TAKUN SAKA 18

Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, sai faman sharar hawaye kawai sukeyi. Hibbah ta fara miƙewa taje ta rungume Ummi, sai Yaya Ammar ma yaje ya haɗasu su biyun ya rungume. Hakan yasa suma sauran duka suka miƙe sukaje suka rungumesu baki ɗaya. Idan ka gansu dole ne su baka sha’awa, su baka tausayi, su kuma birgeka.
Sun ɗau tsahon lokaci a haka kafin su koma su zauna suna mai kallon Umminsu cike da tausayinta da tsananin soyayyarta. Yayinda Hibbah duk ta fisu jin kewar mahaifinsu da ko cikinta baisan ya bari ba. Duk da kuwa yayi ƙwaɗayin a haifa masa ɗiya mace matuƙa ALLAH bai ƙaddara zai gani ba.
“Ummin mu ai kece ZAKIN, SARAUNIYAR DUNIYA TA MATA”. Ammar ya faɗa cike da zolaya yana share hawaye. A tare suka sanya dariyar da basuyi niyya ba. Dan yanda Ammar ɗin ya faɗa yana salute na Ummi dole ne ya baka dariya.
Duk yanda sukaso ɗakko maganar Ummi ta hanasu, sai ma ta shiga jansu da wata hirar cike da tsokana suna kwasar dariya. Gaba ɗaya sun shagala da batun fita aiki da makaranta, balle kuma breakfast ɗin da sukai zaman yi. Kafin su farga sai kiran sallar zuhur sukaji. Nanfa aka shiga jaje da sallami. Ummi kuwa ta dinga musu dariya wai yau itace gwamnatin da sukaima aiki ai.
Suma dariyar sukeyi cike da nishaɗin ganinta cikin farin ciki, da ga karshe kowa yabi hanyar data dace wajen neman excuse a wajen aikinsa. Yaya Umar dama kasuwa ce baida matsala. Su Hibbah kuwa makaranta ce. Haka suka ƙarasa wannan yinin a tare, salla kawai ke fiddasu ƙofar gida har dare. Da za’a kwanta ma Hibbah ta maƙale tare da Ummi zata kwana.
*_WASHE GARI_*
Yau da sassafe duk sukai shirin fita aiki kasancewar jiya basu fita ba. Kamar yanda suka saba kullum yanzu suna ɗan fita da kayansu masu muhimmanci zuwa sabon gida saboda masu gidan yau ma sai da Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka ciccika booth ɗin mota sanan suka fice. Ammar kuna ya dauka Hibbah a mashin shima suka wuce makaranta. Yayinda suka bar Ummi na cigaba da haɗe musu abubuwansu masu muhimmanci da suka rage.
*________________*
Kwanakin biki sun cigaba da gabatowa gab, dan yau gashi har an kawo lefen Hibbah gidan. Lefe ne na ƴar gata da ya bama kowa mamaki. Dan ƙiri-ƙiri yaran Abba suka shiga nuna hassadarsu da baƙin ciki. Ita kanta Hajiya mama da Momy tunma baƙin na nan suke yadda habaice-habaice dan zubarda mutunci. Ita dai Ummi komai batace ba. Dama ta gayyato ƙawayenta iyayen su Zahidah sai matan Sheikh Aliy su mama Jiddah???? da suka amshi lefen. Dama hidimar tarbar baƙi duk da ga gidan Sheikh Aliyun aka yota. Komai sai gani su Hajiya mama sukai ana shigo da shi gidan. Ga makwafta sunyi hallaci duk sun shigo ana komai da su.
Lefe kam yayi sai sam barka. dan Muhammad Shuraim ya kankaroma Hibbarmu mutunci????????. Ita tanama makaranta sai da ta dawone taga akwatina da kayan su sweets biscuits da sauransu. Sosai abin ya bata mamaki har tana ƙorafin kamar hauka. Ita batason fariya. Ai basai ya nuna sunada shi ba.
“Oh ni Ali, yau naga uwar kutsugu. Danma kin samu ya kankaro miki mutunci zaki mana iyayi a gida”. Ammar ya faɗa yana dalla mata harara. Itama harar ta dalla masa tana murguɗa baki. “To karya kankaro mutuncin mana. Wayace masa shi ake jira ya kankaro”.
“Ni wlhy ina so da fatan ganin randa wanann bakin naki na akku zai mutu murus auta.”
“Ai bazaka gani ɗin ba kuwa Yaya Ammar.”
