ta ce, Dan Allah ka hakura da auren nan tun da yarinyar ba ta so kuma yanzu an daina yayin auren dole.” Ya yi saurin daga mata hannu, Dakata don Allah ba na so ki ari halin da ba naki ba ki sawa kanki. komai da kika sani mukaddari ne daga Allah, yanda nake son jawahir ba zan taba cutar da ita ba, ko na kai ta inda za ta cutu ba. Ki sani duk wani Uba an fi so ya zabarwa ‘yarsa miji na gari, ki yi la’akari da shekarun jawahir sha bakwai fa, to a ina ta ga hankalin da tunanin da za ta iya zabawa kanta miji na gari? Ki yi hakuri ki barwa Allah zabinsa Momy ta ce, Shi ke nan Alhaji Allah ya zaba mana abin da ya fi alheri Cikin lokaci kankani an kawo kudi har an sa ranar aure wata biyu kacal. Hankalin jawahir ya kara tashi duk ta fige ta rame ba ta da aikin komai da ya wuce kuka kullum. Ita ta kasa zuwa ta gayawa Dadynta a fasa auren nan do ita ba yanda za a yi Dadynta ya gaya mata magana ta tsaya ja in ja da shi, don haka yamma tana yi a surare ta yi gidan Inna A gigice ta shiga kowa ya kalle ta ya san tana cikin tashin hankali. Inna ta tare ta cikin tsoro da tashin hankali tare da cewa, Ke kuwa yarinyar nan me ya same ki haka kika yi irin wannan ramar haka? Jawahir ta saki wani tsumammen kuka, hankalin Inna ya kara jagulewa tana tunanin ko wani ne ba shi da lafiya ko mutuwa aka yi musu. Ganin yanda Inna ta rude ne ya sa ta yin shiru amma idanuwanta be daina zubar da hawayen ba, Inna ta ce, Jawahir me yake faruwa ne? Ki gaya min waye ya mutu?” Jawahir ta ce, Don Allah Inna ki hana Dady ya hada aurenmu da yaya Haidar wallahi inna ba ma son junanmu ko kadan ni da shi halinmu be zo daya ba, irin rayuwar kowanne daban. ko an yi auren ba dadin zama da juna za mu ji ba. Inna da a zo a na bata zumunci ai gwanda ma kada a yi ko ba gaskiya ba? Inna ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, jawahir ta suka daga kujerar ta rirrike kafar Inna tana gunjin kuka, Ki taimakamin inna kada rayuwata ta salwanta. Inna ki yi wa Dady magana ya janye maganar aurenmu. Innata kamo jawahir ta rungume ta tana rarashinta ki yi hakuri jawahir, komai nufin Allah ne, ba na son yin shisshigi a lamarin aure, don ba mu san abin da Allah ya boye ba, amma zan yi kiran Alhajin na yi masa maga…….sallamar Haidar ce ta katse mata zancenta. Ya shigo wujiga wujiga kamar wanda aka jefo har ya furgitar da Inna. Inna ta ce, Lafiya Haidar me ya same ka haka duk ka yankwane kamar marar lafiya.?” Ya ce, inna. Abba da Aunty sun takura min wai sai na auri waccan kwailar yarinyar. Inna ki dube ni yanda nake a rasa wanda za a ce na aura sai wannan tatsitsiyar, haba inna gaskiya ba a yi min adalci ba.” inna ta daga masa hannu ta ce, “To ya isa haka ka je gida ka kirawo min Auntyn taka. Ka biya gidan kawun naka ka kirawo min shi, ina son ganin sa. ya ce, “To ya yi waje cikin fushi. Jawahir ta sake fashewa da kuka ta ce Inna kin ji irin wulakancin da yake yi min ko, wai ba zai iya fadar sunana ba sai dai ya ce min kwaila ko tatsitsiya amma ake kokarin lika min shi haba inna ai ba ayi min adalci ba. Inna ta ce, “Ki yi hakuri bari su zo sai a san abin yi. Bayan sllar magariba Aunty ta iso shi kuwa Dady sai da aka yi sallar insha’i amasallacin gidan inna sannan ya shigo cikin gidan tuni daman jawahir ta koma gida haidar kuwa daman bai dawo ba. Bayan gaishe-gaishe da wasa da dariya na uwa da ya ya, Inna ta yi gyaran murya ta ce, ” Daman abin da ya sa na tara ku game da maganar auren yaran nan ne. Inna ga a hakura da hadin nan kada zumuncin da ake ta ikirarin ya zo yana lalacewa. Dady ya ce, ” Inna duk ki rabu da yaran nan insha Allahu hadin auren nan nasu babu abin da zai jawo mana sai alheri saboda bayan ranmu zumuncinsu ba zai lalace ba. Amma yanzu ba kwa ganin yanda ba su damu da junansu ba, nan gaba abin ya zame musu gaba me karfi. Inna tace, “Gaskiya haka ne. Aunty ta ce, “To yaran nan fa mu muka haifesu ba su suka haife mu ba, to don me za mu bi son rainsu bayan mun san gaskiyar magana inda take Inna ta ce, to shi kenan Allah ya yi mana zabi na alheri suka yi addua suka shafa kowa ya nufi gidansa. Yau da gobe taki wasa kwance ta shi babu wuya a wajen Allah cikin ikon Allah lokacin biki ya zo ana ta shirye shiryen biki. Biki ne da yaye da ‘yan uwa suke ta yi masa shiri na musamman wanda za mu ce su kadai suke yin abinsu, don Ango da Amarya na cikin mummunan bakin ciki da bacin zuciya. Ba yanda ba a yi d a jawahir ta je ta rabawa kawayenta katin biki ba amma taki da ta ga ma za a matsa mata sai ta gudu gidan inna. Da inna ta yi mata maganar rabon katin bikin sai ta sa mata kuka dole sai aminiyarta ce da manyan kawayenta suke ta shige da fice na bin kawayen duk inda suke suna kai musu katin biki na gayyata. * * * Bangaren Angon kuwa Haidar abun duniya duk ya dame shi, ganin da gaske suke lamarin nan ba za su fasa aura masa wannan kwailar yarinyar ba. idan ya zauna shi kadai yana yawan tambayar kansa cewa, “Wai su abba me suka gani ajikin jawahir har suke kokarin aura masa ita? wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Abbansa ne da sauri ya amsa, “HELLO ABBANA. Abban ya ce, “Ka zo yanzu ina son ganin ka a falon sama.” “To abba ga ni nan zuwa. “Ya mike cikin hanzari ya nufi bangaren babanshi ya hau samansa. “Assalamun alaikum.” “Alaikas salamu, shigo Haidar. Aka amsa masa tare da ba shi umarnin ya shiga . Haidar ya shigo ya durkusa a gaban Abban nashi ya ce, “Abba gani. Abban ya ce haidar me kake so ka nuna min ne? kana so ka tozarta ni a idon duniya su san ban isa da kai ba?. Ya dago a firgice ya ce Abba me ya faru kuma? haidar na nema maka auren yarinya ka ki kula da lamarin ga shi yau saura kwana biyu daurin aure, babu wani shiri da kake yi. Yanzu da ba dan na bawa abokinka katunan daurin auren ya rabawa abokananka ba da haka za a daura maka auren ba abokin ango ko daya, kuma ko wajen jawahir din baka je ba bare ka san me take bukata da za ka ba ta ko? Haidar ya ce, ka yi hakuri Abba ganin dana yi kuna tsaye akan komai duk kun gama wani shiri da zan yi shi ya sa ban mayar da kai ba, amma don Allah Abba ka yi hakuri in an jima zan je gidansu jawahir din don na ji abin ta take bukata. “Yauwa Haidar ko kai fa Allah ya yi muku albarka . Ya dauko kudi dubu dari ya ba shi to Haidar ga wadannan sai ka ba wa jawahir din. “Abba da ka bar shi ga kudi can da na ware zan kai mata na shagalin ‘yan mata kawayenta. Ba komai hada ka kai mata gaba daya ai abubuwan shagalin da yawa. “To Abba an gode, Allah ya saka da alheri. Amin dana Allah yayi maka albarka. Da yamma Haidar ya gama shirinsa ya hau motarsa ya nufi gidansu jawahir. Ya tura maigadi ya yo kiranta . maigadi ya daga waya ya buga cikin gidan mummy ce ta dauka. maigadi ya rissana ya gaisheta kamar tana kalonsa sannan ya fadi sakon Haidar na son ganin jawahir. momy ta ce Ai ba ta nan tan gidan inna maigadi ya gayawa Haidar to sai Haidar din ya shiga ya gaisa da momy ya fito ya nufi gidan Inna. Yayi sallama falon ya shiga ya ga jawahir kwance kan cinyar Inna ya kalle ta ya doka tsaki. A zuciyarsa ya ce, “Sangartacciyar yarinya in an yi auren na ga jikin uban wanda za ki hau. Inna ta ce, “Lafiya daga shigowarka kake tsaki?” yace, “Bakomai inna suka gaisa suna hira tare ya dan taba wasan jika da kaka ya ce, “Inna tursasani fa aka yi na zo wajen waccan. Inna ta ce, “Ai ga ta bari na bagu waje. yace a a inna ki yi zamanki ba sai kin tashi ba, ji zan yi dame da me take bukata. Inna ta ce bari na fita kwafi jin dadin sakewa.” Sunfi tsawon rabin awa ba wanda ya ce da kowa komai, Haidar ya kalli ta ya ya mutsa fuska tare da tabe baki ya yi tsaki, “Ke in banda kinci albarkacin iyayenmu da sai kin raina kanki, don ni banga abin so a jikinki ba. Domin baki da cikakkiyar surar dazaki ja hankalina. Don haka ma in kin shigo gidan sai kiyi hakuri da irin zaman da za kiyi don ba wai wani abu ne zai shiga tsakaninmu ba. Ya debo kudin da Abban ya bashi dubu dari ya jefe tada su. “Ga shinan ba don halinki ba kuma wai a aljihuna na baki ba Abba ne ya bayar a kawo miki tatsitsiyar kawai.” Yayi daya falon da inna tashiga yayi mata sallama, “Inna mun gama zan tafi don akwai ragowar shirin da ban kammala ba. Inna ta ce, “To Haidar a sauka lafiya, ya fito da kudi dubu hamsin ya ba ta ga wannan inna ke ma kya yi hidimar bikin. “To duk ni kadai Haidar ? to na gode Allah ya saka da alheri, ubangiji ya albarkaci wannan auren naku. Shi dai ya yi ficewarsa . INNA ta shigo gurin jawahir ta kula da halin datake ciki don saboda tsananin bakin ciki da takaicin da haidar ya haifar mata sai ya hadu ya dunkule mata a kirji ga hawaye ya ki fitowa bare in ya zuba ta ji sa ‘ida. Kan ka ce meye wannan kirjinta ya hau zafi ga ba daya jikinta sai ya hau kakkarwa yana bari. inna ta rikice tana cewa, “Lafiya jawahir, yanxu fa na barki kalau dake me ya same ki.? Ta nunawa inna kirjinta ta ce inna kirjina ne yake ciwo, “Da kyar take iya maganar. sai numfashinta yakoma fita sama sama, ba jimawa abu ya ci tura idan ta ja numfashin sai ya dade be dawo ba. Hankalin inna ya yi masifar tashi ta kidime da kyar ta iya kiran direbanta a waya ta kira shi ya zo da sauri suka hadu suka kinkimi jawahir suka sa ta a mota inna ta shiga ya ja suka tafi asibiti Inna asibitin da Daddy yake zuwa za muje?” inji direban. “EH can za mu je mana” suna isa asibitn aka dora ta abin tura marasa lafiya a ka shigar da ita wani daki. likitoci biyu suna tsaye akanta. Can suka fito inna ta mike da sauri ta tare su “Yaya likita? Yace, inna ki kwantar da hankalinki, damuwa ce ta yi mata yawa da bakin ciki, amma za ta samu sauki idan an ankiyaye dokokin da likita zai kafa mata. Yanzu mun ba ta gado an kwantar da ita.: A ka nunawa inna dakin da take ta shiga ta zauna a gefen gadon sannan ta zaro waya ta bawa me aikinta ta ce ta buga gidan Dady da gidan Aunty ta gaya musu. Cikin mintuna kadan ‘yan gidansu duka sun zo har Dady da momy can gidan Aunty ma ta sako Haidar a gaba dole ya tuko motar suka zo. Gaba daya sun gewaye gadon da take kwance, kowa ya sa mata ido. Likita ya shigo ya zare ledar karin ruwan da ta ya sa mata wata. likita ya gaisa da Dady ya ce, dady sai an rinka kula da lafiyarta dole ne a rinka barin zuciyarta tana hutawa don a samu nutsuwa a rinka kiyaye duk wasu abubuwa ko maganganu da za su rinka bata mata rai a rinka yawan lallabata da rarrashinta har ta warke, idan ba haka ba tana gab da kamuwa da ciwon zuciya.” Dady ya ce, “Ba komai likita insha Allahu za a kula kuma Allah ma zai kiyaye. Shin kuwa Haidar ya yi zukulu yana tunani a zuciyarsa ya ce, “Anya kuwa ba shi ya haddasawa jawahir wannan matsalar ba? shi fa musulmi ne ya kamata ya yarda da kaddara ko ba komai jawahir yar uwarsa ce yana da imani don haka ya tausaya mata halin da ya ganta a ciki. dazun nan ya gama gaya mata maganganu ga shi yanzu halin da take ciki. Dayan biyu ko rai ko mutuwa. Washegarin jikin jawahir ya yi sauki don tana iya komai da kanta wajen magariba Dady ya matsantawa likita sai ya sallami jawahidr sabo da gobe daurin aurenta Likita ya rubuta mata takardar sallama da magunguna Washegari aka daura auran Haidar da Jawahir, daurin auren da ya samu halattar manyan mutane da ‘yan boko abokanansu haidar da yaya Abba da Nasir. Anyi taro lafiya an gama lafiya mata kuma sun shiga hadaniyar biki. Haka kawayen amarya suke ta shiga da fice na gudanar da hidimomin bikin kawarsu, amarya kuwa ba ta um bare um-um kowa kallon sa take yi. kakarta ta wajen uwa Hajiya Rabi ta zaunar da ita tana yi mata nasiha ki yi hakuri jawahir ki zauna a gidan mijinki lafiya ba ki da wani gata da ya wuce dakin mijinki. Ki rinka taka tsantsan da harshenki, kada ki gaya masa bakar magana ko wace za ta sa shi yayi fushi saboda lahirarki.” kowa dai ya ta mata nasiha zai ce ta ji tsoron Allah ta yi biyayya ga mijinta. An gama biki amarya ta tare a tsantsareren gidan angonta da yake nasara G.R.A. Kowa ya fashe ‘yan kawo amarya sun watse sai ita kadai kwal a cikin gidan sai maigadi da yake bakin get. Tana zaune tana tunanin irin zaman da za su yi da HAIDAR har bacci ya fara daukan ta a zaune ta ji an turo kofa anyi sallama an shigo. Ta yi saurin gyara zamanta . Ya shigo dakin ya nemi waje ya zauna.
.
SALON SO
PART 11 TO 15
.
Ba ce mata komai ba ita ma ba ta kalli gun da yake ba. Can ya ce mata kinci abinci? “EH na ce. Ya janyo ledojin da ya shigo da su da karamar akwati ta siyen baki ya tura mata gabanta ya tashi ya fita. Jawahir ta yi tagumi a ranta ta ce, “O ni ‘yansu, ga me so na can an kawo ni gidan wanda ba ya kauna ta ko da yake ni ma zan zauna ne darajar iyayenmu. “A nan ta tuno nasihar da mommynta ta yi mata. Jawahir ni dai babu abin da zan ce miki sai fatan Allah yayi miki albarka yanda kike binmu kike mana biyayya ubangiji ke ma ya baki ‘ya ‘yan da za su biki haka. Jawahir ta dauki duk abin daya same ki a rayuwa matsayin kaddara. ki kasance me biyayya ga mijinki ki boye sirrinku kada ki buda shi ga wani don Allah ya tsinewa matar da take bayyanar da sirrin mijinta. Duk abin da ya yi miki yi hakuri kada ki kai kararsa wajen kowa. Ki dage ki yi ta yi muku addu’a don Allah ne zai warware muku matsalarku. Ka bacin rai ya sa ki bin boka ko malam babu abin da za su yi miki face ki barnatar da kudadenki a banza kuma ki jawowa kanki tsinuwar Allah ki rike alkur’ani dan zancen Allah ne shi ne waraka ga komai. Jawahir ta saki ajiyar zuciya ta ce, “In Allah ya yarda zan rike nasihar mommyna. Haka ta kwanta ita kadai ga tsoro da yunwa tana jin amma ba ta bude ledojin da Haidar ya ajiye mata ba. Da asuba ta yi sallah ta dauki kur’ani ta karanta abin daya sauwaka ta yi addu’a ta ta sha fa ta cire hijabinta ta ajiye. Ta yi takumi, “Ni kuwa na je na hada break ko kuma na kyalle shi? Kai gwanda na yi ko ya ci ko ba ya ci Allah ya gani dai na fita falon tsarin falon ya yi mutukar burge ta da ba ta sha awa, lallai daddynta ya kashe mata kudi. Ta bude kicin din shiga haduwarsa ya yi mugun gigita ta, sak irin wanda a ke nuno tallolinsu ne kasashen waje, duk wata na ura ta amfanin dan Adam don hada abu a saukake an tanadar mata a kicin din nan, sannan duk wani kayan girki da za su bukata an tanade shi ta bude disk freezer cike yake da kaji, zabi xuwa naman kasuwa duka danyu, sai daya firizar kayan miya ne irinsu attarihu tattasai, tumatir, albasa, koren, wake, karas, kabeji da sauransu. Firinjin tsaye kuwa lemummuka ne kala kala na kwali da na gwangwani da robobin ruwan sha, kamar su swan water, Highland water, da dai sauransu. Ta ga wata kofa daban a kicin din ta bude ta ta shiga ashe sito ne kalolin abinci iri iri buhunan shinkafa, katon dinsu taliya, makaroni, kuskus, buhun sikari da na fulawa, garwar manja da na jan kuli da kuma man shanu, busasshen kifi, daddawa, kanwa busasshiyar kubewa, magi kama daga Reko, onga, kori, Ajino-moto da dai sauransu, babu abin da za ta nema na amfani komai an dire mata.: Ta debo dankali ta fere ta soya ta jona ruwan zafi ta sa citta da kanun fari, ta zuba ganyen shayi me kamshin Nescafe ta koma daki ta dauko ledar jiya gasassun kaji ne manya guda uku ta zuba su a oben ta dumama su. Ta fasa kwai ta soya ta debo filas-filas masu kyau ‘yan dubai ta zuba komai a ciki ta rufe ta juye ruwan shayin a fulas din shayi wanda yake duk saiti ne da fulas din da ta zuba ragowar kayan a ciki. Ta jere komai a tebir ta debo kofuna da filet da cokula duk ta zube kan tebir din ta sa wani farin kyalle me ban sha awa ta rufe kayan kan tebir din. Ta dauki nata break din ta yi dakinta da shi. Ta rufe kofarta ta shiga toilet ta yi brush sannan ta ci ta koshi ta koma gado ta kwanta. Mintina kadan bacci ya yi awon gaba da ita. Shikuwa Haidar da ya tashi da asuba ya yi sallah ya yi karatu ya shafa addu’a gado ya koma ya kwanta saboda baccin gajiya da yake ta dawainiya da shi. Karfe tara ya tashi na safe ya yi mika tare da salati ya duro daga gadon ya nufi toilet. Ya salla wanka ya zo ya gama goge gogensa da shafe shafensa ya yi tsantsararriyar shiga, shiga ta alfarma ya feshe jikinsa da turaruka. A zuciyarsa yake cewa ya kamata na je na gano yanda yarinyar nan ta tashi ko don nasihar da Abbansa ya yi masa kamar haka……. “To Haidar yau Allah ya nufa an daura auernka da jawahir to duk wani nauyi da hakkinta ya koma kanka, amana ce a gare ka, idan ka zalince ta ko ka cutar da ita kai da Allah, idan ta yi maka abin da be yi maka dadi ba ka zaunar da ita ka nusar da ita cikin nasiha da tattausar murya. Kar ganin yanzu ta zama ikonka tana zaune a karkashinka wallahi idan ka zalince ta ubangiji ba zai taba kyale ka ba, sai ya fitar mata da hakkinta don haka ka kiyaye.” Ajiyar zuciya Haidar yayi, “Haka kawai a daure ka da jijiyar jikinka, bari na je na gani ko ta karya. Ya sauka kasa da yake benen nasa a cikin falonta yake. Ya kula da tebir din da ya sha kwalliya da kayan alatu. Ya karasa wajen ya yaye farin kyallen ya bude komai. Kamshi ya daki hancinsa nan da nan sha awar abincin ta kamashi. Ya zauna ya hada ruwan tea me kauri ya debi soyayyen dankali da kwai da kaza daya. Haidar ya rinka ci yana lodawa cikinsa don jiya da daddare bai ci komai ba ya kwanta, yanzu kuwa ai ya yi lodi, ya yi gyatsa tare da yiwa Allah godiya. Ya mike ya nufi kofar dakin jawahir ya ji ta a rufe. Ya samu takarda da biro ya rubuta mata sako kamar haka: “idan kin tashi ki yi break ni mun fita gaisuwar surukai sai yamma zan dawo.” Haidar Ya ninke ya dora kan tebir din. Ya fice. Ya samu abokanansa suna jiransa suka tafi gaisuwar surukai. jawahir sai sha biyu na rana ta farka, tana mikewa ta fada toilet ta yi wanka ta kammala shirinta sannan ta fito falo, ga mamakinta ta ga Haidar ya ci break din da ta shirya masa. Ta hango takarda ta dauka ta bude ta karanta ta tabe baki, “Kada ma ya dawo ni ko kwana zai yi me ya dame ni?” Ta dauko yogougt ta zauna tana yagar kazar tana korawa da nonon har ta koshi. Wajen sha biyu da rabi direba ya kawo Inna da kannanta Auwal da sani da su Hassana da Usaina kannan Haidar. Jawahir ta cukuikuye inna tana tsallen murna. Inna ta dube ta tana dariya ta ce, “Ke cika ni kada ki karasa ni, ni ina can zuciyata ta kasa sukuni sabo da tunanin yaya kwana ke kuma kina kokarin karasa ni. jawahir ta yi dariya, “Amma dai inna a nan za ku kwana ko?” Inna ta tabe fuska ta ce, “Ke ba na son hauka yanzun nan ma za mu juya. Hassana ta ce, “Allah Aunty ni dai gidanki ya ba ni sha awa zan kwana. Usaina ta ce, “Lallai kina so Yaya haidar ya yi tamaula dake kenan.? Jawahir ta ce, ba wani abu da zai yi mata kin ji Usainar nan wai don kar ta kwana, ba abin zai yi miki Hassana.” Inna ta ce, “Babu wanda zan bari, kafata kafarsu. Auwal ya ce, “Su Aunty jawahir ‘yan gayu. “Gaba daya sukai yi dariya. Sani dauko muku ragowar break din Yaya ku ci. Ta tashi ta shiga kicin ta kwaso musu yogouht da lemummuka da ruwan sanyi ta zube musu. Da ragowar gasassun kajin amarcinta. Inna ta gyara zama da jikokinta suka ci suka koshi. Inna ta kara yi mata fada da nasiha. Karfe hudu suka tafi. Jawahir ta mike ta yi sallah bayan ta idar ta shiga kicin ta dauki kaza daya ta yayyanka ta yanka albasa ta sa gishiri da citta da magi ta dora kan wuta. Ta debi kayanmiya yanda zai wadace ta ta markada ta dora ruwan kuskus. Ta gama hada soyayyiyar miyarta ta dafa kuskus dinta da ya sha karas da koren wake ya yi wara wara da shi gwanin kyau. Ta gasa kifi irin manyan nan ta yi farfesun kayan ciki, ta markade kwa kwa a ciki blinder ta tace ta sa madara, filebo, sukari ta hada lemo me dan karen dadi. Ta samu wasu kayatattun fulas ba irin na safe ba ta kuma jere komai a kai. Ta hau saman dakin nasa, ga mamakinta sai ta gan shi a bude ta gyara masa gadon da ya kwanta ta kade komai ta share masa dakin. Ta wanke bandaki ta goge ta kunna turarukan wuta ta fesa Air freeshner a kowacce kusurwa, ta sakar masa A.C Nan da nan sanyin dadi ya soma tashi. Ta rufo masa dakin ta sauko ta gyara falon kasa da nata dakin ko ina ta feshe shi da Air freshner da turaren wuta dan maiduguri ta saki labulayen ta kunna A.C ta rufe kofar falon ta shige dakinta ta rufe ta fada toilet don yin wanka Sai karfe biyar da rabi Haidar ya dawo gidan a gajiye ga yunwa da take azalzalassa don tun break din da ya yi bai sake cinn wani abun ba. Don shi Allah ya yi shi mutum ne mai kyankyami ba ko ina yake iya cin abinci ba. Megadi ya wangame masa get din ya shigo ya rissina ya yi masa barka da zuwa. Ya murda kofar falon ya shiga tare da yin sallama shiru kamar ba kowa a gidan. Daddadan kamshi ya bugi hancinsa, ko ina tsaf a share a goge ya ji gyara, ya yi sha awar yanda take da tsafta take kula da komai. Ya haye samansa yana tura kofar dakin, nan ma sanyin da kamshin dadi suka yi masa sallama. Ya sheka ya limshe ido ya yi godiya ga Allah, shi kansa falon saman nasa ta canja masa tsarin gyara wanda kuma hakan ya fi kyau yana shiga cikin dakin nasa sai kansa ya kwance, wani hadadden zanin gado ta shimfida masa , ai yanda ta dame gadon ya burge shi ya cire kayansa ya fada toitel ya fara wanka.Ya gama shirinsa ya sa kananan kaya. Sun karbe shi kuwa sun yi masa kyau. [07069210827: Ya feshe jikinsa da turaruka ya sauko kasa ya hau tebir ya bude komai, kamshin girkin ya buge shi sha awa da jin dadi suka bige shi. Ya zauna ya rinka dibar garar girki, yana ci komai na kan tebir din sai da ya ci da ya wa ya ci ya koshi ya yi hamdala ga ubangiji. Ya rinka tsiyayar lemon kwa kwar nan yana sha, don Allah daman hausawanmu sun iya hadadden lemo haka, amma muke bugewa kullum yawon siyen juice. Ya cika kofin tangaran da shi ya tashi ya koma kan kushin can gefe daya ya dauki jarida yana karantawa yana kurbar lemon kwakwar. Ita kuwa jawahir tana daki ba ta ma san ya dawo ba ta gama shirya kwalliyarta cikin riga da siket na atamfa kwali wax, rigar fitet ce ‘yar firit,siket din ya yi tsantsan a jikinta. Ta dora daurin dan kwali wuyanta da kunnanta wani rantsattse fashion ne mai kyau. Ta feshe ilahirin jikinta da daddadan turaruka masu kamshi. Ta bude kofar dakinta ta fito kamshin da ya ji ne ya sa shi dago kai ya kalle ta, a ransa ya fada, “Yarinyar tana da kyau sai ka ce Aljana, ga shi ta iya gyran jikinta. Yanda siket din ya matse ta dole ta rinka takawa sannu a hankali gudun kada ta harde. Ta shiga kicin ta debo abinci a filet dan kadan sai ka ce wadda za tabawa dan yaye sai robar nono yogougt dake daya hannun nata. Ta zo ta nutse a cikin kujera ta dauki remote ta kunna T V. tashar CNN ta kunno, sannan ta fara cin abincin, yanda take diban abincin kamar ba ta son ci a yangance. Duk abin da take yi idon Haidar yana kanta, ita kuwa ba ta san ma ya dawo ba bare ta san yana falon. A zuciyarsa ya ce, “Yaushe dama za ta girma tana cin wannan dan mitsitsin abincin kamar na ‘yar yaye. Can wayarta ta yi kara ta dauka, tana dubawa da murnarta ta dora a kunnanta, “Hello Dadyna. sai ta kunna (Handsfree) Daddy ya ce, “Jawahir yaya kike? Ya megidan naki? “Wallahi lafiya lau Dady muna zaune kalau. “Kina son masu aiki ne a kawo miki? Cikin shagwaba ta ce, “Lah Dady mai aiki, ni wallahi ba na son kowa su zo su yi batawa mutane waje. don iya girkinmu mu biyu da gyaran dakunanmu Dady ai duk zan iya. “To jawahir wanke-wanke fa, ga sharar harbar gidanku.? Dady ka san ba na son kazanta da gama girki nake wanke kayan na goge su na mayar inda suke. Harabar gidan kuma dakin saukar baki yana da yaro da yake gyara masa me bawa fulawowiyin gidan ruwa. “To jawahir wa zai rinka ba su abinci ko har da su za ki yi rinka yin girkin? Ta kara shagwabewa, “Uhm Dady wallahi ba zan yi musu girki ba, abincina daga ni sai Yaya kawai. “To shi ke nan jawahir za a samu haidar din na yi mishi magana na ji yanda za a rinka yi da su wajen ba su abinci.” Cikin shagwaba ta ce, “Don Allah Dady kada ka yi masa magana ya zo ya ce sai na rinka girkin da su ka ga wahala zan sha. “To jawahir ai a karkashinku suke, dole ku rinka kula da hakkinsu ko to kwace kuma za ku bar su da yunwa. Cikin shagwaba ta ce, “Haba Dad. to Dady na yarda a kawo tsohuwa amma ba za ta rinka shigo min sashena ba, sai dai ta tsaya can bangaren masu aiki ta rinka da fa musu abincin, ai ya yi ko Daddy.?” “Yauwa ko ke fa jawahir gobe za a kawo ta, Ki kara hakuri jawahir ki dinga biyayya ga mijinki. Allah ya yi muku albarka . To Dad na gode, “good day Dad.” Tayi ajiye wayar ta mike ta dau filet din ta shiga kicin. Haidar ya mike ya haura samansa ya yi dai dai a gadonsa yana tunanin hirar jawahir da Daddynta. A ransa yake cewa, “Ko dai don muna ‘yan uwa ne halayyarmu da ra’ayinmu suke neman zama daya? Gaskiya ta burgeni da za ta rinka yi min komai da kanta, don ni na tsani gidan da me aiki take yi wa matar gidan da mijinta girki, amma jawahir tana da dadin murya ga dadin saurare, ban so suka gama hirar ta su ba. To haka da i zaman ya ci gaba tsakanin miskilan guda biyu. kowanne yana ji da girman kai da miskilanci babu wanda zai wa dan uwansa magana idan har sun hadu da safe za ta ce masa ina kwana. Yayin da shi kuma yake daukan lokaci kafin ya amsa da lafiya lau. To sai ta yi shigewarta daki ba ta fitowa har sai ya tafi. sannan ta zo ta gyara musu dakunansu ta turare da turaren wuta ta feshe ko ina da Air freshner ta zauna ta shirya musu hadadden girki me gamsarwa. Ta hada masa lemo da kanta kullum da sabon samfir din girki da lemon da take yi masa. Ba ta taba barin waje da datti ko kura ko ina fes a gyare dai dai da wanke kwanikanta ita take yin abinta. Ta gyara kicin dinta fes kamar ba a yi komai a ciki ba. Tukwane ne kawai da kaskon suya saboda maiko take bawa Dela me aikinta ta wanke mata Tun da akawo Dela take zaune a bangaren masu aiki za ta yi girkinsu su uku da maigadi da ita sai yaron gidan da ta yi gama za ta wanke komai ta share ta goge da yake ita ma me tsafta ce shi ya sa suke shiri da jawahir din. Haidar kuwa yana jin dadin yanda jawahir take da tsafta komai take kulawa da shi yanda ya kamata, don haka duk san da ya taso daga office burinsa ya yi sauri ya dawo gida don ya narki special din girki da jawahir za ta yi masa. Ya zauna a kayataccen falonsu yana shakar daddadan kamshin falon. Idan ya tashi daga office yana biyawa ta gidansu a gurguje yake yin komai don yana sauri ya koma gida. Idan Aunty ta ce masa ga abinci ya kan ce um Aunty sai na je gida zan ci. Duk da ba magana suke yi wa junansu ba, to amma hakan bai hana su kyautatawa junansu ba Ana yawan kawo mata kannanta Auwal da Sani da kannan Haidar Hassana da Usaina idan yamma ta yi direba ya mayar da su gida Yaya Abba ma da yaya Nasir suna yawan zuwar mata. Inna ma ta na kan zo amma ba sosai ba iyayensu ne dai har yau ba su zo ba. HAIDAR ya samu kwanciyar hankali don ba a bin da ya ke damunsa don haka jikinsa ya kara murjewa kyansa ya kara daduwa kowa ya kalli fatarsa ya san ta goge da jin dadin duniya ita kuwa jawahir da yake abincin be da meta ba to yanda take haka take babu wata ‘yar kiba da ta yi. Shekara daya ke nan da yin auren har yau jawahir ba ta taba lekawa kofar gida ba. Yau asabar da jawahir ta kammala da hada break dinta ta diba ta ci ta gama gyara wajen ta sa turaren wuta ta feshe da gidan ta shige toilet ta yi wanka. Yau shigar turawa tayi ‘yar bingilar shimi ta saka iya cibiya me siririn hannu sai dogon wando da ya dame mata cinyoyi da kafar wandon an bude shi ta hade gashinta a tsakiyar kai ta sa tafkeken ribon ta daure shi. Cikinta a dame kamar ba ta zuba masa abinci ba, fuskar nan tata sai fitar da sheki da wa ni asirtaccen kyau ta ke yi, ta gama feshe jikinta da tuararuka ta fito falon inda Haidar ya ke break ta durkusa ta ce, “Ina kwana?” bai juyo ya kalleta ba ya ce, “Lafiya lau. Ta mike ta isa bakinTV ta dauki takarda da biro ta koma ckin kujera zaman mutu daya ta kwanta tana rubutu. Tun da ta mike Haidar yake bin ta da kallo sai hadiyar yawu kawai yake yi ta yi mugun ba shi sha awa, hankalinsa ya tashi sosai. Ta gama rubutu a takardar ta ninke ta taso cikin nutsuwa ta zo gaban Haidar ta ajiye masa a kan tebir dinta ta juya ta koma daki, shi kuma ya bi ta da kallo. Sai da tashige daki sannan ya ware takardar ya fara karantawa . Yaya Don Allah yaya ina so zan je gidanmu da gidan inna da wajen Aunty. Ina so na taho da sayyid Autan Aunty idan ka yarda. Jawahir Yana gama karantawa ya ajiye ya ci gaba da yin break dinsa sai da ya gama sannan ya mike ya dauko takarda da biro shima ya rubuta mata kamar haka. “In kin shirya ki jira ni na kai ki da kaina, Sayyid kuma in kin ga ba zai takura miki ba kya iya daukoshi Haidar Jawahir duk ta matsu da ta ga amsar da zai ba ta. don ita dai tana so yau ta je gidajen nan ko dan dadewar da ta yi rabonta da fita . Ita jin kanta da miskilancinta ya hana ta ta fito bare ta ga amsar da ya rubuta mata , shi kuma girman kansa da isarsa ba za su bar shi ya kai mata ba. Sai da ya gama kallon sa da hutawarsa sannan ya koma sama. Sai da ta ji tafiyarsa ta fito ta dauki takardar ta karanta, aikuwa sai ta hau tsalle tana murna kamar yarinya. Nan da nan ta shiga shiri a kakale nan a kakale can ko ina ta yi fes kamar wacce aka karawa kyau. Wani dandasheshen less ta saka me dan banzan kyau da shegiyar tsada. Ta yi kyau kamar ka sace ta ka gudu don haduwar da ta yi. Ta kalminta da mayafinta da jakarta duk ruwan less din ne. Takalmin me tsinin dunduniya. ta hakimce a falon tana jiran futowarsa megidan Ba ta jima ba sosai ya fito cikin shiga ta wani danyen boyal baki sai sheki yake yi, hular kansa baka mai gashi, takalminsa baki sai agogon hannunsa na Daimond. Duk sun yi kyau kamar wadanda za su zaben sarauniyar kyau. Ya yi waje ba tare da ya kalle ta ba, ta mike ta rurrufe ko ina ta fito tana takawa sannu a hankali yana kallon ta ta mudubin motar, duk sha awarta ta motsa shi, amma saboda iya jan ajinsa ba zai taba nuna mata ba, ko ya bari ta gane ba. Ta kama murfin mota ta bude ta shiga baya ta zauna, be kalle ta ba kuma be yi mata magana ba be kuma ja motar ba. Ya yagi takarda ya yi rubutu ya cilla mata baya ta dauka ta duba, “Ba ki kai matsayin da zan zama direbanki ba, “Tana gama karantawa ta bude ta fito ta dawo gaban motar ta rufe. Ya kuwa figi motar a guje kamar me shirin tashi sama. Babu wanda ya yi wa kowa magana haka suke tafe sai da suka zo wani super market ya fita ya yo musu tsaraba suka ci gaba da tafiya. Gidansu ya fara kai ta, yana tsayawa ya mika mata takarda ta duba ta karanta a wa daya na baki ki yi ki fito mu tafi. Ba ta ce komai ba ta bude ta fita ta yi sallama falon ta shiga. Aunty tana ganinta ta mike ta taro ta da murna tana jawahir ‘yata barka da zuwa ‘yata ta kaina.” Ta rungumeta ta a jikinta, “Zo mu hau sama Alhaji ya ganki tukunna, “Suka hau ta durkusa har kasa ta gaida Abba cikin fara’a da murna yake amsawa, “Jawahir ke ce haka? lallai yau zan huta da mitar Auntynki.” Aunty ta ce, “Wa ya kawo ki ne? ko kun dauki direba ne? Cikin jin kunya ta ce, “Ai yaya ne ya kawo ni. Tana rufe baki ya yi sallama ya shigo kai tsaye ya wuce gaban Abbansu ya zauna ya gaishe su. Abba ya dafa kan Haidar ya ce, “Yau na ga jawahir na gode muku da yanda kuka rike kanku ba ku mu kunya ba. Haidar ya ce, Yanzu ma cewa ta yi na kawo ta za ta dauki Sayyid ga shi ban gan shi ba. Aunty ta ce, jawahir ta Sayyid ai yanzu ba irin da ba ce da kike zuwa ki dauke shi ya yi kwana da kwanaki a gidanku yanzu ai sai ya takuraki. Cikin jin kunya ta ce, “Lah Aunty wallahi ba komai ai ba zai takura ni ba. To shikenan gobe za a kawo miki shi ya yi kwana biyu kawai. Ta ce, to Aunty na gode. Aunty da kanta ta kawo musu abubuwan ci da sha suka sauko kasa da Aunty. Duk yanda Aunty ta yi don ta ji ko da wani abu a tsakaninsu amma jawahir ta ce kalau suke. Haidar ya shigo ya yi wa Aunty sallama ya fita jawahir ta kalli agogon hannunta ta ga awa dayan da ya ba ta saura minti uku ta mike ta ce Aunty zamu tafi. “Haba jawahir tun yanzu? Ta ce, Ai za mu bi ta gidanmu da gidan inna. “To jawahir na gode Allah ya yi muku albarka. Manya ledoji biyu Aunty ta ciko mata da kayayyaki. Abba kuma ya ba ta dubu ishirin. Daman Haidar ya sa maigadi ya shigo musu da tsarabarsu. Ta bude motar ta shiga awa dayan ta cika dai-dai shi ma ya shigo suka tafi. Gidan Inna ya kai ta shi ma sai da ya ba ta takarda ta karanta kar ki wuce awa daya. Ta shiga gidan inna murnarta da tsallenta ta cukuikuye inna. Inna ma murna take yi ta zaunar da ita “Daga ina haka? ke me Haidar din yake baki kika sake zama baturiya haka sai dai rashin kiba amma kin kara kyau ko dai ciki ne dake? Daidai shigowar Haidar a zuciyarsa ya ce, “Ciki yaya za ayi ayi ciki yanzu ai ta yi kankanta. Ya yi sallama falon ya shiga inna ta tare shi da murna duk bakinta yaki rufuwa ganin jikokinta shar dasu babu wata alamar damuwa a tare da su. Inna jikinta sai rawa yake yi ta rasa inda za ta sa kanta don murna, ta kawo musu wancan ta kawo musu wannan tana ta hira. “Dan ka’ida bature ya duba agogo saura minti biyu awa daya ta cika Haidar ya yi wa Inna salllam ta rinka yi masa godiyar wannan uwar tsarabar da suka kawo mata. Ya fita ya koma mota yana jiranta. Sai hira kuma ta dawo sabuwa tsakanin inna da jawahir har ta manta da dan ka’ida lokacin da ya ba ta, to tana ta shan labarai da abubuwan ban dariya daga inna. Ba