TAKUN SAKA 17

“A rana ɗaya aka binne gawar kakana da mahaifiyata kusa da juna, yayinda aka barni hannun kakata da itama ta koma tamkar zautacciya. Bazance ban samu gata ba a hannun kakata, domin kuwa itace ta shayar dani har na tsahon shekara biyu. Sai dai sam bata son ganina, tunda ta yayeni bata sake yarda na raɓu jikinta ba. Kullum cikin tsangwamata take da nuna ƙyamata tamkar yanda jama’ar gari kemun. Babu maison ganina, babu maison na raɓu ɗansa nai wasa. Nasha cin duka wajen iyayen yara da yaran kansu batare da nasan laifin dana aikata garesu ba. Shekarata biyar a duniya mahaifina ya dawo kauyenmu. ko hutawa baiyiba kakata najin labari ta ɗaukeni ni da kayana taje ta damƙa masa batare da tace uffan ba ta juya ta tafi. A kuma wannan daren ta gudu a garin ta bar ƙannen mahaifiyata su Kawu Hannafi. Har yau ɗin nan da nake baku labari babu wanda ya sake jin labarinta.”
“A yanda mahaifina ya amsheni babu musu ya tabbatarma jama’ar gari ya san ni ɗiyarsa ce, dan kakata na tafiya ya ɗaukeni ya damƙa hanun mahaifiyarsa, ya kuma tabbatar mata dole ta riƙeni dan shima ya dawo gida da zama, dama wani aikine ya sashi tafiya bawai dan yayima mahaifiyata fyaɗe ba. Babu wanda ya iya cewa ƙala saboda tsoron da suke masa. Sai dai dukannin haushinsa da takaicinsa akan saukeshi kainane a gidan. Shima ba sauki nake samu a garesa ba, dan babu irin kalar azabar da bayamin, sai dai kuma wani yana taɓani inhar ya gani sai ya rama mani.”
“Haka na cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙasƙanci, a wajen baban mahaifinku malam Hamza ne kawai nake samun sauƙi. Dan shi mutum ne mai ilimin addini. harma almajirai ke garesa. Sai dai sam bai dace da mace ba (Hajiya mama). Hajiya mama asalinta ba ƴar garin bace, acan indai yay almajiranci aka aura masa ita, hakan yasa ɗanta na fari da suka haifa mai suna Aliyu tun daga yaye da aka kaisa garinsu ba’a dawo da shi ƙauyenmu ba. Sai dai lokaci-lokaci yakanzo ya gaishesu.”
“Mahaifinku Aliyu shine mutum na biyu da yake nunamin tausayi bayan kakanku kuma kawu na, dan duk sanda yazo kauyenmu nakan shiga cikin farin ciki matuƙa. Shine mutum na farko da ya fara koyamin karatun boko, yayinda kakanku kuma kawu na malam hamza yake koyan na addini duk da matarsa bataso. Saboda tsabar ƙiyayyar da Hajiya mama kemin a duk sanda naje gidan sai ta saka Halilu ƙanin Aliyu yamin dukan tsiya. Dan haka tun fil azal bama shiri da Halilu sam. Shakuwarmu da Aliyu ta cigaba da faɗaɗa a duk sanda yazo hutu ƙauyen. Tun mutane basu fahimta ba har kowa ya fahimta, dan yazamto duk sanda Aliyu yazo bashi da abokin yawo sai ni, akoda yaushe muna tare can bakin fadama. Dare ne kawai ke sakamu rabuwa. A randa labari yazo kunnen Hajiya Mama kowa yaga tsantsar masifa a ƙauyen nan. Dan haukacewa tai matuƙa taita bala’in da har sai da Babana ya kama Halilu yay masa dukan mutuwa saboda dukana da yayi. In takaice muku ranar ɗan ƙaramin yaƙine ya kusa tashi a ƙauyen mu. Karku manta na faɗa muku babana mutum ne da lamarinsa sai addu’a. Duk da kuma yana nunamin halin ko in kula kowa yasan yana sona. Dan soyayyar mahaifiyatace gaba ɗaya ta dawo kaina. Sam yaki aure, hasalima yayi alwashin tunda Mahaifiyata ta bar duniya babu aure a sanadinsa shima har abada bazai auri wata mace ba, zai karasa rayuwarsa a hakan dan itace ta farko da yataɓa so kuma itace ta ƙarshe.”
