NOVELSSANADIN LABARINA HAUSA NOVEL

SANADIN LABARINA CHAPTER 1

Cikin dare ya kasa rintsawa, tunanin irin rayuwar da yar sa take ciki ya dame shi, be san ya zai yi ya samar mata ingantacciyar rayuwa ba a halin da yake ciki, irin rayuwar da mahaifiyarta tayi mata shaawa, duk da haka ba zai zauna ya zuba ido Lami ta lalata masa rayuwar ta ba. Ya dade yana sakawa da warwarewa ya rasa mafita haka ya hakura ya kwanta har bacci yazo yayi awon gaba dashi.
Da safe ta tashi da dan kwarin jikin ta, har ta taya Saude yan aikace-aikacen gidan duk da ba masu yawa bane, bayan sun karya suna zaune yar karamar wayar Innan tayi kara alamun shigowar kira, da sauri ta shigo dakin tana fatan ya kasance wadda take jiran kiran ta ne. Ita din ce kuwa, jiya tayi mata flashing bata biyo ba, sai yanzu da safe dama tayi tunanin bata gani ba, waje ta fita zuwa dakin baffan su Saude ta turo kofar saboda bata so suje magaanar da zasuyi.
Sallama sukayi wa juna sannan suka gaisa da tambayar bayan rabuwa, sai kuma ta dora da

“Dama kiran da nayi miki akaan magaanar Hauwa’u ne, ina ganin lokaci yayi da zaki tuntubi B weaffanta da magaanar nan da mukayi kwanaki, a wannan gabar ba lallai ya hanaki ba, dan magaanar da nake miki ma yanzu haka a gidan nan ta kwana, bata da lafiya amma ko a jikin tsinanniyar matar chan, gwara kawai kizo yayi hakuri ki tafi da ita.”

Shiru tayi, alamun maganpma take itama daga dayan bangaren, tana dai ta amsawa da eh, sai kuma tace

“Hakuri zai, idan da rai da lafiya watarana da kanta zata zo har in da yake.”

“Yawwa kin gani, kizo dan Allah ko zuwa gobe ne, zan barta anan din har zuwa goben idan kin tabbatar da zuwan naki sai ki sanar min, akwai abubuwan da zan bata ta tafi dasu.”

“Toh shikenan a gaida yaran da Maigidan.”

Soke wayar tayi a zanin ta bayan sun gama, ta fito zuciyar ta fes, tana kuma fatan idan Innajon tazo ta samu tafiya da ita chan in da take aure, a kalla zata huta da wahala rayuwar ta zata sauya, ko da sanadin labarinta ne, idan mutane suka ji zasu tausaya mata.

***Wunin da tayi a gidan su Sauda ya sa ta kusan mance rayuwar da take a cikin gidan mahaifin ta, har tana dariya da hira tamkar ba ita ba, gabannin magriba aka sake kiran Innan ta amsa cike da jin dadi, bayan sun gama wayar ta dinga murna tana fatan hakan su ya cimma ruwa, da daddare bayan sun gama cin tuwo ta dauko wata yar karamar jaka, me dauke da sarkar kafa da ta wuya, jikin su dauke da tambarin zuciya da wani abu kamar ganyen bishiya, mika mata tayi tace

“Wannan shine abinda mahaifiyar ki ya bar miki Jiddah, ki adana su watarana zasu miki amfani.”

Karba tayi tana dubawa kafin tayi murmushi kawai, bata ce komai ba ta damke su a hannun ta, tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa.

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button