ta yi aune ba ta ga kara minti arba’in da biye a kan awa dayan da ya ba ta zumbur ta yi ta mike inna za mu tafi sai kin zo. Inna ta ce, Au ba sai magariba za ku tafi ba? “Ta ce, “Uhm yana mota yana jira na. “To shi ke nan na gode ku gaida gida. Allah ya yi muku albarka. A cikin mota ta same shi ya kwantar da kujera ya na shan A.C da sautin rediyo ya lumshe ido kamar mai bacci. Ta bude mota ta shiga ta zauna. Ta fi minti goma ba shi da niyyar ta shi bare ya tuka motar su tafi. Ta gaji da jira ta ce, “Yaya na fito. Ya bude ido daya ya ce, Awa nawa na baki.? Ta ce, “Awa daya.” “Sai yanxu awa dayan ta cika.? “A’a Inna ce ta tsayar da ni da hira.” “To kin cinye lokacin da za ki yi a gidanku, yanzu gida za mu tafi sai wani lokacin kuma.” Gabanta ya fadi, duk da dokin da take yi na zuwa gidansu ga shi ta fito din amma ba damar zuwa gidan nasu. Ita girman kanta ba zai bar ta ta ba shi hakuri ba bare ya hakura yakai ta. Kawai sai ta ji hawaye yana zubo mata. Haidar na kula da ita amma sai ya dauke kansa ya ci gaba da tukinsa kamar be san tana yi ba. Tana kukanta har da shassheka amma sai ya karo rediyon ma don kada yaji kukan. Ba wanda ya sake cewa da kowa komai har suka je gida Yana tsayar da motar ta bude ta fito tana goge ido ta bubbude ta shiga dakinta ta fada gado ta yi rub da ciki ta ci kukanta ta koshi. Ta shiga ban daki tayi alwalla ta yi sallar la’asar zuciyarta tana ta zuga ta da kada ta yi masa girki don ya dan dani bacin ran da ta ji, to kuma sai ta yi wani tunani ai ita ta fara bata masa kuma girman kai ya hana ta neman afuwarsa to idan ba ta yi masa girki ba ai ta dada shiga hakkinsa kuma ita ba iya cewa za ta yi ya yi hakuri ba, kuma zai yi bacin ran da ya fi nata, ita kuma ba burinta ke nan ba. Duk da irin zaman da suke yi na rashin yiwa juna magana to amma ba ta so ko kadan ta ga ta bata masa rai. shi yasa kullum take yin abin da ta san zai ji dadi. Ta mike ta fito falo takarda ta gani a ninke, “Na fita unguwa sai magariba zan dawo,” Ta yaga takardar ta fada kicin ta dora girki . Yau tuwon samovita ta yi miyar danyan kubewa da ta burge kaza a ciki. Sai ta gasa masa dan shila ta soya masa kifi ta hada masa lemon abarba ta jere komai a tebir. Yau Dela ta bawa wanke wanken don zuciyarta a bace take. Kafin ya dawo ta gama abin da take yi ta gyara wajen ta shige dakinta ta kulle kofa. Sai da ya yi sallar magariba sannan ya shig, ga mamakinsa sai ya ga tayi abinci a zatonsa yanda ya bata mata ba za ta yi girkin ba, har yana shirin fita Hotel ya siyo musu. Duk kuma sai ya ji tausayinta ya dame shi a ransa sai ya yi da yasanin bai ki kai ta gidan nasu ba. Ya zauna ya ci abincinsa ya koshi yau har da senti ya mike ya je ya sake alwalla ya yi sallar isha’i. Haka ya yi zaman falon har goma na dare amma bai ga fitowar ta ba, abun ya dame shi dan be ji dadin yanda ta takura kanta ba. Haka tai ya hakura ya je ya kwanta zuciyarsa ta na ta tunane tunane. “Washegari da safe da ta gama komai da ya shafe ta ta daddasa kwalliyarta yadda ta saba ta fito yana tebir yana break ta durkusa ta ce, “Ina kwana.?” Ya amsa, “Lafiya lau jawahir kin kwana kalau.?” “Lafiya kalu.” Ta ce ta mike tana koma daki tana mamakin canjin yau da ta samu na sakin fuskar Haidar. Har ya fadi sunanta ba tare da ya ce mata kwaila ko tatsitsiya ba. * ** ****** Haidar bai dade ta fita ba direba ya kawo Sayyid, jawahir ta yi murna da farin cikin ganin sayyid don ta samu abokin debe kewa. Sai magariba Haidar ya dawo sayyid yana jin karar motarsa ya fito a guje ya tarye shi, Haidar ya dauke shi ya rungume shi, “Auta wa ya kawo ka? ina ka baro Auntyn taka? “Tana gida Abba ya ce kada na dade kwana biyu zan yi.” Haidar duk ya gama wani abu da zai yi na game da cin abinci, wanka ya sa kananan kaya na shan iska ya haye saman gado yana shan surutun Sayyid da yake ba shi dariya. Wayarsa ta fara ruri alamar ana kiransa. Haidar ya duba ya ga bai san lambarba ya share ya ki dauka, ta katse dan kanta, can aka sake bugowa be dauka ba ta kuma katsewa. Sai da aka yi sau biyar a na shi dan Haidar ya gaji ya dauka, “HELLO. Ya amsa a kasan makogaronsa. Cikin doki Kausar ta amsa, “Ranka ya dade saraki har yazu mulkin yana nan ne ba a sauke ba?” Ya ce, “Wake magana ne? ko sai na ajiye kan wayar ne.? Ta ce, “A’A ayi hakuri Saraki kausar ce. Yac, “Wa cece kuma me wannan sunan.? “Ranka ya dade Saraki Kausar dinka da kuka yi karatu America tare ka gudo ka bar ta. “Oh. Kausar kenan kin cika na ci, yanzu sai da kika lalubo ni.” “To ya zan yi Haidar wallahi tun ranar da ka taho ban kuma nutsuwa a zuciyata ba sai yau da na ji muryarka. Haidar ciwon son ka ya zamo gyambo a cikin zuciyata. Haidar ni musulma ce ka tallafi rayuwata Haidar ka zo gare ni ka aure ni. “Haba Haidar ka san darajar ‘ya mace da kimarta amma duk na watsar na tunkare ka na ba da kai na ke rokonka da ka aure ni. Haidar wace irin zuciya ce da kai? Ka tuna fa kana da kanne mata kuma nan gaba in Allah ya ba ka haihuwa kila ka samu ‘ya ‘ya mata, to ya za ka ji yayin da ‘yarka ko kanwarka ta fada irin wannan halin da na fa da akan kan wani? Ka san kaddarar ubangiji babu inda ba ta fadawa mutum.” Haidar ya ce, Ki yi hakuri ba burina na yi miki wulakanci ba, ai duk inda masoyinka yake ya fi makiyinka sau dubu, to amma kin ga yau shekara daya ke nan iyayena sun hada ni aure da wata ‘yar karamar kanwata, wadda har a yanzu da nan gaba rainonta nake yi.” Kausar ta ce, Haidar don Allah don Annabi ka amincewa bukatata wallahi ni ba ruwana da wata matarka don ba a kanta zan zauna ba. Ya ce, “To shi kenan Kausar ki ba ni lokaci zan yi shawara. Ta ce, “Haba Haidar. Ya ce, “Uhm no kada ki damu ba matsala insha Allahu komai zai zo da sauki. Suka yi sallama kowa ya dire wayar. Haidar ya fada tunani ko na amince da bukatar Kausar na aure ta, ko ni ma na ji yanda auren yake? To ya zan yi da Aunty da Abba? ko da yake in sha Allahu ba za su zamo matsala ba. Haba dai ya kwanta yana sake- saken abinyi. Washegari yana office wajen azahar jawahir ta yi baki kawayenta ne suka zo. An sha hira kuwa inda jawahir take cewa, “Bilki ai kun yi min rashin mutunci wai duk yanda muke da ku aure shekara daya amma kuka kasa leko ni.” “To ai kin san abun ne sannan ba kwa shiri da shi mu zo wani abun ya faru sai ya zamo matsala, some kin ga yanzu ai komai normal don yanda kike wannan kyallin goshin na san an samu rabo ma ( Hahaha kunji gulma. Hmmm Ni dai Bomboy ba ruwa na idan Haidar yaji ku). Ta yi dariya, “Uhm kwa ji da shakiyancinku ku zo mu ci abinci.” Wajen karfe hudu suka gama shirinsu suka fito za su tafi ta yo musu rakiya har bakin get, megadi yana dan dakinsa yana lazimi, Hira suke yi suna tafawa tare da shewa da dariya. Sai ga motar Haidar ya. [8:35PM, 12/6/2016] : shigo ya danna hon megadi ya taso da sauri ya bude masa get. Haidar ya hango jawahir ba mayafi a jikinta ta yi kwalliya tana ta faman dariya duk sai ya ji kishi da bakin ciki ya dame shi. Yaya za ayi ma ta fito nan a haka? Ga megadi da ‘yan aikin gida suna nan du su gano ta. Lallai ma yarinyar nan. Ya yi parking ya fito gunsu ya nufa kawayenta suka gaishe shi ya kalli jawahir ke me ya fito dake nan? Wa ya ba ki izinin zuwa kofar gida.? Kanta a kasa ta ce, “Kawayena ne suka zo shi ne na rako su. Rakiya ba ta isa ba iya kofar cikin gida har sai kin fito bakin get.? Ya shige ciki ya bar ta a nan. Kawayenta suka ce, “Lallai Haidar yanzu har wani kishinki yake? “To Allah ya sa dai mu jawo miki wata matsalar ba.?” Ta ce, “Haba dai ba komai ai yana da saukin kai shi ke nan kuma fadan ya wuce. “To mu dai mun tafi sai wata rana.” Suka fita ta juyo ta shigo cikin gidan. Yana zaune a falo ta tafi za ta shige daki ya ce, “Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa nesa da shi. “Daman in ba na nan bain da kike yi ke nan ko? Kalle ki yanda kika fita ga megadi da yaran gida duk suna ganin ki ko kin manta cewar ke matar aure ce? To bari ki ji duk da an aura min ke ba tare da ina son ki ba, to hakan ba zai hana ni yin kishinki ba, kuma dole ne na sa miki ido don ganin yanda kike tafiyar da rayuwarki, kada na kara ganin wata kawa ta zo miki kin ba ta fuska bare su zo su bata miki tarbiya ko su rinka zuwa tsegumi su samu damar bugun cikinki kina gaya musu sirrinki ko? Ita dai ba ta ce koami ba ya karaci fadansa ta tashi ta yi shigewarta daki. Tana barin wajen wayar Kausar ta shigo, “Hello Kausar kina lafiya.? “Lafiya lau Haidar shiru banji ka ba. Ya ce, “Kai kausar kin fiya gaggawa, amma ki ba ni adres din gidanku insha Allahu jibi zan zo, ta saki wani ihun murna yayin da take gaya masa adres din gidansu dake Abuja. Suka yi sallama ya ajiye wayar. Washegari yana zaune a office ya kifa kansa da tebir tunanin yanda zai bulluwa da iyayensa maganar Kausar yake yi. Abokinsa ne ya shigo ya sa me shi a haka. Duk sallamar da yayi bai ji shi ba bare ya amsa masa. Faruk ya kwankwasa masa tebir din gabansa. Haidar ya yi firgigit ya dago kansa ya kalli Faruk din ya saki ajiyar zuciya. Ya ce, “Yaushe ka shigo ban ji shigowarka ba.? Faruk ya ce, “Yaushe dama za ka ji ka tafi cikin wannan zurfaffan tunani haka, wai don Allah me yake damunka ne? jiya da yau duk wani sukoko nake ganin ka. Ya ce, “Ga ni nan dai abubuwan ne suka tarar min “Ba dai matsalar jawahir ba, ca nake mun gama wannan maganar da kai. Haidar ya ce, “Ai ni ba zan taba iya abun da ka ce na yi ba. Ciknin zaro ido ya ce, “Ba dai kana nufin har yanzu babu abun da ya hada ku ba?. Aure shekara daya. “To kai me kake tunanin zai faru? kanwata ce fa. yarinya ce, ko hannunta na kama ai raina ni za ta yi.” Faruk ya ce, “Amma wallahi kana daukan alhakinku. Gaskiya ba ka kyauta ba, yaya za ka rinka wahalar da yarinya, kana zaton dutse ce ita ko waliya ce da ba za ta ji sha awa ba? Haidar ya ce, “Ko dai take wahalar da ni tana gasa ni, ka ga dai ni nake gaba da ita ya kamata ta fara neman sulhu da ni, to amma yarinyar nan gaisuwa ce kawai da safe take hada mu. Ga yarinyar ta iya tsara kwalliya komai ta sa sai yayi mata kyau ya yi das a jikinta kamar Aljana. Duk dare yanzu bacci gagarata yake yi, na dinga murkususu ke nan ina juyi sai ka ce dole, ai ba waliyyi ne ni ba, don haka na yanke shawarar aure zan kara a kwanan nan. Faruk ya dafe kirji ya ce, “Aure Haidar! kai kuwa me yayi maka zafi? Ba gwanda ka nemi sulhu da matarka ku dai daita ba. : (Hmmm barshi da kanshi zai sauke wannan jiji-da- kan. Mu dai yan kallo ne kuma yan rahoto. Da fatan dai idan anzo kamen dan leken asiri ba zaku nuna ni ba).
.
((((((((((SALON SO)))))))
(((((PART 16 TO 18)))))
Haba Faruk yaya za a yi na kwantarwa da wannan karamar yarinyar kai. shi kenan na ba da kaina girma kuma ya fadi, ni dai kawai aure zan yi na rabu da ita ta karaci tsiyarta ita kadai. Faruk ya daure fuska alamar ba wasa ya ce, “To kai duk abun da ake gaya maka ba za ka ji ba ko, to shi kenan ka je ka aika ta abun daka ga dama, in kuma abu ya kwabe maka kada ka sake ka nemeni tun da ban isa na ba ka shawara ka dauka ba, “Faruk ya juya ya fice tare da bugo kofar. Haidar ya yi ajiyar zuciya tare da tallefe kansa da hannu biyu, “Gaskiya ba na jin zan iya fasa auren nan, ni kawai zan yi auren nan ne don debewa kaina kewa da sha awa saboda kullum ni na san yanda nake kwana ina cutuwa. To me yayi zafi ni dai ba zan kai kaina ga halaka ba bare na nemi matan banza Allah ya kiyaye mu da aikata zina gwara kawai na yi auren, “Haka dai ranar ya wuni babu wata walwala. Alhaji Sa’adu mashi, babban ma’aikacin gwamnati ne wanda aiki yake yawo da shi ko ina a Nigeria. A haka ne ya zo Kano inda ya yi gida ya tare da iyalansa. Da yake makotaka suke da gidansu Haidar to sai shakuwa da aminci suka shiga tsakaninsu. Kasancewar Alhaji Sa’adu ba shi da wani dan uwa a garin kano to da ya samu Abbansu Haidar sai ya rike shi ya zama dan uwanshi na kut da kut. Faruk da Haidar sa’o’in juna ne tare suka ta so iyayensu suka sa su primary tare, secondary ma tare Faruk da Haidar sun shaku da junansu. Abun ya wuce abotaka ya koma ‘yan uwantaka. Bayan gama secondary dinsu ne aiki ya kuma mayar da Alhaji sa’adu gida wato katsina ya tatara iyalinsa suka koma can gida. Hakan kuwa bai yi wa su Haidar dadi ba sai dai don basu da yanda za su yi ne, to daga nan ne Haidar da yaya Abba suka tafi America karatu. Bayan dawowarsu ne da za a bikin bude masa kamfaninsa da mahaifinsa ya bude masa to sai ya tafi garin mashi ya lalubo Faruk. Bayan bude kamfanin nasa ne dai suka ci gaba da zumuncinsu. To faruk din yayi aure yana zaune kusa da iyayensa Yau Haidar bai samu zuwa office ba don Abuja yake shirin tafiya, don haka tun tara na safe ya kammala duk shirye shiryensa ya nufi hanyar Abuja. A hanya ya lodar musu tsaraba. Bai samu matsala dangane da kwantaccen da ta yi masa, tun da ya san unguwar da suke zaune fitacciyar unguwa ce ta manyan kasa masu fada a ji ne. Kausar kuwa a na can an gama duk wani shirye shirye na taryar gwarzon masoyi. An gyara falo an kayatar dashi, ana jiran masoyi. Kausar ta yi wanka ta sha kwalliya da dandatsetsen less. wanda za mu iya cewa kwalliyarta ce, ta fito mata da kyau. Don kun san ba a mummunar mace sai marar gyara. don duk munin mace kwalliya sai an ga kyata. Don naka gyara da kwalliya shine mace. Kausar baka ce amma a yanzu da yake durfafi yin shafe shafe da mayuka ‘yan kanti za mu iya cewa ta koma fara. Doguwa ce, tana da kiba da fati. ba ta da wani girman nono, kanana ne wanda har sun riga sun zube, amma wayayyiya ce ba ta shiga abin da be shafe ta ba akwai hutu da jin dadi rayuwar duniya. Haidar ya iso lafiya. “Ya kuke murna da rawar jiki a wajen Kausar. Tuni ta sa a ka shigar da Haidar dakin da aka wuni ana gyarashi don zuwasa. Tuni aka gama cika gabasa da kololin abubuwan ci da na sha. Can Kausar ta shigo cikin washe baki tana fara’a don bakin yaki rufuwa ta ta ho ta saurin ta ta zauna kusa da shi a guje ta rirrike hannuwansa, “Oh ni ‘yar nan! Allah na gode maka da ka sake hada ni da abun sona, burin zuciyata wato Haidar, ubangiji yanda ka hada mu a nan yanzu ubangiji Allah ka hada mu a gidansa a dakinsa, a matsayin matar aurensa,. Ta shafa. Haidar ya ce, “Irin wannan doguwar addu’a haka to kada ki yi wacce za ki rike ni a gidanku na kasa komawa gida. Ta kyalkyale da dariya ta rinka zuba masa girke girgen da aka yi masa kamar ta ba shi a baki haka ta rinka yi masa. Suna dade suna hira duk wani dan gidasu sai da ya zo suka gaisa. Haka ya shiga ciki ya gaida Babarta da kishiyar babarta. Ta hau da shi falon sama har wajen babanta sai da ya ce, Baban nata yayi murna da ganin shi don ya yaba da hankain haidar a kan zai turo iyayensa don a yi maganar aurensu da Kausar. Babanta ya yi ta sa masa albarka inda Haidar din yake ta malala masa godiya. Haidar sun sauko daga saman sun dawo wajen hirarsu Kausar sai munrna take kamar ta goya shi. Ya sa yaron gidansu ya kawo musu tsaraba a but din motarsa ya yi wa kausar sallama don yana so ya tafi gida kada dare ya yi masa a hanya. Da kyar ta kyale shi ya tafi don gani take yi kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Haidar daga Abuja duk dumbin gajiyar da ya kwaso bai wuce gidansa don hutawa ba sai ya zarce gidansu, yanda ya shiga a hargitsensa Abba da Aunty suka san ba lafiya ba. Bayan sun gaisa ne ya koma gefe daya ya yi zugum da shi yana tunanin ta ina zai fara ne. Abba ya shi, “Haidar lafiya? Me yake faruwa ne? “Wallahi Abba abun da yake damuna ne na rasa ta inda zan bullo masa bare na gaya muku “Ba komai gaya mana ko meye, kana da wadanda za ka gayawa ne wandada suka fi mu? Ai ka ga babu ko? Gaya mana menene damuwarka?” “Wato Abba tun muna America akwai yarinyar da muka yi alkawarin aure da ita, to bayan mun gama na taho gida Abba kuka tayar min da maganar auren jawahir. Abba don kada na bata muku rai ne shi yasa ban yi muku maganar kausar din ba. Ita dai na gaya mata, na ba ta hakuri, to ta tashi hankalinta sosai, to shi ne na kwantar mata da hankalinta da cewar zan aure ta bayan shekara daya. da kyar Babanta ya amince mata shi ne yanxu kuma uban nata ya takura mata da maganar auren, nake so don Allah Abba ku bar ni na aure ta. Aunty kuwa ta mike tsaye cikin fada take nuna shi da yatsa, “Kai ka kiyaye ni, wallahi ka shiga hankalinka. A aura maka ‘yar uwar tawa auren naku shekara daya ka ce za ka yi mata kishiya, to ba ka isa ba ka yi kadan jawahir ta fi karfin ka wulakanta ta.” Abba ya daga mata hannu ya ce, “Aisha ya isa haka. Haidar tashi ka je gida tukunna sai mun yi shawara za ka ji komai. Ya mike, “To Abba na gode ku tashi lafiya. Aunty sai da safe ya wuce sukuku kamar wanda kwai ya fashewa a ciki Abbansa ya ce, ba a yin haka Aisha ki duba ki gani yaron nan ya yi mana biyayya lokacin da muka tursasa shi auren jawahir yanzu bai kamata ya zo da tasa bukatar mu ki biya masa ita ba, kin san ‘ya ‘ya amana ne a hannunmu duk da cewar mu muka haife su to idan muka zalince su Allah fa ba zai kyale mu ba sai ya tambaye mu, to kin ga dai bai kamata da farko mun bi son rainmu mun yi masa aure ya hakura sun zauna sannan yanzu ya kawo bukatarsa mu bi son zuciya mu hana shi, aikin ga ba mu dai dai ba bare lamarin aure da ba ayi masa katsalandan. Abun duniya duk ya dagulewa haidar duk dai da ya ga alamun nasara a wajen Abbansa, to Aunty fa Ai ita za ta zamo babbar matsala. Yana zaune a falon kasa jawahir ita ma tana waje daya zaune kan kujera tana yi wa Sayyid karatun Alkur’ani yana biyawa. Wayar Haidar ta fara ruri ya daga, “Hello Kausar ina gajiya. Ba gajiya sweety, yaya ka dawo gida? “Lafiya lau kausar ai na sha wahalar tafiya dag kano zuwa Abuja a mota kuma a dawo a ranar, ai akwai wahala. Ko da yake ba komai tun da Hausawa sun ce garin masoyi ba ya nisa, duk ranar da Allah ya mallaka min ke na fanshe wahalata…… Wani katutun bakin ciki ne ya tsayawa jawahir a zuciya, rainin hankali wato a gabana ma yake yi wa mace waya? wallahi bai isa ya yi min wulakanci ba, ina zaman dole a gidansa ‘yar sakin fuska ba yayi min bare mu yi hira amma shi ne yake kyalkyala dariya da budurwarsa, kawai sai ta mike a fusace ya riga ya shagala da yin magana a wayar ta fizge wayar daga hannunsa ta doka ta da kasa. Wayar ta tarwatse sai ta ya daki a guje ta rufe kofa duk da haka sai ta fada gado ta sa kuka. (To in banda abun jawahir kukan me kike) Bari dai mu ci gaba labari mu ji me yake faruwa a zukatan guda biyun. Haidar ya bi wayarsa da take tarwatse kan kafet da kallo, “To me jawahir take nufi da za ta fizge masa waya? Kishi take yi ko kuma dai ta fara raina shi ne? Lallai zai yi wa tufkar hanci kada nan gaba abin ya shafi aurensa. Da safe ya gama shirinsa ya sauko ya nufi tebir don yin break ya ga wayam babu break bare alamarsa. Ya kwallawa sayyid kira ya fito da gudunsa, “Ina Antinka?” “Tana daki.” “To je ka ka kirawo min ita.” Ya kirawo ta ta fito yayin da ta durkusa, “Ga ni.” Ke me ya hana ki yin break? Kina nufin haka zan tafi office da yunwa.? Kanta yana sunkuye a kasa ta ce, “Ai ca nake za ka biya ta wajen masoyiyar taka ka ci a can. Ke ba na son shirme kin ji ko, tashi ki je ki hada mana break. Bakin ciki ya ishe ta ba abin ta ce ba za ta yi ba ta sabawa ubangijinta. kawai sai ta mike tana kuka ta nufi kicin din. Sai tausayinta ya kama shi yarinyar tana burge shi ko don biyayyarta. Ta gama soya dankali da kwai ta dafa ruwan shayi sai dammaman kunun gyada da ta yi masa kofi daya kamar yanda yake sha lokaci lokaci. Za ta wuce daki ya yi kirata, “Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa. Ya ce, “Ta so ki yi break. Ta girgiza kai na koshi. Ya daka mata tsawa. “Ta so mana jinkinta na rawa ta mike ya hada mata ruwan tea me kauri ya mika mata. Ya tura mata dankali da kwai da biredi gaba ya ce, “Ki ci da yawa ko yanzun nan ranki ya baci. Haka ta rinka ci ana hawaye yana kallonta sayyid kuwa ya tafi wajen Dela za ta yi masa wanka. Haidar ya gama break dinsa ya mike ya nufi office jawahir ta kifa kanta a kan tebir din ta ci kukanta ta koshi ta gama ta shafe hawayenta ta koma daki. Sayyid ya shigo an yi masa wanka ta shirya shi ya rinka jijjiga ta dole ta fito ta hada masa break ta koma daki. Zuciyarta tukuku take yi mata sam ta kasa samun sukuni a zuciyarta tun daga wayar nan da ta ji haidar ya yi, “Wato ma ina ruwanta ne da wayarsa.? To me yake neman faruwa da ita ne? ke wallahi na gaji da zaman banza a gidansa ya zo mu yi duk wace za a yi, na cire tsoronsa da shayin komai don ni mutum ce ba dabba ba yanda yake da a gidansu haka nima nake a gidanmu. Yau ma dai haidar daga office da ya tashi gidansu ya kuma waccewa a kan maganarsa ta jiya. Abbansa ya ce, Ka kara hakuri Haidar a bi komai a hankai ba a son gaggawa don gaggawa tana daga shaidan. Aunty ta ce, Alhaji ka rabu da yaron nan, nema yake ya tozarta mu ya bata mana zumunci to wallahi ba ka isa ka shiga tsakanina da dan uwana ba. Abba ya ce, “Haidar tashi ka je gida zan je na nemi Daddyn jawahir din na yi masa bayanin komai, na san shi mutum ne me fahimta ba zai kawo komai ba to daga nan sai mun shirya ranar da za mu je Abujan wajen iyayen yarinyar. Haidar ya rissina, “To Abba na gode Allah ya saka da alheri, ubangiji ya kara girma. Ba komai haidar kai dai ka rike amana kuma ka sawa zuciyarka adalci ya yi musu sallama ya tafi. Yau a falo ya samu jawahir tana kallon wasan Hausa. Be kalli inda take ba ya haye samansa. Ita kuwa daman a cike take ta shi jira take yi ya dawo su yi wace za su yi don ta gaji da zaman gadin gidansa. Sai da ta bari ya kammala dun wani abu dayake yi ya dawo falon kasan ya zauna yana duba jarida sannan ta fara magana ba tare da ta kalle shi ba. “Yaya yau dai magana nake son mu yi da kai. Ba tare da ya dago kai ba ko ya bar karatun jaridar ya ce, Uhm ina sauraronki. Ta ce, “Wai menene matsayina a gidan nan ne? “Bai dago kai ya kalle ta ba ya ce, “Matsayinki kike son sani? Ta ce, “Kwarai kuwa.” “Ya ce, “In dai ba mantawa kika yu ba matsayinki yana na kanwata da kuma wai matata ta aure, don wai zance. Ta ce, “To in haka ne me zai hana ka sake ni ko ma huta daga ni har kai da wannan daurin da bai bayin da aka yi mana. Ya ce, mata, “Ai dama ba ni na gayyato ki ba in wanda ya kawo ki ya gaji da zaman naki za ki ga ya zo ya dauke ki. Zumbur ta mike tsaye ta rike kugu ta nuna shi da dan yatsa, “Kai bari ka ji, ni ba irin ballagazayen matan nan ne da ka saba wulakantawa ba, ni na fi karfin wulakancinka, ina bin ka ne gudun kada na sabawa ubangijina da kuma gudun wargajewar zumuncin iyayenmu da nake yi wa biyayya, to yanzu na gaji da zama da kai don ka san ba na son ka a ka ba ni kai, na yi hakurin zaman shekara a gidanka, to yau hakurina ya kare ba zan sake kwana a gidanka ba dole ne ka sake ni. Tana rike da kugu tana yamutsa fuska tare da girgiza jikinta na jin bala’i. Ya kalle ta daga sama har kasa, dariya ce ta kwace masa ya dai daure ya gintse dariyar ya ce, “Ni nan da kika ganni ba zan taba sakinki ba, in kin ga dama ki zauna in baki ga dama ba ki je duk inda za ki amma maganar rabuwa babu don ni ba wawa ba ne. Idan ba ki sani ba ma ki sani aure zan yi kwana nan. Ta dafe kirji, “Aure! Aure fa ka ce? Da gaske kake yi? Wallahi ba zan zauna a gidanka ba bare matar ta zo ita ma ta raina ni, ban da kaddara ma me zai sa na aure ka? Ni me santalelen saurayi da yanzu ina gidansa. Ya mike kuwa cikin sauri zai kai mata mari ta yi saurin kaucewa ya ce, “Ki yi a hankali duk san da kika sake fadar wani namiji a gabana da sunan yana sonki sai kin raina kanki. “Ya yi hayewarsa sama ya bar ta tana kuka. Haka kawai be yi min abun da na nema ba sannan ya ce aure zai yi, wallahi ba zan zauna ba tafiyata zan yi, duk abin da ma zai faru ya faru. “Da sauri ta fada dakinta ta kama hada kayanta tana zuvawa cikin akwati ta turo akwatin da kyar ta kirawo Dela ta ce ta bawa yaron gida ya sawa Haidar a but din motarsa. Cikin rawar jiki ta karbi aiken uban dakinta duk abin da ta san za ta bukata ta sa an kai but. Ta fito da shirinta za ta fita lokacin Sayyid ya tashi daga bacci ya ce, “Aunty ina zaki? Ni ma zan biki. “Ta shafa kansa, “Ka yi hakuri Kayyid zan siyo maka jirgin sama me tashi. Ya makale kafada alamar bai yarda ba. Ta ce, “To je ka dakin Yaya ka ce ya zo mu tafi. Ya ce, “To Ya hau san a guje. Ita ma saurin ta yi ta fice ta shiga motar Haidar ta tashe ta ta tafi ba ta taba tuka mota da kanta ba sai yau, amma ta iya don duk sanda za su fita da direba sai ya koya mata. Haidar yana jin tashin mota ya turo Sayyid daga jikinsa ya mike zumbur sai sannan ya tuna ya bar mukullin motarsa a falon kasa. Ya gangaro falon kasan da sauri yana salati, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji un. Hankalinsa ya yi mugun tashi. “Na shiga uku. Kadda yarinyar nan ta yi wani wajen yanzu idan wani abu ya samu yarinyar nan yaya zan yi da rayuwata? Ga Sayyid ya ishe shi da ihun kuka yana kiran “Aunty Dole Haidar ya dauki wani mukullin motar ya saba Sayyid a kafada suka fita. Ya shiga mota a hankali yake tuki yana kallon hanya ko zai hango motarsa da jawahir a ciki. Jawahir kuwa cikin nutsuwa da tsoron ta gudanar da tukinta har ta zo kofar gidan Inna tayi hon megadi ya bude mata ta shiga ta yi parking ta sa shi ya jidi kayanta da yake but ya shigar mata da su cikin falon Inna. Inna ta ce, Lafiya na ganki da kaya? Ta ce, “To lafiyar kenan. Inna ta ce, “Me yake faruwa ne na gan ki da kaya kuma kin rame a kan san da kuka zo, ko ba ki da lafiya ne? Ta ce, “To ba dole na rame ba an aurawa wanda ba ya so na ni yana ta gasa ni ga shi nan ai yau ya koro ni gidanmu ko.?” Inna ta dafe kirji ta ce, “Shi da kansa ya ce ki taho gidan? “Shi ne mana Inna kullum sai dai ya kira ni da tatsitsiya ko kwaila, ya mai da ni ‘yar aiki na girka masa ya ci ya koshi wallahi sai kwanan nan ya fara yi min magana amma da ko meye sai dai ya rubuto min a takarda sai ni ma na ba shi amsa a rubuce sai ka ce kurame. Inna ta saka salati, “Au ni ina ta murna na zata ciki ne da ke ashe ba wani bayani. Ta ce, “Uhm inna ke nan, to ko matsayin kyakkyawan kallo ba na samu a wajensa duk na yi hakuri na jure to wai yanzu aure zai yi. Inna ta ce, “Aure, lallai ma yaron nan ban ni da shi boye ki zan yi, zan gyara ki na kula da ke har sai kin zama cikalkiyar mace zai raina kansa ne da ni yake zancen. Duk waigen da Haidar yake yi bai hango jawahir ba har ya iso gidansu. Aunty ya samu a falo tana kallon labarun kasa ya sauke Sayyid ya tafi da gudu ya fada jikin Aunty yana kuka. Aunty ta rungume shi tana cewa, “Haba Auta me aka yi maka kake kuka.? “Bayan Auntyn gidan Yaya ce ta gudu ta bar ni. “To yi hakuri tun da an kawo ka wajena ka ji.” Ya daga kai Ta kalli Haidar, “Ina jawahir din take?” Ya ce, “Wallahi ban san inda ta tafi ba, kawai na ji karar mota, ashe ita ta fice ta yi tafiyarta. Aunty ta dafe kirji, “Ita kadai ta ja motar ta fita? Wato ka yi mata maganar auren naka ko? To wallahi tashi ka fita duk inda take sai ka je ka nemo ta. Abbansa ya shigo, “Lafiya na gan ku haka? Aunty ta ce, “To ba dole ka ganmu haka ba, ya salwantar min da ‘ya. “Wa ce ‘ya?” Jawahir mana, wai be san inda take ba. Abba ya yi saurin zama don jin faduwar gaba da ya yi, ya kalli dan nasa, “Haidar me ya hada ku har ta fita?” Haidar ya ce, “Ni kaina ban san abun da na yi mata ba, ta ji dai ina waya ta kwace wayar ta tarwatsa ta sai na mike na hau sama, to ban ankara ba na ji tashin motata. Aunty ta ce, “Uhm ka ji ba, in ban da rainin hankali yaushe zai je gabanta yana waya da budurwa suna hirar aure. Ni na san wannan rawar kan da kake yi sai ka jawo mana tashin hankali, ka ga in ka ga ba hali ka sakar min ‘ya mu ba neman kai muke yi da ita ba. Abba ya ce, “Duk haka ba ta taso ba, ku kwantar da hankalinku da safe zan je gidan na su sai na ji dalilin tahowar tata. Yanzu tashi ka tafi gida. Aunty ta ce, “Ba fa tabbas din gidan ta tafi dole ne a yi binkicen ta tun daga yau.” Ta dauko mayafinta ni bari na je gidan na su yanzu. Ta shiga mota direba ya ja ta suka nufi gidansu jawahir. Tana shiga gidan ta tarar da mommy da Nasir da su Auwal da Sani. Aunty ta zauna duka suka gaishe ta cikin fara’a ta amsa tana wasa da dariya ta su. Suka gaisa da momy da tsokana irin wasan nan na kannan miji. Ta ce, “Yaya kuwa yana nan? Momy ta ce, “Eh yana sama. Auwal je ka gaya masa Aunty ta zo, “Ya hau da saurinsa ya sauko ya ce, “Ki hau saman Ta hau. Bayan ‘Yan gaishe gaishe da suka yi sai ta gyara zama ta ce, Yaya ina Jawahir din?” Cikin mamaki ya ce, “Au ta zo ne? “Uhm wai rigima suka yi da mijin nata ta taho. Ya ce, “Ikon Allah ai ni ban ma sani ba bari na tambaye ta Ya dau waya ya kirawo momy ta yi sallama ta shigo ta nemi waje ta zauna. Ya kalle ta ya ce, “Ina jawahir take? Momy ta ce, “Tun da aka yi auren ta ba ta zo gidan nan ba. Wani abu ne? “Wai sun yi rigima da mijin ta taho. Momy ta ce, “Oh ni ‘yasu, yara ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba, yanzu duk fadan nan da aka yi wa jawahir sai da ta sabawa nijinta. Aunty ta ce, “A’a ai ba laifinta ba ne, da ai lafiya suke zaune auren nan da ya rakitowa kansa duk shi ya hargitsa musu zaman.” Momy ta ce kin ji irin shashancin ko, ai komai na Allah ne, namiji da aka halicce shi don mata hudu ka hana shi kara daya. Aunty ta ce, A’a ba ta fa da laifi ko ke da kika girma da Yaya ai ce zai kara aure da sai kin hana mu sakewa bare ita da ga yin aure shekara daya a ce namiji zai maka kishiya, ai dole a ji kanku. Dady ya ce, Ai kun san ma ba za ta zo nan ba tun da ta san ba goyon baya za ta samu ba. Tana gidan Inna, tun da ta je hannun Inna kuwa kwato ta sai wani ikon Allah. Aunty ta ce, “Ai maganinsa kenan wallahi gwanda ta hora shi tukunna. Momy ta ce, “A’a ni dai ba na son son kai don dai kin ga ‘yarki ce kawai kuke son ga sa masa gyada a hannu. Dady ya ce, Ba me wahalar min da da, duk zan tara su na san meye matsalarsu. Hankalin Haidar ya kara mummunan tashi yayin da ta bayyana cewa jawahir ba ta gidansu. Goma na dare Haidar ya isa gidan Inna a gigice yana neman jawahir din. Inna ta fututtuke ta ce ita yaushe rabon da ta ga jawahir ma? Wallahi ya je duk inda jikarta ta take ya nemo mata ita in ba haka ba kuwa ya gamu da fushinta. Haidar kamar zai yi kuka magiya yake yi wa Inna idan ita ta boye jawahir ta fito da ita don ya ga motarsa a gare jin gidanta wadda da ita jawahir din ta fito. Inna ta ce, To sai dai in zuwa ta yi ta ajiye motar ba ta shigo ba ta fice, “Ta ce, “Na gaya maka wannan kame-kamen ba zai yi maka ba, ka je ka nemo min jikata. Sha daya na dare ya bar gidan Inna ya isa gidansa. Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, amma haka ya kwana yana juyi da tunanin inda za a ga jawahir. Ga yunwa ta gallabe shi ga ba abinci, shi kuwa ko ruwan shayi be iya dafawa ba, bare ya dafa ya sha. Haka ya yi ta juyinsa har aka yi, sallar asuba. Daga masallacin gidansu ya taho a motarsa. Abba ya yi mamakin ganinsa inda yake tambayarsa, “Lafiya haka da asuba.? “To Abba ina zan iya samun sukuni ba a fa ganta ba. “Ba ka ce ka ga motar gidan Inna ba.?” “Ai Inna ta ce ita ba ta shigo mata ba ajiye motar ta yi ta san tana waje. Allah ya kyauta, Abba ya lallaba shi ya yi wanka suka yi break tare. Abban ya dauko shi suka yo gidan Inna wai ko za su ga jawahir din. Amma Inna tana jin tsayuwar mota ta tura ta wani dan daki ta yi zamanta a falo. Abba da Haidar suka shigo duk yanda suka yi don su bigi cikin Inna su ji ko jawahir tana gidan Inna ta fututtuke ta ce ba ta zo mata ba. Dole suka hakura suka yi mata sallama suka fita. A mota kawai Haidar sai ya sawa Abbansa kuka, “Don Allah Abba ka tainaka min a ga jawahir, yanzu in ban gan ta ba ai na shiga uku ya zan yi da rayuwata? Ya dafa kansa ya ce, Ka yi hakuri Haidar za a ganta ne insha Allahu. Bayan fitarsu Inna ta yiwa danta Aminu da yake Abuja waya ta gaya masa komai ta ce tana so ta turo masa jawahir nan kada ya sake ya ce tana gunsa. Aminu ya amsa da to! Ya ce da kansa zai zo tararta filin jirgi. Jawahir ta gama shirinta a boye direban Inna ya kai ta filin jirgi ta hau zuwa Abuja sai da ya ga tashinsu sannan ya dawo ya shaidawa Inna. Can kuwa Uncle dinta yana Airport yana zaman jiranta. Yana hango ta ya taro ta da murna suka rankaya zuwa gidansa matarsa Maryam ta yi farin ciki da ganin jawahir, don Maryam mace ce mai faran-faran da son jama’a ga ta wayayyiya. Irin gogaggun matan nan ne wadanda suka san makamar kama da namiji. Ba bata lokaci Uncle ya karbi takardun makarantar jawahir ya samar mata University of Abuja. Ba bata lokaci jawahir ta zamo daliba a jami’ar. Jawahir an shiga cikin wayayyun ‘yan matan jami’a ta goge ta kile, ta kara kyau da girma babu yanda za a yi wanda bai yi mata cikakken sani ba, ya gane ta, don yanda Maryam ta ke gyara ta kamar ‘yar cikinta don wani magunguna da tsumi na mata da take dibga mata tana sha. Sai maganin ciko da nono da tsaitsayar da su don har ya zube, shi take ba ta tana sha. Kasancewar hankalinta a kwance yake ta yi ‘yar kiba ta murje jikinta mulmul kamar na jariri, sabon haihuwa. Kirjinta ya cika fam yana tsaitsaye ba shi da alamar rankwafawa, duk wanda ya kalle ta sai ya juya ya kara kallonta saboda tsabagen haduwa da wani shirtaccen kyau da ya kara bayayyanar mata.
