HAUSA NOVELSURBAJO Complete Hausa Novel

SURBAJO Complete Hausa Novel

Zahra Muhammad mahmud

*this page is dedicated to Alhaji Auwalu Bauchi. Nagode da irin dawainiyar yada littafina dakakeyi a facebook dasauran guraren daban saniba,Allah ya albarkaci rayuwarka data zuriarka baki daya*

*page 65-66*

Su mommy sun iso asibitin Lfy, sede suma suna ganin Aisha sunyi matukar tausayamata,har kuka sukayi sabida tausayinta.

Surbajo Al-ameen ne yakirata yasanar daita abinda yafaru,Allah sarki baiwar Allah kuka tadunga yi kamar ita abun Yasama, rokonshi tashiga yi akan zatasa driver yakawota tadubata,kin amincewa yayi yace tabari zezo sutaho tare,haka dole tahakura Dan tasanshi kaifi dayane,

Kwanan Aisha daya a asibitin tafarka, abinda tahaifa tafara tambaya, duk cikinsu anrasa mebata ansa se al-ameen,shima daurewa yayi yamata bayanin,kuka tasamusu tana fadin “Wlh bazan yardaba wato takashemin shi hankalinta yakwanta,inna yarda Allah yatsinemin dole seta biyani yarona. Hakade taita zage zage dasauri suka Kira likita yasake yimata allurar bacci.
Al-ameen ko ranshi yabaci dajin zantukannata,wato ita har yanzu bazatayi hklb kenan.

satinta daya aka sallameta,koda tadawo gida kullum zancanta surbajo takashe mata da ita bazata yardaba,kawayenta se Kara zugata sukeyi akan lalle surbajo ce takashemata yaro.

Kwanan Aisha goma da haihuwa al-ameen yakawo surbajo ta dubata,

Tana ganin surbajo wani ihu tayi tayo kanta,dasauri al-ameen yariketa, kokarin kwacewa take amma takasa sabida jikinta ba kwari masifa ce kawai irinta Aisha,
magana yafara dacewa,
“aisha yakamata ace yanzu kingirma Don Allah yaushe zaki Dena batamin raine?sama da shekara goma kullum da bacin ranki nake kwana menayimiki haka Aisha kike burin kasheni? why Aisha?dama Ashe bada gaske kike sonaba kin aurenine domin kikasheni da bakinciki? Ina son dakike ikrarin kinayimin? Seyaushene zanfara jin dadin zama dake iye Aisha ninefa Aminu amma nikikewa tozarci irin haka ngd,
yana gama fadamata haka yasaketa yabarsu agurin yawuce dakinshi, jikin Aisha gaba daya yagama mutuwa dajin kalaman al-ameen,kuka tarushe dashi agurin tarasa meyadace Tayi, Tunda suke da al-ameen yaune yamata kalaman dasuka dagula mata lissafi Amman batajin zata yafewa surbajo abinda tamata,surbajoce ta katsemata tunani dacewa, “aunty Don Allah kiyi hkr inna batamikine Allah yahuci zuciyarki, Allah kuma yabaki Lfy yajikan babyn yasa masu cetonmune, ko kulata
Aisha batayiba bare tayi tunanin zata amsa,surbajo mikewa tayi tafice daga dakin.

dakinsa tanufa tasameshi yana zuba kaya a wadrop,tayashi tayi suka gama zuba kayan, Lura datayi ranshi abace yake yasa tashiga kwantar mishi da hankali harseda yasamu natsuwa, daganan aka fada rayuwa medadi.

Da daddare daukar surbajo yayi suka tafi gidan iyayensa,
Sunyi murna sosai da ganinta, suma tamusu gaisuwar rashin dasukayi, dazasu wucene mommy tace suwuce da Yusuf Dan tasan sunfisu bukatarshi akusa dasu kawaici kawai suke musu, wayyo dadi,surbajo jitayi kamar ta goya mommy, godiya sukamusu sosai daganan suka musu sallama, Dan gobe surbajo zata koma Abuja sabida Tana da exam,

daga gidansu gidan Yan uwan Maman surbajo sukaje,
Sunyi murna daganinta sosai, sunjima agidan sannan sukayo gida .

washe gari da safe al-ameen yahadasu da driver yamaidasu Abuja,sabida shi ba yanzu ze tahoba se jikin aisha yakara sauki,duk da mamantace ke zaune da ita, se aminan ta dakullum suke gidan.

sannu ahankali Aisha kesamun sauki harta warke gaba daya,lokacin tuni al-ameen yakoma Abuja gurin aykinshi.komawarshi bajimawa akasa Yusuf amakaranta, sabida Yusuf inyafado wata maganar zaka dauka bashine yayitaba.

