SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

SAHIBUL AMRAT COMPLETE HAUSA NOVEL

[5/12, 12:05 PM] Mom Islam Ce: ????????????????????????
SAHIBUL AMRAT

????️????????????

Zainab Habib(Mom Islam

Bismillahir rahmanir rahim,Allah ina roƙonka ka bamu aron rai da kwanciyar hankali ,inda na fara littafinnan lafiya Allah kasa in kammalashi cikin ƙoshin lafiya amin ya rabbi.

Banyishi dan wani ko wata ba ????‍♀️ so in yazo dai-dai da labarinki/ka , arashi ne kawai.

__________________________P 1-2

Safiyar assabar ta kasance safiyace mai cike da ni’imomi mai tarin yawa , kasancewar zafin dayayi yawa a gari sbda damina tana shirin sauka ,
Yau kam alhmdulilh antashi da iska kowa sai hamdala yake.

Cikin iko na uban giji ruwa ya sauka kamar da bakin ƙwarya , mutanen garin sunyiwa Allah godiya da wannan ni’imar da suka samu.

Tashi ɗaya ruwan ya ɗauke ya zamo sai yayyafi , hakan yayi dai-dai da fitowar wata mata daga wani gida mai ɗauke da katangar galan-galan , ginin gidan ginin ƙasa ne ,kai dakaga gidan zaka gane ba wasu masu hali bane .
Budurwar da bazata gaza shekaru 20 ba taci gaba da tafiya tanayi tana wai-wayen bayanta , gyara zaman kwalin dake hannunta tayi tare da share ƙwallar data zubo mata ta kalli jaririyar dake cikin kwalin tana wasa da ƴan yatsunta biyu a baki , jaririyar na ɗiban kama da matar dake riƙe da kwalin hakan zai tabbatar maka da cewa itace mahaifiyar wannan yarinyar.
Tayi nisa sosai da gidan da take ,taje kan wata bola mai cike da ledoji da tarkace na ƙazanta ta ajiye kwalin tare da ajiye wata farar takarda a gefe ta sunkuyo tare da tofe yarinyar da adu’oi , batayi tsoron komai ba ta juya tabar jaririyar da ganin babu mahaifiyar tata yasata fara kuka .
Kasancewar babu wanda ya biyo hanyar bare yaga matar ,hakan yasata arcewa da gudu ta koma anguwrsu , zama tayi a kan dakalin dake jikin ginin gidan nasu ta rushe da kuka mai ban tausayi ,
“Allah sarki Norr kiyi haƙuri bazan iya cigaba da ganinki a gabana ba , gara in nisanta kaina dake ko naji sanyi a cikin zuciyata , sake share zafafan hawayen dake ambaliya a kyakkyawar fuskarta tayi kana ta kunto gefen zaninta ta kuma goge fuskarta ta miƙe ta shiga gidan ,tabbas mutum ma rahama ne ,ko kukan jaririyar nan yana tayata hira yanzu kam babu ita .
Wani ɗaki dake kallon gabas ta shiga tare da sakin labulen ƙofar tana mai cigaba da yin kukan .

Gidane babba amma bashi da yawaitar ɗakuna sosai ,dan ɗakuna huɗu ne ,kuma duka ɗakunan a kulle suke da kwaɗo sai guda ɗaya wanda Zainab take ciki wato wannan budurwar wacce ta fitar da yarinya .
Hular yarinyar Zainab ta hango ,a hankali ta miƙe tare da zuwa gaban ɗan kwandon da kayan yarinyar yake ,ta ɗago hular da hannunta ta kuma fashewa da matsanancin kuka ,da sauri kamar wacce aka zabura ta fice taja mayafinta dake rataye a igiyar dake tsakar gidan ,fita tayi tabi layin da takai yarinyar .
a tunaninta taje ta ɗauko ƴarta ,a fili tace “nayi kuskure Norr nayi dana sanin ƴardake a juji “tana tafe tana magana tana share hawaye .
Dik inda ta gifta yara ne ke kallonta sbda shigar da tayi ,riga da zani ne a jikinta koɗaɗɗu sai wani mayafi ja wanda tsabar jin jiki dayayi shima ya koɗe , bata damu da kallon da yaran suke mata ba ,taci gaba da tafiya , layin data ajiye Norr tabi tun daga nesa take hange tana cewa “ina ɗaukoki Norr zan dinga baki kulawa ba irin ta daba , dana hofantar dake ba .
jin tayi tuntuɓe da ledoji yasa ta tabbatar da ta iso bolar , kallon dai-dai inda ta ajiye Norr tayi taga babu kwalin balle Norr ko zanin data kwantar da ita , wata rufaffiyar takadda taci karo da ita wacce ko ba’a faɗa mata ba ,zatace wanda ko wacce ta ɗauki Norr itace ta ajiye wannan takaddar .
Jiki na rawa ta sunkuya , ta ɗauka tashi ɗaya jiri ya fara ɗibanta da sauri ta sauka daga kan bolar ta nemi wani itace dake gefe nesa da bolar ta zauna tare da rafka uban tagumi , yanzu kam tama kasa kuka bata ma san yaza’ayi kukan yazo mata ba ,sai uban faɗuwar gaba dake ziyartar ta .
Lahaula walaƙuwwata illa billa ,ta dinga mai-maitawa ,a hankali wasu siraran hawaye masu ɗumi suka fara sintiri a kyakkyawar fuskarta , ajiyar zuciya ta sauke tare da damƙe takardar dake hannunta.
Cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙe taci gaba da tafiya kamar ƴar maye ,
Tana isowa gidan nasu ta zube a tsakar gida tare da ɗora hannu a kanta ta tsala uban ihu tace “Norr !!” idan kaga inda Zainab take kuka dole zai baka tausayi sbda kukanda takeyi muryarta ma bata fita sosai.
A hankali ta rakuɓe jikin bango tare da rafka tagumi gunani iri-iri ne ya ziyarci zuciyarta.
Wane hannu Noor ta faɗa ?,shin waye ko wacce ce ta ɗauki Norr ?” Allah kaga halin da nake ciki Allah ka dawomin da Norr dan isar annabi ” ta ƙarashe maganar tana share hawaye .

