TAKUN SAKA 19

“A fito lafiya hajjajuuu”.
Maigadin ya faɗa cike da shaƙiyanci.
★★★★
A ɓangaren su Yaya Muhammad kam sun cigaba da hotonsu da tunanin Hibbah nacan na waya da Shuraim ne. Sunyi hotuna sosai da jama’ar da ke a sashen na Ummi kafin su fito domin tafiya massallaci karsu rasa salla. Kusan tare suka fito da gayyar su Kawu Hannafi da ƙannen Momy da yayunta.
Cikin tsari gayyar motocin ɗaurin aure suka bar anguwar batare da kowa ya farga babu Abba a tafiyar ba. Yayinda aka bar mata na cigaba da himar abinci da shagali a cikin gida. Sun isa massallacin juma’a gab da za’a fara khuɗuba. Kamar yanda aka tanadar musu gaba saboda za’a ɗaura aure duk aka basu hanya suka shige. Sai da suka nutsu waje guda Sheikh Aliy ya fara gabatar da khuɗuba mai taɓa zuciya akan kashe-kashen dake faruwa a ƙasar nan na zalunci. Tare da jan hankalin hukuma da gwamnati akan sake jajircewa. Hakama jama’ar gari ba zama zasuyi kallon gwamnati da hukumaba suma. Dolene a miƙe da addu’a kuma kowa ya zama jami’in sirri akan abinda bai gamsu da shi ba. Sosai khuɗuba tai tasiri a zukatan bayin ALLAH. Da ga haka aka fara gabatar da sallar Juma’a.
Kasancewar mutane sun san da ɗaure-ɗauren aure bayan idar da salla babu wanda yay yunƙurin tafiya. Sai lokacin su kawu Bello suka fahimci babu Abba tare da su. Nan fa aka shiga tambayar juna, sai dai kowa yana cewa bai gansa ba maybe bai ƙaraso ba..
Miƙewa ƙanin Momy yay ya fita a taron da zummar neman wayar Abba suji ko ina ya tsaya…..
★★★★★
Addu’a Hibbah ke karantowa tana ƙara kutsa kanta cikin gidan da batasan kansa ba. Sai da ta ga ta bacema idon maigadin sanann ta ɗan dakata ta sauke numfashi. Haggu da damanta ta kalla ko zataga ƙofar shiga. Cikin sa’a idonta ya hango mata window. Da sauri ta nufi windown tana addu’ar ya kasance inda zata iya hango su Abba.
A rufe windown take, dan haka tai gaba cikin takaici da fatan samun mafita a gaba. Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke saboda cin karo da ƙofar kitchen irin ta bayan nan. Ta kama handle ɗin ta murɗa a hankali cikin sa’a ta buɗe. Wani irin daɗi ne ya baibayeta kamar ta tashi sama. kitchen ne babba, komai na amfani akwai, da alama ma ana amfanin da shi, dan yanzu hakama ga alamun anyi girki a ciki. Gaba tai zuwa ga ainahin ƙofar kitchen ɗin ta cikin falo, tai saurin maida kanta baya saboda ganin Abba zaune tare da wani mutum a dining ɗin abinci jere tamkar masu shirya fati.
“Ina fatan kukun nan taka ta fita ko?”.
Mutum da ke tare da Abban ya faɗa. Ƴar dariya Abba yayi, cikin salon narke murya tamkar wanda ke gaban mace yace, “Karka damu nace taje waje ta zauna. Bakuma zata shigo ba sai na bata umarni kaima ka sani”.
“Hakane baƙon ya faɗa yana sumbatar hannun Abban”.
Wani irin mugun faɗuwa gaban Hibbah yay. Tai saurin kauda abinda zuciyarta ke bijiro mata ta sake maida hankali akansu.
“A.G kasan a ƙage nake da son jin abinda ke bakinka, duk da kuwa kwana biyu ina tare da kewar harka saboda jiyya data cikuykuye rayuwata. Amma soon zan dawo, fatana a ɗaura auren nan yau cikamakin bukatuna su sake shiga tafin hannuna sannan na dawo. Kaima kasan banida wani buri da ya wuce dukiyar ƴaƴan Aliyu cigaba da kasancewa a hannuna. Hakan kuma naga bazata taɓa tabbata ba har sai na aura musu ƴaƴana, sannan na bisu ɗaya bayan ɗaya na halaka su. Dan duk wadda ta fara samun ciki a cikin ƴaƴana to mijinta ne zai fara baƙuntar lahira. Ko ƴaƴan nawa da mahaifiyata basu san da shirin nan nawa ba. Sai na gama da su kaf sannan na ɗinke bakin zaren *_TAKUN SAAƘA_* ta da Asiya. Wadda ubanta ne ya fara sarƙata akan mugun bugun da yay mini tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya kacal a duniya.”
