HAUSA NOVELSURBAJO Complete Hausa Novel

SURBAJO Complete Hausa Novel

Rayuwa suka cigaba dayi cike da so da k’aunar juna, kullum Surbajo na k’ara rok’onshi yadawo da Aisha shiko dagewa yayi akan se Surbajo tayi ciki sannan ze dawo da Aisha,hakanne yasa Surbajo tafara tsayuwar dare tana rok’on Allah yabata ciki dan Aisha tadawo d’akinta.

Bangaren Aisha kuwa ciwon zuciyar tane yatashi kuma tashi me tsanani, dan Inna har ta cire ranta akan Aisha dan kowa yaganta ze d’auka inyafita kamin yadawo ze tarar ta mutu,batasan waye akantaba ko numfashi ta oxygen take shak’arsa abun gwanin ban tausayi,Inna da sauran k’annanta sede susata agaba suna kuka,likitocin dake dubata sunayin iya bakin k’ok’arinsu dansuma suna tausaya mata.

Ajidad’i yau tashirya kiran Al-ameen dan haka bata batayi tunanin komai ba takirashi,seda takira yafi so biyar ba’a d’aukaba can taji yad’aga ,tace,

“Haba namijin duniya ba fad’a me yakawo gaba kuma,”tunda ta fara magana yaganeta ranshi ne yay masifar baci da kiran data mishi sabida ta tuno mishi abinda yafaru tsakaninsu katseta yayi da cewa,

“Banyi mamakin kiran da kikamin ba sabida nasan wacece ke,kuma dama duk inda karya take ba’a rabata da bin maza, nayi danasanin had’uwa dake Jameela,ke shaid’aniyace me kai jama’a wuta, daga yau se yau inkika k’ara kirana sena miki abinda baki zataba stupid kawai, be jira amsartaba yakashe wayar yana huci kamar tana gabanshi.

Itako Ajidad’i bata d’auki zancan nashi serious ba kullum seta kirashi baya dauka kuma bata denaba,dataje gurin bokanta yamishi asiri hkr yabata yace baze iya ba sabida Al-ameen akwai tsari ajikinshi.
Duk da haka bata hkr ba sabida tasha alwashin Seta lashi zumarsa,ci gaba tayi da kiranshi shi kuma yak’i yasata a blacklist ne acewarsa ita bata isa tasashi yin hakanba tai ta kiranshi harta mutu.

Allah maji rok’on bawa.

Yau Surbajo da zazzab’i ta tashi ga kasala,danko Yusuf takasa yimasa wanka Abbanshine yashiryashi driver yatafi kaishi makaranta,sannan yadawo kanta,
Wanka yamata Itama yashiryata sannan yabata abinci taci tana gama ci ama’i yataso mata da gudu tayi cikin bayi tafara kwara aman,binta yayi bayin yataimaka mata ta gyara jikinta sannan ya wanke inda ta b’ata suka fito, be jira komai ba yad’auketa suka nufi Asibiti,awon farko likita yatabbatar musu da tana da ciki har na wata biyu, ga mamakin Al-ameen Surbajo tafishi murnar samun Cikin har sujudul shukur tayi, murna sukayi bata wasa ba babu kamarma Surbajo sabida burinta ze cika nason Al-ameen yadawo da Aisha.

Suna isa gida tasamishi daru akan wlh seyaje Kaduna aranar yadawo da Aisha in ba hakaba wlh seta cire cikin,hankalin Al-ameen inyayi dubu yatashi rasa yazeyi da ita yayi dan yasan ta sarai bata fad’in abinda tasan bazata aykataba, bashida zab’in daya wuce yabi umarninta,shiryawa yayi driver d’inshi da excode d’inshi ne suka masa rakiya yatafi Kaduna.wanda hakan ba k/aramin dad/i yayiwa Surbajo ba.

Se sha daya na rana suka isa Kaduna.

Gidan iyayensa yafara zuwa yasanar dasu abinda yakawo shi sunyi murna sosai dajin zancan fatan alkhairi sukayi masa gamida yimasa nasiha akan yayi adalci atsakanin Matanshi godiya yamusu, mommy tafara tsokanarshi dacewa,

“Allah ya soka bata gama iddah ba data gama sede kashiga layin zawarawanta,”dariya yayi sannan yamusu sallama ya nufi gidansu Aisha.

Yana zuwa yasamu labarin abinda yasameta, hankalinshine yatashi dan bayason ganin wani na wahala sabida shi, Asibitin yanufa sanda yaga Aisha jiri ne yad’ebeshi ze fad’i da sauri excode d’inshi suka tareshi.

