HAUSA NOVELSURBAJO Complete Hausa Novel

SURBAJO Complete Hausa Novel

“Lalle Allah yayi gaskiya da yace be saukar da ciwo ba seda yasaukar da maganinsa, Aunty Aisha bayi murnar samun saukinki karki ce zaki nemi gafarata nadade da yafemiki Allah yakara miki lfy da zaman Lfy,”tafadi tana sake rike hannun Aishan da kyau, dagowa Aisha tayi tana kallon Surbajo cike da mamakin kalamanta Wanda bata taba tsammanin zata furtasuba gareta,ahankali ta juyo da kanta gurin Al-ameen tana kallonshi shima ita yake kallo yana murmushi magana zatayi amman yarigata, Yace,

“Shshh banason kiyi mgn duk abinda zaki fada munganeshi dan haka kuma dukanmu mun yafemiki Allah yabaki lfy uwargidana kinji,”kukane ya sake kwacewa Aisha jin kalaman da yamata yakara sawa tanajin kunyarsu sosai.

“Aunty wai kukannan na menene ni kimin kudinsa nasiya kidena yimana asarar hawayenki a banza,”inji Surbajo.

Waigowa Aisha tayi tana kallon Surbajon data turo baki gaba alamar shagwab’a,rungumeta Aisha tayi tana kuka take fadin,

“Wallahi ke y’ar Aljannah ce Surbajo,babu kishiya irinki a wannan zamanin,base anfad’aminba wlh nasan kece silar da Al-ameen ya waiwaye ni sabida nasanshi farin sani inyayi fushi da abu baya waiwayarsa har abada nagode miki don Allah kiyafemin wlh sharrin shed’anne da kuma na k’awaye pls kuyafemin dukanku nasan na cutar daku kugafarceni,”tafashe da kuka me tsuma zuciya.

Rungumeta sukayi duka suna fad’in Sun yafemata duniya da lahira.

Ranar wuni sukayi a gurinta yayinda Al-ameen ya ayka driver ya dauko su Inna da Yusuf,Inna rungume Aisha tayi tana kukan farin ciki da Allah yatashi Aisha Lfy.

maman yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????

Zahra Muhammad mahmud

 

*pure moment of life writers*
*pml*

*page 79-80*

Sannu a hankali jikin Aisha ke k’ara warwarewa, wanda hakan faranta ran su Inna yakeyi kullum Surbajo natare da ita tana bata labarai dazasu dunga sata nishad’i sabida likita yace adena barinta ita d’aya gudun karta dunga tunani.

Surbajo shawara taba Al-ameen akan in ciwon zuciyar Aisha yagama warkewa meze hana suga likita gameda rashin haihuwar da akace bazata sakeyiba ko Allah zesa adace da Maganin anan.shuru Al-ameen yayi yana kallonta daga bisani yajawota jikinsa yarungumeta sannan yace,

“Baby wlh you are too good,zuciyarki me kyau ce Baby, Allah yamiki albarka yasa y’ay’an dazan haifa su d’auko kyawawan halayenki,narasa taya zan nunamiki ina sonki ni kaina banawa kaina irin son danake miki pls Baby kirik’eni amana duk wuya dun runtsi karki gujeni wlh narasaki nayi imani mutuwa zanyi bazan iya rayuwa babu keba pls,”yafad’i yana sake rungumota.

Rungumeshi itama tayi sannan tace,

“Dear Kenan,toni ay arayuwata banida abin danake so sama dakai, inasonka fiye da kaina haka zalika nima bazan iya rayuwa babu kaiba,babu wani k’unci ko tsanani dazesa nabarka insha Allahu you are my soulmate dan haka babu me rabamu se mutuwa,”kiss takai mishi a goshi ayko ruk’ota yayi suka shiga romancing d’in juna ta ko’ina sosai suke enjoying abinda sukeyin seda taga ze wuce gona da irine tayi k’ok’arin hanashi, shiko nuna mata yayi besan zancanba sabida itace ta tsokanoshi dan tunda sukazo garin betab’a kusantartaba sabida bata yarda setacemasa yazeyi haka su dasuke da marar lfy haka dole yake hak’ura,shiyasa yau yace besan zancanba seda ya moreta son ranshi dan har kuka tafara yimasa sannan ya kyaleta.

watansu guda a Rasha Aisha ta warke sumul sede d’an abinda ba’a rasaba,zancan matsalar rashin haihuwarta ma and’orata akan magani wanda sede fatan Allah yasa a dace.

