HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

_for you Ayshat yusuf ayushat,marubuciyar sanadin auren xumunci thanks for the honourable dedication(s)..tè queiro mucho????_

_29_

Sosai ta shige jikin sa sautin kukan nata na tsaga ko ina daga hanyar jinin sa ayayin da Dumin ta ke kewaye brain din sa

Anan take sarahn ta soma jin Duk wani nauyi da tashin hankalin na warware mata duka suka lumshe idanun su..

Ana shi bangaren shiru yayi Yana sauraron kalaman dake cikin kukan nata da ta zage tana yi har tana jan shessheka..

Sun dade a haka ..

Hannun sa ya sa yana dan saussauta mata abun da ta keji cikin lallamin sa da take kewa.

Har ya samu ya nitsu ya dago serious crying face din ta don su hade ido..

Ko da ya dago sai ta kasa bude nata idanun nata
Akan tafin hannun sa ta kuma daura kanta tana zubda masa hawaye kamar dan dayayi watannni aru aru bai ga mahaifiyar sa sa

Abun sai ya dada damun sa…
kenan sarah ta bukace ni a lokacin da bana nan? he can easily tell from her face expression dat she needed him many times And he was not there for her..

Shaukin tunanim haka ya sa shi awani halin jin dadi da tausayin ta matika,baki na bari yace

“sarah”

Jin muryan san ya sa ta dada sauke tears tana dada kwanciya kan hannun sa a dan birkice ya dada cewa im here sarah”ki bude idanun ki mana
Gani na dawo miki,i promise i wont leave again..
pls talk to me…dint you misss me ..heyy….ya dada dago closed eyes din nata hannun sa har na rawa

Jikin ta duk ya sake Cikin dauriya ta dago da kanta ta bude ido ta sauke masa su akan fuskan sa.

Kirjin ta sai hawa yake alaman tayi kukan ne da dukan zuciyan ta, batayi tsammanin kewar sa yayi mata muni a zuciya har hakan ba,amma meyasa bata iya nuna shi a fuska.

nan ta daure fuskan ta tam
Tana jan shesshekar kukan tana kallon sa da jajayen idanun ta..

Duk tausayin ta ya kashe masa jiki Ya sake kawo hannu a hankali Sai ya shiga goge mata tears din ta cikin kulawa

Ta kure sa da ido
A hankali ta furta

“mahfud”

Ya na bin lips din ta da kallo yace yes sarah,

Im here dont cry anymore ok?..

Cikin sanyin jiki ta gyada kai tana ce makan ta Allah yasa ba mafarkin ka kawai take yi yanzu ba..
I just cant take it anymore..i miseed you soo much hero..
I wish you were her with me many times..

Yayi murmushi ya dago ta suka hade ido tare da hana ta sauke kukan da ta sake shirin fashewa da shi..

Ya riko hannun ta yadada jaddada mata”ba mafarki bane sarah am here for you heroine,c’mon zo muje ki fada min ,meye kike ma kuka

Tayi murmushii da kyar ta bi bayan sa suka shige offishin tan tare

Nan Ya zaunar da ita yana daga tsungune agaban ta suna kallon juna

Da kyar ya lallaba ta cikin tausasan kalamai Ya shiga bata labari da hakurin rashin jinsa da zuwan sa na dan tsawon lokaci

A cewar sa ranar da suka rabu ranar mahaifin sa ya kira sa da wani babban magana..

Cewa hukuman masu bincike yamen sun samu
Kakar sa mahaifiyar baban sa wanda ta bace shekaru da dama har sun bari akan ta mutu

He have to be there for his dad a wannan lokaccin dayake bukatar karfim gwiwar na kusa da shi

Don yasan bazai masa sauki ba wajen re-uniting da mahaifiyar sa da ya dauka ta mutu tun tuni ba

Shikan sa mahfud din yana so ya ga kakar sa,
Sakamakon yanzu su biyu ne da mahaifin nasa basu da wani dangi..

Sai wayannan da suka raine sa a nigeria..

Cikin haka bayan sun dawo gida germany da kakar nasa
Bai wani dade ba kuma mahaifin nasa ya hadu da asalin kanwar mahaifiyar sa mai suna Wardah.

Its was such a huge turn for thier lives

Lokaci guda suka same karin family member har guda biyu

itama tare da su ta zauna,ita ta basu cikakken labarin cewa mahaifiyar mahfud ita tayi sanadiyar mutuwar kowa da kowa acikin gidan su,mahaifin su da mahaifiyar su just to satisfy her selfish cultistism desires
Bayan mahfud ya kufce mata.