Kuka Al-ameen yake sosai tausayi da soyayyar Aisha ne suka shiga zuciyarshi akaron farko fad’i yake, “Aisha kiyafeni bansan halin dakike cikiba namaida igiyar auranmu guda biyu dasuka rage don Allah kitashi wlh ina k’aunarki inkika mutu bazan yafewa kainaba please,”ko motsi Aisha batayi batama san yanayiba abinda ya sake karya zuciyarshi kenan yadunga kuka kamar yaron daya rasa uwarsa.

Likitane yamasa bayani gameda cutar Aisha kuma yabashi shawara akan Inde da hali to afitar da Aisha kasar rasha domin duba lafiyarta.,Al-ameen yagamsu da shawarar likitan dan haka tun agurin yakira wayar masu yimasa visa inze fita yace yanason visa zuwa rasha nanda Kwana biyu ko nawane ze biya na mutum biyar yakeso yau komai dare ze kawo hotunan sauran dan ayi musu passport sabida basu dashi .

Aranan akasa Aisha a motar Asibitin zuwa international hospital dake Abuja tare da rakiyar mamanta da Al-ameen da tawagarsa inda k’annan Aishan aka kaisu gidan su Al-ameen,iyayensa sun tausayawa halin da Aisha take addu’ar samun sauk’i suka mata

Karfe goma na dare suka isa Abuja,adaren yakai hotunan Surbajo,Yusuf,Inna,Aisha,sabida shi yana dashi visa kawai za’a masa,harda passport,se sha biyu yashigo gida,Surbajo tafirgita da ganinshi nande yakwashe komai yasanar da ita, kwana tayi tana kuka da sassafe tasa Al-ameen yakaita Asibitin ananne tai kuka bana wasaba dakyar aka rarrasheta. Ranar da ita aka kwana a asibitin fafur tak’i komawa gida.

Da sassafe jirginsu yad’aga zuwa rasha,

to Aisha Allah yatashi kafad’a .

Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????

Zahra Muhammad mahmud

*®Pure moment of life writers*
*P.m.l*

*page 77-78*

*Rasha*

Sun isa lfy tun a Airport suka tarar da motar ambulance najiransu da kuma wata personal car,suna sakkowa akasa Aisha a Ambulance d’in zuwa Asibiti su kuma suka shiga d’ayar motar suka bisu abaya.

Likitocin dasuka duba Aisha ba k’aramin fada suka rufesu dashi ba akan barinta da ciwo da sukayi yaci k’arfinta. Sude ba baka se kunne, angama yimata duk abinda yadace sannan aka sallami su Al-ameen,sabida ba’a jinya a Asibitin sede kazo kaduba Mara lafiya kawuce.

Hotel yakaisu me kyau sosai,d’aki biyu ya kama d’aya na Inna d’aya nasu.tunda suka shiga d’aki wanka kawai sukayi suka ci abinci, suka rama salloli kowa yabi lafiyar gado sabida sun gaji sosai.

Tunda sukaje Rasha jikin Aisha yafara sauk’i, kullum Al-ameen natare da ita yana bata kulawa sosai,Surbajo Ma ba’a barta a bayaba tana yi dede gwargwado gashi duk dare seta tashi tayi sallolin nafila akan Allah yaba Aisha lfy,cikinta bashi da laulayi shiyasa take samun damar yin komai,Inna ko har cewa take ita bata ga amfanin zuwa da itaba sabida komai da yadace tayi Surbajo ce keyi se albarka take sa mata.

Abinda Surbajo takeyi game da Aishan bak’aramin farantawa Al-ameen rai yakeyiba sonta da k’aunarta kullum k’aruwa yake azuciyarshi ya yarda Surbajo me k’aunarsa ce ba kad’an ba shiyasa yabata wani matsayi a zuciyarsa wanda be ba kowaba se ita.

Satinsu biyu da zuwa Aisha ta farfad’o,numfashinta
ya dedeta shiyasa aka cire mata abun oxygen d’in da’aka samata kuma anrage mata yawon na’urorin da’aka baibaye jikinta dasu,lokacin suna gida ta farkan daga can asibitinne aka musu waya akan suzo ta farka. Al-ameen da Surbajo har karo suka dunga yi gurin fitowa daga d’aki shaf sun mance da Inna da Yusuf (dayake agurin Inna yake kwana,)driver suka sa yakaisu asibitin.

Aisha na ganinsu kuka ta rushe dashi ta runtse idanunta sabida bazata jure kallonsu ba,da saurinsu suka karasa inda take Al-ameen ne yarungumota jikinshi hawaye na zuba a idonshi shafa kanta yakeyi alamar tayi shuru,Surbajoma kukan takeyi taruko hannun Aisha tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button