HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Shiri tayi mai kyau ta kama hanyar Fara aiwatar da shawarar da ta yanke na karshe aranta..

After 6 hours misalin karfe 4.30 na yamma
Devh singania imperial college cike take dam da mutane da manyan officials don tabbatar da sakamakon fafatawar..

Ana daf za’a fara sarah ta samu damar isowa…

Duk dama Tayi duk abubuwan data ga ya dace amm Still zuciyan ta bai kwanta ba da taga babu mahfud anan din..

Anyi speech masu ilmantarwa cike da tunatar musu da su wanene a idon jama’a..

Duba da su mutane dayawa afadin Duniya musamman kaskantatu marasa galihu zasu na kallo a field din aikin su yanzu
Yasa Board members na humanatarin activist da human right suka bada gargadi mai tsauri akan su jajirce wajen kare nasu tarbiyan su kafin suce zasu karbe ma wani dan adam nashi hakkin…

A cewar su Bazai yiyu marar mutunci da kima ya yi ikirarin zai kare hakkin dan adam ba..

Darajah, tausayi,mutunci da jajircewa wajen basiran zama da al’ummah Shi ake fi bukata don kare suna da martaban organisation din Gaba daya na duniya

Don haka ba bata lokaci

Aka sanar da sakamakon gasar,
Sai dai wannan karon daban ne..sabida yarda kowa ya nuna zakowar sa ma wayannan jajirtaccun dalaibai

A cewar su kowa yayi kokari amma team din da suka basu daman shiga org sunfi kowa nuna tausayin su da kulawar su..uwa uba jajircewa da gskiya.

Sarah bukar ita ta jagiranci award din da kuma licenced din sa aka bada kowane memebr team din ta..

Murmushi mai dauke da Kuka ne ya dan kufce mata amma ta kasa bari ya sauke mata da hawaye…

Shikenan burin ta ya cika..

Mahfud is always right gashi ta sake tashi
Ta bada mahaifiyar vashika karfin gwiwa a yayin da nata ma ya dawo mara..

Taga mutane kam ba adadi,
Musamman ma Memebers din sabon office din da zata fara aiki da su na human right

Tun daga nan suka fara dada cusa mata ra’ayin kara zage damtse wajen daukar aikin ta da muhimmanci ….

Sosai abun yayi tasiri a zuciyan ta..musamman da yazo a yanayin da take ciki na wani nl rauni da rashin Sanin Me zatayi nan gaba..

 

Bayan waje ya lafa kowa ya dan watse hutun sati biyu da aka bata take so ta koma gida gaba daya nigeria tun da yamma ya rufa sai ta sa aranta Haduwar su sa mahfud anan sama sai da dare

Dama abubuwa da yawa na damun Ta game da haduwar nasu

Kunyar sa take ji yanzu, sannan zuciyan ta na matukar bugawa musamman idan ta tuno da yanzun yasan sirrin ta da duk abunda take ciki a rayuwa

Hakan ya sa ta nitsu sosai ta shiga kundun tunani

bayan ta gama shirin ta tsaf misalin karfe 10 saura na dare ta taho rai walia hotel..

Ta dan kwan kwasa door din Shiru
Hakan ya tabbatar mata da cewa yana chan saman kenan ba bata lokaci ta bishi..

Anan yaje ya bada kofa baya yana kallon bakin titi daga saman verandar benen daya zauna kamar yadda suka saba..

Durus ta tsaya tana bin kyakkwar hallitar sa da ido duk dama yasan ita din ce ta zo amma bai juyo ba tukun..

Shiru ne ya ratsa wajen na dan mintoci

Bugun zuciyar su na dada karuwa..
Gani take kamar bashi ba..

Haka shima ya dade da shiga wani yanayin da bazai iya fassara shi ba..

Har ta iso daff da shi, hasken bakin suman kansa sa da ya dada haska fatar sa dake shekin kyau ke dada dauke mata ido..

A sanyaye ta dan dafa kafadar sa wanda ya sashi lumshe idanun sa yana zugar iskan daya zo da sabuwar kaunar ta da tausayin ta aranshi…

Hero,I did it..
Tace cikin sanyin murya mai dadi da ke sarkafewa har yana cracking cikin kunnen sa

Tana jin yadda yake gode ma Allah duk dama bai fada da karfi ba..

Hannun da ta dafa shi ya kamo a hankali ya juyo ya kure ta sassanyar idanun sa..

