MAKAUNIYAR KADDARA 62

*Page 62*
………Kawai jitai hawaye sun ɓalle mata babu gaira babu dalili, ta zube a farkon kujerar shiga falonta na farko ta cigaba da zirarwa batare datayi
yunƙurin sharesuba ko sau ɗaya. Har cikin ranta tanajin nadamar shigar masa ɗaki kai tsaye ba tare da jiran izini ba, sai dai ALLAH shine shaidarta batai
tunanin matarsa na cikiba, dan duk tunaninta sashenta itama ta nufa.
Zumbur ta miƙe da saka bakin gyalenta tana share hawayenta saboda jin takun tahowarsa, tai saurin nufar ƙofar itama dan bata buƙatar ma ya shigo ya
sameta. Kusan cin karo sukai yaja da baya itama taja tana ambaton, “Sorry bansan ka tahoba”.
Yanda yaji muryarta a shaƙene ya sakashi kallonta da ƙyau batare da ya amsaba. Abinda kawai zuciyarsa ta bashi akan maganarsu aunty Zakiyya ne, dan
haka ƙarasa shigowa da jawota jikinsa kawai yay ya rungume. Wani irin sabon kuka ne taji ya taho mata dan haka ta sakeshi dan duk yanda taso riƙesa ta kasa.
Ba komai ya sata gagara riƙewarba kuma sai ƙamshin turaren aunty Farah da taji jikinsa nayi. Ƙoƙarin janye jikinta tayi ba tare da shi ya ɗagotaba. Tai
saurin nufar ƙofar fita tana share hawayen da mayafinta.
Da mamaki yaɗan bita da kallo zuciyarsa na raya masa ‘Anya kuwa zancen su aunty Zakiyyar ne kawai. Dan idan bai mantaba yaga basket a ƙofar falonsa
da ƙamshin turarenta. Kafin ya shigo nan din yayi tunanin ko Khalipha ne daya shiga ɗazu ya ajiye dan lokacin da yazo a bedroom ya samesa, kamshin turarenta
kuma ya barsa akan kawai dan ya shaƙane sanda suna tare a falon.
Kansa kawai ya ɗan girgiza dayin murmushi, a kan laɓɓansa ya furta, ‘Oh mata kenan’ dan yanzu ya gama da Farah itama, koda ya rakata mota ma ya bartane
tana kukan.
Bayan Zinneerah ɗin ya bi, sai ya isketa a general falo tsaye. Tana ganin fitowarsa tai saurin ficewa baki ɗaya kuma. ‘Tofa babbar magana’ ya faɗa a
fili murmushi na suɓuce masa.
Shi ya rufe ƙofar sannan ya iso wajen motar inda Zinneerah tai tsaye bata shigaba. Fuskarsa ya daidaita da ƙyau yana isowa, batare daya kalletaba
yace, “Shiga muje”. Yay maganar yana buɗe mata baya. Ganin yanda yay kicin-kicin da fuska dama kuma ba wasan yake da itaba yasata shiga babu musu, sai da ta
zauna ya gyara mata mayafinta daya fito sannan ya zagaya ya shiga shima mazaunin driver, Farah na gefensa itama ta cika tai fam.
Har zai sama motar key sai ya fasa, Kallon Farah yay sannan ya juya ya ɗan kalli Zinneerah. “Kun gaisa da juna?”. Ya faɗa a dake.
Kusan a tare sukace masa a’a. Sai Zinneerah kuma tace, “Aunty Ina kwana”. Kamar Farah zata share saita motsa laɓɓanta ciki-ciki tace, “Lafiya”
saboda hararan da AK ya zubo mata.
Daga haka motar ta ɗauka shiru. Shima bai sake cewa komaiba yay mata key da harbata gaban gate. Ficewa yay kai tsaye dan dama maigadi ya buɗe masa
tun ganin sun fito sun shiga.
Shaiɗan ɗin daya fahimci yana kai kawo a zukatan matan nasa ya sakashi saka karatun alkur’ani a motar, a ransa yana nema musu sassauci ga ALLAH dan
shima yasan zafin kishi tunda yana dashi. Lokaci-lokaci yakan kalli Farah ya duba Zinneerah kuma ta mirror. Ganin yanda duk suka maida fuskoki gefe sai suka
bashi dariya amma ya gimtse baiyi a fili ba sai a ransa. Harko suka iso gidan nasu daga Farah har Zinneerah babu wanda yayi ko tari. Bayan ya gaisa da
maigadi ya ida shiga cikin gidan ransa fal mamakin ganin motoci da yawa a harabar gidan kamar har yanzu bikin sukeyi basu gamaba danma babbace.