Yanzu haka ita ma warda Allah ne yasa ta samu warkewa daga ciwon haukan data dade tana fama da shi har ba a san inda ta ke ba tsawon lokaci

Duk a Sakamakon kasa sadaukar da ita da maman mahfud tayi a kungiya tasha bakar azaba amma Allah yayi kwanan ta na gaba..

Bayan bacewar mahfud da muyuwar famlyn su sanadiyar sa Sai Allah ya kawo karshen ta itama.
Nan ne suka ji mutuwar ta kasar egypt.

Mahfud da mahaifinsa Sun jimanta sosai da lamarin don dama shi baban mahfud ya san kan labarin amma bai sani in details ba,

A kullum sai ya tambaye kansa To meye matar sa ta rasa da har zata shiga kungiyar asiri ta lalata rayuwar kowa da kowa na kusa da ita?

Duk dama ya bada kansa laifi sosai amma sai yake ganin a matsayin sa na world class scientist multi billonaire ai Ya bata tarin dukiya da jin dadin rayuwa ita da danta..

Sai dai yasan lokacin sa ne tabbas bai bata ba.

A har yau idan ya tuna yadda ta lalata rayuwar mahfud akan hakan sai yaji ya shiga damuwa sosai..

Tun yana karami take amfani da shi ita da kawayen ta suna lalata da shi as ritual offering..

Sai gashi Allah ya kare shi ya zamto da na gari ya kuma kare kansa cikin imani da tausayin na kasa dashi….all thanks to that woman hajiya bilkisu a ganin sa bazai taba mancewa da ita a duniya ba data cire dan sa daga halin da yake ciki ta kuma bashi rayuwa mai inganci fiye da yadda zai iya bashi..

Shiyasa ma idan mahfud idan yace zai zo nigeria duk da baison abun da zai raba sa da dansa a yanzu amma ko sau daya bai taba hana sa ba..

Yanzu haka kakar mahfud wanda ake cewa little granny Ita ta daura ma mahaifin sa aure da sister mahaifiyar sa anty warda suna zaman su..

Sai suka ma kansu alkawarin cewar zasu tsaya ma juna domin su sake karfafa dankon sabon zuriar da Allah ya basu..

Dalilin daya hana sa cumunicating da kowa kenan musamman ita sarahn da ya san yadda suka rabu da ita akai..

Yayi kewar ta sosai…. amma idan ya tuno da abubuwan da tace ya mata alkawari akai sai ya kasa neman ta.

Sosai kowa ya san labarin sa da ita musamman little grannyn sa..

‘Suke basa shawarwari akan lamarin yanzu haka…..”anty warda ce ta dada karfafa masa gwiwar akan ya zo nigeria, ta dage akan ya zo ya fada ma sarah kyakkyawar niyyar sa da soyayyar sa da yake mata ko zata amince..

”A bangaren sarah kuwa farin cikin ya dame ta ji take Ranar kamar a mafarkin ta yazo duk da ma mahfud din ya sha gwada mata ba hakan bane..

Lokaci guda sai taji ta daina tunanin kowa duk wani kunci da tashi fadin zuciyan ta ya kauce

Sai ta sa hankalin ta akan mahfud din da tuntuni yake bata hakurin rashin amsa kiran ta a lokacin da take bukatar sa

Theres no daubt that duk inda taje ta dawo babu wanda zai kai mata shi
Har yau bai taba gazawa ba, bata samun abun kushewa mai karfi ajikin sa..hakan ya sa wani bin take mugun jin tsoron sa awani fanninzuciyan ta

Bayan dogon magana da suka yi na kewa da an dade ba ahadu ba,ta sake tana zubo masa labarai kala kala game da aikin ta da achievement din ta

Sosai yaji dadi Yana yabata har ransa dama yasan zata iya over coming worries din ta ko da baya nan din
He become sooo haooy for her

Kamar yadda itama ta nuna farincikin ta da samun familyn sa dayayi

Tasan dama bazai yuwu ya kyaleta haka kawai ba
duk dama tasan akwai alkwarin hakan a tsakanin su

She just imagined he’will be here for her as a friend kamar yadda ya nemi alfarma a ranar da suka rabu..

Hirar su yaki karewa
Sun dade basu tare amma duk wanda ya shigo ya gansu zaiyi tunanin kullum suna magana ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button