SURBAJO Complete Hausa Novel

doctor ne yakatseshi dacewa yanason ganinsu a office akwai magana,dasauri suka bi bayanshi zuwa office din,hakuri yasoma basu sannan yace Aisha tawahala da yawa wanda hakan baason faruwarsa ga me nakuda, kuma hakan yafarune sakamakon shan kwayoyin hana daukar ciki datayi amfani dasu acan baya, sanadin hakanne yajawo mahaifarta tasamu matsala inde bawani ikon Allah ba ze wuya tasake haihuwa arayuwarta,
Al-ameen gaba daya rikicewa yayi ,dajin zancan likitan,haka mamantama,hakuri doctor din yadunga basu daga karshe yabasu takardar data tabbatar da bincikennasu,
Bayan Sun baro office din doctor, dakin daaka kwantar da Aishan bayan anfito da ita daga operation din suka shiga,tana kwance Tana bacci, har yanzu akwai oxygen din a hancinta,tausayintane yakamasu duka,
suna nan zaune aka kawo musu gawar babyn Rufe cikin shawul kamar me rai, Al-ameen ne yaamsheshi yabudeshi,wasu hawayen ne suka zubomasa, ganin babyn ba inda yabaro Yusuf, maana shima dashi yake kama,mamanta yaba itama tagani tamasa addu’a,wayarsa yaciro yadunga daukar babyn hoto,sannan yaamsheshi yatafi gida domin amasa sutura,
gidan iyayensa yakai gawar suma suntausayawa Aishan gamida yimata fatan samun sauki, shikuma Allah yajikansa, bayan sun shirya yaron suka masa sallah,makabarta suka nufa domin birneshi,itakuma Momy ita Da amal,da matar kabeer asibitin suka nufa,domin dubo Aishan.
Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*this page is dedicated to Alhaji Auwalu Bauchi. Nagode da irin dawainiyar yada littafina dakakeyi a facebook dasauran guraren daban saniba,Allah ya albarkaci rayuwarka data zuriarka baki daya*
*page 65-66*
Su mommy sun iso asibitin Lfy, sede suma suna ganin Aisha sunyi matukar tausayamata,har kuka sukayi sabida tausayinta.
Surbajo Al-ameen ne yakirata yasanar daita abinda yafaru,Allah sarki baiwar Allah kuka tadunga yi kamar ita abun Yasama, rokonshi tashiga yi akan zatasa driver yakawota tadubata,kin amincewa yayi yace tabari zezo sutaho tare,haka dole tahakura Dan tasanshi kaifi dayane,
Kwanan Aisha daya a asibitin tafarka, abinda tahaifa tafara tambaya, duk cikinsu anrasa mebata ansa se al-ameen,shima daurewa yayi yamata bayanin,kuka tasamusu tana fadin “Wlh bazan yardaba wato takashemin shi hankalinta yakwanta,inna yarda Allah yatsinemin dole seta biyani yarona. Hakade taita zage zage dasauri suka Kira likita yasake yimata allurar bacci.
Al-ameen ko ranshi yabaci dajin zantukannata,wato ita har yanzu bazatayi hklb kenan.
satinta daya aka sallameta,koda tadawo gida kullum zancanta surbajo takashe mata da ita bazata yardaba,kawayenta se Kara zugata sukeyi akan lalle surbajo ce takashemata yaro.
Kwanan Aisha goma da haihuwa al-ameen yakawo surbajo ta dubata,
Tana ganin surbajo wani ihu tayi tayo kanta,dasauri al-ameen yariketa, kokarin kwacewa take amma takasa sabida jikinta ba kwari masifa ce kawai irinta Aisha,
magana yafara dacewa,
“aisha yakamata ace yanzu kingirma Don Allah yaushe zaki Dena batamin raine?sama da shekara goma kullum da bacin ranki nake kwana menayimiki haka Aisha kike burin kasheni? why Aisha?dama Ashe bada gaske kike sonaba kin aurenine domin kikasheni da bakinciki? Ina son dakike ikrarin kinayimin? Seyaushene zanfara jin dadin zama dake iye Aisha ninefa Aminu amma nikikewa tozarci irin haka ngd,
yana gama fadamata haka yasaketa yabarsu agurin yawuce dakinshi, jikin Aisha gaba daya yagama mutuwa dajin kalaman al-ameen,kuka tarushe dashi agurin tarasa meyadace Tayi, Tunda suke da al-ameen yaune yamata kalaman dasuka dagula mata lissafi Amman batajin zata yafewa surbajo abinda tamata,surbajoce ta katsemata tunani dacewa, “aunty Don Allah kiyi hkr inna batamikine Allah yahuci zuciyarki, Allah kuma yabaki Lfy yajikan babyn yasa masu cetonmune, ko kulata
Aisha batayiba bare tayi tunanin zata amsa,surbajo mikewa tayi tafice daga dakin.
dakinsa tanufa tasameshi yana zuba kaya a wadrop,tayashi tayi suka gama zuba kayan, Lura datayi ranshi abace yake yasa tashiga kwantar mishi da hankali harseda yasamu natsuwa, daganan aka fada rayuwa medadi.
