TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAKA 19

     Da sauri A.G ya riƙo hannun Abba cikin marairaicewa yake faɗin, “Gaskiya ina da bukata, shine ma dalilin da yasa na kiraka nan. Ka barsu kawai su ɗaura tunda ko baka akwai masu amsa da bayarwa, ni kuma ka ragemin zafi anan. Dan kwana biyun nan matasan ma da muke ɗan samu mu taushe wa’azin malaman nan ya fara tasiri a ransu gudunmu sukeyi shegun.” Abba ya buɗe baki zaiyi magana A.G ya sake marairaice masa da rungumosa jikinsa cike da salon shaiɗanci da bushewar zuciya irin ta masu fasadi da rashin tsoron ALLAH a ban ƙasa????. (Wa’iyazubillah. ALLAH mun tuba ka yafemu????????????????). 

(Ya ALLAH ka gafarta mana badan halinmu ba, ka kare mana zuri’armu da mazanmu da ƴan uwanmu da matasan al’ummar musulmi baki ɗaya????????????. Abba ɗan homo, A.G ɗan homo, da ire-irensu abokan ƙazantarsu da yawa dake lullube da rigunan mutunci suna cin dunduniyar al’umma da addini. Kuga dai A.G, ya shige cikin jami’an tsaronmu jajirtattu yana tsula tsiyarsa ta hanyar ruguza shirye-shiryensu batare da sun sani ba. Shin kamar yanda ya faɗa Master yaronsa ne? Su Master kema aiki?. Mu cigaba da kasancewa a cin TAKUN SAAƘA domin jin yaya take ne?)

       

        Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake yi, ta shiga tafiya da baya-baya zuciyarta na tsitstsinkewa tamkar zata faɗo waje. Wani irin duhu-duhu idanunta suka farayi, abinda takeji a labari shine yau a zahirin rayuwa take gani ga ƙanin mahaifinta da idan aka tsaga jininsa za’a ga nata a ciki. Innalillahi wa inna-ilaihirraji’u. (Dole ne kafin a daura auren nan tayi wani abu) wannan tunanin ya sakata zabura ta fito a guje. Kotakan maigadi dake zaune yana sauraren redio bataiba ta buɗe gate ta fice. Saurin miƙewa yay yana tambayarta lafiya?. Ina batama san yanai ba. Yay saurin bin bayanta wajen, sai dai kafinma ya leƙo ta kusa kaiwa titi inda take tsammanin mai napep ɗin nan na jiranta.

       Waige-waige ta shigayi dan babu mai napep babu alamarsa. Cikin hakki da rawar jiki ta ciro wayarta dake maƙale cikin zani ta hau laluben wayar Yaya Muhammad. Harta katse bai ɗaga ba. Ta sake kira nan ma bai ɗaga ba. Ta maida akalar kiran nata kan Yaya Abubakar tana fassewa da kuka. Sai dai shima harta katse bai ɗaga ɗin ba. 

        “Yaya ku ɗaga dan ALLAH”. Ta faɗa a kiɗime tana zubewa ƙasa da sakin wani kuka mai ban tausayi. Tunanin kiran Ammar ne yazo mata a zuciya. Cikin sa’a kuwa ya ɗaga a bugu biyu, sai dai batajinsa sosai sai tsananin hayaniyar ƴan ɗaurin aure. Da ga can shima sai faman faɗin, “Hello! hello! Auta bana jinki wlhy, ki yi haƙuri zan kiraki za’a fara ɗaura auren ne”. 

    Kafin tace wani abu ya yanke wayar ƙit. Daga wayar tai zata dasa da kasa sai kuma ta fasa. Tai azamar yage niƙaf ɗin fuskarta ta jefar da tunanin fara gudu tabar cikin anguwar kozata sami abun hawa. Inda rabo sai ta isa massalacin kafin a fara ɗaura auren.

         

      ★★

   Matashin saurayin da ke can baya kaɗan da Hibbah cikin wata farar mota ya gyara zaman abinda ke kunnensa, cike da girmamawa yace, “Boss ta fito. da alama abin hawa kuma take nema, tunda na kaɗa mai napep ɗin da ya kawotan”.

      Bansan amsar da aka bashi ba da ga can, ya dai gyaɗa kansa cikin ƙara bama wanda yake maganar da shi girma, tamkar yana gabansa ya sake faɗin. “Yes Master. Insha ALLAH”. Da ga haka yay ma motar key tare da harbata kan titin ya nufi Hibbah da ke tsaka da tattare hijjabi da alama gudun da ta yankema zuciyarta shawara take shiryamawa. 

         Sai dai jin tamkar tahowar mota a bayanta ya sata sauri juyowa ga titin tana ƙoƙarin yin alamar tsaidawa. Bai tsaya ba sai da ya ɗan gota ta sannan ya dawo da baya. Yana tsayawa ko tunanin taga waye bataiba ta buɗe murfin ta shiga baya. “Bawan ALLAH dan ALLAH babban masallacin juma’a na Sheikh Aliy Maina zaka kaini, ka taimakeni kayi sauri na roƙeka dan ALLAH.”

        Jin shiru bai amsata ba bai kuma tada motar ba ya sakata cigaba da magana cikin tsumar jiki da ƙaguwa. “Malam dan ALLAH ka taimakeni, wannan ita kaɗaice damar da nake da ita ta ƙuɓutar da ƴan uwana da ni kaina. Tana kufcewa mun faɗa gararin rayuwa”.

        Yanzun ma komai bai ceba. Sai handkerchief ɗin da ke saman cinyarsa ya ɗauka ya jefa mata a kan fuska. Hannu tasa ta kaɗe handkerchief ɗin da faɗin, “Malam wane irin wulaƙanci ne haka? Minene wannan ka………”

      Ta kasa ƙarasa abinda take shirin faɗa ɗin saboda duhu da ya mamaye ganinta baki ɗaya. Tai ƙoƙarin fisgo numfashin da ke san kufce mata tana kai hannu bisa ƙofar da laluben neman sa’ar buɗewa. Sai dai ina abinda ke jikin handkerchief ɗin ya gama tasiri a cikin jikinta, tai baya jikin kujerar yaraf tamkar wadda aka zarema rai. 

         Sassanyan numfashi Habib ya sauke yana mai ƙoƙarin hana kansa yimata kallon ƙurulla ta cikin mirror ɗin gaban motar ko dan kima da darajar wanda ya sakashi ɗakkotan. Ya ɗan murmusa yana ma motar key tare da harbata kan titi…………✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR????????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button