NOVELSUncategorized

KWARATA 35

  ???? —— 35

      Har yaci gaba da cin abinci kuma yaji gaba ɗaya moƙoshin nashi abincin baya wucewa , tsananin ɓacin rai da damuwa suke ta kartar masa zuciya , dakel ya haɗiye yawu mai ɗacin gaske , kallon Al ‘ ameen yayi yace kiramin Umar….


     Wayar ya ɗauka da sauri ya fara kiran wayar Umar , saida Umar ya ɗauki wayar ya miƙawa Dikko cikin ladabi , ansa Dikko yayi cike da ɓacin rai yace har yanzu kana anguwar ko ka fita ne … ?

    Magana Umar ɗin yayi , Dikko yace tou kaje ka kaima An mata waya zanyi magana da ita yanzu ² yi sauri karka ɓatamin lokaci , saida ya jira abinda Umar zai faɗa sannan Dikko ya kashe waya ,

Ina zaune ƙofar gida dani da Alajina muna fira Umar ya faka da machine inshi , kallo ɗaya nayi masa na kauda kaina yayin da na ciro wayana na fara ƙoƙarin kiran Wane Yaro ,

     Sallama yayi suka gaisa da Alaji nima ya gaisheni , ansawa nayi babu yabo ba fallasa , ɗan gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa dan girman Allah saƙo aka bani wurinki , daina kiran wayar Wane Yaro nayi na tattara hankalina kaf wurin Umar nace waye ya baka saƙon ne …?

     Cike da ladabi ya miƙomin waya bayan ya kira number ya miƙomin yana cewa kiyi magana an ɗauka , cike da wasi² na kara wayar a kunne na tare da cewa Assalamu Alaikum….

     Ansa sallamar yayi yana mai ci gaba da cewa An mata kinaso in saka ƙafar wando ɗaya dake ne ? Shiru nayi banyi magana ba , Dikko yaci gaba da cewa na rantse da Allah ki kama kanki wannan iskanci birthday in da kika taro ki warwareshi tun kafin inzo wurinki ina fushi , banda kyau idan na ɓata rai ki roƙi Allah ya rabaki da ganin fushi na amma na rantse da Allah…. Saida yayi rantsuwa mai sa faɗuwar gaba sannan yace idan kunne yaji ….

        Sai kuma yayi shiru bai ida faɗar maganar ba , ni kuma na ɗaura da cewa idan ka barni na huta baka ƙaunar Allah , tsoki nayi tare da miƙawa Umar wayarshi naci gaba da magana na da Alaji ,

Cike da masifa Dikko yace Umar ya maidomin wayar , bani yayi nima kuma na ansa , cikin sigar lallashi yace An mata nine bana ƙaunar Allah ? Wai mi yasa kike min magana haka babu ɗa’a , ai kasan gidanmu ba’a koyamin ɗa’a ba shi yasa ma har nayi rashin ɗa’ar a cikin gidan ubana ,

      Dikko yace idan kinajin rashin kunya ki fita daga cikin mutane ki zageni idan kin isa , ni nasan baki isa kimin rashin kunya inda babu kowa ba , dama kin tsaya a gaban waɗanda ko naso nayi miki hukunci zanyi haƙuri a haka kike tunanin bakyajin tsoro na ne ? Idan dai bakijin tsoron Dikko maza ki tashi daga inda kike kice Dikko ƙarya kakeyi nafi ƙarfin ka takuramin ki faɗi haka kiga yadda zanyi wasan kura dake wallahi ….

     Kamar wata sakara na miƙe na matsa daga inda su Umar suke , ashe shi kuma yayi wayau ne dan kar in riƙa wulaƙantashi ne a gaban yaronshi , saida na matsa sannan nace ƙarya kake ni nafi ƙarfinka kuma nafi ƙarfin ka takurani dan banajin tsoronka kayi duk abinda kakejin zaka iya yi na matsa daga cikin mutanen….

     Dikko yace tou babu komai dani dake aga fasashshe , ni zanzo katsina insha Allah gobe talata , ke kuma zakiyi birthday ranar laraba sai nazo , kuma karki sake kiyi mafarkin gemuna na faɗa miki….

    Gemun banzar ka gemun wofi , Allah ya sawaƙe min in ganka a barci na , cikin murya mai saukar da kasala yace nifa bana san cika baki bayan nasan komai , kawai yarinyar kirki taga ustaz ta maƙale mishi aidai kina so na ko…. ? 

