SURBAJO Complete Hausa Novel

Gurin al-ameen sukazo,wanda yazuba uban tagumi hankalinshi atashe,burinshi Allah yasauketa Lafiya,kiranshi office doctor din tayi,tayimasa bayanin abinda ke faruwa,ba musu yasa hannu a takardar cs din gami da fatan Allah yasa ayi asa’a.
Gurin mamanta yazo yamata bayani,kuka tasa, Tana adduar Allah yafito da Aishan Lfy,
Sunanan zaune akafito da Aishan fuskarta dauke da oxygen a hanci alamun numfashinta be wadataba,zaa kaita dakin operation,mamanta kuka tasa Tana mata addu’a,duk juriya irinta soja,Al-ameen komawa yayi kamar yaro, kuka yake sosai yana mikawa Allah rokonshi,
Ankwashe sama da awa biyu,sannan likitocin suka fito,dasauri,su al-ameen suka nufesu,tamvayarsu Al-ameen yake ya aisha take,daya daga cikin likitocinne yace,she is fine,but am sorry to say,we lost the baby,
Godiya ga Allah Al-ameen yayi, daya tsallakar da Aishan siratsi,yayinda agefe daya kuma yanajin dacin mutuwar babyn,gamida tausayawa Aishan duba da ganin yadda ta dora buri akan dan.
doctor ne yakatseshi dacewa yanason ganinsu a office akwai magana,dasauri suka bi bayanshi zuwa office din,hakuri yasoma basu sannan yace Aisha tawahala da yawa wanda hakan baason faruwarsa ga me nakuda, kuma hakan yafarune sakamakon shan kwayoyin hana daukar ciki datayi amfani dasu acan baya, sanadin hakanne yajawo mahaifarta tasamu matsala inde bawani ikon Allah ba ze wuya tasake haihuwa arayuwarta,
Al-ameen gaba daya rikicewa yayi ,dajin zancan likitan,haka mamantama,hakuri doctor din yadunga basu daga karshe yabasu takardar data tabbatar da bincikennasu,
Bayan Sun baro office din doctor, dakin daaka kwantar da Aishan bayan anfito da ita daga operation din suka shiga,tana kwance Tana bacci, har yanzu akwai oxygen din a hancinta,tausayintane yakamasu duka,
suna nan zaune aka kawo musu gawar babyn Rufe cikin shawul kamar me rai, Al-ameen ne yaamsheshi yabudeshi,wasu hawayen ne suka zubomasa, ganin babyn ba inda yabaro Yusuf, maana shima dashi yake kama,mamanta yaba itama tagani tamasa addu’a,wayarsa yaciro yadunga daukar babyn hoto,sannan yaamsheshi yatafi gida domin amasa sutura,
gidan iyayensa yakai gawar suma suntausayawa Aishan gamida yimata fatan samun sauki, shikuma Allah yajikansa, bayan sun shirya yaron suka masa sallah,makabarta suka nufa domin birneshi,itakuma Momy ita Da amal,da matar kabeer asibitin suka nufa,domin dubo[truncated by WhatsApp]
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*This page is dedicated to Maman gidado,juwairiyyatu,maman Irfana, Hafsat Dahir,maman Muallim, Mrs Lukuman,mrs Shamsur.thanks for the care and support am really appreciate it*
*page 61-62*
Tunda Al-ameen yadawo da surbajo gidan kullum ba
ranar banza da Aisha bazata nemi surbajo da rigimaba. Itako bata kulata ko kadan,lokuta da yawa dakinta take shigewa tabarta Tana ‘ba’batu.
Yau asabar tun safe surbajo keta shiri,sabida Al-ameen yace, tashirya suje makarfi,murna gurin surbajo baa magana,kamin Tara tayi tuni tagama shiryawa ita Da Yusuf,oga kawai take jira yafito,dayake ba girkinta bane Aisha ce dashi,
Se karfe goma Al-ameen yafito cikin shirinshi na tafiya,lokacin surbajo duk tagama kosawa,koda yashigo dakinta, kauda kanta tayi gefe, ita ala dole tayi fushi.
Karasawa yayi kusa daita,yaruko hannunta yace,
“haba my charming princess, menayi kuma ake fushi Dani?
Turo bakinta tayi gaba, alamun shagwaba,tace,
“ay bandauka yanzu zaka fitoba,nadauka se wata safiyar,
Dariya yayi kawai,azuciyarshi yasan kishine yamotsa nanko batasan shikadai yakwanaba.amma afili cewa yayi,”am so sorry baby it will never happen again OK, yadaga mata gira daya????ya kashe ido daya.
Murmushi tayimasa, metafiya da hankalinsa,sannan,tamike tadauki jakar kayansu,shikuma yarungumo Yusuf suka nufi mota.
Tafiyace sukayi mecike daso da kaunar junansu,Al-ameen ne ke driving din dakansa.
