SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Ummah ta budi baki zatayi magana yace tsaya kar ki ce komai
Nifa nasan duk abunda kike ciki na rayuwar ki,kuma kisa ranki hakan yasa nake daga miki kafa
Tun farko,do this job ke ma zaki ji dadin sa.
So gudluck …..
Nan Ya ajiye mata sakon envelope mai dan tsayi yayi gaba abun sa.
Takai minti 20 tana kallon sa daga bisani ta kauda kai ta koma ta zauna daga kan kujera
budewa ta yi ta duba,
Duk abunda take bukata na rubuce anan,
dan zaman ta da kawayen harkan ta yasa yanzun ta iya karanta abu, kuma tana jin turancin jifa jifa atleast tasan yes come go da sauran su.
Wayarta ta dauka ta kira sahura sun kai minti 50 suna magana daga bisani ta fice ta dawo gida. ..
Kwana biyu bata leka ko ina ba domin daga cikin takardan ranar sabon aikin ta zai fara daga kwana biyu masu kamawa
Da shike anty sahura ta dawo sai naga sun sa karfi sosai wajen shigar dani makaranta
Ranar da ummah zata fara sabon aikin ta ranar suka sakani avwani nigerian international academy.
wanda ake biyan akalla dubu 250k kowani session..
tsarin ilimin su na da bala’in kyau da tsari don haka ummah tayi min alkwarin zata nema min lesson teacher idan ta samu wasu kudin don nima na iya abubuwan kamar sauran yara..
Haka ma anty sahura ta min nasiha mai shiga jiki da ratsa kwakwalwa cewar ta,na dage nayi karatu don nan gaba ni zan rike su,su ma sa’a suka ci suka samu aiki mai kyau suke kokrin ganin bansah wahala irin nasu ba a rayuwa..tace amma nan gaba komin su zai iya karewa sabida haka na dage kar na basu kunya musamman ma ummah na dake wahala sosai akaina….
A Haka na shiga karatun da imanin zan yi ne don na biya ladan zufan mahaifiyata da duk wani fadi tashin da take yi,
Sosai na cire hidiman rayuwar duniya na sa jaratu na agaba duk da wahalar da nake sha wajen shiga tsarin wayewar makarantar..
Gashi an maida ni baya, sai naga duk nafi yan ajin mu girma wani bin har kunya nake ji amma su kam ba ruwan su,
Jira ma suke nayi magana suyi min dariyar don kowa ya gane ban iya turanci sosai ba.
Anan na kame kaina bani da aboki ko abokiya..
ummah kuwa ta kama aikin ta, wajen babban ogan ssa danjuma mai suna abdul aziz shayal..
A reknown popular industrialist yana da kudi kudi na fitina..
shine ya raini ssa danjuma da irime iren sa sun fi akirga shi asalin dan kano ne amma mahaifiyar sa lebanese ce so fari fatt ne kamar jini zai fito afatar sa.
Ba laifi ya tsufa don kuwa tamkar yarinya karama haka yake kallon ummah,
Farkon zuwan ta ya gaya mata asalin shi tun da ya ganta anan gidan ssa danjuma ya ji ta burge sa shiyasa yace yana so tayi masa aiki,
ya kuma tambayar ta nawa ake biyan ta a aikin ta ummah bata boye masa komai ba ta fada cikin gaskiya,
Bata sani ba ya bincika ganin tana da gaskiya sosai yasa ya shiga bata gwaji kala kala batare da ya taba kusantar ta ba..
Wani bin har ya kance ta bishi bashin kudin aikin ta, duk da yasan tasan yana da shi amma sai bata taba masa complain ko rashin kunya ba..
Haka zata zo da safe tayi masa danna a kafadun sa da kafafun sa yana shan iska a farfajiya haka zata yi jigilan dafe dafe tana kawo masa cike sa ladabi da biyayya.
ranar da na gama exams na zangon farko wato first term,sai aikin ya dan fara bata tough time sabida tulin lokacin nan a tsarge take don har yau oga shayal bai taba kiran ta kan gadon sa ba amma baya so ko kadan idan yace ta zo ta kawo masa wani complain duk dama yana mugun respecting din ta da yanayin ta,bata da hayaniya sannan tana da ladabi akan aikin ta..
Ana cikin haka ranar ya kira ta cikin dare misalin 1 saura duk sai ta rasa yadda zata yi ta fice,
Gashi nakanyi karatun dare sabida yadda na sa abun Araina
Gani take idan tace zata je aiki a wannan lokacin zanyi suspecting wani abu gashi ta tabbata in har ta fice zan ji kuma zan fito..
