TAKUN SAAKA 6
Koda suka isa makarantar sai da ya sakata tai addu’a kafin ta fita a motar, ya miƙa mata 1k tare da mata gargaɗin ta dage akan text din da yaji Ammar ya faɗa zatayi. Inba hakaba bazai kaita chaina ɗin da take burin zuwa ƙaro ilimin kimiya da fasaha ba”.
Cike da son cikar burinta ta tabbatar masa insha ALLAH zata dage wajen cinye text ɗin da maki mai yawa. Daga haka ta shiga ɗaga masa hannu har yay reverse yabar wajen. Ƙoƙarin nufar department ɗinsu tayi ranta fal saƙe-saƙe itama. Ta duba department ɗin su Zahidah a ranta tana tunanin suma sunzo tuni, dan suma sunce mata suna da text yau tun 8am.
★★★★
Koda su Hibbah suka fita a class bata nema su Hafsat ba. Dan tanason samun nutsuwar ƙarasa aikinta na jiya. Kai tsaye ɗakin dake ajiye da na’urori mai ƙwaƙwalwa na department ɗin nasu ta nufa. Dan tana ɗaya daga zaƙaƙuran yara mata matasa dake baje kolin basira da ƙwazon da ALLAH ya basu akan ilimin kimiya da fasa.
Ta samu ɗalibai irinta masu naci da ƙulafuci ɗai-ɗai a ɗakin. Bataima kowa magana ba ta zauna a table guda ɗaya
dake daga can lungu tana sauke ajiyar zuciya, tsabar yanda take nacema Computer ɗin wajen saboda daɗin da take mata har security ta ƙirƙira ta saka dan tanada ajiye-ajiye da yawa a ciki. Akwai wani yaro da suke ƴar tsama da shi, shima yanada ƙwazo matuƙa akan fannin, ya taɓa mata manaƙisar lalata mata securitys ɗin data saka domin binciken abinda take ɓoyewa a Computer daba tata ita kaɗai ba. Aiko data tashi ita sai da tai masa ɓarnar daya gwammaci da bai aikata mata ba, dan babbar ma’ajiyarsa ta Computer ɗinsa dake gida taima kutse, tare da aikata ɓarna da har iyayensa sai da suka saka police zuwa har gida domin kamata. Sai dai kasancewar tana da Yah Abubakar hakan bata faruba, sukai ƙoƙarin ganin sun rufe case ɗin.
Flash ta ciro a bag ɗinta tai connecting da Computer ɗin ta shiga abinda ya kawota cike da ƙwarewa da fatan nasara. Kusan mintuna goma sha uku tana abu ɗaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take akai-akai. Harma ta fidda rai da nasara sai gashi cikin amincin ALLAH ta kuma dace. Wani lallausan murmushi ta saki da ambaton kalmar “Alhmdllhi” tana rungume Computer ɗin dan farin ciki. Tuno da bata sanarma Yah Abubakar bane ya sata saurin ɗauka wayarta. Batare da tunanin komai ba ta dailing number ɗinsa. Sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Ta tura baki gaba alamar jin haushi tana ƙoƙarin sake kiransa. Nanma ɗin dai babu amsa. Cikin takaici ta ƙara ƙoƙarin sake kira a karo na uku sai ga nashi kiran ya shigo.
Ɗagawa tai da sauri tare da kwaɗa sallama cikin karaɗinta da shagwaɓa. Daga can Yaya Abubakar ya amsa yana faɗin, “Autar Ummi lafiya dai ko? Ina cikin aiki ne fa”.
“Lafiya lau Yaya dama fa wani abu zan sanar maka. Jiya baka dawo da wuri bane har nayi barci, ɗazun kuma na manta ne saboda Abba”.
“Okay to ina jinki”.
“Uhm yauwa Yayana. Kasan wani abu? Jiya muna fitowa a school wasu masu power bike suka kusan turemu, sanadin hakan ma har Hafsat ɗin gidan aunty Kulu ta samu rauni a ƙafarta sai da akai mata gyara a asibiti. To ni kuma tun a jiyan na jefa musu agogon nan nawa, yanzu haka na gano inda suk…….”
Kafin takai ƙarshen maganar tata ma Yaya Abubakar ya miƙe a zabure da ga can yana faɗin, “Masu power bike?!”.
