HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Nayi shiru na dago ina duban ta,a sanyaye nace haka ne ummah nayi miki alkwari bazan saba miki ba…

Tace haka nake son ji ki bar wani zanjen aiki kam ni zanyi, tunda na wuce lokacin karatu ko wani abu,sai dai na taimaka miki kema ki taimaka ma wasu
Ta dada bani close look tace “Saratu,inason Ki girma da son ki kare mutuncin ya mace aduk inda take,kar kiyi zalunci kar kiyi cuta ki zama mai gaskiya da rikon amana,kar ki bari duniya ta tayyara kowa kamar yadda ta so ta tayyara mu,kiyi adalci ma duk mai bukatar haka..
..ta dada matso hannuna tace” amma kisa aranki ke saratu ce,kar ki taba mancewa da kanki, saratu ne yar gidan bukar kar ki taba mancewa da inda kika fito.kallon ta kawai nake yi nakasa magana dabida na fahince me magana yake nufi.

Wato Tuna kaina kadai zai sa na rike dukan alkwarin datake so na rike akan rayuwa ta nan gaba.

Ganin yanayi na yasa ta sake hannu tare da maida hawayen dake so ya sauko mata afuska ta ta cigaba da cin abincin ta..

wani duniyar tunanin na shiga,sai nake dagowa hala rayuwa na mugun ma ummah na wahala fiye da yadda nake tunanin no wonder naga take samun karfin gwiwa da wayewa who knows whats shes going trou amma har yau ban kawo wani zargi araina ba.

sai na shiga kulle kullen yadda zan tabbatar mata da ni yar halak ce,daga wannan ranar na kudira araina zan yi dukan abunda da ummah na tace tana so na zama a rayuwa..

bayan kwana biyu da faruwar haka,alhj shayal ya kira ummah.
Daga wannan ranar rayuwar mu ya fara shiga wani sabon tsari,

bisa adalcin sa ya yanke ma ummah wani gurbi daga cikin arzikin sa na sabgar sa da harkokin gona da kiwon kaji da da dabbobin gida na zamani
Sai ya mallaka mata halak malak tare da gida madaidaici mai dauke da komai da komai har da mota nissan mai kyau na mata…

A cewar sa yayi tunani tunda bata yi karatu ba,zata iya jan jari ta kuma rike sa da kyau da ilimi da basiran da Allah ya bata.

Duk dama ya bata shawaran tayi makantarr yaki da jahilci bai hana shi jan kunne ta ta lura da duniya ba

Duk da karfin gwiwar ummah da kuma buri da ta sa akaina yau sai take ga kamar bai kai na alhj abdl azeez ba saboda tausayin labarin ta daya keji yasa ya dauki nauyin karatu na, daga yanzu har lokacin da zan gama masters..
signed and sealed.

ya kuma cewa ummah ya mata haka ne sabida yaga zuciyan ta kuma ya tabbatar da cewaa ta cancanci taimakon sa fiye da dubbai da ya taimaka musu suke lalata rayuwar su da na wasu.

Tayi kuka mai cike da godiya,ranar ji take tamkar qayar dake soke azuciyan ta aka cire mata,kamar amafarki haka take jin kalamn sa
yace mata lokaci yayi da zata yi aikin halak din ta don ta cimma burin ta na rayuwa sannan ta dawo da kimar darajar tarbiyan ta da qaddara ya taba mata shi..

hatta sahura sai da ta ta niko gari ta zo ta yi godiya ma alhj shayal wanda har i yanzu gane yake ma bai mata komai ba…

Ganin rayuwar ummah ya samu babban rabo ya sa sahura ta soma jin aranta tunda itama ta samu rufin asiri sosai yaci ace ta itama ta sake harkan tsira tun wuri kar abun yayi nisa…

 

Su ukun da ummah da anty sahura suka dawwama wajen bani rayuwa sai dai na kanji suna maganan sa amma bantaba ganin sa ba

Cikin kankanin lokaci aka samo min lesson teacher wanda baijin ko zo da hausa shiyasa ni agaba da karatu har nakan ji na tsane kaina amma da wasa da wasa har muka saba da shi soai

da shike Allah yayi min baiwar daukar abu dawuri sai gashi kafin hutu na ya kare na iya abubuwa fiye da yadda ake tsammani