Dariya A.G yayi da faɗin, “Baka da dama Gwarzo. Wato kai sam baka manta bashin gaba.”
“Har abada kuwa A.G. Naso fanshewa akan budurcinta hakan ya gagara, abin takaici da baƙin ciki ta sake hawa kaina, aka aurama Yayana uwa ɗaya uba ɗaya shi ya mora bayan na ƙwallafa rai. Tazo ta katantane komai, duk hanyar dana ɓullo akan wasoson dukiyarsa sai tabi ta toshe ta hanyar fargar da shi. Shiyyasa yanzu daya mutu bayan ya tara musu na shirya hawa kan dukiyar, sai dai nafison nacita a gaɓar da Asiya zatafi jin ciwo da raɗaɗi, kamar yanda na ɗauki tsahon shekaru ina jin ciwo da raɗaɗin abubuwa masu yawa a kanta. Wannan dalilin ya sani yin dakon shekaru goma sha tara ina haƙurin cigaba da juyata tana haɓaka har zuwa yanzu da wasan zai fara. Sai na ɗan-ɗana-ma Asiya azabar ciwon mutuwar ƴaƴanta ɗaya bayan ɗaya a tafin hannunta”.
“Anya kuwa hakan ta kasance Gwarzo? Dan wannan ƙaramar ƴar tata ta fi sauran yaran tsaurin ido da rashin tsoro. Shiyyasa nake ganin wautarka na canja ɗanka da zai aureta zuwa wani daban, duk da nasan wanda ka canja ɗin yafi ɗanka kwaƙwalwa da wayo da hatsabibanci. Kagafa shekararta sha takwas kacal amma take da dabarar ƙulla agreement da ƴan sanda akan a ƙwamusheka ranar aurensu domin yayunta su kuɓuta daga auren ƴaƴan naka. Ina jimaka tsoron wannan yarinyar fiye da kowa cikin ƴaƴan matarka. Koda yake nasan Master bazai taɓa yarda da mace ba”
“Humm kai kasan tun randa ka bani labarin nan da mamakin yarinyar nan nake kwana nake tashi a raina. Yanzu haka fa tana can tana jiran ku tattareni kenan fa?. Batasan kai ɗin mutumina bane.”
Atare suka kwashe da dariya. Yayinda Hibbah dake makale tana saurarensu ta daskare a tsaye, dan zuwa yanzu ta gama fahimtar dattijon jami’in nan ne dai A.G da ya sakata bibiyar Master…….
Maganar Abba ta katse tunaninta.
“Karka damu ita na gama da lamarinta kaima ka sani. Shi wanann yaron dana kawo ya canji Junaidu dan ya aureta kamar yanda ka faɗa yafi Junaid hatsabibanci kaima ka sani, sannan a tafin hannunmu yake a kuma gaɓar da muke more ƙuruciyarsa. Ana gama ɗaura auren zanbi shawararka na biya mata kuɗin karatun tafiya China kamar yanda take buri, da wanann damar zanyi amfani na ɓadda rayuwarta. Dan rashin nata ne zai fara karya rayuwarsu saboda tsananin son da suke mata matsiyatan sai kace ƴar gwal. Ku kuma da ya ɓaddata zaku amfani da wannan damar ne ku fito ku nunama duniya shi wannan Master ɗin da kuke nema ruwa a jallone ya sace ta. Kaga shikenan babu mai zargin Halilu Hamza gwarzo kenan ko”.
Ya kare maganar da shaƙiyancin da ya sakasu sake kecewa da dariya. Jikin Hibbah ne ya kama rawa. Tai saurin kai hannu ta toshe bakinta jin kuka zai kufce mata. Dai dai nan A.G ke faɗin, “Gaskiya mun iya maida mutane wawaye. Kowa ya saki baki kullum muna aikin tukuru na son kamo Master, basu san shi kansa Master ɗin mune muka ƙirƙiresa ba. Yana gama tattare mana kuɗaɗen shima zamu ɓaddashi a doron ƙasar baki ɗaya, mu kuma cigaba da amfani da rigar jami’an tsaro wajen tsula tsiyarmu. Yayinda duk wanda ya fito da niyyar aikin gaskiya mu ɓadda banza, dan mu ba gyaran kasarne gabanmu ba. Wanda suke gaba damu kuma mu cigaba da kwantar musu kai muna nuna mun fisu san ƙasar da cigabanta, da tabbatar musu aiki muke tuƙuru. Kaga mun toshe ko ina kenan”.
Dariya suka kuma kwashewa da shi, har sai da kira ya shigo wayar Abba sanann suka tsagaita. Ya miƙe yana faɗin, “Alhaji Alu ne ke kira, ina kyautata zaton suna wajen ɗaurin aure tashi muje dan nasan ana gab da ɗaurawa kar ayi babu mu.”