Uncategorized

TAKUN SAKA 24

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Twenty Four_*

…………Kusan karfe tara na dare amare suka fara isowa. Sheikh Aliyu Abdul-Ra’uff Maina ne ya fara isowa da tawagarsa. A bisa al’adarsa na kai duk ƴaƴansa gidan aurensu kuma. Ba wani gayya bace yayo. Mota uku ce kawai ta ƴan uwansa mata sai ɗaya mazan ƴan uwansa sai ɗaya shi da Amarya Maimunatu da ke jikinsa tana faman kukan rabuwa da gida tamkar kowacce amaryar ƙwarai.

        Ya fara damƙata a hannun Ummi matsayin uwa kafin ya damkama Yaya Muhammad da musu addu’ar zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, harma da sauran angunan da amarensu. Da ga haka yay musu sallama ya taho ransa fal kewar ɗiyarsa data kasance ta ƙarshe a cikin ƴaƴansa da ya aurar. 

       Tamkar jira suna barin ƙofar gidan gayyar abokan su yaya Umar ƴan ɗaukar sauran amaren uku suka iso anguwar suma. Dama su su Yaya Umar ɗin duk suna nan gida basuje ba. Suna can gefe sun kulle kansu suna tattauna batun Hibbah dan sam hankalinsu baya a kwance. Yaya Abubakar ma tun ɗazun baya gidan da alama shima dai duk akan Hibbah ɗinne.

       Sosai gidan ya kacame da hayaniya. Suma sauran amare duk sai da aka kawosu sashen Ummi aka damƙasu gareta kafin a mimmiƙasu sashen su. Waɗanda bazasu kwana ba suka firfito domin a maidasu. Aka bar masu kwanan nan da ƙawayen amare.

      Hayaniyar mutane yasa Ummi bata maida hankali akan rashin ganin Hibbah da akace tana tare da su Zahidah ba. Gaba ɗaya hankalinta ya ɗauke. Har takai gidan ya koma tsit batasan kai kawo da ƙulle-ƙullen da ƴaƴanta keta faman yiba akan autar tasu.

★★★★

        A can gidan ɓangaren su Abba kam dole aka kwashi Junaid zuwa asibiti, yayinda ran Abba ke a ɓace a jagule matuƙa. Babu abinda zuciyarsa ke kitsa masa sai ɗaukar alwashi kala-kala akan Ummi da zuci’arta. Musamman Hibbah da yakeji zai iya dasa wuƙa a maƙoshinta a halin da yake ciki. Dan tabbas kuwa yaga *ɗan hakkin da ka raina shike tsone maka idanu* har yaushe ma aka samu cikin Hibbah aka haifeta da zata iya ruguza masa shirinsa na tsahon shekara da shekaru?. Bama ita ba, hatta da Master ɗin ya ɗauki alwashin bazai bari ba. Dan da’alama Hibbah da su Ummi ɗinne suka sashi wargaza zancen auren.

        Irin waɗan nan tunane-tunanen yaketa faman yi da kaikawo a ɗakinsa tun barin su momy da Junaid zuwa asibiti. Sai hayaniyar ƴan biki da har yau suketa gutsiri tsoma yake faman jiyowa. Wayarsa ya ɗauka ya shiga neman number A.G amma sai taƙi shiga saboda network. Cike da haushi ya wurgata saman gadon yana dafe kai. Tsabar ruɗanin da yake ciki ko salla baiyi ba gaba ɗaya yinin yau. Babu azhar, la’asar, magrib balle isha’i. Bai kumayi tunanin yinsu ba har dare ya raba ya cigaba da ƙullawa da kwancewa batare da ya samo wata mafitaba akan al’amarin.

       Da ga wajen amare kuwa su Amlah kuka sunsha shi har sun godema ALLAH. Su kansu babu irin kalar tsinuwa da zagin da basu rakito sun sauke akan Ummi ba. Ga ƙawayensu na tayasu da tunzurawa. Tashin hankalin dukan da Isma’il yayma Junaid ne ya ɗauke hankalinsu zuwa can suma sukabi su Momy asibiti dan suna tsananin son ɗan uwan nasu ɗaya namiji tilo a cikinsu.

     To har dai gari yay tsit alamar rabawar dare babu wanda ya dawo da ga asibitin. Hakama sauran ƴan biki babu wanda ya farga da rashin su Ummi balle tunanin rashin kawo amare har yanzun.

