TAKUN SAKA 17

“Na cigaba da rainon cikin Muhammad a ƙarƙashin kulawar Aliyu har ya cika watan haihuwa, sai a lokacinne kuma wani baƙo ya taɓa zuwa wajenmu da ga ƙauyenmu. Dan kuwa babu zato babu tsammani sai ga Hajiya mama da Halilu. Cikin farin cikina na nuna murnar ganinsu, sai dai tun a tsakar gida Hajiya mama ta katse murnar tawa ta hanyar daka tsalle ta dire tana kallon cikin jikina. Aliyu da abin nata ya bashi mamaki ya tambayeta ko lafiya. Kai tsaye ta nuna masa ciki da tambayar ina aka samosa?. “Mama ƙyautace da ga ALLAH ya bamu mana tunda jinin ɗanki ne”. Aliyu ya bata amsa kai tsaye dan shi ba mutum bane mai ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana a magana.”
“Cikin daka tsawa tace “A gidan ubanwa ya zama jinina? To idanma zaka dawo hankalinka ka dawo. duka-duka ƙaddararren auren naku watansa takwas kenan ace da wannan tulelen cikin mai kama da shekarre. Sai dai idan ɗan shege ne aka zomaka da shi da ga waje kamar yanda aka samota itama za’a nana maka”. Wannan magana ta tashi hankalin Aliyu dani kaina, ya shiga rantsuwa akan sam ba haka bane ba, amma sam hajiya mama taƙi saurarensa. Hasalima washe gari suka juya ƙauye ita da Halilu. Babu shiri shima Aliyu ya bisu batarema dana sani ba. Dan nima tunda hajiya mama ta ɓunta maganar jingina cikina da bana Aliyu ba sai ciwo yaymin rijif. Ba ƙaramar ƙurace ta tashi akan cikin jikina ba. Har takai da malam yace a jira na haihu sai a san mai gaskiya. Cikin amincin ALLAH kwana goma sha ɗaya dayin wannan al’amari sai ga naƙuda. Batare da ALLAH ya ƙaddaramin shan wahala ba na haifo Muhammad Aminullahi. Wanda tunma yana cikin jininsa daka kallesa kaga Aliyu tamkar yayi kaki ya ajiye. Bakin kowa ya mutu tun daga haihuwar Aliyu, har takai dangin hajiya mama sunzo taron suna, kafinma taron wata tsohuwa tazo ta zauna dani dan malam yace koda wasa kar Aliyu ya kaini ƙauyenmu. Babu kowa a dangin mahaifina da mahaifiyata bayan malam da Halilu. Duk da hajiya mama bataso ba Aliyu yayi bajinta dai-dai karfinsa.”
“Bayan haihuwar Muhammad abubuwa da yawa sun buɗe mana musamman ƙofofin arziƙi. Dan abin tamkar roƙo sai ga alkairai nata shigowa, cikin shekara biyun danai ina shayar da shi harmun canja gida, Aliyu ya sai mota. Wannan arziƙi shine ya sake saka damuwa tsakanina da Hajiya mama. Dan gaba ɗaya ta tashi hankalinta akan bazanci ni kaɗai ba sai Aliyu ya ƙara aure. Shi kuma da yake mutum ne mai taurin tsiya yace bashi da ra’ayin zama da mace fiye da ɗaya yayi kenan dan yanaso na. An buga an buga yaƙi. Ganin fitinar ma tayi yawa sai ya daina zuwa ƙauyen bisa shawarar mahaifinsa. Sai dai kuma an gudu ba’a tsira ba, dan kuwa hajiya mama na ganin an kulleta ta ko ina sai ta canja salo, ta kwantar da kai ta nuna nadama a lokacin da akace mata ina da wani cikin. Da farko malam bai yarda da ita ba, sai da akaja lokaci ina gab da haihuwa bansan yaya akaiba sai ga Halilu da jakar kaya wai yadawo zama da mu zai dinga tsare shago da Aliyu ya buɗe a kasuwa tunda shi aiki baya barinsa zama. Hankalina bai tashi ba, dan ni a tunanina ai yanzu na wuce da duk wani shaiɗancin Halilun na kafin aure na. Dan haka na amshesa hannu bibbiyu na kuma saki jiki da shi. Shima kuma sai ya kwantar da kai yay tamkar babu komai a ransa. A wanann karon ma na haihu lafiya namiji, wanda yaci suna Abubakar, shima dai gaba ɗaya ya kwaso kamanin Aliyu. Tun bayan haihuwar Abubakar Halilu ya fara fiddo min wasu sabbin halaye, sai dai sam baya yarda yayi a gaban Aliyu da Malam ko gaban mutane. Iya ni kaɗai yakemawa sai Muhammad da zaita duka babu gaira babu sabar, hatta da Abubakar na goye bai ƙyale ba. Ko kallon inda yake banayi balle na nuna nasan yanayi