Labarai

Daga gida ake fara samun tarbiyya, Inji Rahama Sadau

Sau da yawa akan ce wasu jaruman Kannywood suna yin wasu abubuwan da gayya don a dinga cece-kuce akansu wanda wasu ke ganin hakan ne kasuwancinsu.

Wasu na ganin idan har ba a maganar jaruman, kasuwarsu ta mutu. Hakan ke sa wani lokacin da kura ta lafa sai su kara taya da sabuwa bayan wani dan lokaci, Tsakar Gida ta ruwaito.

Musamman masu bibiyar shafin Rahama Sadau na TikTok a ‘yan kwanakin nan za su ga yadda take wallafa hotunanta da shiga da ba ta dace ba.

Wani lokacin ta na wallafa hotunanta tare da maza yayin da ta dafa su ko kuma a yanayin da bai dace ba. Idan mutum bai kula da cewa Rahama ba ce zai iya musanta cewa ita musulma ce ko kuma bahaushiya.

Duk maganganu da kuma tareren da ake yi wa jarumar ba sa yin tasiri akanta, don ba ta fasa koma don sai dai ma ci gaba da ake samu.

Akwai lokacin da ma ta ce maganganun soshiyal midiya ba sa tasiri akanta, kuma ba sa sanya ta sauya ra’ayinta dangane da abubuwan da ta ke yi.

Kwatsam jiya sai Jarumar ta yi wata wallafa a shafinta na Twitter wanda kana gani ka san neman magana ta ke yi.

Kamar yadda ta wallafa:

“Charity Begins At Home.”

Ma’ana, Tarbiyya a gida take farawa.

Wannan karin maganar na bature ana amfaninda shi ne musamman idan an ga mutum yana yin wasu abubuwan da ba da dacewa.

Nan da nan mabiyanta suka fara caccakarta, tare da sukar iyayenta suna ganin ba a bata isashiyar tarbiyya ba.

Wani Najeeb ya ce:

“Maganar gaskiya iyayenki sun fadi anan.”

Wani Musa Ibrahim Babagerei ya ce:

“Tabbas iyayenki sun gaza ba ki tarbiyya da yadda za ki gaza girmama na gaba da ke.”

Shi kuwa H_kabir hotonta ya wallafa tare da wani namiji da ta rungume yayin da ya yi tsokaci da:

“Wannan ke ce.”

Daga LabarunHausa

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button