*_WASHE GARI_*

           Sassanyar iskar sanyin asuba, da sabo da tashi sallar asubar ne ya saka Hibbah farkawa da ga nannauyan barcin da ya dunƙule rayuwarta tun daren jiya bayan master ya maidota hankalinta da ga sumarwa. Da ƙyar ta iya buɗe idanun da sukai mata matuƙar nauyi. Ta kai hannu bisa kanta da ya sara mata tana ambaton, “Wash ALLAH Ummi kaina”.

        Jin shiru babu alamar Ummi a kusa da ita ya sakata ƙoƙarin ganin ta tashi duk da azabar da kan nata ke mata ga jiri-jiri hajijiya-hajijiya na ɗibar idanunta da taketa kokawar ganin ta buɗesu ko kaɗanne.

         Da ƙyar ta iya tashi zaunen cikin lalube ta jingina jikinta da fuskar gadon. Tsahon mintuna kusan goma taja a zaune haka duk da kuwa kunnuwanta na jiyo mata salla a mabanbanta masallatan da takejin tamkar bana anguwarsu ba. Sai da yanayin nata ya ɗan dai-daita ta sake shiga kokawar buɗe idanun tana ambaton sunayen ALLAH.

        Dishi-dishi take ganin ɗakin da ya kasance baƙo a gareta, har ganin nata yaɗan dai-daita. (Tabbas wannan ba ɗakinta bane, ba kuma ɗakin Umminta bane, to inane?) ta ayyana a zuciyarta tana sake bin ɗakin da kallo cikin ƙarfin hali. (Sabon gidan mu) zuciyarta ta sake ayyano mata duk da bataji gamsuwa ba a cikin ranta. 

    Kokawar son tunano abinda ya faru jiya ta shigayi da zuciyarta. Cikin amincin ALLAH kuwa komai ya shiga dawo mata dalla-dalla. Ƙirjinta yay wata azabar bugawa ta zabura da niyyar dira a gadon sai dai rashin ƙarfin jiki ya dakatar da ita ga hakan. “Innalillahi wa-inna’ilairraji’un inane nan? Wanene na shiga motarsa?”.

        Ta faɗa a fili jikinta na rawa. Sakkowa tai a gadon cikin dabara, tai ƙoƙarin kunna wutar ɗakin mai haske. A take kuwa ko ina ya gauraye kasancewar akwai wutar. Da bin bango ta nufi ƙofar data gani, sai dai koda ta murza a kulle take. A take wani tsoro ya sake dirar mata a rai. ta zame a hankali tai ƙasa zuciyarta na wani irin tsitstsinkewa. (Idan har hasashenta yayi dai-dai azzalumi Abba ne ya farga naji sirrinsu yasa aka satoni aka kawo nan. Shikenan an ɗaura auren yayunna da ƴaƴansa. Shikenan zai kashe min ƴan uwa) ta shiga ayyano hakan a ranta. Tai saurin dafe kanta da ya sake sara mata.

     “Abba mi mukai maka da zafi haka? Miyasa kai azzalumi ne maci amana. Ya ALLAH ka karemin ahalina daga cutarwar waɗanan azzalumai fasiƙan mutane. Ya ALLAH bamu da wani ƙarfi sai naka, kai ne bangonmu abin jingina ka tallafi maraicinmu dana mahaifiyarmu ka bamu kariya”. Yanda take maganar tana kuka abin tausayi. 

    Sai kuma taɗan zabura saboda tunowa da ko sallar Azhar na ranar jiya batayi ba. Dan a dai-dai lokacin da akeyinta tana tare da su Abba. Miƙewa tai a zabure. Duk da jirin da ke kwasarta bata saurara ba sai da ta dangane da ƙofar da take ƙyautata zaton toilet ne da ƙyar. Cikin sa’a kuwa ta samu toilet ɗinne, duk kuma abin amfani akwaishi a ciki. Shawarar zuciyarta tabi cike da dauriya ta haɗa ruwan wanka mai zafi sosai, kayanta ta cire tana faman layi da dafe kai. Bayan ta cire kayanta da ƙyar cikin ruwan ta shige gaba ɗayanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya da numfashi. Yanda ruwan ke ratsa kowacce gaɓa ta jikinta haka jijiyiyin jikinta ke saki a hankali wani ɗan ƙarfi-ƙarfi na mamayeta. Sai da taji hankalinta ya dawo jikinta kafin ta miƙe daga ruwan da har ya huce tai wanka sama-sama. Ganin sabon brush ya sata ɗauka tayi sannan ta ɗaura alwala. Tasan bata da wasu kayan anan. Babu kuma tabbacin samu dan haka ta maida wanda ta cire ta fito. Dan gaba ɗaya hankalinta kuma ya koma ne ga sallolin da ke a kanta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button