Tsoki nayi ban bashi ansa ba na kashe wayar naje na bawa Umar ko sallama banma Alaji ba na shige gida raina a ɓace ,

      Murmushi Dikko yayi bayan na kashe waya tare da cewa An mata rigima , zaki zo kusa dani kuma inaji a jikina wata rana zaki rumgumeni ki kalli cikin idanuwana kice Dikko ina sanka , yana maganar yana nuna yanda Sultana zatayi , cikin farin ciki yaci gaba da cin abinshi bai sake kiran Umar ba , kuma koda Umar ya kira dan ya faɗa masa cewa Sultana ta tafi bai ɗauka ba , 

     Shima Alaji kiran wayana yayi tayi naƙi ɗauka , ya gaji ya tashi yayi tafiyarshi , shima Umar tafiyarshi yayi gida ,

Ni kuma ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa nayi ruf da ciki bansan dalili ba , maganar Dikko yake dawo min a zuciyana , karki sake kiyi mafarkin gemuna , cike da fargaba zuciyata ke cewa kodai Dikko ya gane ina kallon masa gemu ne …. ? Tsoki nayi na gyara kwanciyata ina tuno kyakkyawar fuska Dikko , tunani dai barka tai a zuciyata har bacci ya ɗaukeni….

 Da safe Alaji yazo ya kaini kasuwa dan Babana baya nan kuma motana tana wurinshi , siyayya na bada mamaki nayo domin fa Alaji yana da hidima kuma yana da gabata , ya kashe kuɗi duk yanda tunani baya tunani , ko kayan da zan saka wurin partyn zagayowar shekarar aihuwata wallahi masu masifar kyau da tsada ya siyo min abun dai zabburgewa sai wanda ya gani ,

      Bayan mun gama siyayya nace masa ya tafi zanyi kitso idan na gama zan kirashi ya ɗaukeni , Alaji yace to saida ya ƙaramin kuɗi ya tafi ni kuma na shige shagon “yan arna da basa gane yare na , na fara faɗa musu abinda nake so amma dan ubansu wai basu gane ba , saida wata rantsatstsar karuwa maiji da iskanci har iskanci yayi mata sign tayi musu bayani , girar ido za’a sakamin akaifa da kuma atach duk gashina saida nasa aka yimin ƙari saboda tsabagen wawanci irin nawa ,

     A ƙofar gidanmu kuwa 5:00pm Dikko suka kafe motocinsu , aikawa yayi a kirani amma sai akace masa na tafi kasuwa , maimakon ya tafi sai yace zai jirani har na dawo , 

     Duk lokacin da minti ɗaya ya wuce sai Dikko ya kalli agogo ranshi ya ƙara ɓaci , shiru ² babu ni har aka kira magrif , cikin damuwa yace ma Al ‘ ameen muje zan dawo anjima ,

      Tashin motocinsu sukayi gaba ɗaya suka taho , suna fita anguwar mu kuma muna shigowa hannun riga mukayi dasu wato suna fitowa mu kuma muna shigowa ,

     Babu abinda na sauko daga mota nace ma Alaji ya tafi sai Allah ya kaimu , sallama mukayi dashi ya tafi ni kuma na shige gida , ina shiga na shirya a gaggauce domin Baban Amisty zaizo , naje kasuwa har nayo kawalcin mace zan haɗasu , itace karuwar da muka haɗu ta tambayeni sana’ar da nakeyi nace mata karuwanci nakeyi , tace ashe tafiyar ɗaya ce ? Nace mata Eh musayar number mukayi har na bata labarin iyayensu Amisty tace suna da mai ne ? { kuɗi } nace sosai ma , shine tace a cikin daren nan in bata aron kowa a cikinsu ita kuma tamin alƙawarin zata ɗaukomin su dukansu a cikin yanayi mara kyau tou shine zan haɗasu , duk da dai malami da mawaƙi da karuwa basu da amana amma zuciyata ta yadda da ita 100% ,

    Har ƙofar gida Baban Amisty ya ɗaukeni kuma yanzu ma muna fita Dikko yana shigowa , akace masa yanzun nan muka fita ko bakin titi bamu kai ba , da sauri ya biyo bayanmu ko zai sameni amma bai iskomu ba , ganin baisan ta ina zai samoni ba yasa ya haƙura ya koma ƙofar gidanmu a ranshi yayi alƙawari ko zankai yaushe ban dawo ba zai jirani ,

Daga gidanmu ƙofar soro muka nufa gidansu Mamy ƙarfe 8:18pm mukayi parking a ƙofar gidansu kamar yanda tayimin kwantance , bayan mun tsaya na kirata a waya , babu jimawa ta fito cikin shiga mai ɓatar da hankali , tana isowa ta kama mota ta buɗe ta kashe a gidan baya , shi kuma yaja mota muka tafi , shegen tsoho kenan yace ina muka nufa ne ? Yayi maganar yana kallona ,

    Murmushi nayi tare da cewa nifa guzirin dare nayo maka itace zaka tambaya bani ba , kaga ni kullum muna saka rana amma abun bai yuwu ba shine dana ga mai buƙatar ruwa a tsakar rana nace tazo ina da ƙatuwar randa { tukunya } a gidana har yoyo takeyi { ɗiga } kaga kuwa idan har ta riƙe babban kofi a tausayawa ruwan nan domin saita ƙare shi kaf hankalinta zai kwanta , juyawa nayi na kalli Mamy sannan nace a ina zakisha ruwan ne …. ?

