TAKUN SAKA 19

*_Typing????_**_Chapter Nineteen_*
………..Kamar yanda suka saka ɗaurin aure bayan sakkowa sallar juma’a su Ummi basu canja ba. Gida ya gama cika da dangin Momy da na Hajiya mama anata hidimar girki. Sai wasu tsiraru da ga abokan arziƙin Ummi na nan anguwa dana nesa.
Anguna kam suna can a gidan da suka samu aro anan anguwar da abokansu. Sai dai tunda safe sun shigo sun gaida Umminsu. Tare da sake lallashin ƴar ƙanwarsu Hibbah da duk tabi ta takura kanta. Zazzaɓin nata yama sauka tunda safe amma duk ta zama wata kalar tausayi. Magana kaɗan sai ta kama hawaye. Ga ƙawayenta na secondary cike da ɗaki amma duk ta ƙi sakewa. Sai faman shaƙiyanci suke mata ta kasa maida murtani dan bakin ya mutu murus.
Kusan sha ɗaya wata ƙawar Ummi ta shigo ta sata tashi dole tai wanka. Mai kwalliya ta shigo tai mata dai-dai misali dan da farko ma catai bataso sai da Ummi tai magana. Itama taci gayunta ɗas tamkar wata ƴar talatin. Dan sam Ummi bata da ƙiba, ALLAH yayi mata jiki mai ƙyau, shiyyasa da yawan mutane idan akace itace ta haifa su Yaya Muhammad sukan musa, inba ka nutsu wajen kallon fuskarta ba sai ka ɗauka yayarsu ce kawai.
Amarya Hibbah ta fito ras abinta, tamkar ka saceta ka gudu. Ƙawayenta nata tsokanarta akan gaskiya ya kamata a ɗauka hoto a turama ango. Banza tai musu dan ita sai ma yanzu ta tuna da wani ango. Tun jiya damuwarta kawai rabuwa da ahalinta batashi take ba. Ga shi tanajin kewar su Zahidah da babu dama suzo nan suma suna gidajen iyayensu.
A ɓangaren amare su Ameera ma kowacce ta ɗau kwalliya ta gani kasheni, da ka gansu kaga amare kam dan anata zuba iyayi da gwalli. Su barin gidan ma ko’a jikinsu suke jinsa. Ga ƙawayensu sun zagayesu sai taɓara da zancen banza suke zubawa suna sheƙa dariya.
Ƙarfe sha biyu da kusan kwata anguna suka shigo gidan cikin kwalliyar fararen shaddoji tas iri ɗaya. Hatta da Ammar irin kayan ya saka shima. Idan ba’a faɗa ba sai ka ɗauka shima angon ne. Guɗa mata da ke kai kawon girki a tsakar gida suka shiga musu. Kowa na yaba ƙyawun nasu da yima mahaifinsu addu’a da babu rabon ya ga wannan rana.
Ummi da ƙawayenta na zaune a falo suka shigo. Tai sagade tana kallonsu idanunta na cika da ƙwalla. Tanaji a ranta inama ace Aliyu na raye wannan rana…… Durƙusawar da sukazo gabanta sukai duka ne ya katse tunaninta. Tasa hannu ta share ƙwallar da suka taru mata a ido tare da kai hannu ta dafa kan Yaya Usman da ke kusa da ita. Sai kawai ta fashe da kuka. Har rige-rigen matsawa suke gabanta kowa ya riƙe hannunta idanunsu na cikowa da ƙwallan suma.
Sosai abin ya birge mutane ya kuma basu tausayi. Ummi ta shiga kwarara musu addu’oi da sanya albarka ana amsawa da amin. Kafin a kira Hibbah itama mai hoto yay musu. Itama kanta sai da tai hawayen jin daɗin ganin ƴan uwanta kamar ka sacesu ka gudu dan ƙyawun da sukayi. Sai dai tanajin ɗacin kasancewar su Amlah matsayin matansu bayan su Zahidah.
Suna tsaka da hotunan kira ya shigo wayar Hibba. Tayi ƙoƙarin sharewa aka sake kira. Yaya Muhammad dake kusa da ita ya ɗauka wayar ya duba. Ganin Shuraim ke kiran nata ne ya sashi hararta yana miƙa mata. “Auta bana son rashin ji fa. Maza kije da ga waje sai ki ɗaga”.
Kanta kawai ta ɗaga masa. Tare da tashi tabi ta kitchen ɗinsu ta zagaya baya domin kiran Shuraim ɗin……
“Yauwa A.G zamu iya magana yanzu na fito”.