Babu wacce ta motsa a cikinsu, dan haka shima sai bai tanka musuba ya buɗe motar ya fita. Ganin haka yasa suma duk suka fito kusan lokaci guda.
Kallon juna sukai, sai kuma kowacce ta ɗauke kanta. Farah tazo ta gitta Zinneerah ɗin tanabin bayan AK da yay gaba abinsa ya barsu a wajen, dan harga ALLAH
idan ya cigaba da zama yana kallonsu dariya zata iya kufce masa. Dan tsaf ya fahimci itama Zinneerah ɗin A ce a fannin kishi kenan. Koba komai kishin nata a
karo na biyu ya tabbatar masa da shima ya samu karɓuwa a gareta, miskilancine kawai ya hana ta bayyana kamar yanda ya buƙata.
Sashen Hajiya iya suka nufa kai tsaye, inda sukaci karo da tarin takalma kala-kala ajiye, da alama baƙin da suka tara waɗan nan motocin duk sune anan
ɗin.
Cikin nutsuwarsa da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga, Farah na biye dashi Zinneerah a bayanta. Da sauri Farah ta nema komawa da baya saboda cin karo
da fuskar mahaifinta da tai hakimce cikin kujera. AK yay saurin riƙo hannunta yana magana ƙasa-ƙasa. “Malama ki nutsu mana” Ya faɗa yana duban Zinneerah
datai musu kallo ɗaya ta ɗauke idonta.
Kai Farah ta ɗaga masa idanunta cike da ƙwalla. Ya nuna musu hanya alamar su wuce. Babu musu suka nufi ƙarasawa cikin falon ran Farah fal mamakin
zuwan Abban nata babu dogari ko ɗaya, sai ƙannensa biyu Matawalle da waziri, da babban amininsa da kowa ya sansu tare wanda ƙanine a wajensa shima amma
kusan tare sukai rayuwarsu, sai dai ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai da suka zo kusan tsakkiyar falon Zinneerah ma taci karo da Babanta da Abbah, harma da Maman
Sadiq.
Ita kanta tsoro ne ya kamata, dan babu shiri ta fara satar kallon mutanen dake a falon, sai ga idonta akan Hajji lanti, da Hajiyar da aka kaita gidanta
wadda ta kaita gidan aunty Zakiyya. Ai batama san lokacin da ƙafafunta dake rawa suka goceba ta durƙushe a wajen.
Hajiya iya ce tai murmushi da faɗin. “Haba Inno ya da zubewa haka ƙasa. Tashi kizo nan kinji, kema Farah taho”.
Miƙewa Zinneerah tai da ƙyar tabi bayan Farah da itama gaba ɗaya ganin Abbasu ya sata tsurewa, dan tsoronsa suke matuƙa saboda bai musu da sauƙi duk
da yana tsananin sonsu kuwa. Shi dai AK tuni yakai zaune gaban Uncle Ahmad yana gaida iyayen nasa da surukansa cike da girmamawa. Ganin haka yasa Zinneerah
da Farah suma suka shiga miƙa gaisuwa garesu duk da basusan iyayen juna ba, garama ita Zinneerah tasan su Mammah.
Bayan an gama gaishe-gaishe duk da su sun gaisa dama a tsakaninsu harma da gabatar da juna tunkan isowar su AK ɗin. Harma mai-martaba mahaifin su Farah
ya shigar da ƙorafinsa na rashin sanar masa da auren AK ɗin na biyu. haƙuri Baffah ya bashi tare da masa bayanin a yanda abun ya kasance bada shiriba. Yasha
mamaki matuƙa, amma cewar hajiya iya zaman nasu nada nasaba da auren yasa mai-martaban yin shiru bai nema ƙarin bayani akan zancen little ba da yana a falon
jikin Abbah, dan tunda ya gansu shi da mmn Sadiq kuma ya maƙale musu cike da murna dan duk duniya su yafi sani fiye da kowa, tunda ko uwarsa batai wahalar
da sukai a kansaba bayan ta haifesa.