TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAAKA 7

 *_Typing????_*_Chapter Seven_*

……….Lokaci da aka basu da ga gidan gwamnati na kamo wannan gagarumin ɓarawo da babu wanda yasan ainahin kamanninsa na zahiri yay matuƙar tada hankalin kowacce hukuma ta ƴan sanda dake a jihar. A ɓangaren jami’an ƴan sanda na farin kaya tuni sun duƙufa wajen bincike suma. Musamman da ya kasance jami’ansu ne suka sami nasarar samo wheelchair da sauran kayan da ɓarawon yay amfani da su a waccan ranar.

            Tabbas wannan ɓarawo yana da matuƙar wayo da dabaru kala-kala da ganosa ke bama duk wasu jami’ai wahala kai tsaye. A duk ɓarnar da zai aikata yana aikatata ne da maban-banta fuskoki da salo daban-daban kuma. A kusan shekara biyu kenan da fitowarsa a bayyane babu wanda zai iya cewa ga fuskarsa ta ainahi ko samun wani labari nasa koda ƙanƙani ne.

        Duk da dai wasu a cikin jami’ai da suka ƙware sosai wajen aiki da binciko mai laifi sun taka rawar gani sosai wajen kafa masa tarkuna na musamman amma yana tsallakesu saboda duk tsiyar da zai shuka ba gaba gaɗi yake aikata ta ba sai ya shirya da shiri na gaske.

          Bayan zama na musamman da sukayi jiya game da binciken da sukeyi akansa furucin matashiyar budurwa ya shigo cikin jerin abubuwan da suka zauna domin tattaunawa. Lokaci ne da bai kamata suyi sakaci da duk wata dama da zatazo musu ba komin ƙanƙantarta. Dan haka basu tsaya sanya ba wajen bibiyar matashiyar budurwa mai cikakken suna *_MUHIBBAT ALIYU HAMZA_* da jami’insu ya kawo musu labarin alwashinta akan abin farautarsu. Dan haka suka kasance biye da ita tun a safiyar yau, tun daga ƙofar gidansu har zuwa cikin makaranta, shigarta class da fitowarta zuwa Computers room. Dukkan binciken data gudanar har zuwa kiran da taima Yaya Abubakar duk akan idon wanda ke biye da ita ne batare data sani ba…

        

         Sosai tashin hankali ke tattare da Muhibbah ganin inda aka kawota. Duk da Yayanta jami’in tsaro ne na ƴan sanda mai muƙamin d.p.o bata taɓa zuwa police station ba. Amma a yau sai gata a cikin headquarters na ƴan sandan farin kaya tsumu-tsumu batare da tasan laifin data aikata ba.

         Wani lafiyayyen office aka kaita da yaji kayan more rayuwa tamkar ba’a hukumar ƴan sanda ba. Ta saci kallon dattijon mutumin dake zaune kansa duƙe yana aiki kan takardun dake a gabansa. Cikin girmamawa wanda ya shigo da ita office ɗin ya ƙame yana salute ɗinsa.

        Sai a lokacin ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi ya dubesu ita da shi. Kansa ya jinjinama wanda ya kawota ɗin idanunsa a kanta. Gurin zama ya nuna mata da faɗin, “Ɗiyata bismilla zauna ko?”.

        Ajiyar zuciya ta saki dan har cikin ranta ta ɗanji sanyi. Gaishesa tayi da girmamawa zuciyarta na sake samun nutsuwa da shi. Ko ba’a faɗa mataba a yanayin shigarsa da shekarunsa ya isa tabbatar mata shi ɗin mai faɗa aji ne a hukumar.

           Ɗan kafeta yay da idanusa na kusan sakan ashirin ko ƙyaftawa bayayi. A take tsigar jikinta ta fara tashi tsoro na sake faɗaɗa a zuciyarta. _Hasbinallahu wa-ni’imar wakil_ ta shiga maimaitawa tare da sunayen ALLAH. 

          Murmushi ya sakar mata da yin ƙaramar gyaran murya yana ɗauke idanun nasa a kanta. Cikin taushin murya yace, *“Muhibbat Aliyu Hamza ko?”.*

        Hibbah ta jinjina masa kanta cikin dakiya da dauriyar hana bayyanar gazawarta tana faɗin, “Eh yallaɓai”.

       “Ɗalibar koyon kimiya da fasaha a babbar jami’a ta jihar nan?”.

     Nanma kanta ta jinjina masa da faɗin, “Eh yallaɓai”.

        “Uhm masha ALLAH. ALLAH yay riƙo da hannayenki ki zama abar alfahin ƙasarki baki ɗaya. Ina matuƙar son naga ƙananun yara musamman ma mata masu himma da ƙwazo akan abinda yay mana ƙaranci irinki”.