(((((((SALON SO)))))))
(((PART 19 TO 20))))
HAIDAR ya kasa samun nutsuwa dole ya nufi gidan abokinsa Faruk don yanke shawarar da za ta fisheshisu. Yana zaune a falo Faruk ya hada kai da guiwa yana ta tunani tare da karanta wasikar jaki. Faruk ya shigo falon tare da yin sallama. Bai jira an amsa sallamar ba don ya san ba zai samu ba ya karaso ya dafa kafadar Haidar ya ce, Me yake faruwa ne da kai aminina? Wace matsala ce kuma take kokarin danno maka kai ne? Kai da za ka yi auren ke ce raini. Ya ce, “Kyale ni Faruk abin duniya duk ya dame ni, ko ka san jawahir ta gudu ban san inda ta nufa ba. Faruk ya dafe kirji ta gudu fa ka ce? Me ya hada ku, ko na ce me ka yi mata? “Uhm kai dai a yi sha’ani, wai daga na yi maganar aure zan yi sai yarinya ta gudu. Faruk ya ce, “Ai madallah ka ga irin abin da nake jiye maka ko, to ai ga irin ta nan yanxu sai ka je ka bunciko ta a duk inda take. Haidar ya ce, “Wallahi ni dai ina zaton tana gidan Inna don mota ta da ta dauko ta taho da ita, na ganta a gidan Innan. Sai dai amma Innan ta kafe ta ce jawahir din ba ta gidanta. Faruk ya ce, Ka ga taso mu kaje kawai mu shammace ta ba tare da munyi sallama ba mu shiga kawai in tana ciki za mu gan ta. Suka mike suka yi gidan Inna Haka suka danna kai falon Inna babu sallam abun mamaki ba jawahir sai Inna da ta yi zumbur za ta tashi ta ce ni har kun tsorata ni lafiya kuka shigo min haka babu sallama? Faruk ya durkusa yana gaishe ta Haidar kuwa zubewa ya yi a kasa yana yi wa Inna magiya inna don Allah don Annabi Inna ki taimaka ki fito min da jawahir. Inna ta ce, Haidar me kake fada ne? Ni na san inda jawahir take ne? Faruk ya ce, “To ai ni abin da ya fi ba ni mamaki ya a ka yi motar ta zo nan gidan, “Inna ta ce, “Ni dai ina zaune aka aiko min da mukullin motar na ajiye na zata ma ko tare suke da Haidar din motar ta lalace musu suka ajiye ta, su je su dawo. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta ce ga mukullin motarka nan kada ku sake zuwar min idan ba jikata kuka gano min ba. Haidar cikin marairaita kamar zai yi kuka ya ce, “To yanzu Inna ya za a yi da neman jawahir din.? Cikin fada ta ce, To ya za a yi kuwa? Da ka rike ta hannu bibbiyu ai da haka ba ta faru ba ko? Yanxu da ka yi sakaci da ita ta bata ai ko wa sai ya huta. A dauki yarinyar nan cikin girma da mutunci ‘yar uwarka ta jini a baka amma ka rinka wulakanta ta. Ya yi saurin cewa, “Wallahi Inna ba wulakantata nake ba wai don kawai na ce, zan kara aure shi ne ta yi tafiyarta. Inna ta ce, “Uhm ai ka ga yanzu ta bar maka filin gidanka ka fi sakewa kai da Amaryar taka sai ka je kai ta yo auren. Faruk ya ce, “Inna hakuri za a yi in dai an san inda take din a fada mana. Ta ce, “To ban sani ba ku tashi ku ba ni waje. **** Maganar jawahir kuwa tana gidan Ankul dinta ta dage da karatu don makaranta biyu zan ce take yi. Tana zuwa jami’a yayin da kuma Ankul dinta ya daukar mata lakcara guda yake dada tunasar da ita da nusar da ita halayyar dan Adam, yanda ake iya zama da su sannan yana koya mata dabaru na iya kasuwanci da yanda za ka sarrafa kudi duk kankantarsu don juya su. Ta bangaren jawahir kam ma iya cewa Alhamdullihi, don komai a ka gaya mata ya zauna a kwalkwalwarta kenan da yake yarinya ce me kaifin basira da kokari. Jawahir ta gama nazarin abun da aka yi musu lakca a yau ta mike a gajiye ta shiga toilet ta yi wanka ta gama shirinta ta fito falo ta samu Auntynta a zaune. Maryam ta kalle ta tayi murmushi, “Tubar kallah ‘yar gidan Ankul ba dai kyau ba, zo ki zauna na dora miki inda muka tsaya don so nake yi ki mallake Haidar tsab yanda ya raina ki yake kiranki da tatsitsiya ko kwaila to yanzu ki zame masa dan hakin da ka raina. Yanzu abin da zan fara miki da shi shine zan koya miki kissoshi kala-kala don haka dauko littafi da biro ki rubuta komai don gudun mantawa. (Saboda haka idan kuna so nima na fada muku to kowa ya/ ta dauko biron shi/ta domin nima saida na rubuta sannan na iya kawo muku badon haka ba……..hmmm. Gani nan ina zagayawa fa. Hhhhh su o’o akwai akwai tsoro ji harda rawar jiki kar na ganta ba paper). Jawahir ta mike ta dawo da littafi da biro, “To yanzu za mu fara da kissar tsafta don ita ce kan gaba a kan komai. Ki kasance mai tsaftar gidanki ko da yaushe cikinsa da wajensa. Kicin dinki ya zamo a gyare a share, a goge ki turara masa turarukan wuta me dadin kamshi. Toilet dinki ya zamo kullum cikin gyara idan kika wanke kika goge komau kika cire yana ki masa nasa turaren wutar na musamman ya kasance cikin kamshi wanda mutum ya yi bahaya wannan kamshin zai kashe masa jin warin bahayan nasa, idan ba ki da lokacin yin wanki da kanki to a ajiye almajiri idan sun kai kala biyu zuwa uku ki ba shi ya wanke ya goge miki, idan kin tashi sai ki turare kayan naki da turaren kaya sannan ki jera a kwaba. Sai kuma kwabar ki sa mata turaren kaya don gudun warin ruma da dai sauransu. Ki kasance mai kwasar shimin mijinki, gajeren wandonsa, hankijinsa da dai wani karamin abu da yake amfani da shi ki wanke, ki goge su ki turare su da turaren kaya ki adana masa su. Idan kin shiga wanka ki rinka amfani da daddadan sabulu me kyau da dadin kamshi. Ki rinka cuda hammatarki, kasan nonuwanki, matse-matsin cinyarki, ki rinka wanke gabanki sosai da sabulu me kamshi, duk wani lungu da sako na jikinki ki wanke shi ki gyare shi fes in da ko ina mai gida ya sa kansa zai ji kamshi. Ki kasance ko yaushe cikin gamsasshiyar kwalliya, ki daure da asuba idan kun yi sallah me gidanki zai ja ki ku koma gado ku kwanta, to ki yi kokarin hana kanki bacci. Har sai shi ya yi sai ki janye jikinki a hankali ki tashi ki nufi kicin don hada muku karin kumallo. Kada ki yi masa break kala daya saboda saurin ginsa ki yi masa kalolin break kowanne ki zuba a fulas gudun kada ya huce. Daga nan ki jere su a tebir ki gyara wajan ki da turare ko ina da daddadan kamshi me sanyaya zuciya, sai ki je ki yi wanka ki bata lokaci wajen yin kwalliya wannan fa kwalliyar safe ce ta barka da tashi me gida. Za ki saka les ko atamfa ko shadda ko boyal duk dai wanda ya samu, za ki feshe jikinki da kalolin turaruka masu kyau da dadin kamshi wanda har za a kasa tantance wane irin kamshi kike yi, to sai ki nufi dakin maigida. Ba a tashin miji da hayaniya ko surutu ko ki yi ta jijjiga shi kina kiran wane! ka tashi lokaci ya yi, in kika yi irin haka za ki bata ran maigidanki. Abin da kawai za ki yi shine da kin shiga dakin mijinki kin ga yana bacci ga lokacin tafiya Office ko kasuwa ya kusa, to sai ki zauna a gefen gadon ki sa hannuwanki kina shafar fuskarsa kisa bakinki kina hura kunnunsa a hankali kina shafa fuskarsa tare da dan jan karan hancinsa. Ko ki fara shafar kasan mararsa kadan-kadan. To za ki ga ya tashi a nitse ba tare da magagi ko tsaki ba, da ya mike ya shiga toilet ko kafin ya fito sai ki yi saurin gyara gadon ki debo masa kayan da zai sa hade da best da gajeran wando da dan hankici duk kuma ki feshe su da turaruka masu dadin kamshi ki debomasa takalmansa ki goge su fes, da ya fito daga toilet ki yi gaggawar daukan tawul ki rinka tsane masa ruwan jikinsa sannan ki debo mayukan da yake amfani dasu ki rinka shafa masa a hankali kina yi kina ba shi labari na ban dariya a hirar nishadi. Ki taimaka masa wajen sa kayan nasa, ki sa karamin kum ki taje masa sumar kansa, ki dada dauko turaruka ki kuma feshe shi da su, ki sa masa gilas idan yana da ra’ayi. Ki riko hannunsa ku taho zuwa kan tebir kuna tafe a hankali kina yi masa rausaya tare da yawan shigewa jikinsa har ku iso tebir din. Ki rinka zuba masa komai kina turo masa gabansa kada ki damu da sai kin ci a lokacin, ki rinka hada masa abinci me yawa a gabansa ki rinka tura masa kina yi masa shagwabar bai ci da yawa ba, ko ki ce ke ba ki yarda ba sai ya cinye da sauran abubuwan da za su ja hankalinsa ya saki jikinsa sosai ya ci abinci ya koshi. Idan ya mike don ya tafi office ki roko masa jakarsa kina yi masa ‘yar shagwabar Honey da ka tashi daga office ka yo gida kada ka tsaya wani wajen ka ji. Honey idan ka isa office ka tsaida hankalinka ka yi aikinka a nitse kada ka yi tunanin komai bare ya sa min kai a damuwa. Za ki ga ya rungumoki tare da shi miki albarka duk kuma inda yake hankalinsa yana kanki Allah Allah zai yi ya dawo gida don ya tarar da ke. To da ya tafi office ke kuma a wannan lokacin za ki samu ki yi baccinki kafin lokacin girkin rana ki kula me mijinki ya fi so, me ya fi sha awar ci don ki kiyaye wajen girka masa su, shinkafa da miya, ko tuwon shinkafa da miyar taushe, ko danyar kubewa, ko miyar agushi, ko miyar wake da ganye, ko tuwon dawa, ko na masara, tuwon semovita ko ki daka masa sakwara, ko ki dafa kuskus ko taliya, zaki hada masa da soyayyen naman kaji ko gasasshen naman kasuwa ko farfesun kayan ciki, ko farfesun kan rago ko na jelar sa ko farfesun naman karamar dabba, ( A nan ana magana ne idan mijinki mai hali ne, idan kuwa ba mai hali ba ne sai ki yi masa abin da kika tabbatar yana jin dadinsa dai-dai rufin asiri) To idan kika duba abin da ya fi so a cikin yi masa kika gama komai kafin ya dawo, ki dada gyara gidanki ki turare shi da nau’in kamshi kala kala, ki shiga aiki sake fesa wanka sai ki yi kwalliya ki hade da siket ko riga da wando ko doguwar riga ko dinkakken shadda, ko atamfa, boyal, yadi, material, da dai sauransu, to ya kasance karamin dinki ne dai-dai jikinki ki saka wanda da zarar maigida ya dawo za ki tafi cikin salon murna ki ringume shi kina me yi masa barka da zuwa. Ki fara raka shi dakinsa ki cire masa kayan jikinsa ki hada masa ruwan wanka da turaren wanka a ciki da ya shige tolet sai ki kwashe kayan da ya cire ki rataye masa a anga. Ki fito masa da kanana na shan iska. Da ya gama shirnsa ya fito sai ki zo a nitse cikin dabara ki rinka loda masa abinci yana ci kina fara loda masa wani yanda zai ci ba tare da ya gane ya ci da yawa ba. Kina zuba masa sanyayyen abin sha yana ci yana sha, har sai ya koshi ya yi kat sai ki jawo shi ku baje kan kafet ko kujera kuna wasanni da hirarraki masu dadi ko kallo ku, ki rinka karanta masa labarai masu dadi, amma ki kasance ko yaushe kina manne a jikinsa ki rinka yi masa shagwaba kina mai da kanki karamar yarinya a gabansa kina zama doluwa marar wayo ki rinka sa yin dan sokoncin zai rinka sa mijinki dariya, to yawaita masa irin wannan abubuwan shi zai kara muku shakuwa da fahimtar junanku, za ku kasance cikin bege da son junaku ko da yaushe. Idan kin tabbatar kin wa mijinki lodi da abincin rana to yunwa ba za ta gallabe shi da dare ba, don ba a so da daddare a ci abu me nauyi an fi so a ci irinsu hadin salak, sharfar taliya me romo gasasshen nama, ko hanta ko zaka, farfesun kayan ciki ko na naman romon kai, ko na jelar sa ko naman karamar dabva, kai da dai duk abin da Allah ya hore muku marar nauyi. To kinga wadannan duk inya ci va za su yi masa bauyi a ciki ba bare su hana shi su kuni su takura shi wajen aiwatar sa sunnah Jan hankalinsa ta suffofin kwanciya kala-kala. Duk abin da kika kula ya fi so to ki lakanci abun duk sanda kuke tare ki rinka kirkiro wasu abubuwan ma da bai san da su ba. Ki saki jikinki da shi ki cire kunya ki rinka sarrafa shi kina dan kukan kissa tare da kiran sunansa a hankali kina hadawa da kalaman soyayya don tafiyar da imaninsa. Ki kasance cikin yawan shan kunun aya, shan zuma, shan rake, lemon zaki, kankana, gwanda, abarba, nono, dabino, cukwi, tufa, inibi, kin ga wadannan ki kasance cikin yawaita cin su ko da yaushe don suna karawa mace ni’ima da amfani sosai a jikinta. Ki nemi garin bagaruwa gwangwani daya, garin kurna gwangwani uku, garin habbatus sauda rabin gwangwani, garin dakakken dabino ki rinka samun busasshiyar aya ki daka sai ki hada su waje guda ki samu lafiyayyen nonon shanu marar tsaki kina diban wadannan kayayyakin da kika hada kina damawa da nonon kina sha, to wannan shi ne sirrin yanda kika ga nonuwanka sun cuccuko sun yi manya suna tsaye ba su da alamar rankwafawa. Jawahir ta ce, “Au Aunty kina nufin garin nan da kike ba ni damamme da madarar shanu yana da nasaba da cikuwar nonuwana?” Aunty ta ce, “Kwarai kuwa shi ya sa kika ga ina yawan gasa mana naman karamar dabba ruwa ruwa da kuma romon kai da farfesun wannan sirrika ne na mata. Duk abubuwan da na lissafo a baya su suke bamu ni’ima a jikinmu mu mata suna sa ihu kyan fata, yawan, amfani da man zaitun da habbatus sauda suna sa fata ta yi mul-mul da santsi kamar ta jariri.” Jawahir ta ce, “To Aunty ni da ba a gidan miji nake ba amma kike ta dirka min magunguna da tsumi ina sha. Kuma kullum sai kin sa ni na yi turare na tsugunno da na jiki, meye fa’idar hakan.? Ta dafa kafadarta daya ta ce, “Diyata ke nan, ai duk wannan shiri nake yi miki nake tsumaki don duk sanda Haidar ya kusance ki to haihaita haihaita sunyi sallama da kowacce irin mace don ba me iya gamsar da shi sai ke, na gaya miki Haidar sai ya dawo tafin hannunki, sai yanda kika juya shi. Jawahir ta fada cinyarta tana kyalkyala dariya, “Na gode Aunty sai ya san wadda yake cewa kwaila ko tatsitsiya.”
.
(((((((SALON SO))))))
(((PART 21 TO 24)))):
:
.
Bangaren Kausar kuwa kullum cikin yowa Haidar
waya take safe, rana, yamma da dare ma ba ta bar
shi ya huta ba kan maganar aurensu tun yana boye
mata yana cewa ta jira shi har dai ya fito ya gaya
mata gaskiyar batun matarsa. Amma ya ba ta
hakuri da ta jira iyayensu su dan samu nutsuwa sai ya tada maganar su zo.
Amma da ta kai ta kawo yau da Kausar ta tayar da
hankalinta sosai don gani take yi kamar Haidar din
sake subuce mata zai yi a karo na biyu, ganin
yanda ta samu kanta ne ya sa Haidar ya je yake
tuntubar mahaifinsa da zancen. Abbansa ya ce, Yanxu Haidar ba za ka hakura da
auren nan ba, kana kallon maganar nan ce ta tayar
muku da rigima ga shi ba a san inda ‘yar uwartaka
take ba ko?
Haidar ya ce, Abba ka tausaya min mana, yau
shekarar jawahir daya kenan da barin gidan nan. Abba kana kallon kullum ina hanyar gidan nan
don cin abinci ni ba na iya cin abincin waje bare na
rinka zuwa Otal ina ci. Abba ba ka tausaya min na
samu na yi auren nan ko ni ma na samu nutsuwa a
gidan?
Abba ya ce, “Yanxu kana ganin idan ka yi aure surutun mutane ‘yan uwa da abokanan arziki ba za
su dinga ganin ba ka damu da batan matarka ba?
Ka ga abin zai zama abin surutu ko?
Haidar ya ce “Wallahi Abba jawahir tana hannun
inna don ita ta boye ta.
Ya ce, “Ka tabbata? Daga bakin wa ka ji? Wallahi Abba migadin gidan Inna na ritsa na ce ko
ya gayan gaskiya ko na debo masa ‘yan sanda shi
ne yake gaya min tana gidan Inna to idan na je wa
da Inna maganar sai ta koro ni, ni dai ina ganin
gwara na yi auren in ta ga na yi auren za ta dawo
da ita. Abba ya ce, “To shi kenan Allah ya zaba abin da ya
fi alheri, zan je wajen Alhaji ibrahim din duk abin da
muka tattauna sai ka ji. Ya ce, “To Abba na gode.
Ya mike ya tafi.
Abban Haidar ya samu Dadyn jawahir yake gaya
masa yan da suka yi da Haidar din, Alhaji Ibrahim ya ce, ai ni tun da na ga hankalin Inna bai tashi ba
na san cewa jawahir tana hannunta. To na sha
tuntubar Aisha a kan maganar, to idan a ka bar
maganar ai anyi zalinci kuma an shiga hakkin
Haidar, shekara guda mace ta gudu ta bar ka kuma
a hana ka yin aure, ai da zalunci, ni dai kawai ina ganin in Allah ya kai mu jibi mu je gidansu yarinyar
a gama maganar komai Haidar ya samu mata kawai
Lokacin da suka je Abuja gidan kaninsa Alhaji
Aminu suka sauka tukunna sai da suka huta suka
samu nutsuwa sannan suka dinguma har Alhaji
Aminu zuwa gidansu Kausar. Sai bayan tafiyarsu sannan jawahir ta dawo daga
makaranta.
Antinta take bata labarin zuwansu Dadynta,
Jawahir gabanta ya fadi, “Lafiya kuwa Aunty.? “Eh
to, wallahi ban sani ba don sun tafi tare da Ankul
dinki kuma be gaya min inda za su je ba ko dalilin zuwansu ba.
Jawahir ta ce, “To Allah ya sa dai ba ganowa suka
yi ina nan ba. Amin da ‘yata, don ba na so a raba ni
da ke. Suka yi dariya.
Gidan su Kausar an yi wa su Alhaji kyakkyawar
karba inda iyayenta suka nuna karamci da dattako. A lokacin mahaifinta ya ce ya yanke ranar aure sati
biyu masu xuwa kawai nan fa a ka yi ta murna ana
sa musu albarka. To su Alhaji su daga nan suka
hawo jirgi suka juyo gida shi kuma Ankul din ya
koma gida.
Suna zaune da matarsa a falon suna tatraunawa jikin maryam duk ya yi sanyi da jin abin da ya
kawosu, Alhajin Abuja. Jawahir ta shigo falon tare
da yin sallama ta tafi kusa da Ankul dinta ta zauna
dab da kafarsa a kan kafet ta ce, “Ankul barka da
dawowa.
“Yauwa ‘yata sannu “Ankul me ya kawo su Dady? Ko sun san ina nan ne?
Ya girgiza kai, “Dady bai san kina nan ba kawai
abin da ya kawo su ne, shine na yi musu rakiya.
Ankul Dady bai tambayeni ba?
“Ai bai san kina nan ba ne shiyasa.
“Ankul ko dai maganar auren Haidar ce ta tashi suka zo suka gaya maka?”
“In ban da abinki idan auren Haidar ne ai sai su yo
min waya ba sai sun zo ba ko?
“Eh to, haka ne Amkul'” ya ce, “Kwaso littattafanki
mu gani, “Ta mike ta nufi dalinta.
. * *
Lokacin da suka isa gida suka shaidawa Haidar
halin da ake ciki, a satin suka hada hada kayan lefe
da komai da komai mata suka kai, duk wannan
halin da ake ciki hankalin Haidar yana kan jawahir
don haka ya je ya shirgo mata kayan fadar kishiya akwati uku hadaddun kaya na gani na fada, don
tsadaddu ne a ciki ya ai ka wa Inna ya ce a gaya
mata tun da ta rike masa mata matarsa ta hana shi
to ga kayan fadar kishiya ne don ba a gaya musu
da baki ba. Inna ta karbi kayan ta samu waje ta
adans su. Biki ya zo bangarensu Kausar sun sharyawa bikin
don kalolin fatin da za a yi da komai da komai
Kausar ce ta bude bakinta ta yi ta hidimarta ba ta
jiran ango don ta san halinsa auren ba dada shi ya
yi da kasa ba, ta yi hidima da bidirinta. Fati daya
kawai Haidar ya je shi ma, sai da ta dame shi da magiya sannan ya daure ya je.
Amarya ta tare a gidan angonta Haidar. Babban
falon gidansa na amfanin kowa da kowa ne, a
falon akwai kofa da take kallon gabas ita ce in an
bude an shiga sashen jawahir da katon falo da
dakuna uku a ciki, sai toilet, kicin da suke a ciki. To idan an dawo falon akwai wata kofar da take
kallon yamma wato tana kallon kofar bangaren
jawahir to ita ma in ka shiga katon falo ne da kicin
da tolet shi Amarya Kausar ta shiga, to a tsakiyar
babban falon bene ne wanda za ka hau ka je
turakar megidan, shi ma falon falo ne, da ya kushi dakuna biyu na bacci da tolet da kicin, sai wata
kofa da za ka bi a saman dai, shi kuma makeken fili
ne da aka kayatar da shi aka yi masa rumfa don
hutawa, to nan saman shi ne na megida Haidar.
Zama ya yi dadi tsakanin Ango da Amarya sai dai
sabanin halayya da ta zo bamban ta ango da amarya, don ita Kausar ta samo masu yi mata aiki
har mutum uku ta cika masa gida da mutane ke
nan, shi da yake dan hutu ba ya son hayaniya, to
amma duk dawowar da zai yi zai tarar da Kausar
uwar lalaci a mike a doguwar kujera ko kan kafet
masu aikinta suna yi mata tausa, wani karin abin haushi wai ba ta iya girki da kanta sai dai me aiki ta
yi musu wannan dalili shi yake hana shi cin abincin
gidan, an gudu ba a tsira ba kenan, don kullum sai
ya biya ta gidansu ya ci abinci
Karin abin da yake bawa Haidar Haushi da Kausar
wai gadon da suka kwanta sai dai ta kirawo me aiki ta gyara, wai ina abubuwan da jawahir take
sanya musu a gidan da dakunansa suke kamshi
ne, duk yanzu wannan kamshin mai dadi babu. Shi
wai shi yaya zai yi ne ya dawo da jawahir dinsa ne,
ko don lafiyayyen girkin da take yi masa mai dadi
ga ladabi da biyayya, duk yanda ya bata mata rai ba za ta fasa yi masa girki ba ko ta ki gaishe shi, ga
shi ya yi auren wayayyiya wadda ta yi karatu a
waje amma babu biyan bukata.
Don zamansa da tatsitsiyarsa ya fi sau dubu dari,
duk hanyar da ya bi don Inna ta dawo masa da
jawahir ya bi amma magana daya take gaya masa ita ma ba ta san inda take ba.
. Lokacin da jawahir ta ji labarin auren Haidar ta yi
kuka sosai ta tashi hankalinta har sai da Inna ta zo
Abuja don rarrashinta. Don lokacin Ankul dinta
yana legos. Jawahir kuka take kamar rainta zai fita
Inna kuwa sai sai rarrashinta ta ke yi tana bata
hakuri jawahir ta ce, ni ba wani abu ne ya sa ni kuka ba irin yanda ya wulakanta ni ya yi aure kin
ga ya sake nunawa duniya cewar bai damu da ni
ba kenan. ‘Inna ta tausayawa jawahir don ta
fuskance ta kishi ne yake damunta.
Inna ta ce, “Ki yi hakuri idan kina so ma yau sai na
mayar da ke gidanki. “Da sauri jawahir ta dago kai tare da saurin katse Inna, “Haba-“Haba Allah ya
sawake ai sai ya ga na damu da shi ne ya sami
hanyar da zai kuma wulakanta ni.
Inna ta ce, in dai wannan kike ji kwantar da
hankalinki domin kuwa yanzu Haidar ta damu
dake wanda ba kya zato, auren nan da ya yi ya yi shi ne don na yi fushi na dawo masa da ke ne, ta ba
ta labarin yanda hankalin Haidar ya tashi na
rashinta da yanda a kayi auren har kayan fadar
kishiyar da ya kai mata da irin korar karen da take
yi wa Haidar din, ko ba komai in kalaman Inna ya
sanyayawa jawahir zuciyarta har ta ji tana sha awar ta koma gidan Haidar ko dan ta ga wanne irin zama
suke yi da Amaryar ta sa.