Da daddare daukar surbajo yayi suka tafi gidan iyayensa,
Sunyi murna sosai da ganinta, suma tamusu gaisuwar rashin dasukayi, dazasu wucene mommy tace suwuce da Yusuf Dan tasan sunfisu bukatarshi akusa dasu kawaici kawai suke musu, wayyo dadi,surbajo jitayi kamar ta goya mommy, godiya sukamusu sosai daganan suka musu sallama, Dan gobe surbajo zata koma Abuja sabida Tana da exam,
daga gidansu gidan Yan uwan Maman surbajo sukaje,
Sunyi murna daganinta sosai, sunjima agidan sannan sukayo gida .
washe gari da safe al-ameen yahadasu da driver yamaidasu Abuja,sabida shi ba yanzu ze tahoba se jikin aisha yakara sauki,duk da mamantace ke zaune da ita, se aminan ta dakullum suke gidan.
sannu ahankali Aisha kesamun sauki harta warke gaba daya,lokacin tuni al-ameen yakoma Abuja gurin aykinshi.komawarshi bajimawa akasa Yusuf amakaranta, sabida Yusuf inyafado wata maganar zaka dauka bashine yayitaba.
*jama’a albishirinku*
aminan aisha de lokaci yayi inda kowaccensu tasamu mijin aure, kuma duka mazajen a kaduna suke sede anguwace kowa datashi.
Se anriga yin bikin zuly da sati biyu zaayi na Ruky,wayyo rawarkai, ay Aisha ce tadauki nauyin yimusu setin kujeru dukansu, abun yamusu dadi sosai.yayinda azuciyarsu ko mugun fata suke mata.
Anfara hidimar biki su aisha bazama sune can sune nan,
ranar asabar aka daura auran zuly da mijinta Musa,sosai akayi bidiri abikin inda aka Kai Amarya gidanta dake makarfi road can hayin rigasa, layin tattali blocks, semuce Allah yabada zaman Lfy.
haka lokacin bikin Ruky ma yazo aka sha biki inda ta auri wani mesuna baballe itama ankaita gidan mijinta dake unguwar dosa layin commissiona road.
muje zuwa riders
Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*this page is dedicated to my sweet Aunty,hajiya meelmoh, owner of meelmoh magazine.Allah yatsareki aduk inda kika shiga*
*page 67-68*
Al-ameen ne zaune, yayinda surbajo Tay matashin kai da cinyarsa, Suna hira.
Al-ameen ne Yace,
“madam yaushe zaki bani new baby ne?yafadi yana shafo cikinta,dariya tayi medaukar hankali,hannu tasa Tana wasa da dimples dinshi,sannan tace,
“lalle ma my dear nan,nafahimceka sokake inyi saurin tsufa, inbanda abinka ay yanzu hutawa yadace inyi Dan haihuwa barkatai seyajawo natashi ayki dawuri,cuno baki tayi sannan tacigaba,dan haka ni kadena wannan maganar yanzu kabari sena gama karatu.
Al-ameen mamakine yacikashi naganin zallar kuruciyar surbajo, wacce yafahimci dole seya setamata hankali,magana yafara da cewa,
“baby yakike magana kamar bakida ilimi,menene aybu inkin haihu yanzu,karki sawa kanki akida tawasu mutane marasa tunani,tonide soyayyar dazaki nunamin itace kihaifamin yara,taya yaro daya kawai kice kinaso ki huta,hutun jaki da kaya ko?.itade Tunda yasoma mgn kallonshi take Tana murmushi, Dan dama tafadine taji mezece.
Kallonta yayi yaga Tana dariya,dakatar da maganar yayi yana dubanta,rungumoshi tayi Tana dariya tace,my Legend kenan maida wukar surbajo tsokanarka takeyi,haifa maka yara inde Allah yabamu yanzu nafara so no need to be worry, rumgumeta shima yanada dariya yace,