SURBAJO Complete Hausa Novel

Dawowa d’akinta yayi d’auke da takardar, akwance yasameta Tana ihun hannunta daya karye, tsawa yadakamata sannan yace,
“Dagani har Surbajo baki cuci kowaba Illa kanki,kuma nide ban yafemiki ba Wanda nasan itama bazata yafemikiba, yarinyar nan bata tare miki komaiba Amman kika d’auki karan tsana kika d’ora mata,bakiji tausayin wahalar datasha da cikin ba kika iya zuwa aka kashe abinda zata haifa,to Alhmdllh Allah yasaka mata ta hanyar data dace, ga result d’inkinan Wanda likitan daya amshi haihuwarki yabayar, nacewa keda haihuwa se wani ikon Allah sakamakon magunguna nahana d’aukar ciki dakike sha”, wurga mata takaddar yayi,sannan yad’ora da cewa “kinma kanki A’isha.kuma kitattara naki ya naki kibarmin gida nasakeki saki d’aya”
,wata gigitacciyar ‘K’ara tasaki bayan yagama maganar.
Dak’yar tajawo jiki tazo gabanshi tana kuka tana rok’onshi ya gafarta mata,hankad’eta yayi yafice daga d’akin kai tsaye harabar gidan yanufa,umarni yabawa megadi dacewa yatabbatar nanda 30minutes Aisha tabar masa gida kuma inta fita yakullemasa gidan, driver yasa yakaishi gidan iyayensa.
Maman Yusuf
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS(P.M.L.W)*
*page 71-72*
Koda ya’isa gidansu still ranshi abace yake dak’yar ya iya yimusu sallama,
Hankalinsu tashi yayi dasuka gansa ayanayin dabasu saba ganinsaba, tambayarsa suke meyafaru dashi,seda yad’an natsu sannan yafad’amusu abinda yafaru, Dukansu bawanda be firgita dajin labarinba, Daga ‘karshe fatan Allah yasa hakan shi yafi alkha’iri suka masa, inda Mahaifinsa ya’kara dacewa, “Ka rage saurin yanke hukunci cikin fushi”,amsawa yayi da insha Allahu yadena.
Aisha dak’yar tamik’e tafara neman mayafinta kuka take kamar ranta zefita,ga hannunta dayake mata azabar ciwo ahaka tadaure ta hada iya abinda zata iya d’auka tabarmasa gidansa cike da d’umbin danasani, tabiyewa k’awaye gashi sunkaita sun barota,rasa ina Zata sa kanta tayi,
Driving take amma ko gabanta bata gani Allah ne kawai yakaita gidansu Lfy, Tanayin parking da gudu tashige cikin gidan tana kuka me tsuma zuciya kan mamanta tafad’a, wacce ke zaune Tana yankan alaiyahu dasauri taajiye wuk’ar Tana tambayarta meke faruwa?,
Cikin kuka Aisha ke fad’in,”wayyo Allahna Inna nacuci kaina nabiyewa sharrin k’awaye gashi yau sunkaini sunbaro,yau mijina yasakeni had’e da sakamakon bazan sake haihuwaba arayuwata”,wani kukan tasake rushewa dashi, Mamanta jikintane yakama rawa kamar mazari jin zancan Al-ameen yasaki Aisha dak’yar ta’iya tambayar Aishan metayimasa?, nanfa Aisha takwashe komai tasanar da Inna, wani gigitaccen Mari Inna tawankawa Aisha har so biyu tuni Aisha tasoma ganin taurari sabida Marine bana wasaba, cikin ‘bacin rai Inna tace,
“Aisha gaskiyar Aminune dayacemiki kanki kika cuta to wlh kannakin ko kika yiwa, Aisha yaushe rashin imaninki yakai haka ki iya kashewa mace y’a tun aciki keko mekike nema wandau Aminu yagaza gurin yimiki, wlh kinyi rashin mijin da keda samun kamarsa har abada azamaninnan, natayaki murna seki zo mujeru agidan arasa gane wacece uwar acikinmu, zancan bazaki haihuba kuma sakayyace Allah yama wacce kika zalinta”.
Maganganun Inna sunshigi Aisha sosai take numfashinta yafara barazanar d’aukewa, kamin Inna tayi wani yunk’uri tuni Aisha tazube ak’asa sumammiya,
Agigice Inna tayi kanta tana kiran sunanta Amman ina ko numfashi batayi, ruwa tad’ebo ta yayyafamata shima abanza, arud’e Inna tayi k’ofar gida neman taimakon jama’a,nan da nan aka shigo akad’auki Aisha zuwa Asibiti.