Acikin kwanakin su ummah na faman tsara min rayuwa ta shima aljh yana shirin komawa inda ya fito kamr yadda ya fada

sau daya ta bani awaya muka gaisa da shi,nan na dada tababatrwa cewa gaskiyan ummah ne yana da kirki sosai
don anan ma bai barni ba sai da yamin nasiha yasa na masa alkwarin akan zan rike mahaifiyata duk halin da take ciki

Har ana zan koma makaranta sannan ummah ke ce min ai ogan ta ya sauya min makaranta
Amma yace idan ya shirya zai sanar da ita. .

Ni kuwa abun sai bai dame ni ba don ban kawo komai araina ba tukun..

Ummah kuwa ashe yadda zata min bayanin abubuwan da ake ciki yake damun ta,sun sa Ranar akan zasuyi maganan da anty sahura amma tayi tafiya

Duk sai ta shiga damuwa don ko gidan da aka bata ta kasa komasa sabida bata san yadda zata tun kare ni da maganganu dayawa ba

Ana saura sati biyu tafiyata france aka min visa da sauran su in a very official way ranar na fara kawo tunani kala kala sabida nima na san ma’anan abubuwa da yawa tunda ina karantawa kuma ina ganewa

sai nadan shiga rudani musamman da na lura idan nazo ma ummah da magana sai ta kaucar da ta rufe bazata rmtaba saurara na ba

Sai na damu sosai wani tunanin yasa nace zan tambaye anty sahura kawai don nasan ita kam bazata boye min komai ba

Dazu da safe naji ummah na waya da ita kan cewa ta dawo.

bayan fitar ummah da kamar awa biyu nima na fito na tara adaidaita ya kaini gidan anty sahura.

Ban taba fita nayi nisa ba ba sai ranar dan haka
Nake ta faman rakube rakube da kwatancer da ranar tayi na samo na iso

Gidan shiru ba kowa sosai yayi min kyau dama ta gaya min ta siya gidan kanta sabida naga ta bude saloon dan dai dai sai bai dame ni nasan sauran details din ba..

Mamakin da nasha shine ganin motoci har biyu manya,nace baki tayi ne ko duk wannan arzikin anty sahura ne,?

Wani bugu zuciya ta tayi, nace “ummah zata sa a kaini kasar waje ga anty sahura da uban arziki wani irin aiki ne haka suka samu?

na isa daf bakin kofar ta da har na daga waya na zan kira ta sai naji muryan ummah na tana kuka cikin tashin hankali

da har zan bude kofar cikin azama sai naji muryan namiji yana mata magana abunda ya dada shawo kaina suna na danake ji yana ambata yana cewa Dole agaya min meke faruwa..

Wani irin bugu zuciya ta yayi amma haka na daure na koma ta jikin window na sa kunne na da kyau ina kallon su da madubin glashin da aka dan bude shi kuma ina jin duk abunda suke fada

Alhj shayal ne da naty sahura da ummah a tsakiyan su duka suna tsaye,

anan na ji wasu mahaukatan bayanai wanda suka juya mini setin kwalwalwata sam sai na dena gane komai daga abunda nake jin ummah na furtawa da bakin ta.

kafata ne ya kasa dauka ta sai bari nake ina karkarwa, don bansan kokacin dana koma bakin kofar ba shiri na bude na kuso kai na ciki….

 

 

*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*

 

*OFFICIALCATTY????*[2/23, 23:15] ‪+234 802 646 5734‬: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_welcome to the world dear boy areef Allah ya raya mana kai da imaani_

_YA ZUL JALAL WAL EKRAM_

_PAGE9_

Durus nayi tsaye daga bakin kofa ina maida musu kallon firgita da suke maido min,

baki na na bari nace ummah?me nake ji haka ummah? Abun da kike fada gaskiya ne ummah kiyi min bayani..?
Jiki na rawa yake,sai na kasa controling kaina na ganin ta kasa amsani ya sa na yanke hukunci sai na sulale na fada kasa sumammiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button