Jawahir ta ce, “Shi kenan Inna ba komai Allah ya
kara rufa asiri.
Kwanan Inna biyu a Abuja ta juyo zuwa gida,
Maryam ta ce da jawahir kada ki damu diyata, ni na san shirin dana yi wa jikinki kowanne namiji in dai
ya dandana ki to ba ba zai iya kusanta ki da wata
mace ba, ni na fada miki haka kuma ki hakura ki
koma gidan Haidar ko don ki ba ni labari gaba,
idan ya dandani zumarki. Jawahir ta ji kunya ta
mike da gudu ta bar wajen. Bayan Inna ta koma gida washegari ta nufi gidan
danta Alhaji Ibrahim mahaifin jawahir, su momy da
Abba Nasir zuwa su Auwal da Sani sun yi murna da
ganin Inna gida ya rude a na ga Inna ga Inna. Inna
ta zauna cikin jikokinta ana wasa ana dariya Momy
kuwa tana ta hidimar kawo mata ababan ci da na sha. Momy ta zauna suka gaisa Inna ta ce,
“Maigidan kuwa yana nan.? Momy ta ce, “Eh yana
nan bari na yo miki magana da shi.”
Momy ta samu Dady rigingine a kan gado yana
kallon sili da alamu tunani yake yi, Ta yi sallama tare
da cewa, “Barka da hutawa. Ya amsa da yauwa: Inna ce ta zo take son magana da kai. “Ya mike
zumbur ya ce, “To gani nan fitowa.
Ya zo ya durkusa har kasa ya gaida Inna, ya ce
“Inna da kanki kika taho maimakon ki aiko na zo.?
Ta ce, “Kamawa ta yi daman na zo a kan maganar
yaran nan ne, ya ce, “Wanne yara?” “Ta ce, “Wanda ka hada auren dole yanzu kuma
kuka je kuka yi masa auren da yake so, ita kun
hana ta wanda take so ta mutu kenan ko.?
Ya ce, “Inna Allah ya ba ki hakuri wallahi ba haka
ba ne.”
Dady ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri kada ki yi haka ba mu san abin da auren
nan ya kunsa ba, kada mu yi wa Allah shisshigi a
lamarinsa.
Yanxu ki yi hakuri ki dawo da jawahir nan gidan
gobe sai na sa a mayar da ita gidanta.
Inna ta katse shi, “Kana nufin a mayar da yarinyar ya ci gaba da wulakanta ta ko?
“Wallahi Inna ni na san ba zai wulakantata ba, in
kika yi la’akari da yanda ya gigice da batan jawahir
din. Inna ai kun hora shi ya horu ba zai sake ba.
Inna ‘ya ‘yan nan duk namu ne wa za mu ki a
cikinsu.? Duk wanda za ta aura ai ba kamar Haidar din ba ko Innata?
Ta ce, “To shi kenan ai kokarinka ni ma na fi son a
karfafa zumunci. “Yauwa Innata yanxu ina jawahir
dina?
Tana can gidan kawunta. Dady ya rike baki “Wanne
kawun nata? “Tana da wani kawunne bayan Auta Aminu?” Alhaji ya ce, “Ikon Allah yanxu duk
binkicen nan da muka yi ta yi tana Abuja.?
Sallamar Haidar da Abbansa ne suka shigo nan fa
Abban ya nufi Innar ya durkusa gaban Inna yake
gaishe ta, “Haidar kuwa gaban Dady ya je ya gaishe
shi, shi ya ki kallon Inna. Dady ya ce, “To ni na amsa gaisuwarka ba ka gaida
uwata ba.?
Haidar dai ya yi shiru bai ce komai ba bai kuma kalli
Inna ba. Abba ya ce, “Ai yanzu ma shi ya je ya taso
ni dole har da kukansa shi fa sai an nemo masa
matarsa jawahir. Tun sallar la’asar ya tashi daga office ya je ya sani a gaba ga shi har bayan issha ya
ki tafiya gidansa shine na ce ya zo mu je wajenka
ko za a sami wani dan labari.”
Inna ta ce, “Daman abin da ni ma ya kawo ni kenan
na zo a karbo min takardar sakin jikata ita ma ta je
ta auri wanda take so.” Haidar ya yi saurin tasowa ya rike kafar Inna don
Allah don Annabi Inna ina jawahir take.?
Ta ce, “Ina
ruwanka da inda take ba kayi aurenka ba, to ka ba
ta takardarta ita ma ta auri wanda take so.”
Haidar ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri ki yi min rai ki dawo min da matata wallahi
zan kula da ita ba za a kuma samun kuskure ba.
“Inna ta ce, “A’a, ka je dai ka rike matarka ita ma sai
ta samu wani.
Haidar ya ce, “Ki rufamin asiri “Inna wallahi ko
cewa kika yi sai na saki Kausar za ki dawo min da jawahir sai na sake ta, don ni jawahir ta fiye min
kowace mace.
“Inna ta ce, “Ni da kake fushi da ni ba ka kula ni. Ya
yi saurin cewa, “To yi hakuri mu shirya don Allah
Inna jawahir tana ina.?
Inna ta ce, “Jawahir tana Abuja gidan kawunku tun washegarin ranar da ka koro ta daga gidanka na
tura ta can. “Tuni Haidar ya mike ya nufi bakin
kofar waje.
Abbansa ya ce, “Haidar ina za ka ne? Ya ce, “Abba
Abuja zan tafi yanzu.”
Dady ya ce, “Ba ka da hankali ne ka dubi lokaci fa yanxu karfe tara ka baro matarka a gida ba ka
gudun hakkinta, ka yi hakuri ka koma gidan na yi
wa kawun naku waya gobe za su taho a jirgi insha
Allahu a gobe za a dawo maka da matarka.”
Ya rissuna ya karayi musu godiya sannan ya tafi
gidansa cike da nishadi. Daga nan su ma suka gama tattaunawa a tsakaninsu Inna direbanta ya
maidata gida. Abba ma ya nufi nasa gidan.
Washegari sha biyu na rana a Kano ta yi wa Ankul
da Aunty da jawahir da ma tun goma na safe
kannan Momy suka tafi gidan Haidar don wankewa
jawahir kayanta tare da kade mata kura suka share mata sashinta suka gyara komai.
Dady da Momy sun yi mamakin ganin yanda
jawahir ta girma haka ta kara kyau da haske kamar
ba ita ba. Yaya Abba dai da Nasir sai da suka yaba
kyan nata.
Da yake Inna ma ta zo nan dai aka hadu da Inna da Ankul da Dady da Momi da Anti Maryam a ka yi ta yi
wa jawahir fada da nasiha yanda za ta zauna da
mijinta da kishiyarta lafiya, ki ci gaba da yi wa
mijinki ladabi da biyayya kada ki yarda wata rigima
ta kuma hada ku da mijinki sai mun saba miki.
Gaba daya kuma suka yi ta sama ta albarka. Anti Maryam ta ja ta daki ta dada yi mata bayanin yanda
za ta yi amfani da magangunnan da ta hada mata.
Da magariba suka raka ta gidan mijinta kamar
sabuwar Amarya. An dai sake yi mata fada da
nasiha daga nan kowa ya fashe ya barta.
Ta shige sashenta ta kuwa garkame kofa sai karfe goma na dare Haidar ya shigo gidan. Dakin Kausar
ya shiga ya same ta a mimmike a gado ya zauna a
gefenta ya tambaye ta jawahir kuwa ta dawo?
Ta ya mutse fuska tare da tabe baki kai da ka je ka
dawo da ita ba ka san ta dawo ko ba ta dawo ba
bare ni da ban san ta ba, ko na taba ganin ta ne? Be kuma ce mata komai ba ya yi tolet don inda
sabo ya saba da rashin ladabi na Kausar. Da ya
gama shirnsa ya nufi dakin jawahir sai ya ji shi a
kulle sai ya haye samansa ya yi dai-dai a gadon
bacci.
Har ya fara bacci ya ji shigowar Kausar ta bi shi gadon suka kwanta. Da safe jawahir ta riga su tashi
don haka ta hada birek dinta iya wanda za ta ci ta
gyara babban falon nan da dakunanta kamar
yadda ta saba ta turare su kamshi ya wadaci ko ina
ta shiga ta tsala wankanta da kwalliyarta ‘yar
ubansu. Shadda ganila ta saka wadda ta sha dinkin surfani
duk bulu da yalow da yake kwambineshin ce, ta
sha a don gwal fuskar nan tata sai sheki take tana
shainin. Ta zama cikakkiyar mace sosai kirjinta
kamar ya fashe don cika. Jikinta kuwa wani fitunan
nan kamshi ne yake tashi kamar an yi barin turare a jikinta. Ta fito falonta ta zauna, ba babban falo ba.
Ta dauki break dinta za ta fara ci kenan ta jiyo taku
an yo sashenta.
Haidar har ya tashi ya yi wanka ya gama shirnsa
cikin kayatacciyar shiga ta alfarma kamai yanda ya
saba, amma gimbiya Kausar ana gado a kwance ana ta sharar bacci.
.
((((((SALON SO))))))
((((((PART 25)))))))
:
.
Yana saukowa babban falon ya ji fitinan nan
kamshi jawahir mai har gitsa masa kwalkwalwa ya
yi hamdala ga ubangiji yayi godiya ga Allah da
jawahir ta dawo hannunsa
Bai ganta a babban falon ba don haka ya yi sallama
a nata falon ya tura kofar ya shiga. “Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya
hallici wannan kyakyyawar budurwar yarinya sai
ka ce balarabiya. Anya ba aljanu ne suke
yaudararsa suna neman bude masa ido ba.?
“Me ya sa kika tafi wani wajen ba da izinin mijinki
ba har tsawon shekara daya? Kina ganin kinyi dai dai kenan? Ko kin manta aure kike yi? Ya za ki da
dumbin zunubin tashin hankalin da kika sa mijinki
a ciki.?”
Ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka don Allah
yaya kayi hakuri ba zan sake ba. Ya ce, “Shikenan
ba wani abu sai dai ki kiyaye gaba. Kin ga yanzu ba mu kadai ne a gidan ba kina tare da abokiyar zama
don haka ki kiyaye kin san ba na son hayaniya
bare abin da zai daga min hankali. Shiru ta yi ba ta
ce komai ba don ta san idan ta yi magana hawaye
ne zai zubo don wani dunkulallen abu da ya tokare
mata makogaro, ni na san ba komai ba ne sai kishi. Ya ce, “Ba ni break din na ci, “Ta mike tsam ta kai
masa gabansa ta durkusa tana hada masa shayin
ya yi kauri da madara, bonbita, neskofi, da
sauransu. Ta bude masa fulas din soyayyen dankali
ne da wainar kwai, sai gasasshiyar kaza da ta gasa.
Ya ce, “Je ki falo na ki dauko biredi. “Ta dan yi dum ya ce, “Ba ki ji ba ne? Ta ce, “Yaya matarka fa tana
saman?
Yace, “Ba komai je ki, ki dauko min ai bacci take yi.
Haka ta tafi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki
shi dai yana tsananin kaunar jawahir yarinya me
tsananin hankali da biyayya ga saukin kai ga kuma uwa uba ta hada komai da yake tsananin SO a jikin
mace.
Jawahir dai har ta hau sama ta sauko ba ta ga
matarsa ba. Ta shigo falon ta da siririyar sallamarta
ya amsa mata ta zo gabansa ta durkusa ta miko
masa, ya ce, “To zauna mu sha ta girgiza kai, ya hada kai tare da cewar ba na son gardama zauna
mu sha.
Ta zauna suka fara birek Haidar danna birek dinsa
yake yi yana ci sosai don yaushe rabon da ya yi
break ma a gidansa tun jawahir tana nan.
Ita kuwa a yangace ta ke ci kamar mai cin magani ya kalle ta ya ce, “Ke ba za ki bude baki ki ci ba ne?
Wato kin fa dawo za ki rinka kin cin abinci ki kuma
ramewa ko? Can da yake suna tursasa ki ki ci ai ga
shi nan kin yi kiba to ni ma na daina kyale ki dole
na matsa miki ki ci ki koshi. Haka ya takura ta ta ci
da yawa. Daga nan ya fita ya tafi office cikinsa da koshi.
Jawahir kuwa ta rufe kofar falonta ta yi zamanta a
dakinta. Dan haka ba ta san wainar da suke toyawa
ba. Da ta ji yunwa ragowar birek dinsu na safe ta
dauka ta ci ragowar kazar da Yogourt roba biyu ta
ji ta koshi kuwa. Shi kuwa Haidar a office duk ya kasa samun sukuni
ganin yanda jawahir ta koma. Karfe shida ya tashi
daga office ya yi gida. Ya yi sallama falon shiru ba
kowa bare a amsa masa. Ya haye samansa ya tube
ya yi wanka ya dauro alwala ya yi sallar magariba
ya sako kananan kaya ya sauko kasa ya shiga dakin Kausar.
Tana tare da ‘yan aikinta suna aikin bautarsu na
matsa mata kafa wannan abu yana konawa Haidar
rai.
Suka yi gaggawar fita daga dakin. Ya zauna tare da
cewar, “Ina abincina.? Ta ce, “Na ga ba ka cin abincin masu aiki shi ya sa
ban ajiye maka ba, ya ce, “Okey kin kyauta. “Ya
mike ya fice kawai ya shiga dakin jawahir shiru sai
dai ya ji motsin ruwa a bandaki wanka take kenan,
don haka ya nemi gefen gadonta ya kishingida
yana shakar daddadan kamshin da dakin ya ke yi. Jawahir da ba ta san da mutum a dakin ba ta gama
wankanta ta dauko tawul iya gwiwa ta fito gashin
kanta duk ya bazu ya manmanne mata a fuska ta
bude kofar tolet din ta fito. Tana ‘yar wakarta ta
nufi gaban mudubi. Subhanallahi! Ai tuni hankalin
Haidar ya so gushewa don ganin kyakkyawar kirar jawahir, jiki mulmul da shi ga shi jajir santsi yake yi
da sheki, santala santalan cinyoyinta kamar na
Baturiya.
Ta zauna gaban mudubi ta fito da mayukanta da
hadin turarukanta ta fara mulke jikinta. Sam ba ta
kula da wani a dakin ba tana shirin yaye tawhul din don shafe jikinta sai ta hango kamar mutum ta
mudubin tuni ta razana ta yu kara cikin
dimautacciyar murya da takaicin rashin kwancewar
tawul din ta ya ce, “A’a jawar meye haka?
Ta ce, “To Yaya ai tsoro na ji ban san ka shigo ba, ya
ce, “Okey sorry, sorry je ki ki gama shirinki. To kuma sai ta kasa shirin a gabansa sai daya dakin
ta shiga ta karasa shirinta ta fito cikin doguwar riga.
Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan yarinya da
kyau take ga iya diresin kamar aljana. Abun da
Haidar yake fada kenan a zuciyarsa. Har ta zo
gabansa ta durkusa ta ce, “Sannu da zuwa yaya.” Ya ce, “Yauwa jawahir kin ci abinci? Ta girgiza kai
ya ce, “To me kika ci.?
Ta ce, “Yogourt da ragowar naman daxu. Ya ce,
“Shi ne zai rike miki ciki? Me ya sa kike son sakaci
da cikinki ne?
Me ya sa baki girka kin ci ba.?” Ta ce, “Ai gani na yi ba ni kadai ce a gidan ba.
To in ban da abinki jawahir ke da gidanki sai an
girka an ba ki? Ke da na san ki da kyankyami, za ki
rinka cin abincin me aiki ne?” Ta girgiza kanta, ya
ce,
To kin gani ki rinka girkinki kina ci kin ji ko.
Yanzu me za ki ci, ko za mu fita muje mu sayo wani
abin ne ko kuma mu je gidan abinci.
Ta girgiza kai, “A’a zan girka wani abu yanxu
Ya dube ta ya ce, “Dare be yi miki ba. Ta ce, “A’a ba
komai. Tun da ta soma magana yake jin wani abu, zil-zil yana tsarga masa don jin dadin muryarta da
shaukin begenta. Ya mike ya fita jikinsa a sanyaye
kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya fito ya hau
samansa sai ya tarar da Kausar a kwance a kan
gadonsa tana nishi. Ya isa kusa da ita da saurinsa
ya ce, “Lafiya?” Menene ya faru? Ba yanzu na barki a dakinki ba. Ta ce, “Wallahi fama nake yi da ciwon
mara tun safe daurewa kawai na ke yi ka daure ka
kaini asibiti yanzu.”
Haidar ya ce, “Yanzu ya dace mu fita asibiti mu bar
jawahir ita kadai a gidan? Kausar ta ce, “Haba
Haidar me yake damunka ne me zai same ta, ba ga masu aiki nan a gidan ba, ko ka fi so ni na kwana
ina murkususu?”
Ya ce, “To shikena tashi muje. Lokacin da suka fito
don tafiya sannan jawahir ta fito falon za ta shiga
kicin wannan shi ne karo na farko da jawahir ta ga
Kausar ita ma Kausar ta ganta. Ba su yiwa juna magana ba sai Haidar da ya ce zamu fita yanzu
zamu dawo.
Jawahir ta shiga kicin kamar ba ta ji me yake cewa
ba, suka fice jawahir ta zauna a babban falo ta
kunna kallo, salkamar da taji ce ta sata saurin
juyowa. “Lalala Bilki yau ke ce a gari?” Gaskiya ba ki da alkawari, ni na za ta ma kin manta da ni.”
Bilki ta ce, “Haba jawahir ya zan yi na manta da ke,
kin san tun ranar da muka zo nan gidan Haidar ya
kore mu nake jin tsoron kada nazo na jawo miki
wata fitinar. To sai da na ji labarin aurensa na so na
zo sai na ji tsoron kada ya cire min kafa daya shi ya sa na hakura na fasa zuwa.
Jawahir ta ce, “Yanzu ya aka yi kika zo?
“Uhm ke dai bari, tare muke da direba munje gidan
kawar Hajiyarmu kusa da ku ne na ga ba zan iya
wuce gidanki ba.
Jawahir tayi murmushi, “Amma gaskiya na gode na kuma ji dadin zuwanki, don akwai labari da labarai
ma sai dai ga shi dare ne da za ki daure da kin zo
min da rana mun wuni muna hira.
Bilki tayi ajiyar zuciya ta ce, “Kina ganin in na zo
babu wata matsala ko Haidar yana nan.”
Jawahir ta ce, “Ba komai wallahi ba zai ce miki komai ba.
To shi kenan jawahir na fita kin ga dare ya yi sai na
zo din
“Okey Bilki na gode don Allah ina sa ido kada fa ki
ki xuwa.”
“Insha Allahu zan zo” Tayi sallama ta tafi. Jawahir ta soya indomie da kwai ta gasa masa kifi
ta hada masa lemon kwakwa da madara ta zuba a
jug ta cilla masa kankara ciki ta jere komai a kan
tebir din falon ta shiga sashenta ta ci na ta ta watsa
ruwa ta wanke bakinta ta je ta yi kwanciyarta. Sai
goma na dare su Haidar suka dawo. Kausar ta wuce dakinta Haidar kuwa ya nufi tebur din da
abinci yake don yunwar da yake ji tun break din
safe da ya yi a dakin jawahir.
Ya bude komai ya ci ya yi kat, ya rinka shan lemon
kwakwar nan yana nishadi a kasan zuciyarsa
kuwa sai shiwa jawahir albarka yake. Da ya gama ya murda kofar dakinta yau ma a rufe gam, ya
koma dakinsa yau ma ya kwanta yana murkususu
da ya rufe idonsa kyakkyawar surar jawahir yake
gani. Ga wata muguwar sha’awarta da tayi masa
mugun kamu haka ya rinka juyi yana murkususu.
Sai da asuba ya tashi ya yi alwala ya yi Raka’atainil Fajri ya yi ta karatun Alkur’ani ya yi addu’arsa ya
shafa. Ya dade yana lazimi sannan ya sauko falon
kasa ya zauna ko zai ga jawahir ta fito ya samu ya
ganta ko zuciyarsa ta lafa da tsananin radadin
kaunarta.
Ya yi sa’a kuwa ta bude kofarta ta fito tana sanye da abaya da karamin farin hijab, da ya sha adon
bakin les, tana rike da carbi a hannunta ta yi kyau
kamar ita ta yi kanta.
Duk motsin da tayi sai komai na jikinta ya motsa.
Yanda jikinta yake girgiza shi yake dada motsawa
da Haidar sha’awarta. Jawahir ta yi mamakin ganinshi a falon, don haka
ta karasa gabansa tayi saurin xubewa ta gaisheshi.
Ta mike ta nufi kicin idonsa na kanta.
Ya ce, “Jawahir” Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya
ce, “Don Allah idan break za ki hada ki hada da
mu.”(HMMM GASKIYA JAWAHIR AKWAI HAKURI DON NA TABBATA A IRIN KISHI NA MATA BA KOWACCE XATA IYA GIRKI TA BAWA KISHIYAR DA ITA BA XATA YI BA).
.
(((((((SALON SO))))))
:
(((((PART 26))))))
:
. Ta yi dan dum kamar ba za ta yi magana ba sannan
ta ce, “Kai da wa?”
Ya ce, “Ni da Kausar”
Ta ce, “Ko a musulunci dakin da ka kwana nan ne
yake da hakkin yi maka abinci. To amma tun da
hakan ba ta samu ba ni ya zama dole na hada maka, amma ita kuwa wadda ka ambata ban ga
dalilin da zan girka mata wani abu na ba ta ba, don
ba zamanta na ke yi ba, kuma ni na ajiyeta ba.
Kafin ya ce, wani abu ta juya tayi komawarta dakin.
Jawahir bata fasa hada break din ba don idan tayi
kamar za tayi fushi sai ta tuno abubuwan da Anti Maryam ta gaya mata to sai ta daure tayi ko ba
komai yanzu tana ganin nasara don kulawar da
Haidar yake yi mata ba kaman a farkon aurensu ba.
A babban falon ta shirya masa komai ta koma daki
ta tsala wanka ta yi kwalliya ta gani a fada da wani
tsadadden material ta yi kyau har ta gaji da kyan, ta sha adon gwala-gwalai kamar ka sace ka gudu.
Kamshi ne yake tashi a kowacce kafa ta jikinta. Ta
fito falon Haidar yana bisa tebir yana break shi ma
ya sha tsantsarerren adonsa da shiga ta alfarma.
Yana hango jawahir ya fara sambatu a zuciyarsa,
“Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi kyakyyawar halittar yarinyar nan, ko yaushe zan
ga fuskar da zan latsa jikin yarunyar nan, har na
gani gado daya da ita? Kai wannan rana da na
suma dan dadi Tina daya daga cikin ‘yan aikin
Kausar ne ta zo ta
kama kafar benen Haidar za ta hau, jawahir kuma sannan ta fito daga sashenta shi ne ta doka mata
tsawa, “Ke zo nan
Tina ta taho jikinta na rawa ta durkusa kasa a
gabanta, jawahir ta ce, “Uban wa ya ba ki ikon
hawa benen nan? Ko dakin sa’anki ne a ciki? Me za
ki yo? Wa ya aike ki?
Tina ta ce, Anti ce ta ce na hau na share.
Jawahir ta ce, “Wacece Anti?”
Tina ta ce Kausar Jawahir ta ce, “Ke dabbar ina ce
ko na ce
mahaukaciyar ina ce da za ki zo ki haye dakin megida?
Ko ku hudu aka auro ne ban sani ba? Tina ta
girgiza kai, “To wallahi ki sani wannan ya zamo na
farko na karshe ko falon nan kada na kuma ganin
dayar ku ta zauna a ciki, da kun shigo ku yi wajen
uwar dakinku ko kuma ku yi zamanku can bangaren masu aiki don ni ba zan yarda da
kwashe kwashe da tarkace ba.
Tina ta ce, “Ki yi hakuri Anti zan kiyaye gaba.”
Jawahir ta ce, “A’a ni ba Antinku ba ce, ga Antinku
can wadda ta kwaso ku ta zo ta zube ku. Ya kamata
a ce kuna gidan mazajenku kuna bautar aure amma ga shi kuna zaune kuna bautawa wata
katuwar banza, don kwadayi, wato kun fi
kwadayin abun duniya da rahamar Ubangiji ko?
Tina ta girgiza kai, jawahir ta ce “To ki gayawa
ragowar ‘yan uwanki ku yi kokari ku fito da mazaje
a yi muku aure ku je can ku samu ‘yancin kanku ku yi wa Allah bauta.
Tina ta rissina tana cewa, “Mun gode Anti insha
Allahu za mu gabatar da masoyanmu. Jawahir ta yi
mata izinin tafiya ta fita. Haidar yana zaune yana jin
su ko ba komai
zuciyarsa ta yi dadi da kalaman da ya ji jawahir tana yi yana alfahari da hankalinta. Gefe daya kuma
yana tunanin ko dai jawahir ta fara son sa ne don
ya ga kamar tana kishinsa, to Allah ya sa haka ne.
Kausar ta bude kofar sashenta ta fito tana yamutsa
fuska ta dokawa jawahir harara ta nufi wajen
Haidar tana yamutsar fuska irin ta marasa lafiya ta ce, “Darling cikina fa ya ki daina ciwon kuma sai na
rinka jin kamar yana harbawa ko cikin wata biyu
yana fara motsi ne?
Haidar ya kamo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa,
“Kausar
kada fa ki wahalar min da baby, ba kya son cin abincin ne yunwa ce take sa shi motsin dole bude
bakinki na ba ki, ki ce. Ta bude ya zuba mata,
“Yauwa kausar ko ke fa ai gwanda ki ci.
Jawahir ta ji wani katutun bakin ciki da kishi ya
tokare mata makoshi, lallai ma tsanar da mutumin
nan yake yi min ta kai tsana, duk tsawon lokacin da na dauka a gidansa ya kasa kusantata amma daga
zuwan wata har ya ba ta ciki, wallahi ba zan yarda
ba sai dai a yi wacce za ayi.”
Ta nufi gun su gadan-gadan a lokacin da Haidar ya
sa mata cinyar kaza ke nan a baki jawahir ta
tankwabe tare da dankar wuyan Kausar ta ce, “Wallahi sai ta yi amansa, ai ni ba baiwarta ba ce da
zan yi mata girki ta zo tana ci.”
Haidar yayi yayi ta sake ta taki shi kuwa ya fitar da
hannu ya shara mata mari. Jawahir ta yi saurin cika
Kausar yayin da ta dafe kuncinta zafin marin ya
gigita ta inda ta rarumi faramtin tangaran me nauyi ta kwadawa Haidar a gabansa tuni Haidar ya dafe
wajen ya kwalla kara ya zube kasa.
Hankalin jawahir ya yi mutukar tashi da ganin halin
da Haidar yake ciki sai ta sa kuka na shiga uku
yaya, Yaya don Allah kayi hakuri wallahi ba da
sanina na yi maka ba, Yaya ka yi hakuri ka tashi na tuba na daina ba zan sake ba. Kausar kuwa kofa ta
nufa ta kirawo megadi da yaron gidan suka kama
shi suka sa shi a mota ta shiga ta tuka motar suka
tafi asibiti. Aka kama shi aka shigar da shi daki
suka tsayar da Kausar a waje can likitan ya fito ya
ce ta je ta nemo dan uwansa namiji. Kausar ta mike ta shiga motarta ta yi gidansu Haidar.
Ta yi salllama falon inda ta samu Abbansa da Anti ta
durkusa ta gaishe su ta ce, “Daman Haidar ne ba shi
da lafiya har an kwantar da shi a asibiti shi ne na zo
na fada
Cikin hanzari Abba ya mike ko direba bai jira ba ya fita ya hau motarsa ya tafi inda Kausar ta shiga tata
motar ta rufa masa baya. Anti ta ce mata, “Duk halin
da ake ciki ta yo mata waya ta gaya mata. Ta ce to.
Lokacin da su Abba suka isa sannan Haidar yana
bacci don haka Abban ya wuce office din Doctor,
likita ya mike tsaye ya mikawa Abban hannu suka gaisa, sannan suka zauna. Likita ya ce, “Daman
Alhaji larurar da take damun Haidar ce abin babba
ne. Cikin firgita da dimauta Abban ya ce, “Me ya
same shi? Likitan ya ce, “To dai a bincikenmu mun
gano
buguwa ce mai tsanani ya yi a gabansa wadda har ta jawo masa mutuwar gabansa, don ba shi da
wani kuzari da zai iya kusantar mace bare ya iya
biya mata bukatarta. Abban ya dafe kai tare da
fadin, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, yanzu shi
kenan
dana ya nakasa? Likita me ya jawo masa buguwar.? Likitan ya ce, “Kada ka damu Alhaji za mu yi bakin
kokarinmu na ganin ya samu lafiya ya dawo
normal.
Abba ya yi masa godiya ya koma dakin da Haidar
ya ke ya
zuba masa ido yana bacci. Jawahir kuwa tun bayan tafiyarsu Haidar asibiti ta
kasa samun sukuni sai kuka take yi tana tunanin a
wane hali Haidar yake yanzu, ta kasa samun
sukunin zuciyarta. Kawarta Bilki ta yi sallama ta
shigo, “A’a lafiya jawahir na ganki haka?
Jawahir ta ce, “Kyale ni Bilki na bi ta dokin zuciya na aikata abin da zai dame ni. “Me yake faruwa ne?”
Jawahir ta kwashe komai ta gaya mata. Bilki ta ce,
“Wallahi ba ki kyauta ba, don yanzu Haidar son ki
yake yi sosai da kin sani ba ki yi masa wannan
dibar albarkar ba, don ba mutunci ba ne mace ta
kai hannu kan mijinta da niyyar duka. Tace, “Uhm kyale ni Bilki zafin marin ne ya gigita ni
ban san lokacin da na kwada masa ba, karar da ya
yi ce ma ta dawo da ni hayyacina.”
Bilkisu ta ce, “Yanzu ba surutu za ki tsaya ba tashi
mu je asibitin ki ga yanda jikin nasa yake. Ta ce,
“Kai anya kuwa na je?” Ta ce, “Kwarai ma kuwa, ai tashi kawai mu tafi.
“To ai ban san asibitin da ta tafi kai shi ba.
“To bari na gano idan direban ya dawo sai mu
tambaye shi wanne asibitin ne, ta yi waje. A can
asibiti kuwa Abba ya koma gida Kausar tana
waje, Haidar ya farka Faruk ya gani a gefen gadonsa a zaune, Faruk ya ce masa, “Sunnu ya
kake jin jikin naka? Ya ce, “To da sauki zan ce,
“Haidar ya yi tsu can ya ce Faruk ina jawahir?”
Cikin mamaki Faruk din ya ce, “Me za ka yi mata?
Haidar ya ce, “So nake na san halin da take ciki.”
“Me ya same ta?” In ji Faruk, Haidar ya kwashe yanda abin ya faru ya gaya masa, Faruk ya ce, haba
Haidar me ya sa za ka mare ta? Ai kai ma ba ka yi
dai-dai ba. Wallahi yanxu jawahir tana tsananin son
ka tun da take yi maka duk abin da kake so, kuma
take tsananin gudun bacin ranka, ga shi har ta
kasa jure kishinta ta nuna karara. Haidar ka rage zafin zuciya in ba haka ba wata ran zai kai ka ya
baro ka.
Haidar ya ce, “Ai yanxu ya ma kai ni ya baro din, ni
dai don Allah so nake yi ka je gidan ka gano min
halin da take ciki inda hali ma don Allah ka rarrashe
ta ku taho tare.”
.
SALON SO
♡♡♡♡27 ♡♡♡♡
.
Faruk ya ce, “Ba ruwana babu inda za ni bare ta
zo ka ci mata mutunci ta zo ta rinka ganin h rashin
kirkina.
Haidar ya ce, “To ni ka kai ni wajen ta na ganta,
Faruk ya yi murmushi, Haidar ko dai ka so ma
son ta ne?”
Haidar ya rintse ido ya ce, “Wallahi ban san
lokacin da son yarinyar nan ya yi min dirar mikiya
ba, ya shige ni.
Inna kwanta da daddare Allah Allah nake gari ya
waye don na ga kyakkyawar fuskar matata kuma
kanwata, wallahi ni kadai na san yanda tsananin
son jawahir yake raina, kai abin da na yi wa
Kausar a gananta ma na yi ne don na auna na ga
tana so na kuwa ko ni kadai nake shirme na.
Faruk ya ce, Ka ga irin abin da na so ka gane
tuntuni ka ki, to yanzu kuwa in ta ji halin da kake
ciki sai ta ce don ka ga ba za iya kwanciya da ita
ba ne, shi yasa ka nemi shiri da ita.
Haidar ya ce, “Ai likita ya ce zan warke fa”. Ko da
yake yanzu ne lokacin tantance wanda take
sonka don Allah da wadda a kayi auren sha awa.
“Haidar ya ce, Ni dai don Allah ka je ka taho min
da sahibata ko don na ga halin da take ciki.
Faruk ya ce, “Zan je ai yanxu
Kausar ta turo kofar ta shiga fuskarta a murtuke
babu alamar fara’a, ta je gefe daya ta zauna ba
tare da ta kula wani a cikinsu ba. Faruk ya mike
Haidar bari na je in dawo ko? Duk yanda muka yi
zan zo ka ji.
Ya ce, “Don Allah ka je fa yanzu kada ka ki zuwa
ka ji. Faruk ya ce Insha Allahu kuwa yanzu zan
je.
Faruk ya fita ya bar su Haidar ya juya ya kalli
Kausar ya ce, “Me ya same ki ne na ga kamar
ranki a ba ce? Ko cikinne yake ciwo?”
Ta zumbura baki, “Kai yanzu har ka manta da
barnar da Jawahir ta yi maka a jikinka har kake
cewa a je a taho da ita? To wallahi ni ba zan
yarda ba don ta ga ita ba ta da amfani a wajenka
shine za ta nakasta min kai, wato ka zamo marar
amfani, to wallahi ba zan yarda ba don ita ma sai
na nakasta ta, sai dai duk abin da za a yi a yi.”
Haidar ya daka mata tsawa ya ce, “Ke ki shiga
hankalinki kina ganin duk da son da nake wa
jawahir da ta yi miki abu sai da na yi mata marin
da ta gigice, to wallahi ki shiga hankalinki idan
kika sake kika taba min mata wallahi sai kin yi
mugun raina kanki, don sai kin yi mamakin abin
da zan yi miki.” Ta mike ta yi waje tana kunkuni
ta zari mota ta nufi gidan Yakumbon Haidar wato
kakarsa ta wajen uba, ta je ta zayyane mata
maganganun karya da gaskiya ta gaya mata,
Yakumbo ta hau sababi ka ji mu da tsinanniyar
yarinya don ba ta son sa shine take neman
hanyar kashe shi, to wallahi bi ba yarda zan yi
ba, tashi ki koma asibitin gani nan zuwa yanzun
nan, “Kausar ta koma asibiti ta tarar su Anti da
Momy da su Yaya Abba sun cika asibitin taf, ana
ta jajen abin da ya faru.
Shi kuwa Faruk da ya je gidan Haidar yayi
sallama falon, su jawahir suna daga kicin suka
amsa sallamar suka fito falon, Faruk ya nemi
waje ya zauna jawahir da Bilkisu suka gaishe shi,
faruk ya ce, Haidar ne ya turo ni na zo na ga
halin da kike ciki in kuma da hali ki zo mu je yana
son ganinki. “Jawahir ta sunkuyar da kai ta ce,
“Gaskiya Yaya Faruk ba zan je inda yaya yake ba,
don in na je ban san irin wulakancin da zai yi min
ba, ka ga kuwa da na je ya bata min rai ai gwara
ban je ba.
Faruk ya ce, “Wallahi Haidar yana wani hali na
mutuwar sonki kin san miskilancinsa ya rasa ta
hanyar da zai bi ya nuna miki Kaunar da yake
miki don yanzu da kin ga irin magiyar da lallamin
da ya rinka yi min sai na zo gare ki dakin
tausaya masa.
Kafin ta yi magana Bilki ta ce, “Faruk bari mu
karasa girkin da za mu kai masa sai mu fito mu
je.” Faruk ya ce, to shi kenan bari na je na dawo.