Sun dade a haka suna kallon kallo kowa da kalar abunda yake ganowa .

Sai dai a lokacin Bayan Tsantsar so da kaunar Har da tsoro da fargaba na gauraye da nunfashin su..

A karo na biyu data yi yunkurin sauke idanun ta daga nashi,don sosai zuciyan ke ke naman rikita ta ta rasa sukuni..

Gashi ra riga ta yanke shawarar ma rayuwan ta..

Cikin sanyin jiki ta juya zata tafi bata hankara ba ya jawo ta kusa da shi…
cikin wani irin kallo mai tatarre da yanayin da ita kadai ta ke fahimtar sa yace” mata congratulations heroine..dama nasan nakii ne..u did it..

Batace komai ba har Ya tallafo fuskan ta suna dada shagala wajen mance da rudanin su
Zuciyan su ce kawai ke magana amma basu sani ba

A hannun nasa ta sakalce masa fuska Tace “no, hero we did it..
Yayi murmushi

Bai sake cewa komai ba..
Ya dan sauke ajiyan zuciya ya dan gyara makan sa positiion
Ita kanta bata san lokacin da ya zube gaban ta ba ”

Ji kawai tayi yace “sarah will you pls marry me?.

Wani difffff taji a zuciyan ta wanda ya dada shigowa da ita hankalin ta daga yanayin da suka shiga ciki”muryan ta har na rawa tace what?

Anan ya mike yana kallon ta cikin ido Yace yes”Ki zama mace na farko da zan yarda da ita na so ta na rike amanan ta ta rike nawa.
I want to spend the rest of my life with you sarah.i love you..

Tayi shiru….Ya kai mintuna 10 hakan yana jin yadda jikin ta ya dan razana duk ta tsime waje guda da alamun bata tsammani wannan babban maganan daga bakin sa ba..

Jin tayo shiru ya sa shi dada mikewa ajikin ta dai dai setin fuskan sa ya sa nashi har suna shakar numfashin juna da kowannen su take sakewa cikin bugun zuciya..

Yace sarah..pls say something, i wundt play around with this you know.

Cikin rudewa Tace” me kace?
A take ya kuma maimaitawa zaki aure ni?
Ta dago suka sake hada ido ya sake marairacewa yace pls marry me sarah..

Nan bakin ta ya shiga rawa ta rasa amsar me zata bayar ganin yanayin sa zai sa ta iya cewa “yes din.his looks is soo merismerising.

hakan Ya sa ta yi na maza ta dan ture sa ajikin ta..

Ta juya masa baya Neman nitsuwa take makanta sai dai ta kasa samun shi bata iya cewa komai ba sai kawai ta juya da niyyar za ta fuce ta barsa anan wajen..

One step kawai ta kai taji shaking and demanding voice din sa na kiran ta..
Kasa kara gaba tayi sai dai bata juyo ba.

Yace i know what you are feeling now, nasan na miki sauri but belive me i love you sarah..
Dan Allah ki aure ni

Ta rumtse idanun ta sosai ,cikin dauriya ta juya daga nesa ta jije tace”
about yestaday night, im sorry..

Yadda tayi maganan ya sa shi ya gano matsalan ta

magana ya bude baki zai sake yi ..tayi hanzari ta kauce tayi gaba abun ta

Duk da baiso hakan ba, amma sai ya sa aran sa bata so ta yanke hukunci ne a cikin rudewan ne….

Ko bacci bai iyayi ba anan ya cinye daren sa yana sakawa yana warware wa..

Ita kuwa a hargitse ta isa gida ko zama ta kasa yi sabida nauyin da zuciyan ta ke mata

Meyasa mahfud yace zai aure ta a wannan lokacin?

Ko dan yana so ya rufa min asiri ne?he’s just pityn me
Im not sure if he love me sabida bai taba fada min hakan ba sai yau.

Ya Allah, i cant take this help me out
Nasan mahfud zai iya yin komai dan na samu rayuwa mai kyau

Amma i dont think i can let him secrifice his life for me this way,nasan kawai don ya kare ni daga abunda nake tsoro yake so ya daura makan sa zama dani har abada ..

no ..no tafada cikin azaban tashin hankali da ya mantar da ita duk wani salama azuciyan ta..

Cikin haka taji an yi kykyawwar knock a bakin dakin ta…

Cikin sauri ta dan mike tare da nema makanta nitsuwan dole..

A hankali ta karasa tana tambayar waye amma ba amsa ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button