TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAKA 17

        “Musalta muku halin da na shiga awanan tsakanin bazai musaltu ba. Dan saida na gwammace da bai baninba. Dama akan tafiyarmu hajji ansha dabi hajiya mama tace bata yardaba sai dai ya biya musu shi da Halilu. Bansan miyazo kan Halilu a lokacinba shi ya nuna goyon bayan naje, harda nunama hajiya mama bayajin daɗin abinda takemin, ai koba komai na haihu da Aliyu ya kamata a ɗagamin ƙafa zuwa yanzun. Hakan da yayi ya saka malam jin daɗi. Tun daga sannan ma suka koma ɗasawa dan shi malam ya yarda da tuban Halilu ɗari bisa dari. A cikin wannan tarnaƙin na samu cikin Ammar. Wanda yazomin da matuƙar wahala da jigatuwa. Bani kaɗaiba hatta mahaifinku yaji a jikinsa kafin ALLAH ya sa na haihu ko nace akaimin cs aka cirosa. Babanku na ɗaukarsa ya gansa ƙato da shi ga kamanninsa sak nashi tako ina sai cewa yay “Lallai kaci suna Aliyu gadanga kodan wahalar daka bama matata”. Hakan ya sani murmushi, dan har cikin raina naji daɗin sunansa da zai maimaitamin cikin ƴaƴana. Ammar yaci suna Aliyu, a wannan sunan kam kowa ƙin zuwamin yayi, ƙiri-ƙiri suka nunamin jin zafina da suke, sai malam da Halilu da canjin nasa keta bani mamaki ne sukaita komai. Dama dangina nidai wani bai taɓa nemana ba, garama da maganar siyamin mota da gida ta fito su kawu Bello sunzo wai tayani murna. Bandamu da a yanda sukazo min ɗinba nai musu alkairi Aliyu yay musu suka koma. Bayan haihuwar Ammar babu jimawa Aliyu ya fara ciwo a tsaitsaye, inata fama da shi yaje asibiti yaƙi, har dai ta kaisa da kwanciya sannan ya yarda mukaje. A gwajin farko aka gano yanada ciwon ƙoda, yama daɗe a jikinsa dan harya harbi hantar sa. Hankalinmu ya tashi amma sai yayta kwantar mana akan shi ya samu sauƙi. Na jigatu a wannan tsakanin, daga zuciya har gangar jiki. Ban samu nutsuwa ba sai da jikin yay sauƙi ya koma kan harkokinsa. Ashe dauriya kawai yakeyi dan ganin hankalina ya kwanta. Haka mukaita lallaɓawa wataran ya kwanta kwana biyu ya mike ya cigaba da hidimarsa harna yaye Ammar. A watan dana yaye Ammar a watan ciwo ya kai Aliyu ƙasa, har takaisa ga kwanciyar jiyya. Dole Hajiya mama da Malam suka dawo gidan nan da zama muna kula da shi tare dan abin yayi tsanani. Da yake kwana ya ƙare kwanakinsa goma sha bakwai kacal a kwance ALLAH ya amshi abinsa. Mun shiga gigita, mun shiga ruɗani irin wanda bama zai musaltu ba. Dan har wata ƙaramar mahaikaciya na koma a tsakanin nan, sai da malam ya dinga min addu’a na dawo hayyacina. Hajiya mama taso a tafi ƙauye dani nayi zaman takaba. malam yace a’a a ɗakina zanyi. Ta dawo cewar yara su dawo hannunta. Nanma yace a’a ni zan cigaba da rike abina. Duk ta inda ta ɓullo sai ya goce, ganin babu mafita ta haƙura na cigaba da takaba. Su kuma suka koma ƙauye. Acikin zaman takabanne na fara laulayin cikin da ni nasan ina maƙale da abina tun cikin satin da Aliyu ya rasu, sai dai yana bayyana ga kowa Hajiya mama tace bana Aliyu bane…………..✍

*_Bara mu dakata anan, naga page ɗin nata ƙara tsaho????????????_*

   ZAFAFA KARO NA FARKO

SUNAYEN SU:

1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL

2_KAI MIN HALACCI

NA MISS XOXO

3_BURI DAYA

NA MAMUH GEE

4_DAURIN BOYE

NA SAFIYYAH HUGUMA

5_SAUYIN KADDARA

NA HAFSAT RANO

    DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500

SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU

1-DAURIN GORO

NA HAFSAT RANO

2-ALKAWARIN ALLAH NA

SAFIYYAH HUGUMA

3_QAUNAR MU

NA MAMH GEE

4_IGIYAR ZATO 

NA MSS XOXO

5_WUTSIYAR RAKUMI

NA BILLYN ABDULL.

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500.

SAI ZAFAFA TAKU NA 3,

1_MIN QALB

NA MAMUH GEE

2_SARAN BOYE 

NA BILLYN ABDULL

3_KIBIYAR AJALI.

NA MISS XOXO

4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA

NA HAFSAT RANO

5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU

NA SAFIYYAH HUGUMA

DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)

SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU.

1-ALKIBLA

NA SAFIYYAH HUGUMA

2_DALAAL 

NA MISS XOXO

3_UBAYD MALEEK

NA MAMUH GEE

4_MABUDIN ZUCIYA

NA HAFSAT RANO

5_MAKAUNIYAR KADDARA 

NA BILLYN ABDULL 

DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)

SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS)

1-SO DA ZUCIYA

NA MSS XOXO

2-TAKUN SAAKA

NA BILLYN ABDULL

3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO

4_DAB’IZAR ZUCIYA

NA SAFIYYAH HUGUMA

5-DEEN MALEEK 

NA MAMUH GEE

DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500.

YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:

ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH..

BANK NAME: KEYSTONE BANK

SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:  

08184017082

IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA: 

09134848107

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button