Bilki ta zuzzuba komai a fulas ita kuma jawahir
ta je ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfa
ja! Super Holland dinkin filet ne ya kama jikinta
sai zani da dankwali da ta daura, farar hoda
kawai ta shafa a fuskarta sai dan man leben da
ta shafa ta dauko jan mayafi da jan takalmi ta
saka, kunnanta fashon din yari ne me jan dutse a
tsakiya. Bilkisu ta tafa mata “Amma
yarinyar nan kin yi kyau, kwalliyar taki ta burge ni
sai dai kash kin manta a shafa hadin turarukanki.
Jawahir ta yamutsa fuska, “Kin san fa inda za mu
je za ki ce na shafa hadin turare. Bilki ta ce, to
meye ba wajen mijinki za ki ba, ai gwanda ki
shafa turarukan da kamshinsu zai gigitar da shi
kuma ga karin lada a wajen Ubangiji, don duk
sanda mace ta yi abun da zai farantawa mijinta
har ya ji dadi a ransa to Ubangiji zai ba ta ladan
da ba ta san adadin yawansa ba.
Jawahir ta ce, Haka ne bari na shafa don na
fuskace shi yana son kamshi.
Sun jejjera fulas-fulas din a dan kwando me kyau
ta lullube shi da farin yanki me adon bakin les da
fulawoyi a jiki. Faruk ya dawo suka dunguma a
motarsa zuwa asibiti.
A lokacin ba kowa duk sun tafi sai kausar kawai
da take zaune kan kujera tana karanta jarida, ba
ta daga kai ba balle ta kalli wani a cikinsu. Faruk
ya ce, “To ga ta nan na cika alkawari ko, ga ta
na kawo maka
Haidar ya yi murmushi ya ce, “Ai kuwa na gode
Bilkisu ce ta fara gaishe shi tare da yi masa ya
jiki. Cikin fara’a ya ce, “Ai jiki Alhamdullahi.”
Jawahir ta durkusa cikin dari-dari da rawar
murya Kamar
mai shirin kuka ta ce, “Yaya ina wuni? Ya jikin?
Ya ce, “Lafiya lau jawahir ya naki jikin.?
Ya sa hannu ya dago ta daga tsugunnun ya shafi
kuncinta, ya ce, “Wai haka kuncinki ya tashi
hannuna ya fito radau na marin da na yi miki,
sorry Babyna ki gafarce ni, “Kafin tayi magana
aka turo kofar aka shigo tare da sallama,
Yakwalkwal ce ta shigo rike da hannun Sayyid.
Sayyid ya fincike da gudu ya nufi jawahir yana
cewa, “Anti na anti na, shine rannan kika gudu
unguwa kika bar ni ina ta kiran ki ba ki zo kin tafi
da ni ba. “Jawahir ta dauke shi ai yau da kai zan
tafi kai ta kwana a can ko? Jawahir ba ta ankara
ba ta ji saukar mari a kuncinta, Yagwalgwal ce ta
kuma hau fada, “Annamimiya me kuma ya kawo
ki wajen jikana kin so ki kashe shi, Allah bai baki
nasara ba shi ne kika biyo shi nan ki karasa shi
ko?
Haidar kuwa tuni ya diro daga gadon jinyar ya
tare jawahir yana cewa, “Haba Yagwalgwal ya za
ki doke ta ita ma fa ba lafiya ce da ita ba, me ta
yi miki?”
Yagwalgwal ta ce, “Ubanka ta yi min, shege
sallamamme so kake yanda uwarka ta mallake
Alhaji kai ma jikan mallake ka za ayi,
“Yagwalgwal ta ci gaba da nuna jawahir da dan
yatsa tana yi mata sababi, daga yau na gaya miki
ba ke ba Haidar in ke mayya ce ki ci kanki da
kanki, haka kawai hankalinsa ya kwanta yana
zaune da matarsa lafiya za ki zo ki bata musu
zama.
Jawahir ta mike jikinta ba kwari za ta fita Haidar
ya yi saurin riko hannunta yana cewa, “Haba
Yagwalgwal ya za ki zo ki korar min matata ki ce
sai ta tafi? Ai ba ita ta kawo kanta ba ni na sa a
je a dauko ta in ta tafi waye zai yi jiyya ta?
Kawai mutum da matarsa a nemi raba su. Kan ya
rufe baki bakinsa Yagwalgwal ta ba shi nasa
marin ya dafe kunci ita kuma ta ci gaba da
sababi tana nuna shi da dan yatsa, “Ka shiga
hankalinka ka san da wacce kake magana, idan
ba ka san ciwon kanka ba ai ni na san ciwonka,
yarinya ta nakasa ka ka zamo marar amfani
amma ba za ka guje ta ba, wata rana ma ranka
za ta raba ka da shi.
Jawahir ta fincike hannunta ta yi waje cikin sauri
Haidar ya yunkura zai bi ta Yagwalgwal ta rike
shi, Bilkisu ta bi bayan jawahir yayin da Faruk ya
rufa musu baya. Da kyar da ban hakuri ya shawo
kan jawahir ta shiga motarsa don ya mayar da su
gida. Faruk ya ce, “Don Allah don Annabi jawahir
ki yi hakuri da abin da tsuhowar nan ta yi miki.
Jawahir ta yi saurin katse shi, “Haba yaya Faruk
ka fi kowa sanin ta yanda a ka yi aurenmu da
yaya, ba son sa nake yi ba na aure shi don
biyayyar iyayena na zo nake zaman hakuri da shi,
ya tashi ya dankaro min kishiya ni duk hakurin da
na yi a kansa ba a gani ba kenan.
Fashe da kuka Faruk ya ci gaba da rarrashinta ki
yi hakuri jawahir ki tuna aure kike, aure kuwa
bautar Ubangiji ne kada bacin ran wasu ya sa ki
sabawa megidanki kin ji?”
Yanda na san ki da hakuri da ladabi da biyayya ki
ci gaba da yi komai me wucewa ne wata rana sai
labari kin ji?”.
Ta daga kai ya ce, “Yauwa ko ke fa gobe ku
shirya da wuri sai na zo na kai ku ta ce to. Ya
sauke su a gidan shi kuma ya koma asibitin shi
kuwa Haidar tun bayan fitarsu jawahir da
Yagwalgwal ta rike shi don kar ya bi su gado ya
koma ya kwanta ya yi rigingine ya rufe idonsa.
Maganar duniya babu wadda ba a yi masa ba
amma ya yi musu shiru ko motsi bai yi ba dole
suka gaji suka hakura suka bar masa dakin.
Faruk ya shigo ya dinga lallaminsa yana ba shi
baki tare da va shi hakuri sannan ya tashi ya
jawo kwandon da jawahir ta jero masa kayan
abinci.
Dakakkiyar sakwara ce lukui da miyar agushi mai
wadataccen nama, sai jalof din taliya da lemon
kwakwa. Haidar ya ce, “Ka ga yarinyar nan da
zan bata mata rai ba za ta ki yin abinci ba don
gudun kada ta bar ni da yunwa.” Faruk ya ce, ai
haka ake so ka ga yanzu sai ka rike ta da kyau
ka nuna mata garanci wanda ba ta samu ba a
baya. Haidar ya ce, “Allah dai ya ba ni lafiya amin
in ji Faruk yayin da ya zuba musu abincin a filet
din da ta zubo suka ci sosai dan shi kansa Faruk
ya yaba da dadin girkin nata.
Can kuwa Bilki ta mike don tafiya gida, “To ni zan
tafi jawahir sai dai gobe zan zo da wuri na raka
ki mu sake dubo shi. Jawahir ta hangame baki ta
ce, “Don kin ji Faruk ya fada ba kya tsoron mu je
a yi mana wani sabon wulakancin da ya fi na
yau.?
Bilkisu ta ce, “Insha Allahu hakan ba za ta faru
ba gwanda ki je, kada su samu kafar raba ki da
mijinki ga shi kuma yanzu kuna son juna. Jawahir
ta ce, “Shi kenan Allah ya kai mu goben na gode
Bilki da kaunar da kike min, da ba ni shawarwari
masu kyau da kike yi, Allah ya kara mana dankon
zumunci a tsakaninmu amin. Da haka suka yi
sallama ta tafi.
Jawahir ta shiga dakinta ta kwanta tana tunanin
abin da ya faru yau da ita.
Faruk ya fita ya yi sallar insha Haidar ya kalli
Kausar ya ce ke ba za ki yi sallar ba ne na ga ko
magariba ba kiyiba?
Ta ce, “A’a ina ruwanka a yin sallah ta ka ga
malam kawai ka ji da abin da ya dame ka. Faruk
ya turo kofar ya shigo Kausar ta zuba masa
harara tare da jan tsaki ta mike ta bar dakin.
Faruk ya taimakawa Haidar ya yi Sallah, Haidar
ya daga hannu sama ya dade yana addu’a
sannan ya shafa ya xuba tagumi.
Faruk ya cire hannun tagumin ya ce, “Haba
malam menene kuma? Ka yi hakuri a kan larurae
da ta same ka, ka yarda da kaddara ko?
Haidar ya ce, wallahi ba wannan ne ya dame ni
ba halin da jawahir rake ciki nake tunani kada fa
ta Gudu
gidan Inna ta kuma boye ta ka san ranta ya ba ci
dazu da abin da Yagwalgwal ta yi mata. Faruk ya
ce, “Ba na jin za ta fita har gida na kai ta kuma
na babbata hakuri ka san yarinyar akwai biyayya”
To don Allah ka je ka taho min da ita ta kwana a
wajena ka ga gidan ba kowa sai masu aiki.
“Faruk ya ce, “Ka yi hakuri da safe ai za ta zo ka
ga yanzu dare ya yi yanxu haka ma ta kwanta.
Haidar ya ce, “Haba Faruk don Allah ka taimaka
min ka je ka taho min da jawahir yanzu duk
girman gidan nan ta kwana ita kadai sai masu
aiki? Faruk ya ce, “Shikenan bari na je amma sai
na biya na dau Hafsa don ita ma ta zo ganin
likita.”
Haidar ya ce, “Ko dai ta harbu ne.? Faruk ya yi
murmushi ya ce, “To ga mu dai ga Allah don mun
sa rai.
Ya fita yana dariya ya biya ya dauki matarsa
Hafsa suka tafi. Ya ce, Ya ku ka yi da likitan? Ta
ce, “Gwaje gwaje ya yi min ya kuma dauki
fitsarina ya ce da safe a zo a karbi result din.
Faruk ya ce, “To Allah ya taimaka mana ya sa
abin da muke nema ne, ta ce Amin. Suka yi wa
juna murmushi.
Suka yi fakin a harabar gidan Hafsa ce a gaba
don ita take buga kofar falon nasu da yake kulle.
Jawahir da take takure a falo don zuciyarta cike
take da tsoro da fargaba ka sancewar ta ita kadai
a sashen ta yi tunanin ko ta kirawo ‘yan aikin
Kausar su taya ta kwana sai kuma ta fasa, to jin
bugun sai ya dada tsoratar
da ita. A tsorace ta je gaban kofar cikin rawar
murya ta ce, “Wanene?” Faruk ya ce, “Bude mu
ne, ta kalli agogo karfe tara gabanta ya fadi,
Allah ya sa dai lafiya? Ta bude kofar ta ba su
hanya suka shigo Faruk ya ce, “Sarkin tsoro da
kin zata barayi ne suka zo sa ce ki?” Ta yi dariya
ta kamo hannun Hafsa ta ce, “Wai yaushe rabon
ki da gidan nan? Ko da yake ban sani ba ko kina
zuwa wajen amaryarku Kausar, “Hafsa ta yi
dariya ta ce, Ni ina zan zo gidan nan mutuniyata
ba ta nan ta gudu ta bar min abokin miji ya zamo
abin tausayi a gari?” Ga ba daya suka yi dariya.
Faruk ya ce, “Kar dai a gaji da mu dan mun kuma
zuwa da kokon bararmu da karin ban hakuri
megida ya ce, a zo a tafi dake don Allah ki kwana
a wajensa. Ta yi shiru can ta ce gaskiya ni ba
zan je wajensa na kwana ba. Faruk ya ce,
“Subhanallahi, kin san hukuncin matar da mijinta
ya yi kiranta ta ki zuwa kuwa? Ko kina so ki
hadu da fushin ubangiji ne?
Jawahir ta ce, “Gaskiya Yaya faruk ba zan je ba,
ba Kausar tana can ba?
Ai ita ta saba kwanciya da shi ni in na je ina da
abin da zan yi masa ne? Faruk ya ce, “Haba
jawahir kada ki yi haka mana da iliminki da komai
ki yi hakuri ki amsa kiran mijinki mana.
Ta ce, “Haba yaya Faruk har ka manta irin
zaman da na yi da yaya Haidar a gidan nan ni
bani da hakki a kansa sai shi yanzu yake da
hakki a kaina har zai neme ni?” Ta sa kuka ta
mike tayi daki, “Wallahi ba inda zan je”. Ta turo
kofar dakinta ta kulle.
Hafsa ta ce, “Gaskiya fa ni fa ban ga laifin jawahir
ba, don gaskiya an zalinceta” Faruk ya dakawa
Hafsa tsawa tare da cewa, “Yi min shiru ana
neman sasanta magana kina dada tunzurata. Ya
jawo wayarsa ya yi danne-danne. Haidar ya
dauka, “Hello” Yauwa Haidar ka kwantar da
hankalinka kayi hakuri mun zo mun tarar jawahir
tayi bacci amma don Allah kada ka tsayar da
hankalinka da safe kafin na tafi office zan biya na
dauko maka ita. Haidar kafin ya ce, wani abu tuni
Faruk ya katse wayar ya kuma kasheta gaba
daya don ya san halin Haidar ba kyale shi zai yi
ba.
Haidar kuwa tun daga lokacin wata zuffa ta rinka
tsiyayo masa, hankalinsa ya yi mummunan tashi,
jikinsa sai rawar sanyi yake yi. Ba jimawa zazzabi
mai zafi ya rufe shi. Nan da nan jiki ya rikice a
ranar da sai Abbansa ne da yaya Abba suka
kwana a wajensa. Ba shi da wata magana sai ta
ambaton an bar jawahir ita kadai a gidan nan sai
masu aiki kada wani abu ya samar masa ita.
Yaya Abba ne yake dan karfafa masa gwiwa yana
tunasarsa. Yawan ambaton jawahir da Haidar
yake yi ya sa Kausar ta yi fushi ta baro asibitin
ta dawo gida. Jiyya ta koma hannun yaya Abba
da Faruk, amma asibitin kullum cike yake da yan
uwa da abokan arziki sai dai rashin matansa a
wajen. Duk da haka Yagwalgwal ba ta fasa yada
habaici da kananan maganganu ba don haka Anti
ba ta son yawan zuwa don ita take yiwa
habaicin.
Kamar ita ta haifa mata Haidar din
Yau kwanan Haidar hudu kenan a asibiti suna zaune a
dakin jinyar, Faruk da yaya Abba Haidar ya ce da
su, Faruk da yaya Abba ku fara hada kaya ku
karbo min takardar sallama.” Yaya Abba ya ce,
Ah sabo da me? Cikin raunanniyar murya Haidar
ya ce, “To kun ki zuwa ku rarraso min jawahir ta
zo gareni na ganta ko hankalina ya kwanta. Tun
da haka ne gwanda na koma gidan na yi jinyata a
can inda zan samu kulawarta.
Shi dai yaya Abba ba ya son jawahir ta zo wajen
nan ko don sabo da kananan maganganun da
Yagwalgwal take yi, don haka ya yi shiru bai ce
komai ba. Haidar kawai ya fara hada kaya Faruk
ya tausaya masa, ya ce, “Bari Haidar yi hakuri
bari na je yanzu na shawo kanta insha Allahu za
ta zo.
Jawahir tana zaune tana bitar karatun Alkur’ani
wayarta ta yi kara. Ta tsagaita da karatun ta
dauka, “Hello wa ke magana? Faruk ya ce, “Ni ne
daman na bugo na gaya miki Haidar yana cikin
dayan biyu ko mutuwa ko rayuwa, don ya rikice
an rasa gane kansa sai kiran sunanki kawai yake
yi”
Jawahir ta gigice, “Na shiga uku yaya faruk
yanzu ina yayan yake?
“Yana can asibiti a rikice.”
“Wayyo yaya faruk! Don Allah ka kwantar masa
da hankali yanzu zan zo.” Ya ce, “Ina harabar
gidanku ina jiranki ki fito da hanzari.
Kafin ya rufe bakinsa ya ganta ta fito da wayar
kange a kunnenta. Ya bude mata bayan motar ta
fada, shi kuma ya shiga gaba ya tuka suka yi
gaba. Yana tsayar da motar jawahir ta bude ta
fito a guje ta shiga dakin da yake tana danna kai
ta tarar da shi a gado yana ta faman ihu.
“Wayyo Allah! Ya dafe cikinsa yana ta juyi.” Ga
shi dakin sai shi kadai ba kowa, nan da nan
hankalin jawahir ya tashi, tausayinsa ya kama ta
sai kawai hawaye taji yana zubowa daga
idannuwanta ta zauna a gefen gadon ta dago
kansa ta dora a cinyarta tana rike da shi sai
sannan take yi masa, gani take da tana da ikon
cire ciwon nan ta dawo da shi jikinta da ta yi
domin kawai ya huta a abin da yake damunsa.
“Sannu yaya na kirawo likita ya ba ka magani.
Wayyo yaya cikinka ne yake ciwo? Yaya ko ina
ciwon yake yi?
Sannu yaya, bari na hada maka tea ka sha ko?
Ko za ka iya cin abincin? Don Allah yaya ka
tashi.
A hankali nishi ya lafa sai kadan kadan daga can
ya yi shiru ciwon ya tafi kenan. Jawahir ta
rankwafa kansa, “Sannu yaya”. Ya lalubi
hannunta ya danke a nasa cikin magana sanyi-
sanyi irin wanda yake jin jiki ya ce, “Yaushe kika
zo? Ta ce, “Ban dade da zuwa ba. Ina yaya
Abban ya tafi ya barka kai kadai?”
“Yanzu nan kafin ciwon ya tashi ya tafi gida
amma yanzu zai dawo.”Ta ce “Amma dai bai
kamata su rinka barin ka kai kadai ba kana cikin
wannan hali.”
“To ya zan yi jawahir ke ma da kike ‘yar uwata
matata kin guje ni kin ki jiyyata waye zai jura?”
Jawahir ta ce, “Ka yi hakuri yaya ba wai na ki
zama a wajenka bane ka san halin Yagwalgwal
kar ta zo tana tsinka na a asibiti shi ya sa.
Haidar ya ce, “To shi kenan ba komai zan nemi
likita ya ba ni sallama sai mu koma gida na yi
jinyar a can ko?”
Ta ce, “Haba yaya gwanda ka zauna a nan din ka
ga sun fi kulawa.”
To jawahir ai ba zan juri rashin ganinki ba
gwanda dai na koma gidan.”
Daidai nan likita ya shigo ya dubi Haidar ya ce,
yanxu ina ganin za mu sallameka ka koma gida
tun da Abbanka ya ce kasar waje zai futa da kai.
Don haka ga takardar sallama.
Jawahir ta ce, “To likita yawan ciwon cikin da
yake fa? Likitan ya ce ba komai wannan mun
bashi magunguna sai dai a dinga kula wajen ba
shi ya sha.”
Anan yaya Abba ya shigo ya kalli jawahir ya ce
wato sai yau kika ga damar xuwa wajen mijinki
ko? Kina sane da ba shi da lafiya yana kwance a
asibiti amma ba za ki zauna kusa da shi ba, don
taimaka ma sa ba ko.?
Jawahir cikin biyayya jawahir ta ce, “Kayi hakuri
yaya insha Allahu ba zan sake ba, “Faruk ya
shigo suka kwashi kaya da Haidar suka yi
gidansa.
Dakinsa suka wuce da shi suna budewa kamshi
ya bige su ko ina a gyare fes kamar yana nan.
Jawahir ta hado
musu abubuwan ci da na sha suka ci suka sha
suka yi kat, sannan suka yi musu sallama tare da
kara yi musu addu’ar samun sauki. Jawahir ta
shige tolet dinsa ta hada masa ruwan wanka a
baho ta zuba turaren wanka a cikin ruwan nan da
nan turirin kamshi ya rinka tashi. Ta fito daga
tolet din ta durkusa Yaya ga ruwan wanka can na
hada maka, ya ce yauwa Babyna na gode.
Ya mike ya shige tolet dinshi kansa kamshin da
tolet din yake yi dabanne. Yana shiga cikin ruwan
ya ji wani dadin ni’ima ya ratsa shi ya fara
wankan.
Jawahir kuwa ta fito masa da wasu kananan
kaya, wando je three Quarter (tiri kwata) da rigar
50 Cent marar hannu ta kara feshe su da turare.
Ta debo masa mayukan da zai yi amfani da su
da turarukan. Ta ja masa kofar dakin ta sauka
zuwa kasa nata dakin. A lokacin kuma Kausar ta
dawo ko daga ina take oho ita ta sani.
Jawahir ta shiga wanka ta fito ta gyara jikinta
sai zuba kamshi take yi kamar wadda aka yi barin
turare a jikinta. Riga da wando ta saka da hula
mai harafin sunanta. Fuskar nan tata sai sheki
take yi, jikinta sumul-sumul gwanin sha’awa
kirjinta ya cika fam, da na shanu.
Ta bude kofar ta fito Haidar yana kwance a
doguwar kujera da karamin kur’ani a hannunsa
yana karatu. Kausar tana kujera me zaman
mutum daya tana zaune da jarida a hannunta
tana dubawa, kamshin da suka ji ne ya sa su
saurin dago kai Kausar ta saki tsaki ta mai da
kanta ga karatunta.
Jawahir ta wuce kicin ta dauko kofin gilas me
kyau ta bude firji ta dauko robar ruwa ta
Highland ta iso gaban kuherar da Haidar yake
kwance ta zauna a kasa kan kafet ta balle bakin
robar ruwan ta tsiyayo ta fiffito da magungunan
ta mika masa, “Yaya ga magungunan.
Ya dan mike zaune ya karbi magungunan ta
watsa bakinsa ta kafa masa kofin a baki ya sha
ruwan ya ce ta dan danna masa kafafuwansa don
ciwo suke yi masa. Ta mike sannu a hankali ta
rinka mamnatsa masa tana yi masa tausa. Jin
dadin tausar da ya jine ya sa shi fadin wash,
wash a hankali tare da lumshe ido.
Ita kuwa Allah sarki sai ce masa take yi sannu
sannu yaya cikin alamun ban tausayi, shi kuwa
taushin fatar hannunta mai kama da atafa shi
yake neman dimautar da shi, har yana neman sa
shi ya fita daga hayyacinsa, ba dan yana gudun
kada girma ya fadi ba ai da ya rungumota.
A ka kwankwasa kofar falon jawahir ta kalli
Haidar da yake kwance yana lumshe ido don jin
dadin tausa ta ce, “Yaya na je na bude kofar.?
Kai kawai ya iya daga mata don maganar ta ki
fita kanta bude kofar ta ja da baya don ganin
Yagwalgwal ce. Jawahir ta durkusa kasa ta
gaishe ta, ta ce “Munafuka ba zan amsa gaisuwar
taki ba, me kike jira a gidan da baki tafi ba tun da
kiyayyar da kike yi masa har ta kai ki sabauta
masa lafiyarsa ai za ki iya kashe shi ma, don
haka ni gaskiya ban yarda da wannan auren naku
ba ka sake ta kawai na gaya maka ba na son
gayyar tsiya gayyar jarabawa.
Jawahir ta fashe da kuka ta kalli Haidar ta ce,
wallahi ba don na riga na yi wa Dadyna alkawarin
ba zan kuma fita daga gidan nan ba, ba tare da
izininka ba wallahi yau da na bar zaman gidanka.
Ta durkusa a gabansa tana kuka, “Yaya don Allah
don Annabi yaya ka taimake ni ka sake ni ko ni
ma na samu sukuni a zuciyata.
Haidar ya sunkuya ya dago jawahir ya hada ta da
kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar
rarrashi, ransa a bace zuciyarsa ta yi bakikkirin
sai fat-fat take yi kamar ta fasa kirjinsa ta fito
waje. Ya kalli Yagwalgwal ya ce, “Yagwalgwal ina
ganin girmanki kada ki bari kimarki ta zube a
idona, jawahir ‘yar uwata ce ko ba aure a
tsakaninmu ni me rike ta ne ballantana matata ta
sunna ki rika aibata ta a gabana, ai aurena da
jawahir mutu ka raba takalmin kaza.
Yagwalgwal ta kama salati tana tafa hannu,
“Yanzu dan nan ni kake gayawa haka a kan
wannan mai kama da sadakar yallan kake neman
zagina, to bari na je wajen uban naka in kai ban
isa da kai ba ai shi ba zai ki jin maganata ba, tun
da ni na haifeshi ko. Jawahir ta zame jikinta daga
jikin Haidar ta nufi dakinta tana kuka ta rufe
kofarta. Haidar ya kamo hannun Yagwalgwal ya
ce, “Yi hakuri matar ta karfen na san du kishi ne
yake dawainiya da ke, Ta doke hannunsa ni sake
ni me kuma za ka gaya min bayan ka gama yi
min rashin kunya. Ya dada kamo hannunta yi
hakuri zo mu je sama dakina na gaya miki komai
don ki ji yanda abin yake. Da kyar ya shawo
kanta suka hau samansa suka zauna a falonsa,
duk wannan abin da ake yi Kausar tana zaune a
kujerar da take tana kallonsu kawai ba tare da ta
tofa komai ba.
Haidar ya ce da Yagwalgwal “Wallahi yarinyar nan
jawahir tana da mutukar hakuri ga ladabi da
biyayya ga sanin ya kamata da hangen nesa, tana
aiki da ilimin da Ubangiji ya ba ta, idan aka ce za
a yi ta tafiya a yanda a ke yi yanzu, to hakika
hakurin jawahir zai iya kai ni wuta.”
Yagwalgwal ta ce, “Dakata! Don na ce ka rabu da
ita kake kawo min wannan bayanin, ka je kada ka
sake ta ran da ta kashe ka ai ma zo mu dauki
gawarka ko?
Haidar ya ce, “Dole dai sai na fasa miki tarihinmu
za ki yarda da zancena. Haidar ya faro mata irin
tsanar da ya yi wa jawahir tun daga farko da
yanda har a ka yi auren da irin zaman da suka yi
da dalilin da ya sa jawahir barin gidansa har
kawo yau.
Yagwalgwal ta saka salati tana cewa, “Ashe ni
balokokon vanza nake yi kai ne marar gaskiya?
To wallahi ka kula ka rike ‘yar uwarka da kyau
don tana yi maka son gaskiya. Da haka dai suka
yi sallama ya debo kudi me yawa ya bata ta yi
masa godiya tare da sa masa albarka ta ce kuma
za ta zo ta bawa jawahir hakuri idan ta wuce.
Haidar ya juyo daga rakiyar Yagwalgwal ya
murda kofar dakin jawahir ya shiga, kamshin dadi
ne suka buge shi ya sheka ya karasa cikin dakin.
Tana zaune a gefen gadonta hada kai da gwiwa
tana shasshekar kuka, ya zauna a gefen gadon ya
dago ta ya kara ta da jikinsa ya rungume ta,
“Subhanallahi wannan jiki haka mai taushi da
dadin kamshi kamar atufa, Ubangiji ka nuna min
ranar da zan mallaki komai na yarinyar nan da na
nuna mata tsantsar soyayya da kaunar da ba a
taba nunawa wata ‘ya mace ba.
Duk zancen nan a zuciyarsa yake yi wanda har
ya so ya shagala cikin tunanin kyan kirar jawahir.
Sautin kukanta ne ya dawo da shi hayyacinsa.
Cikin taushin murya da magana kasa-kasa kamar
mai rada yake rarrashinta yana dan bubbuga
bayanta, “Sorry Babyna yi shiru haka kada kanki
ya zo yana ciwo kin ji baby na yi hakuri, ta dada
shagwabewa tare da langabewa a jikinsa tana
kuka kasa-kasa cikin sigar kissa da shagwaba
kukan nata me shiga rai da tsayawa masoyi a
zuciya.
Tuni kirjin Haidar ya fara bugawa fat fat,
“Subhanallahi ya salam wai yaushe zan mallaki
wannan tsantaararren jikin mai kama da robar
balo-balo?
Muryarta ya tsinkaya cikin rauni da taushi da
dadin murya tana cewa, “Yaya ka sake ni na
koma gida tun da kakarka ba ta son na zauna da
kai.”
Haidar ya ce, “A’ uxubillahi kada na kuma jin kin
furta wannan kalmar kin ji ko, don ubangiji yana
tsinewa duk matar da ta nemi mijinta da ya sake
ta, kada bacin rai ya sa ki rinka jawowa kanki
fadawa cikin fushin ubangiji kin ji ko? Yi saurin
yin istigifari.”
A hankali ta bude baki ta rinka nanata istigifari,
ya ce, “Yauwa Babyna Yagwalgwal ta ce a ba ki
hakuri. Zumbur ta mike ta shiga tolet don ba ta
son maganar don ita a zatonta tanda Yagwalgwal
take tsanarta da nuna mata kiyayya ba za ta taba
son ta ba.
Haidar kuwa binta ya yi da kallo komai nata sha
awa yake ba shi komai na jikinta burge shi ya ke
yi, wai shi ya zai yi da wannan zazzafar kaunar
da yake yi wa jawahir ne? Ta yaya zai yi ya
shawo kanta su kwanta gado daya ne da shi?
Duk dai da tanxu ba shi da karfin gaban da zai
tabuka mata wani abu to amma ko wasanni da
sun yi shi da ya ji ta kwance kan kirjinsa yana
wasa da wadannan tantsa-tantsan na shanun
nata(nono).
Duk dai da shi ya yi wasa da damar da ya samu
tun farko.
Ya dade a zaune yana zaman jira shiru-shiru
jawahir ba ta fito ba dole ya mike ya fita, tana jin
fitarsa ta fito ta sawa kofarta mukulli. .
Abu wasa-wasa jawahir ta kwana ta wuni ba tare
da ta fito Haidar ya ganta ba ko ta yi saken
kofarta a bude ya shigo. Sai dai wani abin
mamaki da safe za ta hada masa lafiyayyen
break a kicin din wajenta sai ta leko falon ta ga
ba kowa sannan ta jere masa kayan break din ta
kuma ajiye masa maganin da zai sha na lokacin
da robar ruwan Highland ta koma bangarenta ta
kulle kofarta, sai dai in Haidar ya gama shirnsa
ya sauko kasa ya hau tebir ya yi break ya dauki
magani ya sha ya jira ko jawahir za ta bude ya ji
shiru ya taba kofarta ya ji ta a kulle. A lokacin ya
juya ya koma sama sannan ya tashi ‘yar mulkin
tasa wato kausar sarkin ‘yan hutu, to wani abin
mamakin duk da yau kusan a falo ya wuni amma
be ga jawahir ta fito ba bare ya kalli idonta ya ga
yanda ta kwana. Sai da ya ji an yi kiran sallar
azahar ya daura alwalla ya fita masallaci amma
kafin ya dawo jawahir ta fito ta jere masa kayan
abinci, tuwon farar shinkafa ya tuku ya yi mulmul
da shi da miyar agushi, wadda don dahuwa kazar
da take ciki duk ta narke ta dagargaje a ciki.
Ta gasa masa naman rago mai ruwa ruwa ya sha
kayan kamshi ga tumatir da albasa kai dai
kamshi yake tashi. Sai lemon aya da ta hadawa
kanta ta zuba masa a jek ta cilla kankara ya sha
kayan kamshi, ta jere komai cikin kayatattun fulas
masu kyau ta sa farin kyalle mai dauke da
falawoyi a jiki ta rufe ta yi saurin juyawa ta koma
dakinta ta rufe sashenta ta shiga kicin dinta duk
ta gyara kayan data bata, ta wanke komai ta
goge ta mai da shi inda yake, sannan ta shige
tolet dinta ta saki shaya a kanta ta fara wanka. Karfe
biyu da rabi Haidar ya shigo gidan da carbi a
hannunsa, “Yan matan kausar ya ga daya a bakin
kofar falon tana gadin falon ta yi masa sannu da
zuwa ya wuce. Ya shiga falon ya taba kofar
jawahir a bame kamar yanda ta kwana. Ya
girgiza kansa kawai, shi jin kansa ya hana shi
kwankwasawa ya nufi bangaren kausar tana
zaune a kan kujera ‘yan matanta biyu suna
gefenta daya tana yanka mata tufa a kan filet
dayar kuma tana zuba mata abinci a daya filet
din, wanda ya kasa banbancewa da kuskus ne ko
burabusko. Yanda ya gan shi a dundunkule ya
sha ruwa ya yi sharkaf.
Ya zauna gefen ta ‘yan matan suka yi saurin
nikewa suka yi waje. Kausar ta dauki filet din
abincinta za ta fara ci ta kalle shi ta ce,
“Bismillah.” Ya ce, “Wa! Ni?
Allah ya sauwake na ci wannan abincin, ai sai na
yi amai.” Ta tabe baki ta ce, “Au kai fa ba ka cin
abincin masu aiki ko? Ka sa kanka a wahala don
yau na ga abin da za ka ci tun da na ga
Sarauniyar taka fushi take yi bare ta zo ta girka
maka.
Wai ni kuwa yau ka yi break? Don ban ji motsinta
ba bare na ji ko ta girka maka
Ya ce, “Ke za a tambaya ba tare muka kwana ba,
tsakanin ke da ita wa ya kamata ya yimin girki?
Ta tabe baki, “Ka san ni ban tashi a cikin wahala
ba don haka ba zan iya wani aikin komai ba.
Da kake maganar da ni ka kwana ai tausaya
maka na yi nake taya ka kwanciya don kada ka
kwana kai kadai, me kake iya tabuka min? Ka
riga ka zama nakasasshe, in ban da ka ishe ni da
tabe-tabe ka tayar min da hankali babu biyan
bukata.”
Ya daka mata tsawa tare da nuna ta da dan
yatsa, ke saurara kada ki sake ki kawo min
maganar banza a nan, da haka nake? Ko don
lalura ta same ni za ki gaya min maganar banza,
daure ki na yi ko cewa na yi dole ki zauna idan
kin gaji ba dole, ba zan danne miki hakki ba ga
hanya nan sai ki san inda dare ya yi miki.
A ranta ta ce, “Ba inda zan je gwarzon namiji
kamar ka ina zan iya barin ka, idan na yi sake ka
subuce min ta yaya zan yi na mayar da kamar ka
bare yanda na dandani zumarka ai sai dai na ga
ba ka samu lafiya ba tukunna zan ki zama da kai.
Ya gama banbamin fadansa ya fice yana tunanin
tsananin hakurin jawahir da kawaicinta. Ya ji
sallamar Hafsan faruk ya amsa mata cikin fara’a
yau ina megidan naki na gan ki ke kadai? Wallahi
yana office ka san bai taso ba, yanxu ma gidan
yini zan je ya ce na fara biyo wa na ga jikin naka.
Haidar ya ce, “Jiki Alhamdullahi.” Ta zauna a
falon suka gaisa ta ce, “Ina matan gidan ne? Ya
ce, “Bari na kirawo miki su. Ya kwankwasa kofar
jawahir ya ce, “Ki fito kin yi bakuwa, Hafsa ce ta
zo.
Ya juya ya nufi dakin kausar ya ce ki zo kun yi
bakuwa, “Tace, “Wacece?”
Ya ce, “In kin zo kya gani, “Ya juya ya fita. Jawahir
ta bude falonta ta fito cikin dammamiyar riga
body hook da jeans din wando da ya dame mata
cinyoyi daga kasa kuma yake da fadi, kanta ba
dankwali sai kananan kalba da ta tufka ta a
bayanta ta kwanto guda biyar gaba. Ta yi kyau
sai zuba kamshi take yi ta taho da dan gudunta
ta fada jikin Hafsa tana dariya. Haidar kuwa ya
zuba mata ido kallon ta yake yi yana hadiyar
yawu, yarinyar nan kuwa ta san yanda take rikitar
masa da hankali? Ta san yanda kirjin nan nata
yake dauke masa hankali kuwa?