“Hhhhh ALLAH dai ya kaimu ranar shiga labour room, kafin sannan ma nanda kwana goma sha bakwai kacal nasan ya gama mutuwa kodan rabuwa da ni da Ummi. Ayye mama ayye mama, mamaye iye, ayye mama labo labo, mamaye iye. Da aure yana raka aure, mamaye iye, dana biki mun tafi tare. Mamye iye, ko tuƙin tuwo ƙya koya, mamaye iya, har damun fura ƙya koya………”
Kuka Hibbah ta fashe da shi da faɗin, “Ummi kin gansa ko. Wlhy nama fasa dan babu inda zanje to”.
Da farko dariya Ummi da su Yaya Muhammad da suka shigo keyi, sai da sukaga abin nata da gaske ne sai kuma duk jikinsu yay sanyi. Dama su kansu dauriya kawai sukeyi. Dan tun shigowarsu sukaci karo da akwatinan sai zukatansu suka raunana. Suna matukar son Hibbah, gashi aure zai rabasu rana tsaka. Ita kanta Ummi wani lokacin har tambayar kanta take wai miyasa ma ta amince aima Hibbah aure yanzun ne. Itakam bataso a rabata da ɗiyarta. Zuciyarta kan gaya mata su waɗanda ƴayanta maza zasu auro fa? Da ta tuna hakan kuma sai tai shiru ta miƙa wuya.
Ɗaki Ammar ya wuce yana sharar hawaye, dan dama komai da yakeyi dauriya ce kawai. Da gudu Hibbah ta tashi tabi bayansa ta rungumesa. Sai kawai suka fashe da kuka a tare. Duk yanda su Yaya Usman sukaso daurewa hakan ya gagara, suma sai gasu suna share ƙwallan a kaikaice. Saurin barin falon Ummi tai, batasan yaya suka ƙare ba sai da ta fito bayan sallar isha’i ta samesu suna kallo ball Hibbah da Ammar na gaddama harda jefama juna filos tamkar basune suka gama shan kuka ba ɗazun.
Washe gari bayan wucewar su Yaya Muhammad aiki aka miƙa kayan nasu auren gidajen matansu batare da sanin su Abba ba. Dan daga gidan Sheikh Aliy aka ɗauka. Hibbah ce kawai taje aka kai da ita ko ina. Dan haka ranar bataje makaranta ba. Sai da yamma liƙis ta shigo gidan a gajiye, ga ciwon kai. Sama-sama ta gaida Ummi ta shige ɗakinta acewarta zata watsa ruwa.
Tana fitowa wankan ta tsinkayo muryar Ummi na kwala mata kira.
“Tanee! Tanee!!” muryar Ummi dake ƙwala mata kira da ga falo ta cigaba da shiga kunnuwanta. Amsawa tai cikin saka kaya sauri-sauri sanann ta fito. Ganin Ummi zaune tare da Isma’il ya sata ƙalaro fara’ar dole ta yafama kanta. “Uhm su Yaya Isma’il ne yau a gidan namu? Yaushe a gari inji maƙi baƙo?”.
Guntun murmushi ya saki dai-dai yana ɗagowa ya kalleta. “Auta nifa hausar nan taki cikin hausa na dulmiyar dani da yawa.”
“Tofa, abinma ƴar zolayace kenan Yaya Isma’il. Ykk ya Abba da Dubai?”.
“Abba yana lafiya. Nima kuma haka. Dubai kam tana can mun baro musu abinsu, mun dawo ƙasar gado”.
Dariya Ummi da Hibbah sukai a lokaci guda. Yayinda Ummi ta ɗora da faɗin, “Yau kusan sati kenan inata jajen rashin dawowarka. Ga bikin ƴan uwanka nata matsowa ko faɗa maka ba ai ba”.
“Biki kuma Ummi? Badai su Yaya Muhammad bane zasu angwance?”.
“Aiko sune Isma’il, komai yazo ne a ƙurarren lokaci. Su duka huɗun ne insha ALLAH sai Tanee kuma”.
A take alamar shock ta bayyana saman fuskar Isma’il har Ummi da Hibbah suka lura. Da sauri ya ce, “Ummi Muhibbat kike nufi kowa?”.
“Eh ita kuwa Isma’il. Muma dai haka abin yazo mana tamkar haɓo”.
Duk yanda yaso ɓoye ɗacin da ke tattare da muryarsa kasawa yay. “Ummi dama akwai maganar aure akan Muhibbat kenan?”.
Ummi da yanayin Isma’il ɗin ya raba ma hankali biyu tace, “A’a Isma’il. Cikin kwanakin nan dai aka fara. Da yake kuma ALLAH yasa abin a kusa yake sai gashi har an kammala magana. Dan gaba ɗaya bikin yau saura kwana goma sha uku ne”.
“A…ALLAH sarki, UBANGIJI ALLAH ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Ummi. Dama zan wuce ne nace bara na leƙoku. Inga bara inje zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo. Ga tsarabarki nan ke da Muhibbat”.