Se wajan shabiyu na rana suka isa garin,wayyo dadi, surbajo rasa inda zatasa kanta Tayi,suma ‘yan gidansu kowa se tattalinta yakeyi,Yusuf ko, tuni ardo yaamsheshi yanamasa wasa,sosai kowa ke murna da zuwansu,kankice me gari yadauka duka surbajo tazo da mijinta harda Danta,nanfa jama’a sukaita zuwa ganinta,kowa yazo da tsarabarsa yake fita.
Al-ameen har mamakin farinjinin surbajo agurin yan garinsu yake,yaga kowa da farincikinsa yake zuwa ganinta.
Surbajo babu inda batajeba acikin garinnasu,tagaida kowa kuma tamusu abin Alheri.
Shide Al-ameen behanataba,yana zaune tare da ardo da Yusuf,Dan ardo hana surbajo tafiya yawon gidajen yayi da Yusuf din,wannan Abu da ardo yayi,yafaranta ran Al-ameen sosai.
Se magaruba suka baro garin,dan fafur yahanata kwana, ba irin magiyar dabatayiba amma yaki,ardo ma kuma yagoyamasa baya,shiyasa suka tafi.
Karfe takwas na dare suka shiga gida,dayake girkin surbajone sallama kawai yaje yayiwa Aisha yadawo bangaren surbajon, adaren, tamusu girkin abinda zasuci, Dan ta tsani siyan abinci awaje.
***********
Bayan shekara daya,
Rayuwa taci gaba da tafiya, inda abubuwa da dama suka faru,aciki harda auran munawwara inda ta auri wani custom suna zaune a Legos.
Bangaren Al-ameen ko, sauyin gurin ayki yasamu gamida Karin girma ,yanzu andawo dashi Abuja da Ayki,
Da surbajo yatafi, Inda yanemar mata university anan abujan, tafara zuwa, Tana karantar low. Tuni ta yaye yusuf sabida yaron akwai girman jiki, ga wayo sosai bame zaton shekararsa daya Da wata biyar sabida girmansa,a kaduna tabaroshi, gurin iyayen Al-ameen din,tundaga yaye suka rikeshi.
sede duk sanda al-ameen yasamu dama,yazo kaduna gurin Aisha, yay sati biyu Yakoma Abuja,
Bangaren soyayyarshi da surbajo se abinda yayi gaba, kullum burin kowa yafaranta ran Dan uwansa. Surbajo takara gogewa, yanzu tayi kiba, ga wani haske datayi, bame cewa tahaihu har so biyu.
wani zuwa kaduna da Al-ameen yayine yatarar da Aisha kwance afalo ba Lafiya duk tayi amai tabata guri,arude yadauketa yamata wanka yashiryata suka nufi asibiti,
Bayan aune aune daaka matane likita yamusu albishir dacewa Tana da ciki natsawon wata uku,murnar dasukayi fadinta bata lokacine,koda suka dawo gida tattalinta yakeyi kamar kwai, su Aisha abunnema yasamu,se kara narkemasa takeyi,shikuma yana biyemata.sati biyu yazo da niyar yi,amma seda yayi sati hudu,dan kulawa da Aishan, sabida cikin me laulayine sosai,
Koda yafadawa surbajo,murna tayimusu gamida fatan Allah yasauketa Lfy, itace ma tabashi shawarar yakara kwanaki,dan yakula musu da baby da kyau,
Ranar daze tafine, yaje gidansu Aishan yadauko mata kanwarta danta tayata Zama,su Aisha harda kuka,dan taji dadin zaman dayayi da ita,rarrashinta yayi yace takwantar da hankalinta baze dadeba ze dawo,dakyar tasakeshi yatafi.
Tarba ta musamman yasamu agurin surbajo Dan har airport taje tarboshi,tareda bodyguard dinsa.
Suna zuwa gida,taimakamasa tayi, yayi wanka yashirya, suka dawo dinning yaci abinci.kara yimasa Allah yasanya alkhai’ri tayi game da samun cikin Aisha,sannan tace yakiramata ita tamata yajiki.bamusu yaciro wayarshi yakira Aishan bayan sungaisa yace ga surbajo zata gaisheta, da kamar tace a’a sekuma ta tuna yadace taba surbajo amsa,gameda gorin data Mara. Tace to abata sugaisan, kamar abun arziki, surbajo tagaisheta gami da mata fatan Allah yasauketa Lfy, ay kamar jira take,tace, “ameen idan takai zuci, kinki Allah yaso,da kindauka kekadaice me rabon haihuwa?tonima gashi nasamu,kuma Wlh ko kece shugabar matsafa na duniya, sede kiyi kibari wannan cikin yafi karfinki, yargidan masu tallan nono.
Dasauri surbajo tamikawa Al-ameen wayarshi,tana danasanin cewa akirata[truncated by WhatsApp]
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????