TAKUN SAKA 18

A yanda yake maganar ne ya saka wutar kan Ummi da Hibbah ɗaukewa. Sukai tsit a falon harya fice basu iya furta komai ba. Sai kallon juna da sukai suka kuma sake maida dubansu ga ƙofar tamkar zasuga Isma’il ɗin tsaye bai tafi ba.
“Ummi kamarfa ransa ya ɓaci?”.
“Nima abinda ya bani mamaki kenan Tanee. Ko maganar aurenku ce ta ɓata ransa?”.
“To Ummi mizai bata masa rai anan? Maybe dai akwai abinda ke damunsa daban ba wannan ba”. Hibbah ta ƙare maganar tana sakkowa da jawo ledar daya ce tasunce. Turarrukane a ciki da make-up box ƙarami mai ƙyau. Sai takalmi da jakka suma masu ƙyau kala biyu. Na Ummi da nata.
Tana tsaka da ƙoɗa ƙyawun kayan Yaya Muhammad ya shigo. Ummi ce kawai ta samu damar masa sannu, Hibbah kam sam hankalinta baya wajensa. Sai da ya kai zaune yake faɗin, “Ummi lafiya kuwa? Miya faru da Isma’il?”.
“Wlhy ban saniba Muhammad, nima man mamakin yanayin nasa ne ya sani zaman jugum nan.” (gaba daya ta kwashe yanda sukai ta bashi labari).
“Tofa, anya kuwa Ummi Isma’il ba son Hibbah yake ba?”
Da sauri Hibbah ta juyo ta kalli Yayan nata. “Yaya so kuma? Ni?”
“Tabbas auta. Dama zuciyata ta jima tana rayamin Isma’il dan ke yake tare da mu. Dan take-takensa gaba ɗaya sun nuna akwai soyayyarki a zuciyarsa. Shiyyasa naso ace yana nan maganar nan ta taso na aurenkin nan. Koba komai ni hankalina ma zaifi kwanciya da Isma’il ɗin fiye da shi Shuraim ɗin nan. Duk da shima dai babu wani aibu tare da shi dan yau ɗin nanma sai da na sake samun bayanan binciken da na saka akaimin a kansa bayan waɗan can na baya”.
Nannauyan numfashi Ummi taja, gaba ɗaya zuciyarta ta dagule. Dan harga ALLAH tana jin son Isma’il matsayin siriki a gareta. Sai dai kuma ƙaddara ta rigada ta riga fata. Dan babu ta yadda za’a gyara abinda tun farko aka ɓata. Shima harda laifinsa da bai fito ya nuna ba, a yanzu kuma basu da hurumin rusa maganar Shuraim inba so suke su kasance ƙananun mutane ba kuma.
Ita dai Hibbah ko a jikinta. Tama cigaba da harkar gabanta ne dan kallon yaya take masa har cikin zuciya.
★★★
Kwanaki uku Isma’il bai sake dawowa gidanba. Hakan duk sai yabi ya dami Ummi harta ɗauka waya ta kirasa akan tana son ganinsa. Baiko musa ba sai gashi yazo da hantsi. Lokacin su Hibbah duk sun fice sai ita kaɗai.
Ummi tanada dabaru sosai na iya sarrafa mutum bisa ƙyaƙyƙyawar hanya. Shiyyasa ta tarbiyanci ƴaƴanta da tarbiya mai ƙyau da ke bama kowa mamaki da yaba ƙoƙarin ta. Duk da Isma’il yazo mata ransa a cinkushe cikin hikima da dabarun da ALLAH ya bata ta bi da shi da nasiha. Cikin ƙankanin lokaci sai gashi yayi laushi, ya kuma gane cewar laifinsa ne da yabar zancem a ransa bai furtaba.
“Ummi nagode matuƙa da gaske. Kiyi haƙuri ban tashi da uwa ba shiyyasa abubuwa da yawa bana ganesu kai tsaye sai sun ƙure min. Idan kuma ba’an fahimtar dani bane haka zanta kallonsu a yanda na ɗauka. Bazan boye miki ba ina matuƙar jin daɗin kasancewa da ke. Kuma ina miki kallo ne irin na uwa wlhy. Shiyyasa kikaga ko yaushe ina nane da ke. ALLAH ya sanya albarka a auren Hibbah na haƙura. Amma tabbas ina sonta da ƙaunarta. Wasu kuma nagartattun halayenki ne da nata suka jani ga hakan abinda ban taɓa tsintar kaina a ciki ba. Amma dan ALLAH koda wataran inaso ki cigaba da tuna hakan. Kuma kamar yanda kika fahimtar dani wanann bazai zama ƙarshen zumincinmu ba. Zan cigaba da kasancewa da ku a koda yaushe tamkar da. Zanje na nema yan uwana su Yaya Muhammad mu cigaba da hidimar biki”.