Kausar ta shigo tana yatsina kujerar da Haidar
yake kai ta nufa ta zauna masa kan cinya ya ce,
“A’a ke me ye haka? Ta ce, Haba Darling kai ma
ka san nan ne wajen zamana don ka riga ka
sabar min.
Ya ce, “Amma kina ganin bakuwa a wajen ko? Ko
dan rashin kamun kai.” Ya zame ta takaici da
tsantsar kishi suka tokare zuciyar jawahir kamar
ta yi kuka ta dan daure ta ce, “Hafsa tashi mu
koma daki. Hafsa ta mike yayin da take gaisar da
Kausar. Suka shiga dakin jawahir Hafsa ta ce, tab
amma kina shan kallo, haka Kausar din take ba ta
da kunya? Jawahir ta ce, “Ina ruwana da ita? Me
ya dame ni da ita? Tun da ba zamanta nake yi
ba.
“Yanzu haka za ki zuba mata ido tana iskanci? In
ni ce ai sai na nuna mata cewar ita karamar ‘yar
iska ce, bare yanda na ga hankalinsa da
tunaninsa duk ya raja’a a kanki me ya sa ba za
ki sakar masa jiki ku rinka farantawa juna rai
ba.?
Jawahir ta ce, “Kyale ni Hafsa ni na san halin da
zuciyata take ciki a kan son Haidar, to kin san
wani abu da yake damuna? Na tsani na bude ido
na ga Kausar tana yi masa magana ko tana
kallonsa bare ta hada jikinta da shi wallahi sai na
ji kamar na je na shake ta ta mutu ko na huta.
Hafsa ta ce, to bari na ba ki shawara wallahi
yanzu yanda na fuskarki mijinki yana tsananin
sonki mai zai hana ki fito masa da taki irin kissar
kin san Allah nan gaba sai kin dinga tausaya
masa don bin ki zai dinka yi kamar rakumi da
akala saboda ‘yar uwa ba dama ce fa ke, dole ne
ki rikita Haidar, irin wannan cika haka komai ya ji,
me zai hana hankalin Haidar tashi da gigicewa a
kan ki.?
Jawahir ta ce, “To ai ni ba ki sani ba kunyar hada
jiki nake yi da shi sabo da sai na ga kamar zai ce
min ba ni da kunya.
Hafsa ta ce, “Tabdi jan zauna a barki a baya, au
na gaya miki cikin dabara da hikima za ki rinka
sakin jiki da shi kina yawan zama a duk inda
yake ki rinka yawaita kwalliyar da za ta rikitar da
shi kamar irin wannan sai kin zo kina ba ni labari
da bakinki, “Hafsa ta yi zumbur ta mike bari na yi
sauri na leka gidan wunin nan na koma gida kada
Oga ya dawo daga office ba na nan.
Jawahir ta yo mata rakiya Haidar yana falon tayi
masa sallama Hafsa tana gaba jawahir tana biye
da ita Hafsa ta fita daga falon jawahir za ta fita
ke nan Haidar ya yi magana kasa kasa, “Kada ki
fita harabar gidan nan da direba suka xo kada ya
ganki. “Jawahir ta ja tunga suka karasa sallama
da Hafsa tare da yi mata alkawarin zuwa in an
kwana biyu, ita kuma ta tafi.
Ta juyo daga rakiyarta har ta isa kofar dakinta
ya kirawo ta. Jawahir ta tsaya kam, a wajen ba
tare da ta juyo ba ta ce na’am, ya lankwasa
murya ya a raunane ya ce, “Yanzu haka za ki bar
ni na wuni da yunwa bayan kin san ba cikakkiyar
lafiya ce da ni ba, ga shi lokacin shan maganina
har yana kokarin wucewa, ta juyo a raunane cikin
tausayawa ta ce, yanzu ba kaci abinci ba.?
Ya dada langabewa to wa zai ba ni? Ke da kika
san ciwona kike girka min yanzu gashi ba ki yi
min ba. Ta ce, yaya na girka maka mana ta nufi
tebir din ya biyo bayanta yanda ta ajiye haka
yake ba wanda ya taba. “Ta bude komai ta jawo
filet ta fito da tuwo malmala biyu ta cire su daga
cikin ledar da ta zuba a filet din, ta zuba masa
miyar a daya filet din ta tura masa gabansa
kamar mai jira ya fara ci ta tsiyaya masa kunun
aya, ya yi sanyi kuwa karara a gilas kof ta ajiye
masa a gefe. Ta dan langabe kai ganin ya ture
filet din tuwon ta ce, duk yunwar da kake ji dan
wannan za ka ci? Ni jira nake fa ka cinye na kara
maka wani. Ya ce, “Haba Babyna na cinye
malmala daya da rabi ai dole na ji na koshi.
Ta dan marairaice cikin shagwaba ta ce, to ci
naman.” Ta bude masa kamshinsa ya bige shi
har na ji yawuna ya tsinke, ya kamo ta ya zaunar
da ita a cinyarsa to zauna mu ci tare don na ga
alamar ba ki ci komai ba.
Ta langwabe a jikinsa ta ce, “Uhm Yaya na ci
abinci fa a koshe nake.”
Ya ce, to gaya min me kika ci?
“Yaya na sha yogourt da nama na kuma sha
wannan. Ta nuna kunun ayar, da yake kofin. Ta
dauko ta sa masa a bakinsa yaya kai ma dan sha
ka ji akwai dadi. Ya kwankwada, “Uhm akwai
dadi, dan karamin, ta noke tana yi masa dariya
kasa-kasa ta ce, “Yaya ka ci naman tukunna
kada ka cika cikinka da ruwan kunun aya.
Ta yago naman ta sa masa abaki ya kama
taunawa yana lumshe ido um carkwai wannan
dadin haka kada ya tsinken kunne, “Ta kama
shasshekar dariya tana langabewa a kirjinshi tana
yago naman tana ba shi a baki.
Duk abin nan da ake yi dauriya kawai yake yi don
halin da jawahir ta tsunduma shi gaba daya ba
shi da wani kuzari ta dada rikita shi da kaunarta
da sha’awarta ta mamaye kowacce gaba ta
jikinsa, ta mike yaya ka ji ana kiran sallar la’asar
mu je mu yi sallah. Ya ce, to babyna na gode
Allah ya saka da Alkhairi Ubangiji ya yi miki
tukuici da gidan aljanna. Mu je na raka ki dakinki
ko babyna ta langabe a gefensa yaya kada a
tayar da sallah a masallaci ka je ka yi alwalar.
Ya ce, “A’a yau a tolet dinki zan yi alwalar ta yi
dariya to Yayana mu je.
Yau dai a dakinta ya yi sallah don shi ya ja musu
jam’i, ya dade yana kwararo musu addu’a sannan
suka shafa. Yau dai wuni guda cikin farin ciki da
annushuwa suka yi shi, gaba dayan su kokarin
farantawa junansu rai suke yi bugun kofar da ake
yi musu ne kamar za a balla ya sa Haidar saurin
mikewa cikin fushi ya je ya bude, Kausar ce a
tsaye tana girgiza kugu tana taunar cingam tare
da yamutsar fuska, “Lafiya.?
Abin da ya ce mata kenan.
Cikin tsiwa ta ce, “To me za ka yi min ko ka
manta cewar yanzu kai ba cikakken namiji ba ne
ka zama miskini? Ai ni ba ka da amfani a wajena
ita ma da ka ga tana rawar kafa don duk haka
kuke ne ita ma ba me lafiyar ba ce don haka ta
nakasta ka
Ya daka mata tsawa, “Ke kausar ki shiga
taitayinki ni ba sakaran namiji ba ne, ba ki isa ki
wulakanta ni ba.
Ita ma ta hau shi da ma sifa to ka sake ni mana
haka kawai don zalinci ka ajiye ni ka san ba iya
biya Min
bukatata za ka yi ba, kana so da aurena ne na
rinka bin maza kome kake nufi?”
Ya ce, “To shi ke nan na ji ki yi hakuri zan yi
shawara.
Ta ce, “Ina son zuwa gidan kawata. Ya ce, “A
dawo lafiya amma ki dawo da wuri tafi da direba
can sai ya kai ki. Ta juya ba tare da ta ce masa
komai ba.
Kausar tana daukar mota ba ta wani tafi da
direba ita kadai ta yi tafiyarta ta nufi gidan wata
kawarta, ita ma ‘yar Abuja ce aure ne ya kawo ta
nan kano.
Saddika ta tare ta da murna kausar amare yau
nake zancen mun kwana biyu ba mu hadu ba, ina
so in je gidanki ashe kina tafe. Ina angon naki ya
barki kika taho ke kadai.?
Kausar ta dauki lemon da ta ajiye mata ta kurba
ta ajiye ta ce, kyale angon nan nawa ai ni na
kusa barin gidansa. Saddika ta dafe kirji, “Haba
kausar me ya yi zafi haka? Ki tuna irin wahalar
da kika sha kafin ki samu Haidar ya amince ya
aure ki, yanzu idan kika rabu da shi ta yaya za ki
maye gurbin gayen yaro mai jini a jika da naira
kamar Haidar?” Kausar ta tabe baki tare da yin tsaki ta ce, “Ai
wadannan abubuwa da kika lissafa duk sun tashi
a banza don yanzu ya zama solobiyon namiji ba
abin da yake iya yi wa mace.
Saddika ta ce cikin razana, “Ban fahimce ki ba,
me kike nufi?
Kausar ta ce, lokacin da na auri Haidar na same
shi gwarzon namiji me cikakkiyar hallita wanda
ya iya jiyar da mace dadi ko ta ina ban taba
zaton zan iya rabuwa da Haidar ba don ta ko ina
ya yi min
Zamzam ga shi hadadden miji na nunawa sa’a, to
dan bakin cikin matarsa ganin ba ta da lafiya
komai bai taba gudanuwa a tsakaninsu ba shi ne
ta yi min bakin ciki ta kwada masa abu a
gabansa ta nakasta shi har kwanciya ya yi a
asibiti amma likita ya ce ai ya riga ya nakasta.
To yanzu ya dawo gida sai dai in mun kwanta
waje daya da shi ya ruda min jiki da wasanni ba
ya iya aikata komai wallahi ni na gaji gwanda ya
sake ni na huta.
Saddika ta ce, “Gaskiya yarinyar kamar ki da
kuruciyarki da komai zaman hakuri bai kama ki
ba, to amma ba kya tunanin wata rana zai samu
lafiya ki zo kina takaici?
Kausar ta ce, “Ke kuma kin ji ki da wata magana,
likita fa ya ce min ba shi da wata ranar samun
lafiya kina so na shiga yawon bin maza da
aurena ne?
Kinsan ko musulunci ya zama dole ya sake ni.
Saddika ta ce, “Gaskiya ne da ki cilla kanki a
halaka gwanda ku rabu kawai ki auri Bomboy ………… to amma ba kwanaki na ji kin ce
kina da ciki ba.”?
“Ba ciki ba ne ashe batan wata na yi daga baya
na ga al’adata ta zo. A nan ta yi sallar magariba
suka ci abinci ta yi sallar insha sannan ta tafi
gida.
.
SALON SO
PART 28 to 32.
.
Haidar da jawahir suna zaune a falo suna kallo
jawahir ta kama hamma Haidar ya jawo ta jikinsa
yana shafata ba dai bacci za ki yi ba ki bar ni.?”
Ta daga kai ka san ni da baccin wuri bari na je
daki na kwanta, “Ya langabe murya gaskiya ba za
ki tafi ki bar ni tun yanzu ba.”
Ya rungume ta ya gyara mata kwanciya a jikinsa
yana shafa kanta yi bacci a haka in na gama
kallo na kai ki dakinki. Cikin mintina kadan bacci
ya kwashe jawahir dadi ya cika zuciyar Haidar jin
jawahir rungume a jikinsa taushin fatarta da
kamshin jikinta shi suke dada sa shi nishadi.
Kausar ta yi sallama ta shigo falon ba dan sanin
muhimmancin sallama a addinin musulunci ba da
bai amsa mata ba. Ya dako kai ya kalle ta, “Ina
kika je sai yanzu da daddaren nan za ki dawo
bayan na ce ki dawo da wuri.?”
Ta kalle shi ta ja tsaki, “To ina ruwanka da
dawowata da wuri ko ba da wuri ba? Kai ba wani
cikakken namiji ba bare ka ce za ka yi kishina.”
Jawahir ta dan motsa ya sake rungume ta yana
jijjigata kamar yarinyar goye. Kausar ta yi tsaki
an dai fadi ba nauyi miskinin kawai kana
luguiguita yarinya kai ba wani katabus za ka iya
yi mata ba.” Ta shige dakinta Haidar kuwa ya yi
mata shiru ne gudun kada jawahir ta farka amma
ya ji haushin maganar da ta yaba masa. Da ya ji
kallon ma ya ginshe shi ba zai iya ci gaba da
kallon ba, don tsananin dacin da zuciyarsa take yi
Jawahir da tun shigowar Kausar ta farka ta ji duk
abin da kausar ta gayawa Haidar ranta ya yi
mugun baci, ba ta san sanda hawaye ya fara
zubo mata ba. Haidar da ya yunkura zai mike da
jawahir a kafadarsa sai ya kula hawayen da take
yi hankalinsa ya sake tashi ya kira sunanta,
“Jawahir lafiya?”
Tayi saurin zamewa daga jikinsa ta durkusa kasa
tana kuka ta fara rokonsa don Allah don Annabi
yaya ka yi hakuri ka yafe min abin da na yi maka,
ni na jawo maka matsalar da kake ciki wallahi
tallahi ba da niyya na yi maka haka ba kan
tsautsayi ne da kaddara, ina neman afuwarka da
gafararka ko na samu sassauci a zuciyata.”
Ya mike tsaye ya kamo kafadunta ya dago ta ya
rungume ta a jikinsa yana share mata hawayen,
“Yi shiru babyna daina kuka ba so ki kuma irin
wannan tunanin a zuciyarki, ki sani duk abin da
Allah ya yi zai samu bawa daman tun fil’azal
rubutacce ne, kuma babu wanda ya isa ya
kankare shi ko ya goge shi. Don haka ki kaddara
daman can Allah ya yi hakan za ta faru da ni, don
haka ni ba na so na ji kina cewa ke ce sanadi
kada ki kuma fada, ni na yarda da kaddara don
haka ba na zarginki da komai, ki kwantar da
hankalinki ba na son ganin ki cikin damuwa, kin ji
ko. Ta daga kai alamar amsawa, “To mu je ki
kwanta. Yana rugume da ita har dakinta, ya raka
ta tolet ta yi borush ya riko ta sai da ya kwantar
da ita a gadonta ya ja bargo ya rufe ta ya kunna
mata A.C ya sumbace ta a kumatu ki yi bacci
lafiya babyna. Ya juya ya fita ya nufi nasa dakin.
Yana fita jawahir ta mike ta dauko tsaleliyar rigar
baccinta ta saka ta shafe jikinta da humra. Ta
dade feshe dakin da Air Freeshner nan da nan
sanyin A.C da daddadan kamshi suka shiga tashi.
Ta matsa mouth freeshner a bakinta nan da nan
sanyayyen kamshi ya rinka fita ta haye gadonta
ta yi lumtsim da ita.
Haidar ya shigo wanka ya fito ya shafe jikinsa da
turare ya hau gado dan kwanciya amma ina
baccin ya gagara sai juyi yake yi yana tunano
lallausan jikin jawahir da taushinsa, ya san ina
bacci zai dauke shi, ya sa kayan baccinsa ya fito
ya rufe dakinsa ya nufi dakin jawahir.
Ya sa safayar mukullinsa ya bude dakin ya shiga
ya mayar ya rufe. Ya shiga cikin dakin nata
wanda sanyin A.C ya gama ratsa shi, ga man
nan na turarenta mai dadin kamshi yana tashi.
Ya kunna fitila ya yaye bargon da ta rufa ya kalle
ta cikin tsaleliyar rigar baccinta wadda ta kara
fito mata da sigar kyanta, baccinta take yi hankali
kwance.
.
SALON SO
PART 33
.
Ya kashe fitilar ya hau gadon ya shiga cikin
bargon ya sa hannu ya shafo ta. Cikin razana ta
farka a firgice ta yi zumbur ta mike tsorace tana
wayyo Allah na Yaya na shiga uku, wayyo Allah
yaya na ka zo ka cece ni.” Ya mike shi ma ya
riko ta, ta dada firgicewa tare da sa kuka, “Wayyo
na shiga uku yaya ka zo ka cece ni.” Ya ce,
“Jawahir meye haka? Ni ne fa Yayanki Haidar ba
ki gane ni ba ne? Ya kunna fitila ta daga kai ta
kalle shi ta mayar dakanta kan kirjinsa ta kwantar
tana ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya zagaye ta ya
kashe fitilar ya yi gadon da ita. Ya kwanta tana
manne a jikinsa, jikinta sai bari yake yi na
tsoratar da ta yi.
Zuciyar Haidar fes yau ga shi manne da jawahir
dinsa, abar sonsa shi kuwa ya taba jin jiki me
taushi da santsi kamar na jawahir dinsa? Shi dai
bai gushe ba yana sambatu da jin dadin tattausar
jiki har bacci ya kwashe shi.
Da asuba ya riga ta tashi sai da ya dauko alwala
sannan ya tashe ta ta tafi yo alwala kafin ta
dawo ya tayar da raka’atainil fajri ita ma ta tayar
suna idarwa suka tayar da sallar asuba Haidar ya
ja musu limanci.
Suna idarwa suka ja carbi suka yi ta yin addu’a
har suka shafa ya bude musu kur’ani suka biya
tare suka sake yin addu’a suka shafa.
Ta durkusa gabansa yaya ina kwana. Ya amsa
cikin murmushin jin dadi kin kwana lafiya yaya
tsoro? Ta yi murmushi ta mike ya ce, “Ina za ki?
Sai da ta rissana sannan ta ce, “Kicin za ni. Ya
ce “A’a taho kwanciya za mu yi suka koma gado
suka kwanta.
Bacci ya dade da kwashe su wani gigitaccen bugu
ne ya farkar da su a wahalce Haidar ya zare
jikinsa daga na jawahir ya mike ya nufi kofar ya
bude. Kausar ce ta cukuikuye masa wuyan riga
tana cewa, “Kai wallahi sai ka sake ni takardarta
za ka ba ni ba zan iya zama da miskini ba.
Ya wankawa fuskarta mari ya ce, “Ni kika
shakarwa wuyan riga, dan iska za ki mayar da
ni? An ki a sake ki din ki je ki gayawa duk wanda
za ki gayawa. Ta dafe kunci ni ka mara to
wallahi sai ka gane kurenka. Ta juya ta yi dakinta
ta dauko mayafi ta yi waje ta hau mota ta tuka
kanta ta fice daga gidan.
Kotu ta nufa ta shigar da kara.
Haidar yana gida sun gama shirinsu sun ci
kwalliya kamar masu xuwa fati, sun gama
karyawa ke nan yaron gidansa ya yi sallama a
kofar falon aka amsa masa ba tare da ya shiga
ba ya ce Yallabai ana sallama da kai a waje.
Ya ce, “Okey ga ni nan fitowa.
Ya mike ya fita
Da mamakinsa suka gaisa da bako ba tare da ya
san shi ba. Bako ya mika masa zungureriyar
takarda, “Ni yaron alkali ne ga shi wannan
sammaci ne daga kotu matarka tana kararka.
Haidar ya rinka juya takarda a hannunsa cikin
mamaki ya ce, “Okey je ka na gani. Yaron alkali
ya juya ya tafi, Haidar ya shiga gida
Ya cewa jawahir zai je gida yanzu Abbansa yana
son ganinsa. Ta yi masa kyakkyawar addu’a tare
da fatan Allah ya dawo da shi lafiya.”
A hankali ya rinka juya motar yana mamakin hali
irin na kausar. Yana isa gida ya samu Abbansa a
falo da Anti suka gaisa sai ya mikawa Abbansa
takardar da aka kawo masa ya ware takardar ya
karanta. Abba ya hangame baki tare da yin
salati. Cikin yaya? Me ya hada ku? Haidar ya
kwashe labarin komai ya gaya masa. Abba ya
kama salati amma wannan yarinya ta ci mana
mutunci. Anti ta ce ka sake ta kawai ba sai an je
gaban kotu ta tsinka mu ba.
Nan take Haidar ya rubuta mata takardar saki
daya Anti ta karba ta bawa me aikinta tace ta yi
sauri ta je direba ya kai ta gidan Saddika kawar
Kausar su kaiwa Kausar din.
Kausar kuwa tana ganin takarda ta cika da farin
ciki inda a nan take ta yi wa alkalin waya ta ce
ta janye shari’ar ta yi sauri ta koma gidan Haidar
daman ta sa ‘yan matanta sun hada mata
kayanta na sawa da duk wani abu na amfaninta
na kwalliya suka judo mata akwatunanta suka
loda su a but direba ya je su zuwa Airport suka
yanki tikiti suka nufi Abuja.
Abbab Haidar ya dube shi ya ce, “Bana so ka sa
damuwa a ranka bare ka zo abin yana damunka
daman na gama shirya muku tafiya xuwa kasar
waje Kai da
jawahir za ku je asibitin Cairo sabo da haka ku je
ku fara shiri nan da sati daya za ku tafi.
“To Abba mun gode Allah ya saka da alheri
Ubangiji ya kara budi.
Haidar ya koma gida yake gayawa jawahir abin
da ya faru duk da jawahir ba ta son zaman
Kausar a gidan amma ba ta ji dadin sakin da
Haidar ya yi mata ba. Ba su da wani lokaci sai
na shiri da ziyartar ‘yan uwa suna yi musu
sallama.
Ranar da suka je Abuja gidan Ankul Anti Maryam
ta ce ya dai ‘yata in ce ko dai har yanzu kina
shan abubuwan da na gaya miki?
“Ai Anti tun ranar da na bar gidan nan ban yi
fashin shan kayayyakin nan ba, don wasu
abubuwan ma idan na hada har da Yayan muke
sha ba tare da ya san ko meye ba.
“Yauwa diyata na sara miki yanzu na san kin
tsumu kin cika da ni’ima sosai karyar Haidar ya
dandana ki ya kuma kusantar wata matar.
“Allah Auntyna, “Suka tafa. Aunty maryam ta
kwaso mata wasu hadin da ta kuma yi tare da
wani turare na gama da ake yi kafin saduwa da
miji, tsaraba dai sosai ta hada mata don tafiya
Cairo.
Sun je gidan Inna gidan Yagwalgwal, gidan Faruk,
gidansu Bilkisu, gidan Abba, gidan Dady, duk
gidan dangi da ‘yan uwa babu inda ba su ziyarta
ba.
Sha biyu na dare jirginsu ya tashi xuwa kasar
Egypt wato inda za su sauka a birnin Cairo inda
asibitin da za a duba Haidar yake.
Ranar da suka dira gajiya ba ta bar su ba
ramuwar bacci suka yi sai washegari suka isa
asibitin. Aka saka Haidar a computer cikin lokaci
kankani suka gano matsalar ba tare da bata
lokaci ba suka yi masa aiki suka kwantar da shi a
asibitin tsawon sati daya saboda magungunan da
yake sha.
Cikin ikon Allah Haidar ya ware ya samu sauki
kamar ba shi ba. Asibitin sun sallame shi sun
dawo Hotel din da suka sauka. Yana kwance a
kan kafet jawahir tana masa tausa sannu a
hankali yana wash! Wash!! Tare da lumshe ido.
Yau duk ya wani shagwabe mata ya narke mata
ta hana ta sukuni daga ya ce, nan yana cuwo sai
ya ce can. Sai bin sa take da lallama cikin
tausayawa da kyar ta samu ya yi bacci ta shiga
tolet ta yi wanka ta fito ta gyara jikinta da
hadadden mayuka masu kamshi tare da turarukan
da ta mulke jikinta kowacce gaba ta jikinta
kamshi take fitarwa.
Ta saka ‘yar bingilar rigar bacci iya cinya me
hannun shimi ta dada feshe dakin da Air
freeshner. Dakin ya dau sanyi da daddadan
kamshi ta haye gado ta shiga bargo ba ta jima ba
bacci ya yi awon gaba da ita.
Haidar da idonsa yake a kanne yana kallonta ya
mike shi ma ya shiga tolet ya watsa ruwa ya fito
ya gama shirinsa ya hade jikinsa da kamshin
turare, ya kashe fitila ya hau gadon ya kunna dim
night dakin ya yi shiru ba ka jin motsin komai sai
karar A.C Haidar ya manne ta a kirjinsa ya matse
ta gam, ya tura harshensa cikin bakinta ya rinka
tsotsa yana wani salo na daban. Da ya gangaro
zuwa kirjinta yayin da ya zare karamar rigar da
take jikinta.
Bayyanar na shanunta a waje shi ya kara gigitar
da shi jikinsa ya hau bari da rawa ya gigice ya
dimauce har ya manta a wacce duniyar yake.
“KASH
MASU KARATU KU YI MIN HAKURI MU HADU A
KASHI NA UKU DON JIN HANYOYIN DA JAWAHIR
TAKE BI DON SIYE ZUCIYAR HAIDAR YA ZAMO BA
SHI DA TUNANIN WATA DIYA MACE SAI ITA.
SANNAN KU JI KAUSAR ZA TA AURI BOMBOY DIN NE
KO KUMA DAI………… KU BIYO NI
A KASHI NA UKU
AMMA SAI NAGA
COMMENT DA YAWA IDAN DAI
DA GASKE KUNA SUN CIGABAN.
.
SANNAN MURA TA RIKE NI WATA/WANI TAYI/YAYI VOLUNTEER TA/YA SAYO MIN TOM-TOM IDAN KUMA NAJI SHIRU…………. HMMMMMM
.
SAI MUN HADE.
.
(((((SALON SO)))))
(((((PART 34))))))
.
Tunda kun hana ni Tom Tom dina shikenan, amma fa…….. Ko da yake ba sai na fada ba.
.
Jikinta ya rinka rawa da karkarwa kamar mazari. Ta
kasa wani katabus sai kuka data ke yi tana yi masa
magiyar daya hakura ya kyale ta.
Haidar kuwa kusan ma iya cewa hankalinsa baya
jikinsa saboda samvatu da ya rinka yi yana surutai.
Hankalin jawahir ya tashi, ta rinka dukan Haidar tana girgiza shi yayin da ta tsala wata kara shi
kenan Haidar ya cika aiki.
Sai da Haidar ya gama samun nutsuwa hankalinsa
ya dawo jikinsa sannan ya kula da halin da jawahir
take ciki sai nishi take yi sama-sama fuskarta da
fulon da ta ke kai sun jike da gumi da hawaye. Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, ya dago ta yaga ta
koma ta langabe a hankali ya ajiye ta a gadon ya
nufi tolet ya cika baho da ruwan zafi ya zuba datol
yaje ya dauko ta ya sakata a ruwan zafin ya rinka
buda mata kafafuwanta ruwan zafin yana ratsa ta.
Ita kuwa Jawahir sai ‘yar kara take yi irin ta galabaitar nan da wahala. Haidar kamar zai yi kuka
saboda tsananin tausayinta. Sau uku yana canza
mata ruwan ya karanta mata niyyar wanka ta fada
a zuciyarta, ya yi mata wankan tsarki shima ya yi
yana dota a tawul ya kawo ta dakin ya zira mata
doguwar riga shima yasa jallabiya. Ya dauki waya ya bugawa likitan hotal din cikin
lokacin kankani ya zo ya duba jawahir ya yi mata
allura ya ba wa Haidar magungunan da zai bata
tasha.
Likita ya yi musu sallama ya fita Haidar ya tsiyaye
mata madarar kwali a kofi tana manne a kirjinsa duk ta wani langabe don bata da kuzarin komai sai
tsananin kasala da ciwon jiki ga radadi da yake
damunta.
Ya dago kanta ya sa mata kofin a bakinta ta
langabe cikin shagwaba ta ce ni bazan iya sha ba,
yi hakuri bebi na dan sha kurbi kadan kin ji kinga magani zaki sha don jikinki ya wartsake
Ta kurba ta hadiye da kyar, ta kau da kai, “Yi hakuri
dan kara kadan kinji bebi na.
Da lallashi da lallama ta dan sha da yawa ya bata
maganin da ruwa ta sha ya dauke ta suka koma
daki lokacin karfe biyu na dare, ya kwanta a gadon ya dorata a kirjinsa ya rungume ta tana ta faman
raki wayyo yayana bayana kuguna kaina yaya
ko’ina ciwo yake yi min
“Sannu bebi na Allah ya yi miki albarka hakika kin
cika ‘yar halak da ki ka kawo min budurcinki lafiya.
Allah ya yi miki albarka Allah ya saka miki da alheri. Ubangiji ya bamu zuri’a ta gari.”
Ya rinka shafa bayanta yana yi mata tausa kadan-
kadan, yana mammatsa mata jikinta bacci ya
dauketa. Haidar ya rungume ta ya kankame kamar
wani zai kwace masa ita, amma maganar bacci
babu ita don tsananin dadi da zumudi ya hana shi gyangyadawa.
Mamaki ne ya cika zuciyar Haidar yanda ya ji
dandanon zumar jawahir yanzu jawahir din da ya
raina ce Allah ya wadata ta da ni’ima haka? Lallai
dan hakin da ka raina shi yake tsone maka idonka.
Yau dai kam ga shi jawahir ta tsone masa idon, lallai Allah yana sonsa da ya dawo masa da jawahir
bayan subuce masa da tayi a baya, Allah ya taimake
shi bai yi wautar sakin ta ba.
Ai dole ne ya tashi ya yi nafila don nuna godiyarsa
ga ubangiji a bisa wannan baiwa da Ubangijin ya yi
masa, na mallaka masa gwarzuwar mata mai cikar halitta da wadatacciyar ni’ima.
A hankali ya zare jawahir daga jikinsa ya kara mata
fulo don kar ta farka ya nufi toilet ya dauro
kyakkyawar alwala ya zo ya fara nafula raka’a
goma sha biyu ya yi wa Annabi salati kafa dubu, ya
daga hannuwansa sama yai ta kwaraea addu’a, yana yiwa Allah kirari da yaba su zaman lafiya da
zuri’a me albarka shi da matarsa jawahir.
Sai da aka yi kiran assalatu ya tashi jawahir suka yi
sallar asuba, suka koma suka kwanta.
Sha daya
na safe Haidar ya farka ya zare jikinsa a hankali ya nufi toilet ya fara wanka
Jawahir ta bude idonta ta tashi ta daddogara a
hankali ta fito daga wannan dakin ta shiga dayan
itama ta fada toilet
Da yake falo ne da dakuna biyu a cikin falon wanda
suka kama. Jawahir ta fito daga wanka ta tsane jikinta da tawul,
ta shafe jikinta da hadaddun mayukanta masu
kamshi da sa taushin fata hade da santsin jiki. Ta
rinka mulke gabobinta da hadaddun turaruka na
jiki masu dadin kamshi.
Ta tsala kwalliyar fuskarta yanda yaka mata fuskar sai sheki take yi ta yi sumul sumul abun sha awa.
Ta saka wani tsadaddan farin yadi sol mai dishi-
dishin gwal din a jiki ‘yar karamar riga ce fitet me
dan guntun hannu rigar ta yi mata cif a jikinta. Sai
siket din da ya yi mata tsantsan duk wata sura ta
jikinta ta bayyana ba ma kamar kirjinta da yake cike da dukiyar fulani a tsattsaye suna barazanar
tsokane idon me kallon su. Ta sha adon gwal yari
da sarka manya ga awarwaro da zobuna tuni ta
dauki kyalli tana sheki
Tasa farin takalmi tana fesa turare ta ji dhigowar
Haidar ta yi saurin boyewa a cikin labulaye: Haidar shima ya shirya cikin wani lafiyayyen boyel fari kal
me laushi sai fitinan nan kamshi ne yake tashi a
jikinsa kamar ya yi barin turare.
Ya shigo dakin ya kama wara ido don ganin in da
zai hango tauraruwarsa ga shi dai duk kamshinta
ya cika dakin. Kafarta ya hango ta kasan labulan ya nufo wajen
ya janye labulan tasa hannu rufe fuskarta. Ya tsane
yana karo mata kallo cikin zafaffiyar kaunarta da
matsananciyar sha’awarta.
Ya jawo ta jikinsa ya manne ta a kirjinsa yayin da
kaunar ta take dada ratsa zuciyarsa. Cak ya dauke ta yayo falo da ita suka zube akan
kafet don karyawa, tana makale a jikinsa shi ji yake
ina ma zai iya tsaga jikinsa ya tura ta ciki da sai ya fi
masa sauki da yanda kaunarta take addabarsa a
zuciyarsa.
A baki ya rinka ba ta break din cikin lallashi da lallama don shi da da hali ma tauna mata zai rinka yi
don ta samu saukin hadiya.
Sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya rabu da ita
shima ya ci ya yi kat.
Ya shiga wasanni da sassan jikinta in da ita kuma ta
takure waje daya ta ki bude fuskarta. Ya dauke ta cak ya yi gado da ita yana cewa “To
bari mu maimaita abun jiya tun da kin fi so ko?’
Cikin marairaitar murya ta ce, “Wayyo Yaya don
Allah ka kyale ni bana so yayin da ta kwabe fuska
take kokarin yin kuka.
Ya rungume ta “Sorry bebi na kada ki yi kuka da gangan nake yi miki. Rufe idonki, “Ta rufe yayin da
ya saka mata ‘yar batta guda biyu manya a hannun
nata duk ya bude su.
Ya ce ta bude idonta tana budewa taga custume
yari da sarka da zobe manya tafka tafka kirar dubai
sarkar mai harafin H/J, sai daya battar kuma manyan warwaraye ne guda hudu gaba daya
Daimond kudinsu a kalla zasu yi dubu dari biyar da
doriya.
Bude baki tare da kwalalo ido ta ce “Yaya wannan
fa?
“Kyauta ce nayi miki don farin cikin yanda na riske ki.
Ta kankame shi cikin murna yayin da ta lalubi
bakinsa ta yi masa kyakkyawar sumbata, ta ce
“Yaya na gode Allah ya saka maka alheri Ubangiji
ya raba ka da sharrin makiya.” Ya ce “Amin babyna,
na gode da addu’arki Allah yasa mun samu rabon bebi a daren jiya ko kuma in an jima mu samu.”
Cikin shagwaba ta bigi kirjinsa “Um, um ni dai yaya
ba za’a kuma ba da ciwo.”
“To shi kenan kada ki yi min kuka ma arahar
hawaye.”
“Yaya ya aka yi ka samu masu harafin sunanmu.?” Ya ce, “Ai tun ranar da muka fara ziyartar asibitin
kafin ayi min aikin nan naje gurin da suke kerawar
nasa su kera min don zuwan wannan rana.
“Kai Yaya amma kuwa na gode Allah ya saka da
alheri
Ya dora hannunsa akan bakinta ya ce “Shit bana son yawan godiyar nan kuma ki cire wannan
Yayan da kike gaya min bana so.
Cikin kashe murya da kissa ta ce, “To me zan dinga
ce maka?
“Ke za ki zabo da kanki ki rada min.
Ya kawo kunnansa daidai bakinta “To gaya min naji”.
Cikin kasa kasa da murya ta ce, “My love yayi
maka?”
Ya rungume ta yana ihun murna yayi ya yi kwarai
babyna kin iya zaben suna. Ta rufe idonta tana
dariya. Ta kama lumshe ido irin na me jin bacci. Ya ce, “Bacci babyna.?” Ta daga kai kwantar da ita a
kan gadon to kwanta na yi miki tausa.
