NOVELSSANADIN LABARINA HAUSA NOVEL

SANADIN LABARINA CHAPTER 2

“Kece Yayarmu da Anty tace zata kawo mana ke?”

Gid’a masa kai Jidda tayi, sannan tayi masa murmushi

“Zaka ci tuwo?” Tace masa tana kallon plate din dake gabanta.

“Naci tare da Muhammad, amma zan kara naki.”

“Toh muci.”

Ta tankwashe kafarta shima sai yayi yadda tayi, suka shiga cin tuwon a tare, har suka gama Anty na ta kaiwa da komowa a tsakankanin bangaren Maigidan da nata, sai da ta gama hada masa komai sannan ta nutsu ta zauna taci abincin ta watsa ruwa dan a gajiye take jin ta sosai dan ba wani zama tayi ba tunda suka shigo. Wajen takwas da arba’in Baban ya dawo, sun idar da Isha Usman yayi bacci, Antyn tace itama Jiddan taje ta kwanta, ta rakata har daki ta nuna mata duk abinda zata bukata ta kawo mata ruwa saboda dare sannan ta dauko Usman ta dawo dashi dakin tayi musu addua sannan ta kashe musu wutar dakin ta nufi bangaren Baba.

***A zaune ta samesu da Mama, ta bararraje tamkar kwananta ne ranar, ta bude masa abincin har ya soma ci yana bata labarin kasuwa, wani banzan kallo maman ta watsa mata, tayi tsaye ranta na sosuwa da abinda ake mata, dagowa yayi ya kalle ta,

“Halima, karaso mana kika ja tunga anan, kinga yayarki ko? Wai kin sha wahalar hanya shine take taimaka miki da wannan babban aikin.”

Yake tayi ta karaso ta zauna daga kubin damar sa, ta gaishe shi a ladafce ya amsa mata yana tambayar yadda ta baro su

“Ina fatan dai kafar Yaya da sauki.”

“Alhamdulillah dai toh.

“Allah ya bashi lafiya, zan yi kokari a weekend din nan naje na sake dubo sa, ina yar taki? Kin taho da ita ice ko?”

“Eh tayi bacci.”

“Ok madallah, na ganta gobe idan Allah ya kaimu.”

“Amin.” Tace sai ta mike ta shige bedroom din ta zauna a sanyaye, sama-sama take jiyo hirar su har wajejen goma na dare sannan taji tafiyar Maman. Kwanciya kawai tayi dan babu kuma bukatar ta sake komawa falon.

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button