SURBAJO Complete Hausa Novel

Ganin tafarko ne yasa yadauketa yayi toilet da ita yayo musu wanka amma har lokacin taki bude ido har suka fito bata Dena kukanba
Rigar bacci yasamata shima yasa nasa Gado yanufa da ita yakashe musu haske yarungumota jikinshi yana shafa mata baya Dan yagano me ya firgitata har ta sume Sabida bata taba ganin namiji babba ahaka bane shine dalili har yanzu kuka take masa akunne yace mata baby meyasa kike kuka ne nace bazaki mutuba amma kinki kwantar da hankalinki ko wani Abu kikeso
Cikin kuka tace kadon Don Allah kar ka kuma nunamin macijin dazu Wlh yabani tsoro sosai ni bantaba ganin maciji irinshiba agarinmu akwai macizai amma babu irin wannan
dariyace taso kubcewa alameen Amman se yacije yace wayace miki ni na kawoshi ay zuwa Yayi da yasareki ki mutu shine nace masa ay nayafemiki shinefa yatafi
kara shigewa jikinshi surbajo tayi Dan ta tsorata dajin zancennasa can kasan makoshinta tace ngd kado
********
abangaren Aisha kuwa suna barinta agurin dakinta tawuce tana kuka ranta kamar ze fita tunda take baa taba cimata mutunci irinna yauba tana shiga daki wayarta tadauka takira aminanta cikin kuka tashaida musu duk abinda yafaru hakuri suka bata tare da bata tabbacin gobe zasu zo gidan su hadu suyima surbajo dukan tsiya takwantar da hankalinta kawai dasu suke magana
sosai hankalinta yakwanta dantasan aminan nata basa mata karya kuma Tana da tabbacin se Sun ramamata kwanciya tayi ranta fes Dan tasan gobe kashin surbajo yabushe
Damisalin karfe hudu naasuba karar wayar alameen yatashesu abacci da kamar baze daukaba cande yadaure yadauka jin wayar se kira akeyi sunan oganshi yagani akan wayar dasauri yakwantar da surbajo yadauki wayar gaisheshi yayi cike da girmamawa kamar yana kallonshi dagacan bangaren ogan yace
alameen duk abinda kakeyi kaajiyeshi ka komo office gobe jirgin daze daukoka is ready by 7:30am katabbatar kana airport sabida wani aykine yataso nasauri Wanda your attention is needed so am sorry nasan bazakaji dadiba amma kadaure de
ran alameen besoba Amman bashida zabi Danhaka yacema ogan don’t worry sir consider it has been done
godiya ogan yayi sannan sukayi sallama yaajiye wayar
bekoma bacciba sabanin surbajo dake ta aykin bacci dakinshi yaje yadauko duk wani abu daze bukata yasa a trolley yadawo dakin surbajo itama yahada mata abinda yasan zata bukata acikin trolley din wanka yayo yadauro alwala doguwar riga yasa sannan yatashi surbajo dakyar ta tashi toilet yarakata yace tayi wanka tayi sallah kamin yadawo bata musa ba sabida ya hadamasa ruwan wankan
jamata kofar yayi yawuce masallaci koda zefita kulleta yayi tawaje Dan yasan abinda tayiwa Aisha jiya ba hakura zatayiba
karfe shida yadawo daga masallaci surbajo tuni tayi wanka tayi sallah Tana zaune akan darduma Tana lazimi
ganinshine yasa ta kudundune fuskarta ahijabin jikinta wai kunya takeji
murmushi yayi yakarasa inda take yace baby na kunya ta kikeji kuma yanxu kinga tashi maza inshiryaki anguwa zamu dasauri tamike Dan surbajo kafar yawo gareta Waldorof yaje yadauko mata wata doguwar riga yar kanti fara har kasa yadauko su pant da bra da gyale da boy friend jacket tsaf yashiryata har makeup shiyamata amma simple one yamata surbajo ko duk kunya tagama cikata kallon kanta tayi mirror taga tayi kyau sosai ita kadai take Ta murmushi ba abinda yafi burgeta irin acuci mazan daya mata da gashinta yakuma yimata rolling din gyale ja akanta takalminta lowfas ne shima ja se boy friend jacket baka gaskiya tayi kyau