Muryar Abba ta saka Hibbah saurin dakatawa a ƴar barandar kitchen ɗin nasu. Abu biyu ne yaja hankalinta ga Abban. Na farko yanda yake tsaye a laɓe wajen tamkar wani tsohon munafuki, na biyu sunan A.G da taji ya ambata. Wanda inhar hasashenta yayi dai-dai sunan dattijon jami’in nan haka yake shima A.G. Maganar Abba ta sake katse tunaninta.
“A.G nawa, kasan mutunuyar taka tana nan tana jira kazo ka saceni ni da duk masu hannu a ɗaurama yayunta aure da ƴaƴana.”
Batajin mi ake faɗa da ga can, sai dai yanda Abba ya tuntsure da dariya ne ya saka zuciyarta tsargawa duk da batasan wane A.G ɗin ba. Abba ya ciga da faɗin, “Inaga zan fito yanzun nan kuwa insha ALLAH, dama munyi shirin wucewa wajen ɗaurin auren ne. To amma su zan barsu su wuce kai kuma mu haɗu a gidan hutuna muyi magana”.
Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake, tai saurin leka bayanta. Ganin hankalin yayunta da su Ummi duk yana kan yin hoton ya sata saurin jan ƙofar kitchen ɗin tayo waje. Bayan Abba da ya bar wajen tabi da sauri. Kasancewar da sanda yake tafiya saboda kafarsa da bata gama warkewa ba yasa Hibbah cin masa, sai dai a sace take binsa yanda bazai gane ba. Suna gab da fita ta ɓarauniyar ƙofar da ke bayan ɗakunan su Abba taci karo da hijjab ɗin wata mata dake alwala a fanfo. Dauka tai ta saka, tai saurin bin ta gate ta fice batare da an ganeta ba dan harda nikaf. Cikin sa’a ta cimma Abbah ta baya saboda harda gudu ta haɗa duk da tarin mutane dake shirin tafiya ɗaurin aure a ƙofar gidan nasu. Ganin Abban ya shiga wata baƙar mota dake fake a barauniyar ƙofar tasu itama tai azamar tare mai napep.
“Malam dan ALLAH motar can nakeso kabi, amma banason ya fahimci shi ɗin muke bi Please”.
“Babu damuwa hajiya, amma kenan kuɗinki zasu kasance masu nauyi fa?”.
Batare da tamaji abinda yace ba tace, “Babu damuwa muje”.
Kasancewar mai napep da alama kwararren matuki ne ya dinga bin Abba abaya ta yanda bazai iya fahimta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso wata anguwa mai ƙarancin hayaniyar mutane. Da alama sabuwar anguwa ce, dan ga uncompleted buildings nan bar-katai. Sai dai kasancewar inda Abba ya faka motar a farko-fatkon anguwar ne sai ya zama wajen yayi ɗan rukunin gidajen da aka kammala. Tun a titin ta sauka. Ta dubi mai napep ɗin cikin raba hankalinta biyu. “Dan ALLAH ka jirani nan bazan jimaba zan fito. na maka alƙawarin ko nawa ka bukata zan baka”.
Cikin farin ciki da tunanin yayi babban kamu yace, “Babu damuwa hajjaju a fito lafiya”.
Gaba Hibba tai batare data amsashi ba. Ta bi ta bayan gidan inda take addu’a da fatan samun koda karamar hanya ce da zata shiga gidan. Dan Abba na shigewa aka rufe gate ɗin. Sam babu wani hanya data samu, dan haka tai azamar sake dawowa ta gaban gidan zuciyarta na ayyana mata wata dabara. Gate ɗin ta ƙwanƙwasa kaɗan tana waige-waigen bayanta da addu’ar dacewa. Batare da zaton anjita ba taji an buɗe gate ɗin. Tai saurin kallon wajen tana jan numfashi. “Barka da rana”. Ta faɗa cikin matukar kashe murya.
Kallon sama da ƙasa mai gadin yay mata, kafin yace wani abu tai azamar faɗin, “Ni baƙuwar Alhaji ce”.
Maigadi yay ɗan shiru alamar tunani. kafin yace, “Amma hajjaju idan Alhaji zaiyi baƙuwa yakan sanar min, yanzu ko bai faɗa ba ya shige duk da naga kamar cikin sauri yake”.
Cikin ƙara ƙasa da murya Hibba tace, “Ka bama kanka amsa kenan, saurin nasane yasa bai faɗa maka ba inaga. Amma bara na kira maka shi zai fi…..”
Da sauri maigadi yace, “A’a hajiya bama sai anyi haka ba. Nasan inba da sanin Alhaji ba babu wani mahaluki kam da zaizo nan. Bismillah”.
Ya kai karshen maganar yana matsawa ya bata hanya. Wani shegen ajiyar zuciya Hibba taja tana ƙoƙarin haɗiye busashen yawun da ya daskare mata a baki tana ƙoƙarin shigewa.