ɗin. A haka na sake samun ciki na uku, shima na haifi Umar. A wannan haihuwa kam banjita da daɗi wajen Hajiya mama da danginta ba. Dan ƙiri ƙiri suka dinga kwaɓamin magana na mamaye musu ɗan uwa. Babu mai cin arziƙinsa sai ni da ƴaƴana. Duk alkairan da yake musu da yanzu ya bari komai sai ni. Haka suka dinga tsogumi har sai da abin nan ya sani kuka, sai dai ban yarda na sanarma Aliyu ba dan ba’a gabansa sukai ba. Ina da tsohon cikin Usman ne muka dawo wannan gidan, dan haka lokacin dana haifesa sai yazam ƴan uwa sunzo suna haɗe da tayamu murnar sabon gida. A wannan zuwa ma dai ba daɗin naji ba. Dan maimakon tayani murnar haihuwa sai habaicin ina haihuwa bi da bi ba hutu, wai inayine danna mamaye komai na Aliyu shiyyasa duk sai ƴaƴa maza. A wannan karon kam ɓacin ran dana shiga har sai da takai malam yazo da kansa. Dan gaba ɗaya na sauya harshi Aliyun yama kasa gane kaina. Na tubure masa akan ya ƙara aure kozan sami sassaucin cin kashin nan nasu. Musamman ma Halilu da ya zama mai fuska biyu, a gaban malam ya nuna babu wadda yafi ƙauna da so sama da ni da ƴaƴa na. Dan aurensa ma da aka saka da matar daya samo acan cikin dangin hajiya mama yace nice uwar biki. Nasan a zancen nasa akwai manufa, amma sai na watsar da shi kawai. Malam ya lallasheni da kalamai masu daɗi harna huce komai ya wuce muka koma yanda muke da Aliyu.”
“Hidimar auren Halilu ce ta sake canja komai. Dan kuwa naci matuƙar wahala a lokacin. Komai aka nema sai suce a zo wajena shi da hajiya mama. Ko ɗan kwali ƙin saya sukai balle ƙwayar abinci. Idan nace ma Aliyu yayi yayta faɗa akan ai ya basu kuɗaɗe masu nauyi na hidimar nabar damunsa. Haka na shiga tsaka mai wuya a tsakanin. Duk ɗan abinda nake samu na haihuwa na ƙwaƙule nai hidimar Halilu dan nasan bazan taɓa fita a garesuba idan ma na nuna Aliyu baiyiba. to ashe yin danayi ma ba mafita bace dan sabon zancene ya tashi akan eh da gaske na mamaye komai ɗin. Bani da abin cewa dan haka nai musu shiru akai biki aka ƙare lafiya amarya ta tare a tsohon gidanmu da muka taso, dan da hajiya mama ta matsa anan zasu zauna tare damu tunda akwai ɗakuna. Aliyu yace sam bai yarda da wannan gwajin gwalar ba. Salon haɗa rikici. indama kowa da part nashine sai ya amince. Amma flat ɗaya ne a gidan iya na iyalinsa sai BQ. ita kuma tace Halilu bazai zauna BQ da matarsa ba ni ina ciki inacin daɗi. Bayan ƙurar data tashi ta lafa dan malam ya tsawatar suka yarda Halilu ya zauna acan. Sai dai kuma duk wani abu da zasuci acan bazai saya ba, sai dai yazo nan gidan direct ya ɗiba koda kuwa gishiri ne. Ban taɓa faɗama Aliyu ba sai da ya gani da idonsa. ranar naga asalin faɗansa. Dan murje ido yay yayma Halilu tas har nima na samu rabona a ciki. Wata sabuwar ƙurar ta sake tashi akan wanann magana, har takai Hajiya Mama ta nema Aliyu ya sallami Halilu da ga kasuwa shima ya rinƙa juya na kansa, kokuma su dinga raba ribar duk abinda aka tara a ƙarshen shekara. Ƙince musu komai yay akan hakan, yaƙi kuma bashi kuɗin ya ƙi sallamarsa. Shine dalilin da yasa Halilu ke ganin nice na hana shi da hajiya mama. Duk da kuwa a shekarar Aliyu ya biya mata hajji ita da malam da shi sukaje. Wannan karon na samu hutu, dan tun Usman babu wani labari. Hakan yamin daɗi, dan na samu sauƙin wasu fituntunin, duk da shi kullum mahaifinku cikin tambayata yake wai yaji shiru, danshi mutum ne mai son yara matuƙa. Shiyyasa kuka kasance ƴan gata a wajensa. Komai na buƙatunku baya sakaci da shi komai ƙanƙantarsa. Wanann yasa ake ganin ya lalace a kanmu. Shekara na zagayowa ya sake biya mana hajji ni da shi mukaje. Muna dawowa ya sayamin mota tare da danƙamin wani ƙaramin gida yace na zuba haya, sai jari na sana’a.”