dakinshi yaje yashiryo cikin kakinshi na soja dakin Aisha yaje Tana bacci kobaa fadamasaba yasan ko sallah batayiba tashinta yayi dakyar tamike tace meyakawoka dakina yanzu murmushi yayi yace uwargida sarautar mata Allah huci zuciyarki zankoma gurin aykine nazo naji mekike bukata
wani dadine yakamata wato zasu Jidadin cin uban surbajo dakyau cikin sakin fuska tace babu abinda nake bukata se kudi dubu dari hudu yabata taamsa yace to senadawo kikula da kanki
adawo Lfy tabashi amsa daga inda take alameen yayi mamakin yadda tamasa adduar yadawo Lfy abinda batayimasa
dakin surbajo yadawo mamakine yakamata gamida tsoro ganinshi sanye cikin kakin soja
yaganota amma seya basar jakarsu yadauko yaja hannunta yakulle kofar suka fice daga falon suna fitowa wani soja yataso yaamshi kayan yasa aboot suka shiga direba yajasu zuwa airport yayinda excode dinshi ke take bayansu
suna zuwa ba bata lokaci suka shige jirgi kamin jirgin yatashine yakira iyayensa awaya yamusu bayani albarka suka samasa musamman dasukaji da surbajo yatafi hakuri yabasu gameda rashin zuwa yamusu sallama lokacine zewuce shiyasa bakomai suka bashi amsa Allah de yamasa albarka Godiva yayi yakashe wayar gaba daya
surbajo ko inbanda zare ido baabinda takeyi rungumota yayi jikinshi bayan yadaura mata belt jirginsu yadaga zuwa rivers state.
maman Yusuf
Zahramuham[truncated by WhatsApp]
????????????????????????????????????
*SURBAJO*
????????????????????????????????????
Zahra Muhammad mahmud
*sugura Abdullahi, maman Irfana,fatima Radda,maryam Taheer. Don Allah ina kuka shiga kwana biyu pls inkuna tare damu munason sani am really miss you all*
*page 37-38*
Dan misalin karfe Tara nasafe su Ruky suka dira gidan Aisha lokacin ko sallah batayiba
Tana ganinsu wani farincikine ya lullubeta kai tsaye dakin surbajo suka nufa Dan suna da tabbacin alameen bayanan
Dukan kofar suke iya karfinsu kamar zasu karyata
amma shuru baalamar zaazo abude can suka fara dura mata zagi gamida cewa inhar taisa tazo ta bude kofar jin shurun yayi yawane yasa sukace bari sutambayi masu gadi ko tafitane duk da suna tantamar hakan
Duka su ukun sukaje gurin megadin Aisha ce ta tambayeshi ko Amarya daaka kawo jiya tafitane
Baki yawashe yace ah madam you are so lucky oga yatafi da Amarya rivers state dazu Dan su Sunday ne ma suka rakasu airport
ihu Aisha ta kurma tafadi agurin Tana kuka fadi take alameen kacuceni shine katafi da amaryarka ni kabarni agida nashiga uku nalalace ina zansa rayuwata
Dakyar su Ruky suka jata zuwa cikin gidan hkr suka shiga bata itako ina kuka take kamar ranta zefita ita ba bakincikin rashin rama dukanta takeyiba bakincikin surbajo tarigata sanin gidan alameen nacan
har azahar Aisha bata Dena kukaba gaba daya tarasa meke mata dadi aminannata se hkr suke bata gamida zugata akan tamasa rashin mutunci karta yarda da wannan wulakancin
Ranarde Aisha basallah bare salati daga ita har aminannata
*********
Karfe goma nasafe su alameen suka sauka a patacot
Motocin excode dinshi nacan yatarar suna jiranshi
Yana rungume da surbajo suka shiga mota aka jasu zuwa gidanshi dake gra din garin
Tunda suka isa gidan kan surbajo kusan juyewa yayi sabida tsabagen haduwar gidan
gudun karta kunyatashi agaban yaranshi yasa yayi sauri yajata zuwa cikin gidan
Tafiya gagarar surbajo tayi sabida kallon datake alameen daukarta yayi yahaura da ita Sama dayake gidan six bedroom ne duplex
daki yaajiyeta sannan shima yazauna itako zaman yagagareta sabida zabar kauyanci har bangon gidan shafawa ta dungayi da hannunta
jawota jikinshi alameen yayi yace to madam surbajo Kalle kallen yaisa haka zomuje namiki wanka kici abinci Dan ni office zanwuce ana nemana