Uncategorized

TAKUN SAKA 22

      Komai ya kwance musu, tunani ma sun gazayi na neman mafita. Ammar da ke kuka ya nufi cikin gida da zummar sanarma Ummi dama tunda suka dawo sallar la’asar basu koma ciki ba. Saurin riƙosa Isma’il yayi yana girgiza masa kai. “Ammar ba yanzu ba. Ummi bata cancanci sanin wannan tashin hankalinba yanzu. Inaga muɗan jinkirta har a samu mafita”.

         Kuka sosai Ammar ya fashe da shi, hakan yasa Isma’il ɗin rungumesa cike da lallashi.

      Yaya Abubakar da zancen Isma’il yaja hankalinsa cikin gamsuwa da ƙarfin hali ya ce, “Shawararka tayi Isma’il, dolene mu jinkirta sanarma Ummi wannan batun duk da cewar zuwa yanzu tasan babu Hibbah a gidan. Sai musan mi zamu sanar mata dan hankalinta ya kwanta”.

          Cike da gamsuwar jawabinsa duk suka kaɗa kansu. Suna nan tsaye suna tattauna yanda zasu ɓulloma Ummin suka juyo sabuwar hayaniya ta ɓalle a cikin gidan, har takai wasu na fitowa a guje. Da sauri suka shiga, dan tun daga nan suna jiyo kururuwa da ihun Hajiya mama.

      Da ƙyar suka iya kutsa kai cikin falonsu. Inda ke cike da ƴan biki da ke zagaye da Hajiya mama da Abba da Junaid wai zai daki Ummi. Hajiya mama nata zagin Ummi akan itace ta tsara komai akan auren su Yaya Muhammad. Abba ma yana zazzaga tasa masifar da tattaro duk laifin Shuraim (ko nace master) yana azawa kan Ummi. Duk da kuwa sarai yasan gadar zaren da ya ƙulla ce ta rufta da shi. Yayi iya hasashensa kuma ya gagara kamo bakin zaren da dalilin Master na juya shirin nasu zuwa tsarinsa daban, shiyyasa yazo sauke haushin da takaici akan Ummi marainiyar wayonsa. Harda yo gayyar ƴan tayo..

         Isma’il ya finciki Junaid ta baya yana ƙoƙarin riƙe katakon da ya ɗaga wai zai bugama Ummi da ke zaune ta dafe kanta tana jiran saukar katakon. A take mutane suka dare saboda yanda ya zubar da Junaid ɗin a ƙasa ya take masa wuya. Riƙesa Yaya Muhammad yay ƙoƙarin yi amma sai ya fisge jikinsa, da ƙarfi ya daka katakon da ya kwace a hannun Junaid ɗin a ƙasa saitin kansa, jikinsa sai wani irin tsuma yake tamkar mafaraucin zaki. Duk yanda Junaid ke kakarin mutuwa yaƙi ɗaga ƙafarsa a wuyansa, sai ma sake murzawa yake cikin tsananin taurin zuciya. 

       A matuƙar firgice Abba ya ƙai hannu wai zai ture Isma’il. Sai dai ko motsi bai yiba. Sai ma waiwayowa da yay ya duba Abban da wasu irin jajayen idanun da suka bama kowa matuƙar mamaki. Dan gaba ɗaya ya birkuce musu da ga Isma’il ɗin da suka sani zuwa wani daban. 

          “Idan jikinka ya ƙara gigin taɓa nawa saina ɓallaka yanda ko uwar data haifeka bazata sake gane kamaninka ba.”

        A wani irin zabure Abba ya waro idanu yana nuna kansa, “Da ni kake?”.

      Ƙafar da yake murza wuyan Junaid da ke kakarin mutuwa ya ɗaga. Yay wani irin tsalle tamkar ɗan ƙwallo zai buga ball ɗin daga kai sai mai tsaron gida ya halbi hakarƙarin Junaid. Wata irin wahalalliyar ƙara Junaid ya saki tare da jan numfashi tamkar zai shiɗe sai ga aman jini.

       “Innalillahi… Isma’il!”.

Yaya Muhammad ya faɗa da sauri yana kawo hannu zai riƙesa. Saurin ɗagama Yaya Muhammad ɗin hannu yayi idanunsa na kan Abba da gaba ɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake. Dan yanda Isma’il ɗin ke tunkarosa sai yake ganin tamkar zai haɗiyesa da idanunsa masu suffar na Zaki ne.

      “Yaya Muhammad barni na kartama wannan shashashan dattijon warning na ƙarshe. Dan inhar ya sake koda kallon Ummi da wata manufa to lallai saina maidashi abin kwatance. Kai bama shi ba. Ko karen gidan nan ya sake mata kallon banza lallai ni Isma’il zan daddatsa shi gunduwa-gunduwa na cinye namansa ɗanye dan uban da ya haifesa”. Ya ƙare maganar idonsa akan Abba. Yatsansa na nuna Hajiya mama da ta koma jikin bango ta maƙure jikinta na rawa kar-kar-kar. Ga fitsarin da ya cika mata mara tuni ya ɓalle ya fara bin kafafunta yana sauka saman tiles………….✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR????????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button