Visa yamusu daga Rasha suka wuce saudiyya domin yin umarah,wayyo dad’i daga kan Inna da Aisha da Surbajo babu wanda beyi kukan ganinsa a saudiyyaba, nan suka duk’ufa yin addu’o’i babu kamar Aisha da tana d’awafi tana kuka tana rok’on Allah ya gafarta mata kurakuranta,in tafara d’awafin setayi bakwa’i so bakwa’i babu abinda take rok’o se gafarar ubangiji sam bata kwana a masaukinsu kullum a masallaci take kwana kuma ba bacci takeba se rok’on Allah se safiya tayi take zuwa masaukin tayi wanka tad’an kwanta ta huta,su Inna har fad’a suke mata akan tadunga ragewa tunda bacikakkiyar lfy garetaba, itade sede tayi musu murmushi dan yanzu Aisha gaba d’aya ta sauya ko magana batasonyinta sosai seta Kama.

Satinsu biyu a Saudi Arabia suka dawo Nigeria cike da so da k’aunar juna,a airport y’an uwane na nesa dana kusa suka zo tarbarsu abin yamusu dad’i sosai koni nayi farinciki direct gidansu aka wuce dasu,ga mamakinsu jamaa ne mak”il da gidan daddyn Al-ameen ya had’a musu walimah ta murnar dawowarsu,wanka kawai sukayi suka ci abinci suka fito gurin walimar anci ansha an godewa Allah taro yatashi lfy.

Da daddare har d’akin Aisha Surbajo taraka Al-ameen sannan tamusu fatan samun dauwamamman zaman lfy gabad’ayansu, sallama tamusu ta dawo d’akinta tana shiga d’aki tarushe da kuka sabida Surbajo macece me kishin mijinta daurewa kawai take Amman batason taga wata ta rab’i mijinta,gudun kar shed’an yazo yazugata ne yasa tashige toilet ta d’auro alwala tazo tafara kai kukanta ga Allah akan ya yayemata wannan azababban kishin dake damunta.

Maman Yusuf
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????

Zahra Muhammad mahmud

*® pure moment of life writers*
*p.m.l*

 

*Page 81-82*

Washe gari da sassafe Surbajo ta tashi ta had’a musu breakfast me rai da Lafiya,tajera a dining d’in falo,sannan taje tayi wanka tayima Yusuf suka shirya tsab dasu,zaman jiran su Al-ameen sukayi su fito suci abinci.

Har zuwa k’arfe sha d’aya na safiya basu fitoba,abun yayiwa Surbajo ciwo sosai dan haka taja Yusuf sukaje suka ci nasu,d’akinta tadawo tahad’a kayansu duka tafita takira driver yazo ya d’aukarmata kayan,da sauri driver yagama kwashe kayan yasa amota kamar yadda ta umarceshi.

Rufe k’ofar part d’inta tayi taja hannun Yusuf suka fice daga cikin gidan, motar da driver yashirya kayansu aciki tanufa tana zuwa yabud’e mata k’ofar baya tashiga ita da Yusuf,rufe k’ofar driver yayi sannan yazagaya mazauninsa yazauna yace,

“madam ina muka nufa ne?”.

“Abuja ta bashi amsa a gajarce”.

Tada motar yayi suka fice daga gidan yakama hanyar Abujan,tafiya suke sosai cikin awa biyu suka shiga Abuja kai tsaye gidansu yakaita yasauke mata kayan masu gadin gidan suka shige dasu cikin gidan.

Sallama driver yamata yajuya yakama hanyar komawa kaduna.awanshi biyu a hanya ya isa gida lfy.

Surbajo koda ta koma Abujan ranta bedena yimata zafi ba dan har ga Allah yau sun b’ata mata rai bana wasaba,har kuka tadungayi na bakin ciki,tsoronta kar Al-ameen yace ze wulak’antata akan Aisha dan taga kamar yunk’urinsa kenan.

Su Al-ameen basu fitoba se k’arfe d’aya na rana shima kiran sallah ne yatashesu daga baccin dasukeyi,tun bayan dasukayi sallar asubah, sabida ansha love bana wasaba shine suke ramakon baccin da basuyiba
wanka suka shiga atare kowa yayiwa d’an uwansa wankan sannan Al-ameen ya d’auko Aisha suka fito shiryawa sukayi sunyi kyau sosai kowa yagansu ze d’auka sababbin amarene.seda sukayi sallah dayake tun a toilet sun d’auro alwalarsu,sannan suka sakko k’asa,se alokacin kunyar haduwa da Surbajo ta kamasu tabbas sunsan abinda sukayi be daceba ga inda ake so azauna lfy, jikinsu a sanyaye suka karaso falon ga mamakinsu abincine iri-iri Jere akan dinning,dakinta suka nufa suka fara nuking amman shuru baa budeba hakan yasa suka dauka sallah takeyi,juyawa sukayi zuwa gurin dinning din bubbudewa sukayi suka gani ananne suka fahimci taci nata nasune wannan,amman duk da hakan basu fara cin abincinba suna zaman jiranta,gajiya Al-ameen yayi dan haka wayarsa yaciro yakirata seda takusa tsinkewa daga can Abujan Surbajo ta daga kiran bayan ta dedeta natsuwarta tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button