HALIN GIRMA 22

Ad
_____
Halin Girma 22
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**********
Tamkar rana haka harabar masarautar take, komai an shirya shi an tsara saboda shirin tarbar su. Tafiya sukayi doguwa a ciki kafin su kai wajen manyan gine-ginen cikin masarautar.
Ba mota daya suka shigo daga airport din dashi ba, shiyasa ma bata ganshi ha a sanda suke fitowa daga mota. Cikin rakiyar hadiman shashen Ammi da na gidan ma baki daya suka isa babban falon nata, da aka kawata shi matuka ana jiran isowar su. Kamar yadda suka samu tarba ta musamman a Kano haka aka karbe su anan dinma. Hakan ya kara bawa su Mamma nutsuwa da tunanin irin yadda Iman din zata samu kanta a gida irin wannan wanda yake cike da abubuwan da ba lallai ta iya dauka ba.
Bayan sun huta an gabatar musu da abinci ne Ammi ta saka aka rakasu masaukin su, wanda aka ware musu tun kafin isowar su. A gajiya kowa yake dan haka suna zuwa kowa ya mike aka shiga maida maganar yadda aka karbe su da irin sa’ar da Iman din tayi.
Tana jin su bata tanka ba, hankalin ta ya tafi sosai wajensa tana son jin yadda yake dan ta tabbata da akwai wani abu da ya rage masa walwala.
***Tun isowar su ta samu labari wanda dama abinda take jira kenan, ta shirya tsaf babu Kuma abinda zai hanata aiwatar da abinda tayi niyya shiyasa ma bata bari Kilishi ta sani ba balle har ta hanata.
Shigar sa shashen nasa bayan ya bar wajen Bubu hadimar ta, ta sanar mata wanda dama ta saka ta ne ta saka ido tana ganin ya shiga ta fad’a mata.
Tashi tayi tana gyara gashin kanta da ta saka ribbon din tayi sako-sako dashi, ta daura babbar Alkyabba akan kayan da suke jikin ta da ya kasance karamar riga ce mara hannu iyakar ta guiwa kawai, sai dogon wando a k’asan da ta saka saboda yadda zai zama ko ina na jikinta ya rufe.
Turaren da yake cikin Jakarta ta ciro, ta dunkule shi a hannun ta, ta fita ta kofar bayan cikin rakiyar amintacciyar hadimar ta. Tafiyar dake tsakanin bangaren Moh din da nasu da akwai tazara dan haka yasa suka bi ta baya har suka isa. Idon ta, ta daga ta dubi bangaren bedroom dinsa amma sai taga dakin babu haske sai sauran dakunan. Zagayo wa sukayi zuwa gaban ginin masu kula da kofar suka tashi ganin ta, da ido sukayi magana da daya, ya girgiza mata kai alamar eh sannan yace
“Yarima na jiranki gimbiya Lailah.”
Jin haka ya saka dayan saurin bud’e mata kofar, ta kutsa kanta ciki kai tsaye tana jin kamar anyi an gama ta samu cikar burin ta.
Tafiya ta ke a cikin falon tana kallon komai, yadda aka sauya komai kamar ba part din da take shigowa a duk sanda ta ga dama ba, babban hoton da ke manne a jikin bangon dakin ta kurawa ido tana matsawa gaban sa. Iman ce a jiki, ita da Moh ranar da aka daura aure, sunyi masifar kyau kamar kayi musu magana su amsa. Wani bakin ciki ne yazo ya tokare mata a makoshi, taji kamar tayi wurgi da hoton ya tarwatse a wajen amma sai ta daure, ta maida hannun ta baya tana nufar bedroom din nasa in da tasan zata same shi.
Kafin ta karasa ta hango glass cup a k’asa a farfashe, ta durkusa ta dauki ragowar tana kaiwa hancin ta, murmushi tayi tana da yakinin komai ya zama daidai, everything is in order kamar yadda ta tsara. Hakan ya saka ta wucewa Kai tsaye ta murda kofar dakin ta kutsa kanta ciki tana zare alkyabbar da take jikin ta, ta zame a wajen ta fadi.
Muryar sa da ta soma bacewa yayi kokarin cewa
“Waye!”
