SURBAJO Complete Hausa Novel

“Hello Dear ina kwana kun tashi lfy?yajikin Aunty?”.
amsawa yayi da cewa,
“Lafiya lau Baby,jikinta kuma da sauki,munzo muna nurking kofarki baki budeba ko lfy?,kuma yanzu jiranki muke a dinning shuru baki fito ba, pls kiyi sauri mana kizo yunwa muke hi.”
amsa tabashi dacewa,
“Ayya karku damu kuci abincinku mu munci namu nakune wannan,kagaishe da Aunty Aisha bazan sami damar fitowaba yanzu sabida naga gidan na sababbin amare ne yana dakyau abarsu su huta ako’ina nagidan,kasan sababbin aure abun se a hankali a gaban kowama raba abin kunya suke batare dasu sunji kunyarba,sabida cike suke da so da k’aunar juna mantawa suke da kowa inba junansuba nabarka lfy,”tana gama fad’in haka ta kashe wayarta gaba d’aya.
Wani zazzafan gumi ne yaketowa Al-ameen dajin zancan Surbajo,sabida shi bahaushe ne dole ya fahimci bak’ar magana Surbajo ta gasa ma’i,kunyar tace tasake kamashi tabbas basu kyauta mata ba duk da tana musu kawa’ici amman yau sunsa tafara fusata, dan tun suna rasha sede tabasu guri insuka soma rungume rungumen juna,ajiye wayar yayi asanyaye,Aisha ce takatse mishi tunani dacewa,
“Honey tayi fushi damu ko?”
gyada mata kai yayi alamar eh,shuru sukayi dukansu jikinsu ya mutu babu ma kamar Aisha wacce ta d’auki laifin ta d’ora akanta,dakyar suka ci abincin sannan Aisha ta tattare gurin dasuka b’ata ta kwashe komai taka’i kitchen bata fitoba seda ta wanke komai ta adana.
D’akin Surbajo suka koma suna ta nuking ganin taki bud’ewa ne yasa Al-ameen yace bari yaje gidansu yadawo maybe zuwa lokacin ta hak’ura ta bud’e k’ofar, rakiya Aisha tamasa har waje,Al-ameen mamakin inda aka ka’i motar da yay niyar fita acikinta yakeyi,d’aya daga cikin bodyguard d’inshi yakira yatambaya ina driver yaje da motar?,bashi amsa yayi da cewa,
“Nide naga madam takirashi yadebo mata kaya daga cikin gida yasa amotar sun fita amman bansan inda suka nufa back,”hankalin sune yay masifar tashi wayarta yakira akashe take kiran wayar driver yayi bugu daya yadauka yace,
“Hello, good day sir we arrived safely now am on my way coming back from Abuja,”katseshi Al-ameen yayi azafafe yace,
“Hey stupid where did you took my wife and my son,?where?”yafadi cikin tsawa wacce takusa sawa sitiyari ya kwacewa driver cikin rudewa yace,
“Am sorry sir is not my fault she is the one who permitted me to take her to Abuja,right now she is in Abuja sir,”
Kashe wayarshi kawai yayi ranshi ab’ace juyawa yayi yakoma cikin gidan shida Aisha yafasa fitar huci kawai yakeyi meyasa Surbajo zatayi masa haka? shi bawanda ma yafi jin haushinsa irin driver daya ka’ita,
Aisha ce ta matso tana tambayarshi,”me yafarune haka?ina Surbajon taje?ta tambaya hawaye nasakkowa daga idonta dan yanzu bata k’aunar b’acin ran Surbajo ko kad’an kamar yadda itama tasan bata k’aunar nata b’acin ran,amsa yabata dacewa,
“ta koma Abuja ne”ya fad’i kamar me shirin yin kuka.
Kuka Aisha tasa mishi akan wlh se yabi bayanta yau d’innan ita bazata iya jure zama da b’acin ran Surbajo ba “katafi nace!!!!!”,tafad’i cikin k’araji tana kuka da gudu tajuya ta haura sama inda d’akinta yake ta kulle k’ofar d’akin tafad’a kan gado tana kuka,tabbas tasan sunka’i Surbajo bangone shiyasa tagujesu sabida ko da suke Rasha abubuwan dasuka dunga yi agabanta in itace akayiwa Wlh bazata yarda ba amman Surbajo ta dauke idonta, dole wanda suka mata yau yay mata zafi.
Al-ameen kanshi ne yasoma charge rasa wacce zebi yayi,bashida zab’in daya wuce yabi umarnin Aisha dan haka juyawa yayi yafice a gidan,da kanshi yake driving yad’auki hanyar Abuja.
safe trip Angon Surbajo.