A hankali ya rinka yi mata tausar yana dan matsa
mata jikinta. Sannu a hankali bacci yayi awon gaba
da ita ya zuba mata ido yana kallon tsabagen kyau
da Allah ya bata. Ga komai nata cif-cif ba abin da ya fi ba shi mamaki yanda ya jita tamtsan cike da
ni’ima ga kirjinta cike da dukiyar fulani abun da yafi
sha’awa da daukar hankalinsa a jikinta.
Shima kwanciyar ya yi ya manne a jikinta ya
kankame ta har sai da ta yi ‘yar kara ta ce my love
sannan ya sassauta mata rikon. Sai bayan Azahar suka tashi suka sake sabon wanka tare da yin
alwala ya ja musu limanci suka yi sallar Azahar.
Daga nan suka sake sabon shiri shigar kananan
kaya suka yi ke in kin gansu sai ki zata Indiyawa
ne. Suka ci kayataccen abinci me rai da lafiya,
Haidar ya jawo ta jikinsa babyna mu dan fita mu zaga gari ko? In nuna miki wajajen ban sha awa da
na kayatarwa.
Ta noke a jikinsa tare da cewa “my love ka bari sai
gobe jikina har yanxu yana yi min ciwo.”
“Ciwo babyna! Kada fa ya kawo mana matsala in an
jima fa.? Ta bigi kirjinsa cikin wasa tana harararsa, “Allah
Allah my love ka bari zan yi maka kuka.
To na bari na bari babyna, tana langabe a jikinsa sai
shagwaba take yi masa du ta wani narke masa sai
zuba masa sangarta. Shi kuwa gogan ya rikice duk
ta burkita masa tunani da sha’awarta sai riritata yake yi yana lallaminta, tare da taba wasanni a
jikinsa nata ko zai samu ‘yar nutsuwa kwana hudu
yana jirarta ba tare da ya kuma neman yin wani
abu da ita ba, sai yai ta faman riritata yana
sangartata yayin da take zuba masa shagwaba son
ranta shi kuwa yai ta biye mata don bata da masaukin da ya wuce jikinsa, ko yaushe tana
manne a jikinsa yanayi mata tausa ko wasanninsu
na ma’aurata.
Aha har yanxun xa’a bani ko kuwa sai na kuuma?
Idan kuuma ba’a bani ba………… hmmmmmmmmm
.
((((( SALON SO))))
((((((PART 35)))))
:
.
Kamar yau ta sha wankanta ta kayata fuskarta da
dogon wandon ta shima pick colour me baza daga
kasa sai bakin gashinta da ya kwanta a bayanta
yana ta zuba kamshi da sheki.
Ta yi tsananin kyau irin kyan da baya misaltuwa, ta
zira siririyar sarkarta da yari da abun hannu duk na gwal, jikinta sai ni:imtaccen kamshi ne yake tashi
kamar anyi barin turare a jikinta. Ta fito falon in da
yake zaune yana kallon wakoki cikin tashar
turawa.
Ta zo ta zauna a cinyarsa ta sakalo wuyansa da
hannuwanta ta yi kasa-kasa da muryarta yayin da take kashe masa ido daya ta ce “My love ince ko dai
baka yi fushi ba na barka kai kadai?
Ya rungume ta tsantsan a jikinsa “Babyna ina sonki
da yawa kina sani farin ciki koda yaushe duk
sanda na kalle ki ina kasancewa cikin nishadi da
annushuwa, bebi na ki yi wani abu akan yawan kaunarki da nake na zarme da yawa.”
Ta hada fuskarta da tasa ta tallafa kansa ta zira
harshenta a bakinsa ta shiga juyawa cikin wani irin
yanayi na SALON SO.”
Ta fa gigita shi ya ji wani abu yana tsikarar
zuciyarsa ya rikide mata ya shiga sumbatarta ba kakkautawa, ya zira hannunshi cikin rigarta yana
wasa da yana mata wani shu’umin kallo mai
burkita kwakwalwa cikin kunnanta ya rinka rada
mata kiyi hakuri bebi na ki bani hadin kai na nuna
miki irin tsantsar kaunar da nake yi miki, ki taimake
ni bebi na muraya daren yau don samun ladan sunnah”.
Ta yi zumbur ta mike cikin yanayi na tsoro da jin
kalamansa, shima ya mike ya riko hannunta ta
marairaice fuska tana son yin kuka, “Ka tausaya
min Yaya wallahi akwai ciwo.”
Ya rungume ta ya dora kanta kan kafar shi yana rarrashinta “Ki yi hakuri babyna ba zaki ji ciwo ba,
wancan ma don na farko ne shi yasa ki ka wahala
amma ba zaki sake jin ciwo ba, ki taimaka min ki
bani hadin kai gudun kada ciwon mara ya dame ni
kin ji bebi na kin amince? Ta daga kai cikin yanayi
na rauni da damuwa. Ta bashi tausayi ya san bata so don ta wahala ranar
nan, ga shi, shi kuma tun da ya dandani yanda take
ba zai iya hakure mata ya sa mata ido kamar da
daya zuba wauta ba. Amma insha Allahu zai bi ta a
sannu don ta samu sassauci.
Haka ya rinka lallabata yana bata damammiyar madara da gasasshen nama mai ruwa ruwa. Duk
wani abu da zasu gudanar sun gudanar, wanke
baki shafa turaren gabobi, matsa mounth freshner
a baki fesa Air freshner, a kowacce kusurwa ta
dakin inda sanyin dadin ya rinka fita sabo da
sanyin AC da dadadan kamshi da ya hadu ya dauke ta cak yayi gado da ita ya rinka yi mata
wasanni ya taba can, ya tsotsi can ya murza nan
cikin dan lokaci kankani ya kashe mata jikinta da
salon kaunarshi.
Tana jin shi yana zame mata kayan jikinta amma
bata da wani katabus bare ta yi yunkurin hanawa, sannu a hankali ya rinka binta har ya cimma
burinsa.
Ga mamakinta sai ta ji bata ji ciwo da zafi kamar na
ranar nan ba. Bayan hankalinsa ya dawo jikinsa ya
rinka rarrashinta da lallaminta yana yu mata tausa
har bacci me nauyi ya dauke ta. Yayin da shima ya manneta a kirjinsa hannunsa
yana kan nononta yana wasa da shi har bacci ya yi
awon gaba da shi.
Karfe bakwai ta farka ta ji ta manne a kirjin Haidar
ta rasa yanda zata yi don ba taso ta yi motsi don
kada ta yi motsi don kada ya farka saboda yau wata irin
kunyarsa take ji tare da wata irin zazzafar kaunarsa
da take ratsa dukkan gabobin jikinta.
Ya bude idonsa ya rinka dubata cikin sha awa
yayin da tasa hannuwanta biyu ta rufe fuskarta
tana murmushi da ita zata shi a jikinsa suka shiga bandaki tare suka gudanar da wankan lokaci daya
suka dauro alwala suka fito suka gudanar da sallar
asuba a makare.
Ya matsa kusa da ita ya zare hijabin da ta yi sallar ya
kwanto da ita kan cinyarsa ya kura wa kirjinta ido.
Yana kallon manyan mamanta da suke cike jajir da su a tsattsaye basu da niyar rankwafawa kamar
wanda aka da sa su ko da yake dashin Allah ne
Jawahir tasa hannunta ta rufe masa idonsa don
ganin irin shaidancin kallon da yake yi mata ta san
ba za su waye lafiya ba.
Ya dan ciji hannun nata ta janye cikin sauri ya tsirawa fuskarta ido yana kallon kyakkyawar
fuskarta. Ta lumshe idanuwanta ya zura harshensa
yana lasar girarta zuwa kumatunta
Ta sakala hannuwanta a bayansa ta tallabe shi
sosai ya zira harshensa cikin bakinta suka ci gaba
da farantawa juna rai. Bacci ya kuma kwashe su sai shabiyu suka tarka
lokacin suka tsala wanka suka shirya Haidar ya
shirya cikin jins da damammiyar T-shirt me gajeran
hannu jikinta layi layi ne na fari da ja, ya yi kyau sai
kamshi yake kwararawa.
Ya dawo falo ta kwanta a doguwar kujera yayin da ya kunna T.V yana kallon tashoshin Turawa yana
jiran jawahir ta fito suyi break.
Jawahir ta gama shirinta cikin damamman guntun
wando da ‘yar bingilar riga iya cibiya, gashinta ya
sha gyaran sai sheki yake zubawa da kamshi
jikinta kuwa sai fitar da nau’ikan kamshi suke yi masu narkar da zuciya.
Ta ta ko a hankali kamar bata son taka kasar ta fito
falon tun kafin ta karaso falon Haidar ya kafa mata
ido, kaunarta tana kara ratsa shi kamar ya hadiye
ta don so.
Ta tako a hankali har zuwa kan kujerar da yake ta kwanta dai dai a cinyarsa, ya yi wata irin wawar a
jiyar zuciya, ya kuma rungume ta babyna zo muje
na baki break kada yunwa a illata min ke, ta
langabe a jikinsa tare da kiransa “My love ya ce
“Na’am bebyna ya aka yi?
“Wallahi my love gida nake tunani yaushe za mu koma mu ga iyayenmu da ‘yan uwanmu?
Ya kara rungumarta “Haba Bebyna muna tare da ke
ki ke son koma wa gida ki yi min adalci mana ya
kike so nayi da dinbin kaunarki na ga baki damu
dani ba.” Ta yi saurin sa tattausan hannunta ta rufe
masa baki “Yi hakuri my love ba nufina ba kenan wallahi ina sonka ina kaunarka zuciyata tana son
kasancewa tare da kai koda yaushe.
Ya yi mata kyakkyawar runguma yana sumbatarta
da haka suka je suka yi kataccen break.
Ya dauko abayarta ya sa mata ya rufe mata kanta
da karamar hijabi fari mai kyau yaja hannunta suka fice yawon zaga gari.
Hakika ta sha kallo ta yaba da tsarin kasar London
gari ne me kyau da ban sha awa. Ita dai ba don
tunanin iyayenta da ‘yan uwanta ba, da ta roki
Haidar su dawo kasar nan da zama sai dai ba za ta
iya ba saboda kulafucin iyaye da ‘yan uwanta. Sun zaga sosai daga nan suka dire a wani
hadadden gidan abinci girke girkensu sun kayatar
da jawahir ta ji dadin abincin sosai har ta rinka
santi. Sai yamma likis sannan suka koma
masaukinsu.
Washe gari ma wajen sga biyu suka fita, ya rinka zagayawa da ita suka dire a wasu kamfani na kera
akwatuna ya zabo mata set biyu masu kyau sabon
dizayin don a lokacin ma ba su zo nan ba. Da masu
ruwan zuma da masu ruwan toka. Daga nan suka
wuce wani tafkeken
shago na saida gwala gwalai, tare suka rinka zagayawa, duk
in da ya hango me kyau in dai ta bashi sha’awa ba
ruwansa da tsadarta sai ya dauko mata sarkar kafa
me kyau ya kara a kafar jawahir tuni ya ga sun
kara haskakat kafar tata
Ya kuma dakko sarkar hannu itama ya kara mata
subuhanallah tuni yaga kyakkyawar matar tasa ta
sake fitowa sosai
Abin ya ba wa jawahir mamaki, yanda ta ji an buga
kudin mai yawa taga ya biya duk tsadarsu bata re
da ya damu ba. Ta matso dab da shi ta kwantar da kanta akan
kafadarsa ya sa hannu biyu ya rungmeta “My love
don Allah ka daina yawan kashe min kudi don
hidimar da kake yi min ta yi yawa.
Ya dada rungume ta yana dan bubbuga bayanta
kada ki damu bebyna komai na mallaka a duniyar nan naki ne ki daina damun kanki don na kashe
miki ‘yan kalilan din kudi.”
“To Yayana na gode Allah saka da alheri Ubangiji
ya kara budi.
“Yauwa Bebyna, amin”
Ta rada masa a kunnensa “My love” mu koma gida abincin jiya.”
Cikin dariya ya kama bakinta wannan bakin ya iya
kwadayi ko, ta manne kanta a kirjinsa tana
murmushi suka wuce gidan abincin.
“Yan kwana biyun nan jawahir tana fama da yawan
kasala da lalaci ga yawan bacci, yanxu basu fi ya dadewa hira ba sai jawahir ta kama bacci.
.
SALON SO
.
PART 36
.
Abin da Haidar yake dauka yawan gajiyar da ita da
yake yi ne shi yake yawan sa mata kasala.
Yau ma tare suka shiga toilet wanka suka yi suka
cuda junansu cikin farin ciki tare da wasanninsu na
ma’aurata. Ya kinkimota ya fito da ita ta zille daga
cikin sa ta koma daya dakin don ta shirya. Haidar ya gama shirin cikin wando iya gwiwa wato tree
gwata da riga marar hannu me kyau yana ta kyalli
don shima fatarsa ta kara gogewa. Kowa ya kalli
shi yasan fatarsa ta kara goge da hutu da jin dadi
irin na masu da shi.
Jawahir ta gama shirinta wani mini siket iya cinya da ya matse mata cinyoyi sai dai yana da tsaga
gaba da baya.
Rigarta iya kirjinta ta tsaya cibiyarta a waje ta ke
fuskarta ta kara haske da kyau da kuruciya
yarintarta ta kara fitowa fili. Jikinta sai fitinannen
kamshi ne yake tashi me ta da sha awa. Ta dawo dakin da ta bar shi saboda zazzabi da ta
ke ji ga ta shin zuciya, yana tsaye yana fesa turare
ta zo ta kwanta a bayansa tare da zagaye shi da
hannuwanta ya kamo ta ya zagayo da ita gabansa
tare da cewa “Bebina lafiya me yake faruwa ne da
ke, jikinki duk ya canja ga yawan lalaci da bacci.? Ya dauke ta suka koma kan kujera suka zauna
yana lallatse jikinta don ganin ta kamaimai me yake
damunta, duk ta narke a jikinsa ta langabe tana ta
zuba masa shagwaba tare da marairaita.
“Bebina muje asibiti a duba min ke don na san me
yake damunki. Cikin ma rairaita ta ce “My love ni bana so muje
asibiti don kada suyi min allura idan na sha fanadol
ma zan samu sauki” Ya ce “Haba bebyna ya za ayi
na barki haka kin ji jikinki kuwa yanda ya dau zafi
ya kama lallatsa wayar likitan Hotel din ta rike
hunnansa kamar za tayi kuka. Don Allah “My love kada ka kirawo shi wallahi na
sha magani zan ji garau. Ya ce ke dai kin fiye tsoron
Allura.”
Ya hada mata break yana bata a hankali tana kau
da kai alamar ba ta so don bata jin dadinsa ya rinka
lallaba ta yana ririta ta har ya samu ta dan ci. Ya bata magani ta sha ta kwanta a jikinsa tana dan yi mata
tausa tare da mammatsa mata jikinta.
Bacci ya kuma dauke ta ya gyara mata kwanciya a
jikinsa lokacin da ta tashi jikin nata da sauki daga
nan London suka wuce kasar America jawahir tayi
mamakin yanda taga Amerika ashe itama haka take da kyau gaskiya kasar ta bata sha awa.
Nan ma Haidar ya bude bakin aljihu yai ta narka
mata kudi kamar vai san zafin nema ba. Watan su
daya a Amerika suka dire kasar Saudiya jawahir
tayi kyau har taga ji da kyau ta kara haske da
kuruciya, duk wanda ya kalle ta zai gano yaron ciki a jikinta don wani dan ya cewa da ta yi da wani
shirtaccen kyau da ta kara, nonuwanta sun sake
cikowa suna tsaye kyam da su. Haidar yana ji da ita
yana lailanta duk da canjawar da jawahir ta yi
hakan bai sa Haidar ya gano ajiyar da ya yi a jikinta
ba, bare ita da kuruciya ta yi mata yawa ita dai tana jin canji a jikinta amma bata dauke shi a komai ba,
bare ta kula.
Suna ta shirye shiryen dawowa gida sun sayi
tsaraba ta ‘yan uwa da abokan arziki kamar masu
shirin bude kamfanin sutura, da kayan kyale kyale.
Jawahir tana kwance lamo a kan gado zazzabi ne me zafi ya rufe ta lokaci daya Haidar ya shigo ya
zauna gefen gadon yana cewa kasa uwar bacci ba
dai daga wannan ‘yar fitar tawa har kin koma
baccinba.?
Ya sa hannu zai dago ta ya ji jikinta da zafi. A gigice
ya dako ta ya rungume ta a jikinsa yana jero mata tambayoyi “Bebina me ya same ki daman vaki da
lafiya, baki gaya min ba daurewa kawai kika yi?”
Bai jira amsar ta ba ya sabe ta a kafada ya yi waje
da ita, motar Hotel din ya yi amfani da ita ta xuwa
asibitin.
Likita Bilkisu muhd Adam ta karbe ta cikin gaggawa ta shiga yi mata tambayoyi da gwaje
gwaje a lokacin ta yi mata sukanin ta hango
karamin ciki dan wata uku a jikinta.
Haidar ya
juyo cikin farin ciki ya dako kan jawahir yasa
harshensa yana lashe hawayen nata. Yasa hannunsa kasar mararta yana dan shafawa ya
rada mata a kunnenta babyna mu duka mun yi
kuruciya da wauta sai dai mu kiyaye gaba sai dai mi
ta addu’a Allah ya raya mana Bebinmu Allah ya fito
mana da shi lafiya.”
Ta ce, “Amin cikin shagwaba ta ce ka huce my love.”
Ya sake rungumarta na hakura bebina tun da ke
ma ba laifinki ba ne na mune da rashin kulawarnu.
Nan fa sabon tattali da ririta suka tashi don Haidar
daga kansa yake yiwa jawahir wanka wai don
kada ta wahala duk wani abu da take yi masa yanzu shi ya dauke mata nauyinsa. Ita kuma ta kan
shagwabe masa ta ce yana ta aikin lada haka yake
so ta zauna ba nono.
Ya ce “Ai aikin lada da yawa yi min kiss shima lada
zaki samu. Ya turo mata kumatu ta cije shi ya da fe
wajen a’a a’a bazan yarda ba sai na rama. Da ya yi kanta zai turmusheta sai ta daga hannu
sama tana cewa bebinka bebinka zaka wahalar
dashi ya yi dariya ya dumgure ta.”
Ta yi dariya don Allah yaya mu goma gida mana.
Ya zaro ido “Ke yaushe zan yarda mu shiga jirgi da
wannan dan ta yin cikin nawa.” Salon kisa wabi abun ya faru da shi ai mu da mu
koma gida sai kin haihu su ganmu da bebinmu. Ta
marairaice ta fada jikinsa ta saka kuka ya dagota
yana dariya to to sarkin shagwaba yi shiru da
gangan nake yi rana ita yau jirgin mu zai daga
zuwa Nigeria Ta kuma kankame shi tana kyal kyala dariya,
Haidar ya gama luguiguita jawahir dukjansu zube a
gado suna mayar da numfashi.
Hannun Haidar yana kasan marar jawahir yana
shafa bebinsa.
Ya ce ko kin san wani abu? Ta girgiza kai ya ce sai da likitan nan ta fara gaya min kina da cikinsa nan
na gani alamomin hakan daga jikinki. Ga shi yanzu
har ya fara fitowa kamar ba dan wata hudu ba, ta
marairaice murya cikin shagwaba ta ce wallahi ni
kunya nake ji su ganni da cikib nan ai sai suce vani
da kunya daga zuwa jinya, na koma da dan rakiya. Haidar ya dada jawo ta jikinsa yana shafa bayinta
tare da dariya yace in banda abinki ni shi ne shedar
na warke.
“Kinga duk wanda ya kalle ki ba sai ya tambaye mu
an samu nasarar aiki ko ba’a samu ba, ta dada
shigewa jikinsa ta ce yanzu shi kenan kowa yasan abin da muka yi ko?
Ya kara tun tsirewa da dariya yanzu bebina in
banda abin ki akwai wanda ya taba sha a ruwa
ne?” Kowa kika ganshi da ciki ai ta haka ya samu ta
ce “Na shiga uku yanzu momyna da Dadyna da
Anty da Inna da Abbanka haka za su ganni da ciki gaskiya zan sha kunya kai ku wa ka yi min wayyo
babu ruwanka ko?
Washegari jirginsu ya daga zuwa Nigeria da yake
an san da dawowarsu ‘yan uwa iyayensu sun zo
taryarsu babu wanda yasan jawahir tana da ciki sai
dai idonsu ya gane musu. A cikin jirgi, jirgi yana jama’a aka fara sakkowa,
Haidar ne a gaba jawahir tana biye da shi sun yi
kyau sun dade kara ja da fari jin dadi da hutu ya sa
sun haske wajen kowa ya kalle su sai ya sake
duban su ba don murmushin da su ke dokawa ba,
da iyayensu basu gane su ba. Suna sakkowa jawahir zata kwasa da gudu ganin iyayenta Haidar
ya riko ta yana ce matw ki kula kada ki yi min
ganganci da ciki.”
‘Yan uwa suka yunkuro gaba daya suka taro su
jawahir ta durkusa kasa ta kama kafar babanta ta
rike tana me jin dadi da murnar ganinsu. Ya sa hannu ya dagota yana kallonta fuskarsa cike
da murmushi na yanda yaga ‘yarsa ta kwantar da
hankalinta gashi yanda ta kara kyau da haske
kamar balarabiya.
Inna ta dafa kafadarta jawahir ta juyo ta rungume
ta tana murna Inna ta dako ta cikin dariya ta ce ke taurin me nake ji haka? Ko dai kin samo mana dan
London? Kai amma abu ya yi kyau.”
Dady ya ce “Menene?”
Inna ta ce, “Ciki ne da ita da sauri jawahir ta fuzge
jikinta cikin jin kunya taje ta rungume Mominta da
Antinta, ta je ta gaisa da Abban Haidar. Nan fa sukai ta gaisawa da ‘yan uwa ana murnar
ganin juna. Daga nan suka rankaya gaba daya don
raka su gidansu. Jawahir ta yi mamakin canja
fasalin gidan nasu da aka yi, ya yi masifar tsaruwa,
don ya fi na da ma kyau, tsadaddun kujerun da
kayan kyale kyalen da suka suyo a kasar waje. An kawata babban falon da su, sai ka ce falon
sarauniya America don tsananin tsaruwa da kyau
da ya yi sai da aka ci aka sha sannan iyayensu suka
taya su murnar samun lafiyar. Haidar da karuwar
da suka samu.
Kowa ya fashe, sun tattafi ma’aikatan gidan suka kara gyara gidan ko ina ya kara yin fes sai sheki da
kyalli ne yake tashi da hadadden kamshi.
Da daddare “Faruk ya zo suka rungume juna shi da
Haidar suna murnar sake ganin juna.
.
SALON SO
PART 37
.
Jawahir ta shigo masa da kayan ciye ciye suka
shiga gaisawa. Faruk ya ce “Mutumin lallai naga
alamar ka warke har da tsarabar dan london ne ko jafan ko dan ijift ne ko America? Naga alamar
kamar jawahir tana da ciki ko?”
Haidar ya yi dariya ya ce “Ai ma ganinku nayi masu
tambaya yanxu kuwa kowa ya kalle ta yaga
shedar aiki ya yi kyau.
Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa Faruk ya ce, “Bakinmu da nayi muku dai ya kama ku to Allah
ya raba lafiya, Ubangiji ta sa masu amfani ne ya
bamu masu albarka, don Hafsat tana can da nata
tsohon cikin.
Kai mutumin lallai kayu aiki, to Allah ya inganta
mana, Ubangiji ya raba su lafiya da shi. Bayan sun nutsu sun huta suka bude tsarabobi suka rinka bin
‘yan uwa da dangi suna rabo kowa aka bashi
tsaraba sai ya jinjina kudin da aka kashe masa.
Jikaken abu mai muhimmanci da tsaraba da mutum
sai yaga kamar shi suka yiwa tafiyar. Anty Maryam
ma da Uncle har gida suka zo yi wa su jawahir barka da kuma yi musu sannu da zuwa.
Da yake hutun su suka dakko zasu dade a nan a
gidan Ankul din suke zaune wanda ya zauna farkon
aurensa kafin aiki ya maida shi Abuja.
Jawahir ta
sha murna da ganin Antyna Maryam ta rungume ta suna ta dariya cikin jin dadi da walwala kamar sa
hadiye junansu.
Anty ki ce kin kusa haihuwa don naga cikin naki ya
yi tsini da yawa.”
Ta ce “Haka Ankul dinki yake cewa wannan cikin
ya fiye girma da yawa wai yana takura shi don na fiye langwai.
Jawahir tasa dariya ai gaskiya Anty sai yanzu na
gano sirrin da ya sa Ankul ya ke manne miki ko, na
ce ku ke manne wa juna, ashe haka rayuwar aure
take?
Hakika jawahir rayuwar aure aba ce mai dadi da nishadantarwa kwanciyar hankali da samun
nutsuwa. Amma fa duk wa ‘yannan abubuwan
basa samuwa sai ka yi da ce da abokin rayuwa
nagari.”
Haidar ya yi sallama ya shigo tare da cewa da
Maryam “Antynmu ai kin yi nauyi da yawa, da kin hakura da zuwan da sai muzo har gida mu gaishe
ku.”
Ta yi dariya tare da cewar ai bazan iya jure rashin
ganin diyata ba, yanda ake yi min zuzutun kara
kyan da tayi amma da nazo ai na gani idona ya
gane min kyakkyawar kulawar da ka yi ma ‘yata. Ya yi murmushi ya kalli jawahir ya ce, “Bebina zamu
fita da Ankul xuwa dare zamu dawo.” Ta
marairaice fuska kamar mai shirin kuka ya dafa ta
“Haba bebina mene ne kuma bana so ki bata ranki,
ba ga Antynki nan zata taya ki hira ba, sai mun
dawo zai dauke ta su ta fi. Ta yi murmushi yayin da ta juyo ta kalli Anty maryam. Ta ga ita ba ta saurari
su ma, hankalinta yana kan littafi tana karantawa.
Haidar ya riko ta suka yo falon tsakiya ya zauna a
kujera ya dorata kan cinyarsa “Meye damuwarki
babyna?
Ta yi rau rau da ido har sunkawo kwalla ta ce “Ni ba komai va ne ina tsoron kada Ankul ya sake
cewa ka dawo da Kausar ne, ba zan jure ganin
kana yi mata magana ba bare har ka shiga dakinta
ka kwana mun zama mu biyu da matsayi daya a
wajenka ta saki kuka.
Haidar ya rungume ta yana rarrashinta. “Kar ki damu Bebyna, daman can kaddara da
sha’awar kare kaina daga zina ita ta sani auren
Kausar, ki sa a ranki tsakanina dake mutu ka raba ne
takalmin kaza aurenmu auren zobe ne ba saki
ba yaji ba kishiya har avada.
Kuma na ji wai SULAIMAN BOMBOY za ta aura. Ta ce, “waye kuma SULAIMAN BOMBOY?” Ya ce wani yaro
ne dan karami amma ya nace wai shi a lallai sai ita.
Ta ce, “Um. Ta dako kai da sauri “Allah yayana?
Ya ce, “Sosai ma kuwa ta yi saurin kankame shi
tana sumbatarsa, cikin murna ya dako ta yana
dariya muje kada Ankul ya gaji da jira. Suka fito babban falo jawahir ta ce “Ankul ka bar
min Anty ta kwanar min anan.” Ankul ya girgiza kai
ya ce, jawahir kenan har yanzu
dai kina tare da kuruciya, to idan haihuwa tazo
kuma cikin dare ku yi yaya da ita, ku da kuke duk
farin shiga? Gaba daya suka sa dariya suka fice ita kuma ta
koma gun Anty maryam suka bude shafin hira. “Kin
gane ne Anty ni fa yanzu abun da nake tsoro
kada Haidar ya dawo da kausar don ban san yanda
zan yi ba, a da ban damu da aurenta sosai ba don
sannan ban damu da Yayan ba, amma anya yanzu yanda nake son Yaya Haidar muka shaku da shi
yake sona yana ririta ni yana tarairayata kamar kwai,
zan juri ganinshi da wata matar, wai! Naga
mace a rungume a kirjin Haidar, subhanallahi Allah
ma ya kiyaye, Anty ai wuka zan soka mata ta mutu
nan take. Maryam ta tuntsire da dariya ta ce “Allah ya kiyaye
jawahir,” Anty maryam ta ce “Ai na gaya miki wasu
matan su suke jawowa kansu ake yo musu kishiya,
na farko akwai matan da girman kai da ji da kai
tsabagen muskilanci ya yi musu yawa, to yawanci
masu irin wannan halin sai ki ga har mazajensu na aure su ke yiwa ko suna mantawa a karkashin
mazajen su suke? Dole mazan su ne gaba da su, dole
ne duk matsayinki da jin kanki, ki sauke su ki
yiwa mijinki biyayya ko dan ki samu tsira ma ranar
gobe kiyama, domin aljannar mace ta na tafin kafar
mijinta sai ya daga zaki shiga. Abu na biyu kuma shine, kazanta, sai ki ga mace awaje dagwas
dagwas da ita amma da zarar ta yi aure ta haihu sai
kiga ta zama kazama. Ba za ta tsaya ta tsabtace
kanta ba bare abincinsu ko abin shansu.
Wasu matan za ki ga kudin da aka ba su na cefane
a ciki zasu raga su boye baza su yo cefanan na duka ba bare su sarrafa girkin yanda zai yi dadi. Sai
mace tai abinci garau garau ba wadataccan kayan
miya bare mai kiji abinci kadas babu dadi abinci
babu kyau a fuska.
Bayan ta gama girkin ba ta san tai wanka ba ta
gyara jikinta, a’a sai ki ganta daga ita sai daurin kirji tana ta fama da kaurin wuta. Da kin doshi dakinta sai
zarnin fitsarin da warin dauda. Kin kai wa namiji
abinci ya yi cokali biyu ko uku ya ji ya kasa ci ya
ture saboda rashin dadi.
Baruwanki da kwantar da murya bare ki bincike
shi me ya hana shi cin abincin, a’a ke babu ruwanki sai ki ja kwanon gabanki ki kama ci ko ki kirawo
yaranki ki ce kuzo ku dau abinci babanku ya rage,
babu ruwanki da damuwarsa.
Idan dare ya yi kina kwance cikin yaranki kin saki
baki kina munshari kin bude nono kin saka wa
yaron da kike goyo a baki kin riga kin sabar masa, sai da nono a bakinsa zai yi bacci, da maigidanki ya
zo ya taba ki don ki taso yana da bukatarki ki kama
miya kina faman zumburar baki ke an takura miki
kin gaji, daren ma ba za’a barki ki huta ba, saboda
Allah mijin nan naki waliye ne da ba zai bukataci
mace ba in har Allah ya kare shi daga sharrin zina? Ai kuwa dole ya yi kokarin karo aure ko dan ya
samu me debe masa sha’awa.
Jawahir ta ce, “Yanzu Anty kina ganin wa’yannan
dalilai zasu taimaka wajen yo wa mace kishiya?
Anty maryam ta ce “Kwarai kuwa ai wadannan su
ne kan gaba, idan mace ta zamo bata daraja mijinta bata ganin mutuncin iyayensa tana wulakanta masa
‘yan uwa da abokanan arzikinsa to yana kara
aure gudun kada ta rusa masa zumunci da ‘yan
uwansa.
Jawahir ta ce, “To ai Anti in kika yi la’akari da wasu
mazan kwata kwata ba su san darajar mace ba, sun dauki mace baiwarsu abar korewa sha’awarsu, don
wani namijin zaki ga namiji yana wasa da
dariya a waje ki ga yana tayiwa ‘yan mata fara’a
yana jansu da wasa, amma da zarar ya shiga
gidansa sai ki ga ya koma kamar mala’ikan
mutuwa ya murtuke fuska babu alamar fara’a bare wasa, da ya ci karo da kwano ko wani abu nata
akan hanya zai bal da shi, kuma yana da rufin
asirinsa amma sai ya ba wa iyalansa dan kalilan din
kudin da ba za su wadaci girkin gidansa ba, ba
ruwansa bai damu da matsalar da suke ciki ba, bai
ja su a jikinsa ba, bare su saki jiki da shi har su dinga bayyana masa damuwarsu. Anty duk irin
wannan ai rashin adalci ne da sanin
darajar mace ko?
Anty maryam ta ce “Haka ne jawahir amma ni a
ganina idan Allah ya hada ka zama da irin
wa’yannan mazan to sai ka iya zama da su. Na farko mace ta dasa wa zuciyarta hakuri, ta zamo
mai juriya da tawakkali, na biyu ta kasance me
yawan ibada tai ta addu’a tana kai kukanta ga
Allah, na uku ta samu sana’a komai kankantarta
kada ta raina ta ta rike ta hannu biyu.
Na hudu ta zamo mai kyautata masa da yi masa biyayya ko dan ta samu tsira ranar lahira. Na biyar ta
kasance me tsafta da kwalliya da kasancewa
cikin kamshi. Na shida ta kasance cikin koyon iya
kissa da kwantar da kanta tana kaskantar da kanta
ko yaushe tana nuna masa shi ne sama da ita, na
bakwai ta kasance doluwa marar wayo ta zamo me kau da kai da duk wani abu da zai mata, na takwas
ta zamo mace me iya kula da rayuwarta wato tana
cin abubuwan da za su kara mata ni’ima a jikinta.
Na tara mace ta iya kwanciyar aure ta gano wace
irin kwanciyar aure mijinta ya fi bukata, me da me
da me mijinta ya fi sha’awa a jikin mace, sai ta rinka gyara nata yanda zai rinka daukar hankalinsa yana
bashi sha’awa ba tare da na mace daban ya burge
shi ba.
.
SALON SO
PART 38
.
. Abubuwan da mace zata ci su kara mata ni’ima ba lallai sai ta fitar da kudinta
ta sai masu tsada ba, a’a daidai ruwa daidai tsaki, kada ki ce to ke ma ina kika
ga kudin bayan ba baki yake yi ba, ke ba wani abu da za ki siya don gyara
kanki.
To gaskiya wannan rashin wayo ne ai kan ki zaki gyara duk sanda namiji ya
kusance ki ya ji ki zam zam da ke, tsindum da ke dole ne ya rinka tattalinki ya
na baki kyakkyawan kulawa saboda yana son biyan bukatarsa. Amma ke baki
gyara kanki va, kin zauna gundin murhu duk wuta ta kone miki dan ruwan da
yake jikinki, mijinki ya zo ya ji kamas, saboda Allah me kike ganin zai faru?
Dole darajarki ta ragu idonsa, amma idan kika dage da shan su lemo, kankana,
rake, aya gwanda, ayaba, dabino, cukui, inibi, zogale, zaitun, tumatur, kwakwa,
zuma, nono, madara, gurji, dafaffiyar gyada, da sauransu duk irin wannan ba
karamin taimaka mana suke ba na kara mana ni’imar jikinmu.
Ko nera koma ki ka bayar a siyo miki dan kifi ki yi romonsa da kayan kanshi da
alvasa da tumatur kika watsa wake a ciki ya dahu luguf da dan alaiyahu ki yi
shi romo romo shi ma yana taimakawa, ki sami danyar gyada gwangwani daya,
aya gwangwani daya, waken suya gwangwani daya, alkama gwangwani daya, ki
hada ki jika a markado miki ki ta ce shi kamar gasara ki rinka damawa kina sa
madarar ruwa kina sha za ki ga yanda zai taimaka miki ya sakar miki da ni’ima
a jikinki.
Kinga abu mafi sauki idan kika sami ayarki kika jikata ta juku ki ka kai markade
kizo ki tace kayarki ki kara sikari ki rinka sha zata kara miki ni’ima sosai.
To kinga iri iren abubuwan nan idan mace tana yi zata taimaka wa kanta don
kare wulakancin namiji. To idan kuma ta iya gamsar dashi ta san sirrika na iya
kwanciya da da namiji to zata mallake shi a hannunta har a rinka zargin ta
asirce shi ne.
Jawahir ta ce, “To Anty me zai hana murubutanmu ba za su rinka wayar wa da
mutananenmu kai ba, ko dan sanin irin wannan sirrikan kwanciya don su ma su
mallaki mazajensu a hannu a daina yawan mutuwar aure? Maza su daina fita
bariki neman matan banza su rinka tsayawa iya matansu na sunna kawai?