      Cike da bariki tace aishi ruwa ko a tsakiyar hanya shanshi akeyi saidai idan ba ƙishirwar ke damunka ba , amma tunda ni mace ce dole zan matse ƙishirwa har mu isa gida , amma ka daure kar kayi tafiya mai tazara dan lumfashina gaf yake da ɗaukewa , !

     Karkata mota yayi ya ibi hanya , muka nufi kwaɗo , har muka isa babu wanda ya sake magana , a ƙofar gida yayi parking shida ita suka shiga aka barni a cikin mota ,  shigarsu babu jimawa na fara kiran Baban Hafsa inda zamu sameshi ya faɗa mana nace muna zuwa babu ɓata lokaci , Mamy kuma da Baban Amisty bansan abinda ya faru ba , sundai share awa da rabi sannan suka fito…

    Bayan sun fito ta buɗe inda nake zaune tace fito mana haka nan , nace kidai shigo muje , Mamy tace nan zamu sauka , fitowa nayi mukayi sallama dashi tare da ƙara tuna mishi sai mun haɗu wurin party yace in Allah ya yadda , yana tafiya muka samu wuri muka zauna , wayata ta ansa ta tura min vidion data ɗauko nashi abundai babu kyan gani ko ya akayi tayi masa dibara ta ɗaukoshi tasa shi sai iskanci yakeyi , a wayana ta tura bayan ta tura ta shiga whatsapp ta turawa Amisty abinda zata faɗa nake faɗa tana rubutawa…

     Salam aminiyata Amisty , Sultana ce ban sani ba ko kin goge lambana shi yasa na baki sani dan kar ki shiga dogon nazari da tunani , kinsan mage bata cin bushiya , idan kuma maciji ya raɓi bushiya noƙe kanta takeyi yana tahowa da ƙarfinshi dan niyar mugunta sai ta noƙe kanta ya soki ƙayoyinta , maciji baya san tabo daga nan sai ya sari kanshi ya mutu , bushiya sai ta fito taci gaba walinta a duniya , tou haka tsaka take mage kaɗai ke cinta ta rayu amma ke in kakaci ta sai sheƙawa lahira , ganin aljanni a siffarshi akwai tsoro da firgitarwa masana ɓoyayyan sirri suna cewa idan kaga aljani a siffarshi kwanakin mutuwar ka ne yazo , nidai naga aljani ban mutu ba kuma naci tsaka ban mutu ba shi yasa na turo miki kema ki gani shin kina da yawancin kwana ko daga yau kwananki ya ƙare ne….?

   Turawa tayi ni kuma na ɗora da voice note cewa kiyi haƙuri kuma kibi sannu ki warware maganganuna kinsan tsarƙesu nakeyi idan kin gani kiba Hafsa ta tayaki gani….

Bayan na tura muka hau napep muka doshi barhim estate acan Baban Hafsa ke jiranmu , shima dai sun shana yadda ya kamata kuma Allah ya bata nasarar ɗauko min mugu , itama Hafsa tura mata nayi da voice note cewa…

     Duk gudun kare idan yaga kura ɓoyewa yake domin tsira da rayuwarshi , haka mutum idan yaga abun tsoro kuka yakeyi ya rumtse idanuwanshi , irin haka kikaji a lokacin da kika cire towul in dake jikina….. ?

      Ina gama faɗa na sakeshi ya tafi…. , Napep muka hau muka nufo gidanmu , saida aka fara saukeni aka wuce da ita bayan ta shedamin zasu zo wurin shagalin ita da zugar tata ƙawayen , godiya nayi ina ɗaga mata hannu har suka tafi ,

      Kallon agogon hannunshi yayi yaga 11:35pm , daga ina nake a wannan daren shine tambayar daya fara ma kanshi kuma bashi da mai bashi ansar tambayar , ni kuma cike da farin ciki na tunkari ƙofar gidanmu sai tsalle² nakeyi na jin ɗaɗi na shige gida abu na ,

     Jiki a sanyaye DK yaja motarshi ya nufi gida zuciyarshi tana mishi babu daɗi , amma yayi addu’a gobe tazo mishi lafiya ,

      Yau laraba kuma itace ranar da nake wannan gagarumin taro wanda na samu damar gayyato mutane daga sasoshi da dama , tunda safe ake shiga da fice a gidanmu duk inda ka buɗe idonka zunzurutun karuwai ne kawai suke kai koma , wane yaji ga wane waccen taji ga wance , taron motoci ne burjik a ƙofar gidanmu duk wanda ya wuce sai yayi tir da irin matan da dake ƙofar gidanmu !