Al-ameen kwanansa d’aya yajuya Abuja,
Cike da farinciki Surbajo ta tarbeshi domin tayi murna da dawowar tashi,abinci masu rai da Lafiya ta gabatar masa bayan yayi wanka yashirya sannan suka dawo dinning yaci abincin,
Falo suka dawo suka zauna Surbajo na mak’ale dashi, yayinda Yusuf yana makaranta dan ansashi a makarantar,
Tambayarshi take,”dear meyasa kadawo da wuri”? murmushi kawai yamata dan bayason yafad’amata abinda ze d’agamata hankali,
Daminshi tayi da tambayar, “dear nagama kasauya kamar baka cikin walwala meke faruwane? don Allah kasanar dani”,
Ganin tashiga damuwane yasa,yakwashe duk abinda yafaru tasanar da ita,afirgice tamik’e daga jikinshi tana maimaita kalmar,” Itace tayi sanadin mutuwar Babyna ?me muka yi mata da zafi har haka dazata za’bi rabani da abinda nafiso arayuwata? menayimata!!!?
Durkushewa tayi Tana kuka Al-ameen behanataba yabarta tayi sabida zatafi samun sauk’i a zuciyarta,
Seda yaga tayi dayawa sannan yakamota yana rarrashinta ahankali hartadena kukan,seda take natsu sosai sannan tace,
“Dear sakin dakayiwa Aisha bedaceba sabida cuta de tariga data gama cutar damu babu wani abu dazamuyi mata murama, nide anawa ganin kayi hkr kadawo da ita dakinta zefi dan wlh sakinta bashine mafitaba kuma ni nayafe mata sauran tsakaninta da ran data kashene ranar gobe kiyama kuma kaima inaso kayafemata Don…… Marin daya wanketa dashine yasa takasa karasa abinda zata fada, hankad’eta yayi tafad’i ak’asa bebi takaiba yanunata da yatsa sannan yace cikin kakkausar murya,
“how dare you Surbajo?she killed my princess and also she destroyed my happiness, and she make you suffer alot,then for all this, now you are looking into my eyes without fair asking me to forgive her how dare you? That means my happiness it’s doesn’t matter to you thanks you so much”,
yana gama fadin haka yajuya yafice daga gidanma gaba d’aya,Surbajo kuka ta rushe dashi anan gurin daya yardar da ita, Sam ita bataga aybin maganartaba dahar zeyi fushi da ita har haka, kukanta taci gaba dayi.
Maman Yusuf
????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????
Zahra Muhammad Mahmud
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L*
Afuwan nayi mistake din number ne
*page 75-56*
Yana isa gida a kitchen yasameta tana girki, rungumeta yaje yayi ta baya dasauri Surbajo tajuyo dan ganin waye yarungumeta, ganin Al-ameen ne yasa tasaki ajiyar zuciya.
Juyowa tayi Itama tarungumeshi tana fad’in,
“i know my dear bazaka iya fushi daniba don Allah kayafemin Inna b’atamakane bazan sakeba”,
D’ora hannunshi yayi akan bakinta alamar tayi shuru sannan yak’ara sassauta muryarshi yace,
“Baki b’atamin ba baby kawai nayi fushine sabida ina ganin kamar baki damu dani bane Shiyasa amman yanzu komai yawuce kiyi hk’r kinji my lollipop,”yafad’i yana kaimata kiss abaki,janyewa tayi ajikinshi sannan tace,
“To yazancan dawo da Aisha d’akinta da nayi maka d’azu,?kaamince ko har yanzu baka yardaba,?”
Kunnenta yaja da hannunsa yana murmushi yace,
“Ya na iya da gimbiyata tunda kince ta dawo naamince amman ba yanzuba gaskiya”.
“Se yaushe”,Surbajo ta tambaya.
“Se nasa ajiya anan”yashafo cikinta yana dariya,ture hannunshi tayi zatayi magana yadakatar da ita dacewa,
“Wlh this is my final decision Inkuma baki aminceba to nafasa dawo da itan”,dasauri Surbajo tabashi amsa da cewa,
“Aradu na amince Kado,”dariya gaba daya suka sa sabida tuno da irin maganarta tada da takeyi.