*jama’a albishirinku*

aminan aisha de lokaci yayi inda kowaccensu tasamu mijin aure, kuma duka mazajen a kaduna suke sede anguwace kowa datashi.

Se anriga yin bikin zuly da sati biyu zaayi na Ruky,wayyo rawarkai, ay Aisha ce tadauki nauyin yimusu setin kujeru dukansu, abun yamusu dadi sosai.yayinda azuciyarsu ko mugun fata suke mata.
Anfara hidimar biki su aisha bazama sune can sune nan,
ranar asabar aka daura auran zuly da mijinta Musa,sosai akayi bidiri abikin inda aka Kai Amarya gidanta dake makarfi road can hayin rigasa, layin tattali blocks, semuce Allah yabada zaman Lfy.

haka lokacin bikin Ruky ma yazo aka sha biki inda ta auri wani mesuna baballe itama ankaita gidan mijinta dake unguwar dosa layin commissiona road.

muje zuw[truncated by WhatsApp]
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????

Zahra Muhammad mahmud

*this page is dedicated to Aisha Usman,baidau,maman Huzaifa,jidda,baby,mrs smart,nafi Muhd Katsina,eshat Mustapha,fatima Muhd kaduna,raihanat,ummu basma,hajara Abdullahi, Fiddah,maman Mashkur thanks you all,I salute you all*????

*page 63-64*

Yanzu Aisha laulayi yayi sauki,bakamar da ba,iskanci kuma da takama da cikin se abunda yayi gaba,musamman datayi scanning,akace mata namiji zata haifa, karkuso kuga rawar kafa, kawayenta kullum suna gidanta wai sunje jinyarta,abun namata dadi,yadda kawayennata ke bata kulawa,

Al-ameen tuni yagama siyayyar kayan baby,haihuwar kawai suke Jira,yanzu duk weekend a kaduna yakeyi sabida cikin Aisha daya tsufa,

Surbajo tamaida hankalinta kan karatunta, Sam bata wasa dashi ko kadan,shiyasa al-ameen kekara sonta,dan har cikin ranshi yana takaicin rashin karatun Aisha,Wanda ita ko ko ajikinta.

Wata safiyace aisha ta tashi da ciwon nakuda, Allah yataimaka lokacin Al-ameen yazo weekend,
Ihu tadunga yimasa kamar zatayi hauka, duk yabi yarude,agigice yayi asibiti da ita,suna zuwa aka shiga da ita dakin labour.

waya yaciro yakira mamanta, bajimawa tazo asibitin,shuru har yanzu Aisha bata haihuba,se addu’a sukeyi,zuwacan likitan ta fito dasauri,gurinta suka nufa suna tambayarta ya Aishan take,zufa tashare sannan tace musu bleeding takeyi ,dan haka Tana bukatar jini da gaggawa, inba hakaba anything can be happen,
Tahaihune? suka tambayeta arude, as tabasu amsa kuyi sauri kukawo Jinin ko kuma ku biya akwai nasiyarwa,
bamason nasiyarwa muje adebi nawa am group o±,
Donor ne ni,
Bamusu suka nufi lab dashi, bayan sun aunashi suka tabbatar bawata matsala, sannan suka dibi jinin,akaje akasawa Aisha,

Allah gamu gareka,aishafa nacikin mawuyacin hali, duk me imani yaganta ze tausaya ,likitoci sunyi iya yinsu wajen ganin tahaihu da kanta,amma ina dole se ammata cs.

Gurin al-ameen sukazo,wanda yazuba uban tagumi hankalinshi atashe,burinshi Allah yasauketa Lafiya,kiranshi office doctor din tayi,tayimasa bayanin abinda ke faruwa,ba musu yasa hannu a takardar cs din gami da fatan Allah yasa ayi asa’a.

Gurin mamanta yazo yamata bayani,kuka tasa, Tana adduar Allah yafito da Aishan Lfy,

Sunanan zaune akafito da Aishan fuskarta dauke da oxygen a hanci alamun numfashinta be wadataba,zaa kaita dakin operation,mamanta kuka tasa Tana mata addu’a,duk juriya irinta soja,Al-ameen komawa yayi kamar yaro, kuka yake sosai yana mikawa Allah rokonshi,

Ankwashe sama da awa biyu,sannan likitocin suka fito,dasauri,su al-ameen suka nufesu,tamvayarsu Al-ameen yake ya aisha take,daya daga cikin likitocinne yace,she is fine,but am sorry to say,we lost the baby,
Godiya ga Allah Al-ameen yayi, daya tsallakar da Aishan siratsi,yayinda agefe daya kuma yanajin dacin mutuwar babyn,gamida tausayawa Aishan duba da ganin yadda ta dora buri akan dan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button