Yadda yayi maganar ya saka ta sake tabbatar da komai yayi daidai, basu yi mata shirme ko shiririta ba. Karasawa tayi jikin gadon, ta kai hannu ta taba shi ta hasken bedside lamp da ke kunne, take kallon sa, idon sa yayi masifar komawa ciki yana lumshe su tamkar wanda yake shirin yin bacci irin baccin da yafi karfin sa yake neman kai shi k’asa.
“Waye?” Ya sake maimaitawa da k’yar kansa da yake juya masa ya shiga kai masa sakon mayen kamshin da yaji ya karad’e dakin,kamshin da ya dauke shi zuwa wata duniya ta daban, a take yaji komai ya hargitse masa, ya mike da k’yar yana duban ta cikin ido, gaba daya komai ya chanja masa,ta juye masa Iman dinsa gaba daya. Hannu ya kai zai taba ta, ta saka karbi ta tura shi baya ya fad’a saman gadon!
***Text message ne ya shigo wayar ta, ta bud’e da sauri tana fatan ya kasance daga shi, kamar yadda tayi tsammani, shi din ne kuwa,
_”A rako ki shashe na.”_
Haka kawai sakon ya kunsa, kifa wayar tayi tunanin yadda zata fara fadawa Mamma yace a rakota bangaren sa. Da kunya sosai bata kuma jin zata iya,shiru tayi tana wassafa abun a ranta, zuciyar ta na ce mata kawai ta kira mamma ta fad’a mata ai ba wani abu bane, wata zuciyar kuma na ce mata a ah. Ta na nan zaune har aka dau tsahon wani lokaci, sakon ya sake shigowa irin na dazu a karo na biyu, sai dai banbancin lokaci. Amaani ta kira suna zaune suna cin snacks da juice, ta bata wayar tace ta kaiwa Mamma. Sai ta kifa kanta tana jin nauyin Mamma. Tana jin sanda Mamman tazo kanta, tana sababi
“Yanzu haka ake gaya miki anayi Iman? Mijinki yana kiranki tun dazu kika yi shiru. Kunyar me? Zamani ya chanja kinji? Tashi maza ki gyara jikin ki, ga masu kula dake nan da yawa daya sai ta rakaki, tashi maza kina kara bata lokaci.”
Tashi tayi kunya na nukurkusar ta,ta dinga sunne kai taki yarda su hada ido da Mamman, tana kallon ta, ta fito mata da wasu kayan tace ta sauya, sannan ta kawo mata wani abu a cup da madara ta bata ta shanye, ta faffesa mata turarurruka masu kamshi sannan suka fito in da yan matan ke zaune, da sauri suka tashi su biyu, suka sakata a tsakiya suka nufin bangaren Moh din da yake da dan tazara da wanda aka sauke su.
Babu kowa a kofar, kai tsaye ta shiga su kuma suka samu waje daga wajen suna jiran ta dan tace musu ba jimawa zatayi ba, babu kowa a falon babu motsin komai, dakin farko ta bud’e da sallamar ta, baya ciki, sallama take amma ba da karfi sosai ba, a tunanin ta ko ya shiga toilet ta zauna jiran shi, shiru shiru babu alamar sa, ta kasa kunne ko zata ji karar ruwa a toilet sai taji kamar shesshekar kuka, sake kasa kunnen tayi sosai ta tabbatar da abinda taji, sai ta fara tunanin aina take ji, dakin da yake karshen falon ta kalla, babu alamun haske a ciki amma kuma tabbas da ga nan ne sound din yake fitowa. Tashi tayi ta nufi dakin tana taraddadin abinda zata tarar. A hankali ta tura kofar, ta leka da kanta kafin ta shiga da jikin ta gaba daya, tana gama shiga wutar dakin ta kawo, kwakwalwarta ta dauke kamar yadda ake dauke wutar nepa, idanun ta suka sauka akan Moh yayi ruf da ciki a saman gado yana bacci cikin kwanciyar hankali, boxer ne kawai ajikin sa dgaa shi babu komai. Da sauri ta maida kallon ta kan matar dake zaune a kasan tiles din dakin, kanta babu dankwali gashin kan nata da ya hargitse ya barbazu har zuwa saman fuskar ta, shigar jikin ta kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta tana kokarin barin dakin, sai dai bata kai ga barin wajen ba dan ko taku biyu batayi ba, taji sanarwa shigowar Maimartaba, bayan sanarwa ne taji shigowar sa.
Ad
_____