Ƙiran sallahar da taji ne yasata miƙewa ta ɗauro alwalar azhar ta dawo ɗakin nata ta kabbara sallah ,bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama taci gaba da kaiwa Allah kukanta , bayan ta idar da sallah ta ninke sallayar tare da jingina kanta da bango taci gaba da rera kuka .
Sallamar da taji ne yasata share hawaye tare da goge fuskarta da hijab ɗin dake jikinta , ta amsa sallamar tace “wa’alaikumussalam “ta buɗe gefen labule ta leƙa tace “sannu da dawowa baba “.
Baban dake sanye da rigar shadda ruwan goro ,hannunsa riƙe da magirbi yace “yawwa Zainabu me kika dafa mana ne ?” kanta a ƙasa sbda wasu sabbin hawaye ne suka fara zubo mata tace “shinkafa da mai da yaji ” baban yace “masha Allah ina fatan kinci kin ƙoshi ko ?”
Gyaɗa masa kai tayi alamar eh ta miƙe taje ta kawo masa ,lokacin ya shiga ɗakinsa ya zauna yana ƙirga wasu kuɗaɗe .
Da sallama ta shigo ta ajiye masa abincin kana tace “babu ruwa a gidab fa ” baban yace “haba Zainabu koke bazaki fita ki ɗibo ba? ” shiru tayi masa tare da sunkuyar da kai ƙasa a zahiri Allah kaɗai yasan inda takejin zuciyarta,ta miƙe ba tare da tace masa komai ba .

4:37pm yayi dai-dai da fitowar baba daga ɗakin da Zainab ta kai masa abinci , bankaɗa labulen ɗakin da Zainab take yayi ,har zaiyi magana sai yaga tana sallah ,ya fice .

Koda ta idar da sallah ta cire hijab ɗinta ta shiga kitchen , bayan ta haɗa wuta tayi murhu biyu , ɗaya na tuwo ɗaya na miya ,bayan ta gama zuba kayan haɗi ta rufe tukunyar miya ta gyara wutar tuwo ta koma ɗaki .

“Zainab ga pampas kisawa Aisha ” da sauri Zainab ɗin ta fito gudun kar baban ya zargi wani abu yasata miƙewa da sauri har ta kusa faɗuwa ta zo gaban baban tace “to angode “sai kuma taji tsanar mahaifin nata nayi mata mamaya a ranta .

Ɗaga kwandon kayan Norr tayi ta ajiye can ƙasa ta kuma fashewa da kuka yinin ranar dai haka ta yishi babu daɗi ko kaɗan , bayan ta gama girki tasa nata ta sawa mahaifinta ta zuba ragowar a roba ta kawo ɗaki , lokacin anata kiraye-kirayen sallahar magrib ,gari yayi duhu sosai kasancewar ruwan da aka yi kuma har yanzu da hadari sosai .
Bayan tayi magrib ta janyo tuwon ta da dama ta riga ta zuba miya ,tayi tagumi ga faɗuwar da gabanta keyi babu ƙaƙƙautawa, bayan ta gama cakular abincin ta ɗauko murfi ta rufe tare da ɗaukar buta ta kuskure bakinta ,ta dawo kan sallaya ta kabbara isha’i ,bayan ta idar tayi adu’ointa data saba ,ta shafa kana ta miƙe taje ta ɗauko takardar ɗazu wacce ta ganta gurin kwalin data ajiye Norr , gabanta na tsananta faɗuwa ta buɗe takardar tare da fara karantawa ,saƙo ne ta gani kamar haka…

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button