“Bayan lafawar komai Hajiya mama ta haramtama Aliyu zuwa ƙauyenmu saboda ni, hakan ya ɗagamin hankali matuƙar gaya. Nayi kuka harda kwanciya ciwo, amma babu abinda ya canja. Haka na haƙura na cigaba da rayuwa a ƙauyenmu cikin halin tsangwama da ƙyara da ƙyama. Kawu Hamza ne kawai nake jin sanyi da sauƙi a garesa. Sai ko babana idan yaso haka. Na kasa samun miji a ƙauyenmu. Dukan sa’annina sunyi aure wasuma sun hayayyafa, kusan dai aure irin nada kuma na mutanen karkara. Duk wanda zaizo da nufin sona sai dai yay yunƙurin lalatamin rayuwa, dan a cewarsu ni ɗin ƴar shege ce. Hakan na matuƙar bani tsoro. yana kuma sakani kukan da babu mai lallashina. Ban kuma shiga tashin hankalin rayuwa da garari ba sai a shekarar da mahaifina ya rasu. Lokacin inada shekaru goma sha tara cif a duniya tamkar yanda Tanee take a yanzun. Duk da ba kulawa yake bani yanda ya kamata ba shi ɗin garkuwa nane. Dan ko a cikin gidanmu shakkarsa nasa a ragamin wani abu. Dama dangin mahaifiyata ba nuna sunada alaƙa dani sukeba. Sun matukar tsanata saboda mahaifiyarsu acewarsu ta gudu ne dan ni, sun kuma rasa ƴar uwarsu dalilin mahaifina. Rayuwa ta ta sake shiga matuƙar garari dan waɗanda suke ɓoye maitarsu akan mutuncina sun fiddosa. Ciki kuwa harda…..”(kuka ya ci ƙarfinta)
Da ƙyar ta iya haɗiyesa saboda ganin yanda su Hibbah ke kuka. Hatta da Yaya Umar duk jarumtarsa kuka yake rurus. Ummi ta cigaba da faɗin, “Harda Halilu. Dan shine ya kaimin hari na ƙarshe har gida a wani dare. Sai dai ALLAH ya kuɓutar dani saboda ihun da nayi har kakana ya fito shi da kawu Hamza (kakanku). Duk da naga wanda ya shogomin ɗin sai ban faɗa ba, nace kawai ban sanshi ba. Bawai dan ina tsoron faɗar bane, kawai dai ba yaune ranar da Halilun ya fara min irin wannan titsiyen ALLAH na kuɓutar dani ba. Na yau ɗinne dai yaso fin na ko yaushe muni. Washe gari malam da kansa yace na dawo kwana ɗakin kusa da shi, hakan ya baƙanta ran hajiya mama taita masifa a ɓoye, dan tana tsananin tsoron malam. Anyi haka da kwana biyu sai ga Aliyu. Bansan yanda zan musalta muku halin dana shiga ba. Sai dai tabbas naci kukan farin cikin ganinsa matuƙa gaya, shi kansa har ƙwalla yayi, sai dai yayi ƙoƙarin ɓoyemin.”
“Babu zato babu tsammani bayan sakkowa massallacin juma’a sai jin an ɗauramin aure da shi kawai nayi. Firgici ya sakani yanke jiki na faɗi a sume sai da aka yayyafamin ruwa. Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya karaɗe gari, yayinda Hajiya mama ta rikice da ihu da kururuwar sam bata yarda ba da wannan haɗin. Babu yanda ta iya dan malam yafi ƙarfinta. Hasalima ana kammala sallar la’asar ya saka Aliyu tattarani da gani sai kayan jikina muka baro ƙauyenmu. Barowar da ban sake komawa ba sai rasuwar malam da kakana data faru kusan lokaci guda. Bazance muku banyi murna da baro ƙauyenmu ba a lokacin, domin kullum hakan shine mafarkina. Nasha aunawa a raina dama na gudu idan har irinsu Halilu sun cigaba da bibiyar mutuncina, sai gashi ALLAH yaymin sutura na barosa tare da igiyar aure da miji ɗan gaske irin mahaifinku.”
“Nayi matuƙar mamaki lokacin da muka shigo garin nan naga Aliyu ya kawoni wani madaidaicin gida mai ɗakuna biyu da kitchen ƙarami sai toilet da rijiya a tsakar gida. Babu komai a gidan sai katifa a ɗaki ɗaya da ƙaramar Wadrobe ɗin kayansa. Ɗayan ɗakin kuma kafet ne malale kawai sai tv babu kujeru. Sai ƴan kayan girki a kitchen ɗin da alamar shike abinci da kansa. Bai barni na huta ba sai da ya zagaya dani lungu da saƙo na gidan, tare da min bayanin komai na amfani. Da kansa yay mana girkin abu mai sauƙi mukaci a ranar, bayan ya yambayeni girki nace ban iya ba. Dan tunda nake ko zuba manja a wuta babu wanda ya taɓa sakani a ƙauyenmu. Aliyu shine ya koyamin girki, shine ya koyan aikin gida, ya sakani islamiyya. Ya kuma cigaba da koyar dani karatun boko. Kamar yanda bai taɓa zama yamin tambaya akan bayan rabuwarmu ba, nima ban taɓa masa tambaya akan ƙin sake dawowarsa ƙauyenmu ba har ALLAH ya albarkacemu da samun ciki. Ya nuna tsantsar murnarsa da farin ciki akan wannan ciki. wadda har ta ban mamaki sosai, amma sai na shanye mamakina nima ina maijin daɗin zanga jinina bayan mahaifina dana rasa.”