      A karon farko Hibbah ta saki murmushin jin daɗin yabon data samu da ga garesa tana faɗin, “Thanks you Uncle”.

        Murmushi ya sakar mata har haƙoransa na bayyana. “Kinsan miyasa aka kawoki nan?”.

        “A’a Uncle”. Ta faɗa cike da marairaicewarta da taso bashi dariya amma sai ya danne. Cikin ƙwarewar aiki ya ce, “Taimakonki muke nema akan masu power bike ɗin jiya da suka kusan tureku, harma sister ɗinku taji ciwo a ƙafarta”.

        Kallonsa Hibbah tayi cike da tsarguwa. Fahimtar hakan da yayi ya sashi saurin faɗin, “Muna son gano kosu ɗin ƴaƴan waye? a garin nan, mu kuma kamasu mu hukuntasu. Dan bai kamata ba ace dan kawai suna ƴaƴan masu arziƙi ba su dinga shatar tituna suna zabga gudu tamkar nasu su kaɗai. Zasu iya amfani da wannan damar suyita kashe al’umma saboda ƙarfin ikon iyayensu kuma talaka bazai iya kai ƙara a ƙwatar masa haƙƙinsa ba. Yanzu bayan ALLAH ya taƙaita muku wahala jiya da bamusan halin da kuke ciki ba zuwa yanzu ai ko. Kalla nan kiga”.

      Ya ƙare maganar yana ɗaukar remote ɗin da ke gabansa tare da janye idanunsa a kanta ya maidawa ga ƙatuwar tv dake mamake da kusan rabin bangon office ɗin. “Kinsan wannan mutumin?”.

         Fuskar dattijo mai cike da ƙasumba a cikin shigar manyan kaya ta bayyana. Kallon kusan minti ɗaya tai masa kafin ta girgiza kanta. “A’a yallaɓai ban sanshiba. Bamma taɓa ganinsa ba”.

        Wani ya kuma nunowa da faɗin, “Wannan fa?”.

         “Shima haka ban sanshi ba”. Hibbah ta faɗa idonta akan hoton matashin saurayi mai saida rake a Wheelbarrow.

        Cigaba yay da latso mata hotuna kala-kala na mabanbanta mutane tana cewa bata sansu ba. Sai wani guda biyu na kusan ƙarshe data taɓa gani an nuna a labarai kwanaki.

        “Yallaɓai wannan dai na taɓa ganinsa a tv, dan an taɓa nunasa kwanaki a labarai, kuma hoton yata yawo a social media akan cewar shi ɗin babban ɓarawo ne ɗan yahoo da ya yashe manyan kuɗaɗen wani attajiri. Yayana ma yace suma suna nemansa ruwa a jallo. Kuma nemansa kukeyi halan?”.    

        Sosai ma kuwa nemansa muke muma tare da waɗancan na farkon dana nuna miki. Amma rashin mai taimaka mana irinki yasa mun gagara hakan. Amma shiɗin wanene yayan naki?”

      Kanta tsaye batare da tunanin komai ba ta ce, “Uncle shima ɗan sanda ne”. 

         “Woow masha ALLAH. Lallai naji daɗin hakan sosai. Kuma zanso ganinsa shima harma nai masa ƙarin girma saboda samun ƙanwa irinki mai ƙwazon da ya kamata ƙasa gaba ɗaya tai alfahari dake”.

     Murmushi tayi cike da jin daɗin jin za’a ƙarama Yaya Abubakar ɗinta girma ta sanadinta. Shima ganin ta hau yanda yake buƙata saboda ƙuruciya sai ya ƙara faɗaɗa murmushinsa da faɗin, “Idan har kikai mana wanann taimakon da zan miki bayani akansa yanzun to lallai yayanki zai ƙara zama babban mutum, kema kuma zaki rama jin ciwon da aka saka ƙawarki tayi jiya. Da ga ƙarshe zaki samu ƙyauta mai tsokar gaske”.

         Batare da tunanin komaiba ta ce, “Insha ALLAH zan taimakeku Uncle, indai Yaya Abubakar zai ƙara samun girma”.

          Cike da jinjina wautarta fara’ar fuskarsa ta sake bayyana. “Yauwa ɗiya ta. Aikin da zaki mana shine gano mana inda masu power bike ɗin jiya suke.”

      “Lah Uncle ai nama g…..”

Sai kuma tai shiru tare da dafe bakinta saboda tunowa da gargaɗin Yaya Abubakar na ɗazun akan karta sake ta sanarma kowa.

      “Miya faru ki kai shiru ɗiyata?”.

        Da sauri ta girgiza masa kanta. “Babu komai Uncle, inason kai musu magana su fara bani wayata nayi magana da Yaya Abubakar”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button