Shikuwa ya takura sosai har da turo driver sa,gani take hala yau ne yake so ya kira ta gadon sa,ga damuwan hakan aranta ga damuwan yadda zata min bayani washe gari.
Babu yadda ta iya sai ta daure ta fito din asace ta iso har gidan sa
Ganin ta kasa sake ranta yasa shi yayi murmushi,
Yau kusan wata uku kenan da haduwar su amma yana ganin kamar ya karance ta fiye da yadda take tsammani.
Sosai yake tausaya mata haka kawai shiyasa ma yakasa aiwata komai da ita,
ummah tana zama nikuwa dana fito shan ruwa bangan ta ba ya sa na shiga kiran layin ta,
ganin kiran yasa ta rasa ya zatayi inta dauka me zata ce min?
anya kuwa zargi bazai fara shiga zuciyan yata ba, ?duk sai ta damu
Alhj shayal Duk yana lura amma sai ya dauke kai,
anan ummah ta koma gefe ta kira anty sahura tayi mata bayani,
cikin bayanin yake jin abubuwa dayawa hakan ya sa ya kudira aransa yau sai yasan ita wacece…
tana kammala wayar yace mata wacece wannan…?
cikin ladabi tayi masa bayanin komai bata boye masa ba..
Jin tace bata taba kwana awaje ba sabida yarta yasa ya ji wani iri,
“yace mata tayi hakuri dama yana da muhimmiyar maganan dayake damun sa ne kuma baida wanda zai iya fada masa sai ita shiyasa yace ta zo..
abun ya bata mamaki amma dai ta sa a ranta cewa zata saurare sa ,a tunanin ta zai bata labarin wani abu ne ko wani matsalan sa amma sai ya shiga mata nasiha mai cike da nazarin rayuwar duniya
Sosai jikin ta yayi sanyi Gani take kamar Zuciyan sa gaba daya ya bude ya mata karatun ta nutsu akan rayuwa..
Anan itama hankalin ta ya bata wannan mutumin ya gama fahimtar ta gaba da baya,amma meyasa hakan ne bata gane ba,
yace ma umma,zai tafi wajen familyn sa sabida dama hutu yake zuwa amma bazai sake dawowa ba.
Shiyasa yake so yasan ita wacece kuma meyasa take wannan harkan a tunanin sa mace kamar ta mai kawaici sanin yakamata da tunani, bai dace ta shiga wannan layin ba..
sai yace ko dan yarki kike yi?
Ba yadda ta iya ta amsa mashi da eh,
Yace mata ta ina ta hadu da ssa danjuma?
Labari ya na tada labari har sai da ta gaya masa labarin ta kaf da abubuwabln data fiskan ta arayuwa..
Yaji abun har ransa, duk dama jikin sa ya bashi ita ba ko wata irin mace bace tun farko amma baiyi tsammanin labarin ta yakai haka muni ba,..
Bai iya cewa komai ba sabida ya jima yana kai kawo da radadin zafi da hawayen ta ke fitarwa,
yace yanzu aiki daya zaki yi min a yanzu ki kwana nan gidan gobe da safe zan nemeki ..
Tayi godiya ta koma daki ta kwanta..
Sai dai Tunani duk ya hanata yin baccin sanadiyar tono maganan da tayi sai take jin wani sabon yanayin zafi da nadama aranta
Haka har gari Allah ya waye,
kamar yadda aljh shayal ya mata umarni haka
Ta koma gida da safiyan Allah..
Ta same ni har nayi sallah ina kimtsa wajen
Gashi batayi magana da anty sahura ba bata san me tace min ba
..
bayan ta kimtsa ta fito nake cewa ummah,tunda ina hutu ki bari mana ina tayaki aikin naga kamr yanzu yayi miki yawa
Cikin hikmar ta na uwa tace waya gaya miki hakan.
Nace”ai jiya da na ga baki nan anty sahura na samu awaya take cemin aiki kuke yi…
ummah ta dan yi ajiyan zuciya tayi shiru tana kallon na daga bisani tace saratu”idan aiki kike so toh ki dubi littafan ki da kyau kiyi karatu…idan kuma tausayi na kike sai
Ki dage sosai ki cimma burin ki,..dan Allah kar ki bijire ma tarbiyan dana miki don shine taimakon da zaki min,kinji?