     Shi kuma Dikko a safiyar nan tayi mishi babu daɗi dan matarshi aka kai asibiti bata da lafiya sosai , kuma taƙi cin abinci ta rame tayi duhu saboda ciwo da damuwa , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi da guda ² kallo ɗaya zaka mishi ka gane yana cikin damuwa , ga damuwata ga ciwon matarshi ….

     Taruwa akaci gaba dayi duk yaran Baba Ƙarami sunzo gida ya cika taf kuma na duba har yanzu daga Amisty har Hafsa babu wanda ya hau online dan suma suna can suna shirya tasu gadar zaren ,

      Komai fa anyi kowa ka gani a wurin shima yakai wani babban shege , sai 6:00 aka fara tafiya wurin partyn , Nana dai bata samu zuwa ba mijinta ya hanata kuma ta hanu , Karima itama bataje ba amma A ` i da Saude tare dasu aka tafi duk yayuna maza da mata sunje ,

Dikko yana duƙe gaban gadon Sadiya riƙe hannunta yayi cike da damuwa yace Sadiya karki kashe kanki don Allah idan baki so na ki faɗamin sai in sahale miki auren nan ki huta , ni ina da damuwa idan naga kina cikin damuwa ko nayi miki wani abu bai miki daɗi ba ne ?

      Karkata kanta tayi gefe hawaye suna ci gaba da gangaro mata , zama Dikko yayi gefen gado ya tattaro natsuwarshi fuskar Sadiya ya tallafo da duka hannayenshi yace mene ne ? Ki faɗamin wai meke damunki ne ? Dakel ta ɗaga bakinta zatayi magana a daidai lokacin da wayarshi ta fara ringing , cirowa yayi ya duba , Umar ne dan haka ya ɗauka tare da cewa ina ne….. ?

      Bayani Umar ɗin yayi masa , bayan ya gama Dikko ya kashe wayarshi , shafa gefen fuskar Sadiya yayi ina zuwa , yana faɗin haka ya miƙe ya fito daga ɗakin , ita kuma taci gaba da kuka , bayan ya fito yacewa Mom insha zaije ya dawo yanzu , Allah ya tsare tayi masa Al ‘ Ameen da sauran tawagarshi suka rufa mishi baya…. !

     A bakin get suka ɗauki Umar suka nufo inda muke taro , a lokacin anci rabin shagali itama Hafsa ta taho dan ta wulaƙantani tunda gidan Babanta ne , amma tana zuwa labari yasha banban duk wannan taron jama’ar bai hana uban Hafsa rungumeni ba ya yanko cake yana bani a baki , gaba ɗaya wurin aka ɗauki sowa da ihu shi dama Alaji tunda ya ajiye kayan party nace kawai yaje tunda taron mata ne babu maza , kuma yayi tafiyarshi…

      Lallaɓawa tayi ta koma da baya ba tare data bari wani yaji koya ganta ba , ihu akaci gaba dayi sakin sauti akayi yadda ya kamata mata sukaci gaba da farantawa sheɗan ,

       Hafsa tana fita taci karo da Dikko ya fito daga mota , da gudu ta nufi wurinshi tana kuka cikin kuka ta fara faɗa mishi abinda Sultana tayi mata niko nace danma baki ga vidio ba , number wayar Sultana Dikko ya ansa a hannun Hafsa ya fara kiranta ,

 Muna ta cashewa wayata ta fara zurzur dan ba ƙara takeyi ba murzawa takeyi sai kaji sautinta yana shiga maka hannu burbur , ɗauka nayi naci gaba da kwantace ba tare dana jira naji ko waye ba ,

Cikin wata irin murya yace fito gani nan na kasa gane gidan , wallahi banyi tunanin Dikko bane nayo waje , ina fitowa naga Hafsa tsaye da wanda bansan ko waye ba domin ya juya bana ganin fuskarshi sai bayanshi , cike da mugunta nayo wurinta dan a tunani na taga vidio zamu cashe rashin mutunci ,

      Saida nazo gabansu na gane Dikko buɗe baki nayi da zumar nayi magana ya wanka min wani irin gigitaccen mari harsai dana juya kamar ranfa saboda karfin mari kafin in dawo hayyacina ya sake wankamin wani firgitacce wanda saida nayi ɗimuwar tunani na dan wallahi a daidai lokacin da zaka tambayeni suna na bansan abinda zan faɗa maka ba ,

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button