“Alhmdllh naji daɗin hakan Isma’il, ALLAH yay maka albarka. Kaima ALLAH ya baka wadda tafi Tanee ɗin”.
Murmushi ya saki mai sanyi laɓɓansa na ɗan motsawa alamar amsawa. da ga haka ya saki jiki da Ummi suka cigaba da tattaunawa akan hidimar bikin. Bata ɓoye masa zancen barinsu gidan ba da planning ɗinsu akan rusa auren ƴaƴan Abba da yaranta. Shima kansa yaji daɗin haka. Ya kuma tabbatar mata zai bada muhimmiyar gudun mawa. Da ga haka yay mata sallama ya tafi.
*___________________________*
Alhamdulillahi, akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, shirin biki kam da gaske ya ɗau harama. Dan kuwa baƙi harsun fara sauka a gidan musamman na ɓangaren momy matar Abba. Hakama dangin hajiya mama sun fara sauka. A ɓangaren Ummi ne dai babu ko kare da yazo har yanzu. Ko’a jikinta dan dama batasa rai ba. Mutanen arziƙi ma da zata tara anan a cewarta sun wadaceta.
A ɓangaren amaren su Yaya Umar na ɓoye har sun jajje sunyi jere a sabon gidansu. yayinda suma anan su hajiya mama suna shirin zuwa suyi nasu jeren na ƴaƴansu a gidajen Hayar da Abban ya kama.
Itama dai Hibbah kayan nata jeren har sun isa gidanta. Dan kuwa yayunta sun haɗa ƙarfi da ƙarfe da taimakon Isma’il sun mata kaya ƴan gaske na ƴar gata. Dan data ga kayan sai kawai ta fashe da kuka dan daɗi. Ita kanta Ummi da ta gani sai da ta koka a ɓoye. Musamman da ƴan jere suka dawo cike da farin cikin tarbar da suka samu da kuma ƙyawun gidan na Hibbah.
Hibbah Amarya kuwa da su Zahidah amaren su Yaya Usman Ummi da Mama Jiddah ce ke gyaresu da ingantattun magungunan sanyi harda amaryar Yaya Umar. Sai ingantaccen tsumi da duk ta sami iliminsu da ga Sheikh Aliyn ta (karku manta masanin sirrin magunguna ne????). Dan hatta maganin sanyin ma shine ya haɗama su Hibbah da kansa. Sai Haɗaɗɗun kayan gyaran fata na dilka da ƙamshi da Mama Maimoon uwargidan malam ke gyaresu da su itama. Ta ko ina Ummi dai ta zama ƴar kallo.
Gaba ɗaya Hibbah ta tattara batun wasu ƴan sanda da wani master can???? ta watsar, dan kasancewar su waje guda da su Hafsat ya mantar da ita komai. Iyakarsu susha shaftarsu, kowa idan nata angon ya kirata ta koma gefe tasha soyayya. To ita Hibbah ma bazatace soyayyar take sha ba, dan sam Shuraim bai cika damuwa da kiranta a waya ba. Yafi tura mata text massege na sonjin lafiyarta kai tsaye. Ita kuma jan aji yasa itama bata kiran nasa balle nuna damuwarta da hakan garesa. ko sau ɗaya ma bata taɓa ƙorafi ba.
★★★
A yau laraba aka saka dukkan amaren a lalle. Dan kamar yanda aka saka su Ameerah da Hibbah anan gidansu, haka aka saka su Zahidah a nasu gidajen batare da duk wanda ke zagaye da su yasan su waye angunan ba. An dai san ana biki, hatta da Momy da Hajiya mama sunsani tunda anguwa ɗaya ne layi ɗaya. Sai dai basusan anguna ba basu kuma damu da sani ba tunda ba wani mu’amula mai karfi ce a tsakaninsu ba. Hasalima sun tsanesu saboda suna huɗɗa da Ummi. Ko gidan sukazo aka gamu da ƙyar suke amsa gaisuwarsu.
Yau akai kamu da ya kayatar matuƙa anan harabar gidan. Dan ƙarya sosai momy ta nuna ma ƙawayenta data tara cike da gida da danginta. Sai dai kuma koda anguna sukazo fili bisa gayyatar da akai musu sai suka ƙare da bama autarsu kulawa ta musamman. Dan har liƙeta sukai da kuɗaɗe sanda masu kiɗan ƙwarya ke bugawa. Nanfa ƙananun magana suka fara tashi, zukatan su Ameerah fal baƙin ciki da takaici. ji suke wata muguwar tsanar Hibbah na sake shigarsu matuƙa, amma dai duk sun danne a zukata bisa huɗubar iyayensu akan shirinsu.
Oho su Yaya Abubakar ma basusan sunai ba. Su dai kawai burinsu autarsu tayi farin ciki, tafi kuma kowa. Burin nasu kuwa ya cika. Dan ta haska haskawa mai tsayawa a rai duk da ango baizo ba danginsa sunzo ansha shagali da su.