“To ai jawahir matsalar da ake samu kin gane ne, marubutanmu suna iya bakin
kokarinsu na ganin cewar sun ganar da yawancin mutane yanda rayuwar jin
dadi ta aure take, to amma kash! Wani abu da ake kuka dashi wai sai ace suna
bata tarbiyar yara, wai yara kanana suna diban lattattafai suna karantawa, suna
ganin abin da bai kamata ba, wanda gaskiya ni kuma ina ganin ba haka ba ne,
domin idan kinga yarinya ta lalace to dama can lalatacciyarce iyaye suna ina
‘ya ‘yansu suke fita su shiga gidan amare su rufe kansu suna ganin kaset din
blue film ko America, ko ibo, ko fim din Turawa da yake bayyanar da tsiraici
karara da yanda ake nuna soyayya ta kazamar hanya. Wasu ma tare da samari
suke gani to meye ma ba zai faru ba wajan wannan kallon wa’yansu yaran
kuma da ake batawa ba su da wayewar kan ma da za su yi karatun littafin ake
jansu ayi musu fade, shi kenan hanyar lalacewarsu ta samu.
Wasu yaran kuma rashin kulawa ta iyaye da rashin sa ido akan harkokin su ne
yake jawo hakan, wasu tsabagen kwadayi ne da rashin kamun kai da zubar da
tsantsar da darajarsu ta ‘ya ‘ya matar ne take jawowa.
Gaskiya bazan taba yarda ace wai karatun littafi yana sa ‘yan mata suna
lalacewa ba, saboda duk wata mace da ta san darajar kanta to in har ta
karanta littafi ina ganin zata yi kokarin kare mutuncin kan ta ta yi kokarin kai
budurcinta gidan mijinta, saboda ta karanta littafi taga yanda daren farko ya
kasance ga yarinyar littafin, mijinta ya same ta a cikakkiyar mace ta ga irin
tarairaya da
Kulawar da yake bata taga yanda yake sa
mata albarka har da wata dunkuleliyar kyauta da ya yi mata, to ni a ganina
kowace budurwa zata yi sha’awar hakan har ta yi kokarin kai budurcinta gidan
mijinta
Abu na biyu ‘yan matanmu za su iya koyon kissa da shagwaba da kalolin girke
girke da yanda ake tarairayar namiji, zasu san abubuwan da suke kara wa mace
ni’ima wanda za su fara tsuma kansu tun kafin su shiga gidan auren, domin
idan ba’a littafin ba babu in da za su sami hakan saboda al’adar Bahaushe da
kunya babu uwar da zata iya zaunar da ‘yarta ta koya mata wa’yannan
abubuwan don zata yi mata aure, za dai ayi wa ‘ya fada ki bi mijinki ki yi masa
biyayya, to kin je kina ta biyayya yana wulakantaki ke baki san dalili ba to duk
wa’yannan abubuwa ne da bakya yi, amma aure ya samu tattali kissa biyan
bukata, shagwaba, ladabi da biyayya, iya girki, iya kwanciya, amfani da turaruka
masu kamshi da na tsugunno, ta cikin ikon Allah za’a samu zaman lafiya da
fahimtar juna a cikin aure.
Shi turaren tsugunno ana amfani da shi ne wajen turare gabanka ka tsugunna
akai hayakin yana shiga ciki to yana kara hade mace ne ya matse ta kamar
amarya.
Jawahir ta kawo gauron numfashi ta ce, “Anty na fahimce ki Allah ka ganar da
yawancin al’umma ko a sami zaman lafiya a tsakanin ma’auratnmu”
“To amin Jawahir.”
Ba jumawa Haidar da Ankul suka dawo suka ci abinci. Ankul ya ce da Anty
maryam ta tashi su tafi gida akwati guda jawahir ta yo wa Anty na tsaraba ta
dakko ta kawo mata suka rinka godiya tare da sa albarka.
Sai da Haidar da jawahir suka yi sati biyu a gidansu suna hutawa basu da aikin
yi sai wasanni da junansu su ci cima me kyau su sha me kyau suke ta sutura
me tsada su bada kamshi su manne da junansu suna faranta ran juna.
Yau sun cika sati biyu da dawowa don haka yau Haidar ya fara fita xuwa office,
jawahir duk ta damu kamar wanda zai je ya yi kwanaki a can sai da ya
lallabeta har da yi mata wayo sannan ya fice. Da yake ya dade rabonsa da
office din dole ya samu ayyuka kaca kaca sun yi masa yawa shi yasa bai samu
sukuni ba, sai na fadawa aiki kawai.
Haidar yana tafiya kuwa jawahir ta dauki mota ta tafi wani hadadden gidan
gyaran jiki tsadadde na ‘ya’yan wane da ‘ya’yan wance, aka yi mata gyaran
gashi aka gyara mata farce aka wanke kafar aka rangada mata kunshin fulawa.
Jikinta ya sha dulka da halawa, jikinta da fuskarta sai wani santsi da taushi
yake yi kamar auduga yana fitar da wani sihirtacce na kyau.
Tana komawa gida kicin ta shiga ta feraye doya ta dora a wuta ta debo
manyan busashen tarwada ta farke cikinta ta kan kare ta kwara masa ruwan
zafi.
Ta hade markade iya ta yi mata abu landa doyar ta dahu ta tsame ta mika wa
iya ta daka mata sakwara, ta hade miyar busashen kifin nan da ta ji onga, kori,
reko, mai da sauren kayan da su ke sa girki armashi, sannan ta cuko zallar
tsokar nama a firinji ta tafasa shi da albasa gishiri da dan magi.
Bayan ya tafasa ta kwankwatsa attaruhu albasa ta dakko tafasashen naman
nan ta hada a turmi ta daka.
Ta ciro shi ta rinka dunkulawa ta fasa kwai ta zuba gishiri onga reko ta dora
manta a wuta ya dau zafi ta rinka daukan dunkulan naman nan tana tsoma sha
a rwan kwan tana sa wa a manta na soyawa, ta gama wannan ta zo ta yanka
salak ta yi masa wanki sosai ta zuba a filet, ta yanyanka tumatur da albasa ta
gewayesu a saman salak da albasar ta kawo dafaffiyar hantarta da ta yi mata
kananan yanka ta zuba a kai.
Bayan ta yada salak, cream ta zuba heinze beans a tsakiya duk wanda ya kalli
hadin salak din dole yawunka ya tsinke, ta debo kayatattun fulas dinta ta zuba
komai taje ta jere su a santara tebir.
Ta debo fararen gobarta manya ta markada ta tace dusar ta markada kankana
da gwanda da ayaba a duk ta tace dusar ta hada akan ruwan gwaibar, ta
daddara rake ta matse ruwan ta hada akai, ta zuba ruwan kwakwa da ruwan
markadaddiyar aya ta zuba madarar ruwa gwangwani biyu ta kawo zumarta me
kyau ta zuba a ciki ta juya ta saka a firinji.
.
SALON SO
.
PART 39 .
.
.
“Subhanallahi! Lallai jawahir kin hada kyakkywan
lemo mai saurin saukar da ni’ima a jikin ta bar wa
iya rama ita kuma ta kara gyara falon da dakin megida ko ina ta turare shi da daddadan turaren
wuta na kamshi kowacce kusurwa ta feshe ta da
Air freeshner.
Ko ina ta sa ka AC sai sanyin dadi ne yake fita ta
gyara toilet ma shima ta turare shi da daddadan
kamshi, ta rufe sashinsa ta fito ta sakko ta shiga nata sashen ta sake gyarawa ta saki kamshi ta fada
toilet don yin wanka, ta dade tana murzar jikinta da
daddadan sabulu ga ruwan wankan nata ya sha
turaren wanka sai turarin kamshi ne yake tashi
Uku da rabi ta fito daga wanka ta dauro alwala ta
zo gaban mudubi ta fara tsara kwalliya shafa nan goge nan ko ina ya yi das, ta fara gabatar da sallar
la’asar, ta tsara kwalliya da wani pink din les mara
nauyi sai dai anyi masa shafi a ciki, duk da rigar fitet
ce ta dan fara kamata ko don cikin jikinta de da ya
fara bayyana, duk wata gaba ta jikinta ta mulke ta
da turaren kamshi, ta fesa na fesawa ta daura dan kwalin les din ya lafe kan gyaran gashin da ta yi.
Gaskiya ta yi kyau wannan da gasar sarauniyar
kyau zata je babu abin da zai hanata lashe gasar. Ta
dakko turare tana sake fesawa, daidai lokacin da
Haidar ya shigo da kyar yake daga kafa don
tsananin gajiya da yunwa tun break dan safe. Ya zube a kujerar falo yana mai nishi, “Bebina.”
“My love.” Jawahir ta fito daga cikin daki ta zagayo
gabansa idonsa yana limshe kamshin turarenta da
ya ji ne ya sa shi bude ido.
Subhanallahi, duk kyan jawahir sai yaga yau tafi
kullum kyau kamar wata fure aka dasa don kyau tuni gajiyar da ya kwaso ta ware, ya jawo ta
cinyarsa yana yi mata wani fitinannen kallo mai
tada sha’awa da raunannar zuciyar mai bege.
Ta sa hannunta ta rufe masa idon ya ciji hannun
nata ta yi saurin janyewa ta langabe kai cikin
shagwaba tana ‘yar kara tare da yarfe hannun nata.
Shikuwa Haidar tuni ya samu damar zira harshensa
a kyakkyawan bakinta, ya dade yana sumbarta ta
cikin shaukin so da igiyar bege da kyar ta zare
jikinta sakamakon wani nishi da ta ji yana yi gudun
ka da ta jawowa kanta jan gwam ta yi saurin haye wa samanta ta fada toilet dinsa ta hada masa ruwan
wanka, tana fitowa daga toilet din taga ya shigo
idon sa duk ya yi ja saboda fitina, ya sake jawo ta
ya mannata a jikinsa ya sake rungume ta ta
langabe cikin shagwaba take cewa, “My love ka je
ka y wankan kai muke jira fa Bebinka be ci abinci ba. Ya yi saurin cika ta ya dago kai yana shafa cikin
“Haba don Allah me yasa za ki bar min beby da
yunwa kina so ya galabaita ne, taho muje na fara
baki abincin tukuna, in kin koshi nayi wankan. Ta
make kafada ta ce um um ni dai ka shirya muje mu
ci tare. Ya jata ya zaunar da ita a gefen gado, to zauna nan yanzun nan zan fito ba zan dade ba.
Ya shige toilet din da sauri ita kuma ta tashi ta
dakko masa kayan da zai saka farar shirt ce da
bakin wando, ta feshe su da turare bai jima ba ya
fito daure da tawul sai wani akansa, ta yi saurin
tashi ta ciri tawul din kan nasa ta fara goge masa jikinsa, ta jashi gaban madubi ta shafe masa jikinsa,
da lafiyayyan cream me taushi da dadin kamshi, har
da shafa masa farar, hoda ta feshe shi da turare ta
ware masa kyansa ya karba ya saka.
“Au my love na manta ban sa maka man lebe ba”
ya sunkuyo da kansa ta shafa masa. “Inye! Nawan ba, ka kara kyau. Ya yi murmushi
tare da manna mata kiss a lebe ya riko ta suka taho
falo.kasa
suka sauko da kayan abincin ya hau kan kafet aka
baje don jawahir tafi sakewa.
Ta je firji ta tsiyayo hadadden lemon ta a je ya dau sanyi kuwa, ta zo ta ajiye ta dauki babban filet ta
bude fulas din ta sako musu sakwarar ta bude
miyar yayin da kamshinta ya bugi hancin Haidar ya
limshe ido yunwarsa ta dawo sabuwa, ta bude
daya filas din shima ta zubo musu hadin curaram
naman da ta soya da kwai, ta bude farantin hadin salak ta kalli Haidar ta ce, “My love bismillah.
Ya kalle ta yana murmushi sannu bebyna na gode
miki Allah ya saka miki da alheri Ubangiji ya yi miki
albarka, burinki kullum ki faranta min ki yi min abin
da zai sani farin ciki.
“To my love in ban yi maka ba wa zan yi wa, ina alfahari, ina matukar farin ciki da baiwar da Allah ya
yi min ta haduwa da gwarzon masoyi
Suka fara cin abinci dole jawahir ta rinka kyalkyala
dariya saboda yanda Haidar ya ta karkare yana ta
ziri tare da suba santi.
Komai sai da suka ci su ka koshi suka yi kat da su. Jawahir ta rinka tsiyaya wa Haidar hadin lemon
yana sha yana zuba santi shi dai ba don ya ji cikinsa
yana barazanar fashewa ba da ba zai bar sha haka
ba.
Jawahir ta kwashe kayan ta mayar kicin Haidar ya
jingina da kujera ya mimmike kafa ya dauki romote din tibi yana danne dannan tashoshi.
Jawahir ta dawo ta zauna ya juyo ya kalle ta cike da
kulawa yana murmushi ya ce, “Ya aka yi ne
bebyna? Ta jawo jikinta ta kwanta a cinyarsa cike
da sangarta, ya sa hannunsa kasan mararta yana
shafawa ya cire dankwalinta yana yaba kyan gashinta ya koma shafa kumatunta yana yaba
santsin fatarta da taushin jikinta kamar auduga.
Ya dora hannunsa kan kirjinta yana shafawa tare
da limshe ido jawahir ta ture hannunsa tare da
cewar “Meye haka kake yi a jikin ta tsitsiyar
kwaila.?” Ya yi saurin rufe mata baki da nasa ya dinga sumbatarta yana ruda mata jiki da wasanni
har sai da ya tabbatar ta manta da maganar
tukunna ya cikata.
Ikon Allah kenan duk yanda jawahir ta tsani
halayyar Haidar ba sa shiri da juna ba sa son
junansu, yau ga shi sun fi kowa kaunar junansu. Halayyar Haidar da jawahir ta tsana ta muskilanci da
kasaita da jan aji tare da rashin hayaniya ko
kwarniya yau tafi kowa murna da alfahari da
muskilancin Haidar da daukan kansa hade da
isarsa da kasaitarsa.
Tun da babu wata budurwa da ta isheshi kallo bare a kai gabatun magana har ya furta mata so, bata isa
ba kowacce.
So, kauna, aminci, yarda, shakuwa, duk ya tara su
ga tauraruwarsa jawahir. Bangaren Haidar kuwa
kullum sai ya yi wa iyayensa addu’a da fatan
gamawarsu da duniya lafiya saboda yanda suka hada shi aure da jawahir yanda da ya tsani
halayyarta ta miskilanci yau ga iyayi shagwaba.
Yanzu ga shi sun zamo abin alfaharinsa don suna
dada hura wutar kaunar jawahir a zuciyarsa.
Hakika ya yi sa’a da ace da samun kammalalliyar
mace ga kyau ga tsafta ga addini, ga usuli me kyau. Allah ya yi mata baiwa kala-kala na iya furta kalami
wanda lokaci daya zata siye zuciyar mai sauraronta.
Abu na biyu ta iya sahirtaccen kallo wanda zai jawo
afkawar mutum kogin begenta. Abu na uku ta iya
kissa da mutum ya so ta ko da baya ksunarta. Abu
na hudu yarinya ce me nutsuwa ga ta da ladabi da biyayya ga hakuri da tawakkali duk ta tara su.
Abu na biyar ta iya nau’ika na girki da abubuwan
sha ga ta da zakin hannu don duk wanda ya ci
girkin ta yai ta zuba santi da ya bawa kenan.
Abu na shida ta iya kwalliya gwanace wajen amfani
da hadaddun turaruka masu dadin kamshi, da san sutturar da ta dace ta saka kowanne yanayi da
kowanne lokaci.
Abu na
bakwai gwana ce wajen iya tsafta da gyaran gida
tun daga dakunnansu falukansu zuwa kicin
bandaki harabar gida ko’ina da launin turaren da take kamshinsa da yake yi
Abu na takwas ta riga ta gano makamar kama
Haidar domin ta fuskanci abin da ya fi so a jikinta
wata kirjinta, don haka koda yaushe ta kasance
cikin gyara kirjinta tare da sake kaya masu fito
mata da surar kirjinta. Abu na tara ta iya tarairayarsa tana ba shi
kyakkyawar kulawa ta siye zuciyarsa da
kyawawan halayenta, abu na goma na karshe
kuma, ta san sirrinkan kwanciya yanda duk yanda
ya juyata haka take binsa kowanne kokaci kuma
akwai sabon samfarin da zata gudanar masa a makwancinsa.
Ba ta gajiya da shi tana dauriya da jure bukatarsa
har sai ya gamsu don kanshi ba ta da korafi bare ta
nuna gajiyarta, ko ta ce ya fiye fitina
Wa’yannan halaye su ne suka ingiza kaunar
jawahir take dada ruruwa a zuciyar Haidar. Kwance tashi wajen Ubangiji babu wuya, ga shi
cikin jawahir ya shiga wata tara komai na haihuwa
sun tanada sai jiran haihuwar kawai suke yi.
Wata sabuwar sangarta jawahir take yiwa Haidar
saboda ganin yanda take bata tsantsar kulawa.
Cikin nata ya yi nauyi duk da haka ba ta yi sakaci da girkin megidan nata ba, bata sakaci duk yanda
Haidar ya kai da lallaminta da lallabata baya son
yaga tana wani aikin wahala don haka duk safiya
yake shiga kicin ya hada musu break.
Ya taimaka ma ta ta yi wanka shi yake yi mata
kwalliya, ya sa mata kayan da ya san baza su yi mata nauyi a jiki ba, ya rungumo ta zuwa falo kan
kafet ya zauna tana rungume a jikinsa yana bata
break a baki, sai daki ya kwantar da ita a gado
kamar wata jaririy yana yi mata tausa da matsa
sannu a hankali sai ya ga ta yi bacci sannan zai
shirya ya tafi office. Sha biyu na rana jawahir ta tashi daga bacci sannu
a hankali ta mike ta nufi kicin ta fara hada
abubuwan da zata dora girki, duk wani yanke
yanke da dake dake ko markade a bulanda me
take yi mata.
Ita kuma tana kula da girkinta da kuma hada lemummukan da ta san mijinta yafi so da sha’awar
shi.
Karfe biyu taje ta yi salan wayar Haidar ta sake
shigowa bugowarsa ta hudu kenan bayan tashinta
daga bacci.
Ta dauko “Hello Honey, na baka gajiya da yo waya ko”?
.
SALON SO
PART 40
.
.
Bebyna ya za ayi na gaji da jin muryarki hasken
zuciyarta tare da jin lafiyarsu ita da bebyna.
Ta yi shashshekar dariya cikin kissa da jan hankali ta makale murya tare da lankwasar da murya ta yi
masa magana cikin yanga da marairaita.
“Honey na ka kwantar da hankalinka kalau muke
ni da bebynka, sai dai muna kewar dumin jikinka
na dan lokaci.”
“Okey, beby na kada ki damu karfe hudu zan dawo gida mu kasance tare zuwa wayewar gari ko beby
na?”
Ta ce “Um hum thank you Honey na, sai ka dawo
muna jiranka.
Ya sumbaci wayar ya huro mata isa ta cikin wayar,
ta shashshekar dariya da ta saukar wa da Haidar matsananciyar kasala yayi saurin ajiye wayar tare
da jan diguwar ajiyar zuciya.
Jawahir ta mike ta koma kicin ta debo fulas fulas
dinta ta malmala tuwon farar shinkafarta da ya
tuku ya yi luku luku da shi, kowanne ta malmala sai
ta sa alaida sannan ta jera acikin fulas din. Ta juyo hadaddiyar miyar wake da ganye wadda ta
dahu da hanta da koda da manja sai dan man kuli
kadan lallai jawahir kin iya hada abin da zai kara
muku jini da lafiya. Ta juye farfesun kifi irin ragon
ruwan nan ta zai zuba kamshi yake yi, ta bude
oben ta zaro gasashen naman ta da ya ji tumatir da albasa gashi yayi ruwa ruwa sai zuba kamshin
kayan kamshi yake yi. Ta hada lemon kwakwa da
madara sannan ta hada lemon abarba.
Kowanne ta zuba a jug ta cilla kankara ta rufe ta
kwashe kayan taje ta jere su a kasa yanda suke yi
yanzu saboda girman cikinta. Iya ce ta gyara mata kicin din da duk wajen da ya baci.
Jawahir ta shiga toilet ta tsalo wanka tare da tsala
kwalliya ta shafe shafe da hadaddun kamshi na
tururuka daban daban, simpil doguwar riga ta saka
me rubi biyu sai walwalin dutsunan jiki ne suke ta
zuba sheki. Ta dora sirrin mayafin akanta, ta futo falo ta zauna akan kafet ta mimmike kafafuwanta ta
wara su yayin da ta jawo rumote ta latsa TV ta
kama, ita kuma ta jingina da kujera tana kallo.
Haidar ya turo kofar tare da sallamar tasa, ya yi
saurin karasowa in da take ya zube a gabanta, ya
tarairayo ta jikinsa “beby na” ya shafa mararta ya ku ke ya beby na yana dawo na same ku beby na
komai lafiya ko?”
Cikin murmushi take daga kai tana amsa masa tare
da shafar sumarsa ta kansa.
“Sannu beby na zauna anan kada ki tashi na hau
sama na watso ruwa na zo mu fita muje mu ci abinci ko, ta daga kai.
Ya mike ya yi sama da sauri ya fada toilet be jima ba
ya fito ya shirya cikin kananan kayansa ya sakko,
ta mike ta taro shi ya rungume ta a barin damansa
“Muje restaurant mu ci abinci ko.?”
Ta langabe a jikinsa “Haba my love da raina da lafiyata na kasa yi maka girki har sai ka fita waje ka
ci? Honey na na yi mana girki.” Ya rike baki
“Bebyna bana hana ki wahalar da kanki ba? Daidai
sanda suka zauna gaban kayan abincin yana
bubbudawa, ta ce “Wallahi Honey na ba na son
naga ka ci girkin waje ko na wani wajen, shi yasa nake daurewa na yi maka da kaina.”
“San kyau bebyna, na gode Allah ya yi miki
albarka, ya raba ku da cikin nan lafiya”
Amin Honey na gode.”
Suna cin abinci Haidar yana zuba santi, jawahir tana
kyalkyala masa dariya. Da haka suka gama Haidar ne ya kwashe kayan, ya dawo ya same ta ta
kwanta kan kafet ya durkusa kanta yana yi mata
tausa sannu sannu yake matsa mata jikinta tare da
mulmula mata bayanta a hankali ta ke fadin “wash,
wash, tana limshe ido na son yin bacci.
Karar wayarsa ce ta sa ta bude ido, ya dauka “Hello Inna kina lafiya kwana biyu?”
Inna ta ce, “Lafiya lau nake ina jawahir din?”
“Ga ta kusa da ni.”
“Yauwa
daman dai kan maganar da nafara yi maka ne, zan
zo na taho da jawahir don ta yi wankan gida”. “Haidar ya katse ta da “Haba Inna saunawa zan
gaya miki ne ni matata babu inda zata duk girman
gidan nan bai ishe ta wanka ba sai kun dauke min
ita, wanne hali kuke son saka ni?’
Ta daka masa tsawa “Kai marar kunya bana son
shashanci, haihuwar farin zaka yi wa wauta yaushe zamu barta ko mu ma wayaye ne irin ka.? Ta kife
wayar tana mita.
Jawahir ta dora kanta akan cinyar Haidar tana
shafa fuskarsa. “Honey na me yake faruwa ne, don
Allah ka daina damun kanka.”
“Bebyna ba dole na damu kaina ba, suna kokarin raba ni da ke, bebyna wai za ki iya tafiya wankan
gida ki bar ni a nan har tsawon kwana arba’in da
‘yan kai?
Ta girgiza kai cikin yanayi na tausayi da son ta yi
kuka “Honeyna ba zan barka ba bazan yarda su
raba ni da kai ba, babu in da zan bi su.” Daidai lokacin da ta dafe cikinta tana wash, wash!,
yayi saurin rungumarta cikin rikita yana cewa,
“Bebyna menene, me ya faru da cikin nawa.?
My love bayana, cikina, kuguna, duk ciwo suke yi.”
Da sauri ya buga wa direbansa waya ya ce ya fito
da mota zasu asibiti. Ya dakko jawahir direban ya bude musu bayan mota suka shiga, ya rife ya ja
suka nufi asibitin, abinka da lafiyayyen asibiti tuni
suka shigar da ita dakinta daban ita kadai a ciki
Haidar ya furgice ganin yanda jawahir take wahala,
gani yake kamar ciro cikin ya dawo da shi jikinsa
shi ya yi nakudar ya haihu. “My love” ta kirawo shi maganarta kasa-kasa ya
durkusa kanta yana jinta “My love kayi waya su
Mama su zo kada na mutu basu ganni ba.
Ya sake rungume ta yana ta mulmula mata bayanta,
“Ki yi hakuri bebyna, ba za ki mutu ba kin kusan
haihuwa. Idan ki ka haihu sai na yi musu waya su taho da
kwarin gwiwarsu yanzu kuwa idan na gaya musu
hankalinsu tashi zai yi su zo su cika asibitin ai ta
damunki.
“Wayyo Honey.” Ta kankame shi tana nishi likitocin
da suke kanta suna gaya mata ta yo nishi suna danna mata cikin a hankali tana yo nishi jariri ya
fado tare da tsala kuka. Haidar ya yi saurin
daukansa a cikin jinin ya na ta murna.
Likitar ta yanke masa cibiya ta karbe shi ta mika wa
nas don su gyarashi
Wata sabuwar nakudar jawahir ta kama ba jumawa ta sunkuto ‘ya mace ba da jimawa ba wani da
namijin ya kuma futowa.
Ikon Allah, Allah mai baiwa, Allah mai kyauta, har
da kari jawahir ta haifi ‘yan uku maza biyu mace
daya, ‘ya’yan kyawawa kamar ‘ya’yan indiyawa
don kyau da ja, Haidar duk ya rikice don murna waya yake ta bugawa kawai baya tsayawa
gaisuwa sai dai ya basu labarin jawahir ta haifa
masa kyawawan ‘ya’ya har guda uku.
Kafin ki ce meye wannan, tuni asibitin ya cika ya
zama filin barka barka tare da murnar samun
wannan kyawawan karuwar da aka yi. Kwanansu daya a asibiti aka sallame su don ba sa
mun hutun suke ba saboda jama’a da suke ta
tuttudowa ganin wannan kyauta da Allah ya yi
musu da ba kowa ake ba wa ba.
Nan kuma gaddama ta kaccame in da Inna ta daga
gida za a yo da jawahir da jarirai shi kuma Haidar ya ce babu in da za ‘a kai masa mata da ‘ya ‘ya, sai da
Abbansa ya daka masa tsawa ya nuna masa bacin
ransa a zahiri sannan ya bari aka tafi da su jawahir
da yaran gidansu.
Shi kuma Haidar ya yi fushi ya yi nasa gidan ransa a
bace, yana shiga gidan yaga bakinsa yau ba jawahir a ciki can kuma ya rinka hango ta tare da
‘ya ‘yansa ‘yan uku, haba wa, tuni wani sabon farin
ciki ya sake mamaye shi ya shiga wanka ya sake
sabon wanka ya zira farae shaddarsa sabuwa kal
mai laushi sai sheki take yi kamar boyel.
.
SALON SO
PART 41
.
.
Ya debi makudan kudi wanda ba zan iya cewa ko
na wane ba ya zuba a jaka ya fice ya kulle ko ina na
gidan ya fito ya kara gaya wa megadi ya kula da
gida sosai
Ya shiga mota da kansa yake jan motar cikin farin
ciki da annushuwa wani tsadaddaen hadadden kanti yaje wanda duk kayansu da ga waje suke
shigowa da shi. Nan da bude bakin aljihu ya runka
jidar kayan jarirai su tawul, da shawul da riguna
famfas su safa da takalman jarirai komai iri daya
guda uku yake kwasa, sai da ya cika but da kayan
jarirai har da gadaje set me uku na jarirai. Haidar ko ya manta ne da dinbin siyayyar da suka
yo daga kasar waje ta jariran ne? Oho.
Ya je ya siyo katon ragonsa wanda za a yanka
saboda naman gashi ya siyo kwandunan tattasai
da tumatir da attaruhu albasa da kaji da zabi
saboda girkin ‘yan barka ya yiwa direbansa waya ya taho da wata motar kwashe wasu kayan suka
nufi gidan su jawahir.
Tirkashi! Wani aiki sai masu da shi, aka rinka jidar
kayan da Haidar ya kawo ana kaiwa sashen momy
Haidar ya shigo yana ta gaisawa da jama’a suna yi
masa barka. Ya karasa falon Momi ya gaida su Momi su Anti
Babarsa da su Inna da kannansa ‘yan biyu. Dangi
dai rankacakaf kowa ya zo, jariran suna hannunsu
sun sha ado, da tsadaddun kaya ‘yan kantuna
masu kyau.
Sayyada ce take gaya masa ai jawahir tana sashenta ta ce kada abar kowa ya shiga bacci zata
yi, shi yasa aka kwaso jariran ma aka yo nan da su,
saboda yan barka.
Haidar ya ce ai suma jariran suna bukatar hutu da a
kyale su aka yi a jikin uwarsu suna jin diminta suma
suyi vaccin iya in an jima su ka tashi duk me son ganinsu sai ya gansu.
Anty babarsa ta watso masa harara yayin da ya
mike sum-sum ya bar falon ya nufi sashen da aka
ware wa jawahir.
Ya tura kofar falon ya shiga ko ina a gyare sai uban
kamshi da yake tashi, yana kai cikin dakin wani kalar kamshin ya ja mai dadi da sanyaya zuciya.
Ya hangota kan makeken gado tana ta baccinta
hankalinta kwance.
Ta yi kwanciyarta cikin jar sup me zanen ganye ta
kara kyau da haske sai dai ta rame. Ya karasa bakin
gadon ya sumbace ta yana shafa fuskarta tare da hura mata iska a kunnanta.
Ta bude ido
tare da fadada murmushinta “Lah, Honey ka daina
fushin ka zo? Ta tashi ta jingina a jikinsa ya
rungume ta yana shafarta tare da shakar
ni’imtaccen kamshin da yake jikinta. Ya ce “Bebyna ai ba zan iya fushi da ku ba, ina zan
iya bacci ba tare da naji diminki ba, ai ba ni da
kwanciyar hankali in banga ‘yan ukuna ba.
Aka kwankwasa kofar jawahir ta yi saurin kwace
kanta ta matsa can gefe, ta yi izinin a shigo.
Inna ce da sajida suka shigo dauke da kwanukan abinci.
Inna ta sakko mata da filo kasa ta ce zauna anan ta
bude mata kwanon tuwon dawa yana turiri ta
bude miyar kubewa danya da aka burge kaza ciki.
Daya kwanon kuma gasasshen nama ne ya ji
kayan kamshi da yajin daddawa. Sai kunun kanwa a kwanon sha Inna ta debo man shanu ta zuba
mata amiyar ta ajiye mata yajin daddawa, ta ce
“Sakko ki zauna maza ki cinye.”
Idon jawahir ya yi rau rau zata yi kuka, Haidar ya ce
“Haba Inna daman dan ki yi mata izaya da badin
tuwo da kunu shi yasa kika dage sai ta taho nan.? Inna ta ce, “Da Allah i min shiru ku me kuka sani
wannan ai shine gatan me jego shi zai sa mata
koshi ta sami wadataccen ruwan nono da ‘ya ‘yan
zasu sha su koshi ko kasan har yanzu yaran basu
sha komai ba sai zam zam da dabino?
Cikin tashin hankali Haidar ya ce “Inna saboda me? Bayan an siyo musu katon din madara.? Inna ta ce,
“Ai duk wani abu da za’a basu shi yanxu shirme ne
in dai va su fara shan nonon uwarsu ba, nonon
uwa shi ne abu mafi mahimmanci ga jariri. Don shi
yake sa su kuzari yake kara musu lafiya kuma don
haka ki sauri ki ci ga ruwan wanka can yakusa tafasa, idan an daki nonon da ganye zai temaka
wajen zuwan ruwan nonon da sauri
Haidar ya ce “A to ta so maza ki ci tuwon nan ki sha
kunun.
Jawahir ta kalli Haidar a marairaice alamun tsoro a
faskarta. Haidar ya kamo hannunta “Yi hakuri ta so na taya
ki ci kin ji kada ki damu.
Ta zauna kan filon shi kuma ya zauna kan kafet din
suka zuba yajin daddawa da man shanu suka fara
cin tuwo.
Yanda suka za ce shi ba haka suka ji ba, ashe dai shima tuwon dawar da dadi.
Tun suna ci suna hira har abin ya kaisu da shiru sai
dai gyada kai, kawai suke yi suna kai loma tare da
zuba santi.
Inna tana zaune tana kallon su sai da suka kusa
cinye tuwon nan, Inna ta zazzuba musu kunan a kofina ta tura musu gasashen naman shima sun ci
amma ba da yawa ba saboda koshin da suka yi.
Cikin kwana biyu ruwan nonon jawahir ya watada
tana shayar da ‘ya ‘yanta su koshi sosai.
Daddare dai ba sa shan nono sai madara yau
kwana hudu da haihuwar an kawo kayan barka akwati biyar na me jego da jirajirai.
Bayanin kayan da suke ciki zai cika min dan lattafin
nawa ban gama ba, hade da mukulun dankareriyar
mota jif, me ruwan ganye wadda Haidar ya yiwa
jawahir kyautarta da takardun dankareren gida da
yake a Nasarawa GRA shima gift ne ya bata duk saboda haihuwar ‘yan uku.
Sai takardun filaye guda uku kowacce da sunan
yaran mallakarsu ce kyautar ubansu Haidar da
yake ba su.
Kowa ya kalli kayan sai ya yi murna tare da son
barka da wannan hidima da Haidar ya yi. Ranar suna an sa wa jariran mazan sunan baban
Haidar da baban jawahir macen kuma an sa mata
sunan Inna.
Amma duk an boye musu sunan ana kiransu da
Salim, Sadat, Salma, Alhamdulillahi taron suna ya yi
kyau ya kuma kayatar ya burge kowa da yamma aka je dan Haidar da jawahir sun yi shigar kaya iri
daya jawahir ansha gwala gwalai hannu da wuya
da kunne har da sarkar kafa, sai sun jero a gurin
fatin suna rike da hannun juna suna tafiya sannu
sannu suna murmushi tare da hira kasa kasa a
tsakaninsu sai sheki suke yi kamar taurari, Bayan su
kuma Sayyada ce da Sajida sai Auwalu a tsakiyarsu
suna dauke da jariran yaran an yi musu kwalliya ta
ke ce raini Salma ta sha adon gwal har da siririyar
sarka ta kafa da ta hannu masu bidiyo da hoto sai
haskasu suke yi Sa’adu Bori ya saki kida yana wake su cikin wakar soyayya ta yi dadi Jawahir da
Haidar.
Allah ya raya Salim, Salma, Sadat, ‘yan uwa kuwa
suka balle bakin jaka sukai ta yi musu ruwan kudi.
‘Yan uwa da abokan arziki suka rinka ba wa
jawahir kyauta iri iri ta kayan jarirai da kudi da sauran su da haka taro ya watse.
Kowa ya nufi gida, jawahir tana zaune a gidansu ita
da jariranta da Inna sai kakar babarta wadda ita
take yi mata wanka.
Anty Maryam kuwa ta dage da sake hada wa
jawahir sababbin sinadarai na matse ‘ya mace da kara mata ni’ima mace ta koma kamar bata san
namiji ba.
Haidar kuwa kwana kawai yake yi a gidansa da
safe da ya gama shirinsa gidan su jawahir zai taho
ita zata hada masa break ya ci ya dauki yaransa ya
yi musu wasa sannan ya tafi office. Haka in ya dawo ma nan zai zo jawahir ta shirya
masa abinci ya ci ya yi kat yai ta rainon ‘ya ‘yansa ya
na yi musu wasa sai shadayan dare sannan zai
koma gidansa.

1 2Next page

Leave a Reply

Back to top button