Maman Yusuf
[4/12, 11:13 PM] +234 703 962 5239: ????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*page 83-84*
Al-ameen ya’isa Abuja Lfy Kai tsaye gidanshi yanufa masu gadin gidan sunyi mamakin ganinshi sabida ganin ba’a jimaba da kawo madam.
Gaisheshi sukeyi amman ko takansu bayayi cikin gidan yashige,afalo yasameta akwance Yusuf kuma na wasa,tayi mamakin ganinshi amman seta d’auke kanta daga kallonshi,k’arasawa yayi kan kujerar datake kallonta kawai yakeyi Amman ita ko kallo be ishetaba sema rufe idonta datayi.
‘Haba Baby meyasa zakimin haka don Allah? kinsan yadda kika d’agamin hankali kuwa,ay ina ganin bahaka yadace kiyi gurin nuna fushinki ba magana yadace kiyimin sena gyara,amman matakin dakika d’auka wlh yatashi hankalina,”yaruk’o hannunta ay kamar jira take tamik’e tsaye afusace, takwace hannunta tafara magana cikin fushi,
“Wato kama maidani karya ko?banida zuciya a k’irjinane aka fad’amuku? koni akace muku tinkiyace wacce batasan ciwon kantaba? any way ba laifinku bane laifinane dana karya farashina yay arha da yawa, nayi muku kara wacce ni kaina nasan nayi namijin k’ok’ari Wanda duniya ma taji seta yabeni bare ku danayiwa,matarkace ban hanaku kuyi duk abinda kukesoba shiyasa ma nabaku guri danku sake dakyau,inde bawani bak’in cikin kabiyoni ka k’aramin ba pls get out from my side,”tafad’i tana nunamasa k’ofar fita.
Al-ameen mutuwar tsaye yayi yana kallon Surbajo cike da mamakin kalaman dasuke fitowa daga bakinta, tabbas yasan Surbajon shi tana da fad’a amman be d’auka shima zata iya masa ba ya bud’e baki da niyar yayi magana takatseshi da cewa,
“I said get out from my side now!!!!”tafadi cikin k’araji,
Tunaninshi ya karu akan nada yana ganin anya Surbajo bata da Aljanu kuwa shi besanta da rigima haka ba,kasa motsi yayi a inda yake bare yay tunanin bin umarninta.
Ganin bashi da niyar fitane yasa Surbajo fara jifanshi da duk abinda yazo hannunta tana kuka ta fadin,
“Why why?mutane kuka fiye son kanku da yawa?,meyasa jama’a yanzu basu da buri daya wuce su rama cuta ga wanda yay musu alkha’iri?, meyasa……..”kukane yaci k’arfinta ta zube agurin tana kuka.
Al-ameen beyi yunk’urin hanata ba dan tabbas yasan yadda take da kishi kuma ta iya yimusu wannan karar dolene ranta ya b’aci da abinda sukayi mata.jiki a sanyaye yakarasa inda take yarungumota jikinshi yana rarrashinta da duk wata kalma dayasan tana sata nishadi sosai yake rarrashinta seda yajima sannan ta hakura ta dena kukan,mikewa tayi ta dauki Yusuf sannan takai dubanta gurin dayake tace,
“Hak’uri kabiyoni kabani to na hak’ura seka tashi ka koma kaduna kar tajika shuru,yazamana kayi laifi,kuma dama ay saura sati biyu hutunka yak’are,dan haka ka koma can kagama hutun,inkakoma bakin ayki kadawo nan d’in”.
“Haba Baby meyasa zaku dunga yimin hakane? da girma na agari amman ace kun sani agaba kunmaidani kamar wata kwallo kowa da salon dayake bugani,Aisha ta koroni gurinki kema yanzu gashi kin korani gurinta, bakya ganin kamin nakai kaduna yanzu dare zeyi sosai amman ko ajikinki meyasa kike son zama mara tausayine?,pls kibarni na kwana da safe sena tafine.”
“Tab’d’ijan ay wlh sede kafad’i duk abinda Kaga dama amman wlh bazaka kwana agidannanba inko kace seka kwana to wlh ni bazan kwana acikiba, dan haka kajuya katafi dannasan aranka sokake katafin gulma ce kawai irin taku ta maza masu bakin ganga Kaga kawuce ni na rufe k’ofata”.
Murmushin taka’ici yayi,yajuya yafice daga gidan,hotel yakama yakwana washe gari yawuce kaduna,shi abunma dariya yake bashi wato da gaske ne kenan zancan da maza sukeyi nacewa in matanka suka had’a kai to wlh ubanka zasuci, shide ko ba haka bane shi yayarda tunda gashi sanadin had’in kannasu kowa batason shiga hakkin kowa shi Kuma sun maidashi kamar ball wannan ta buga ta ba wannan.