“Yes! Yaya. Kasansu ne?”.
“Kinga auta kina ina? Wannan maganar bata waya bace zanzo yanzu na sameki, karfa ki faɗama kowa bayan ni”.
Kafin ta samu damar cewa wani abu ya yanke wayar.
“Oh Yaya kama tsaya na gama maganata mana zaka wani yanke. To nama fasa faɗa maka sai nan da awa uku”. Tai maganar tana haɗa kayanta da fushi ita a dole taji haushi. Tana ƙoƙarin rataya bag ɗinta a baya kira ya shigo wayar tata. Ganin Zahidah ya sata ɗagawa tana kai wayar kunnenta da nufar ƙofar fita daga wajen.
Tana cikin sauraren Zahidah dake faɗa mata inda take taje ta sameta taga ansha gabanta. Takaici ya sakata janye wayar daga kunnenta ta ɗago domin ganin wane shege ne ya tare mata hanya.
Turus ta ɗanyi tana kallon zaratan mazajen dake a gabanta riƙe da manyan bindugu tamkar wasu mala’ikun ɗaukar rai. Duk da rashin tsoronta sai da taji wani abu mai kama da firgici ya gitta mata. Ta motsa bakinta a hankali idanunta na wani mar-mar.
“Bayin ALLAH lafiya kuwa?”.
Ta tambaya tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Ɗaya da ga cikinsu ne ya nuna mata i’d card ɗinsa da faɗin, “Mu jami’an tsaro ne da ga hukumar ƴan sanda ta farin kaya. Munzo nan ne kuma dominki Muhibbat Aliyu Hamza”.
“Wurina kuma? To ni miya haɗani da ku? Wama ya faɗa muku sunana?”.
“Duk zaki sami amsoshinki idan munje office”.
A tsiwace tace, “Hu’um ai wlhy bazan biku ba, barama na kira Yayan…..”
Zare wayar da ɗaya daga cikinsu yayi ne ya saka sauran maganar tata maƙalewa. Ya katse kiran da taima Yaya Abubakar yana kashe wayarma baki ɗaya.
Wani yawu Muhibbat ta haɗiye da ƙyar tana binsu da kallo tare da ɗalibai ƴan uwanta da hankalinsu ya fara kaiwa garesu suka ɗan fara taruwa domin kallon mike faruwa. Mota suka nuna mata. Da farko batai niyyar shigaba. Amma tuna tana dasu Yaya Abubakar aduniya ya sata shanye dukkan wata fargabarta ta shiga motar tana ƙunƙunin amshe mata waya da sukayi.
Dai-dai lokacin da suke shigewa motar suma Zahidah da aka kai mata labarin anga ƴan sanda na neman ƙawarta ta iso wajen. Hankalinta tashe ta shiga ƙwala kiran sunan Hibbah da sam batama jita ba. A firgice ta lalubo wayarta domin san kiran Ummi ta sanar mata ko zata sanarma cikin su Yaya Umar, dan ruɗewar da tayi tasa tama manta da cewar Yaya Ammar shima anan makarantar yake nasa karatun, yana a shekarar ƙarshe ne ta kammalawa..
★♣♠♣♠♣♠♣★♣♠♣♠♣♠♣★
Ummi na zaune a can inuwar mangwaro dake backyard ita kaɗai tun barin Abba sashen nata bayan ya gama shuka mata shika-shikan rashin mutuncinsa da ya saba. Lalle take sakama yatsun hannunta dan ita mace ce mai son jan lalle sosai. Har takai ta koyama Hibbah kasancewar tun tana ƴar ƙaramarta take mata itama.
Kallon wayarta da kira ya shigo tayi duk zatonta ma Hibbah ce. Batai mamakin ganin Zahidah ba, dan tasan Hibbah zata iya amfani da wayar tata wajen kiranta idan tata wayar babu kuɗi. Ɗayan hannunta tasa ta ɗauka wayar fuskarta da Murmushin tuna a yanda Autar tata ta fita cike da tsoron Abba a tare da ita.
“Autan Umminta yaya dai?”.
Ta faɗa dai-dai lokacin da take ɗora wayar akan kunnenta.