TAKUN SAKA 24

Ɗan kwalinta ta shimfiɗa a ƙasa tare da ɗaukar yagaggen hijjab ɗin ta ta ƙulle daidai wuyan ta saka tama mamakin yanda akai ya yage haka ta tada salla. Duk yanda shaiɗan yaso mata kutse cikin sallar da bijiro mata damuwa da tashin hankalin da take a ciki haka ta dinga turesa tai sallarta a tsanake tana faman zirar da hawayen. Tsaf ta kammala rama sallolin har zuwa sallar asubahi. Taja doguwar addu’a akan wannan yanayi da suke ciki tana kuka. Ta jima a wajen zaune har rana ta fito sosai. Agogon ɗakin ta kalla, ganin takwas har tayi yasata miƙewa ta sake nufar gadon saboda yunwar da takeji da rashin ƙarfin jikinta. Karaf idanunta suka sauka akan wayarta dake tsakkiyar gadon, da alama dai a wajen bacci ta fita da ga cikin zaninta. Wani irin daɗi ne ya lulluɓeta. Ta kai hannu ta ɗauka da sauri tana murmushi da share hawayenta. Cikin rawar jiki da matsanancin ɗoki ta danna kiran number yaya Muhammad.
Sai ɗan yarfa hannuwanta ta ke da cizar lip ɗinta na ƙasa cike da zumuɗin son jin ya ɗauka……
“Ko zaki shekara kiransu bazasu gani ba, koda kuwa ta shiga ne”.
Wata ƙasaitacciyar murya ta faɗa a bayanta. A zabure Hibbah ta juyo duk da rashin ƙarfin da jikinta ke da shi. Babu shiri ta sake zabura tai baya, duk da kuwa tayi tunanin shiɗin zata gani anan tunda yaron su Abba ne. “Shuraim?!” ta faɗa a ɗan kausashe tana masa wani irin kallon tsana.
“A.K.A Master!”. Ya faɗa yana cigaba da takowa cikin izza da kasaitarsa tsakkiyar ɗakin. Sai da yazo gab da ita ya kai hannu saman face nashi ya cire facemask ɗin face ɗin Shuraim.
“What?!!”. Hibbah ta faɗa tana sakin wayarta ƙasa a ɗan firgice.
Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki da cigaba da takawa gabanta har yanzu hannayensa duka na zube cikin aljihun wandon jeans ɗin jikinsa. Ganin yanda ya ke tinkarota yasa ta fara ja baya tana jifansa da wani irin kallon tsana da ruɗanin ganin facemask a matsayin fuskar Shuraim, (kenan sace Shuraim yayi ya maye gurbinsa da shi?). Jin ta dangane da jikin bango ya sata rumtse idanunta da ƙarfi zuciyarta na wani irin harbawa dan gaba ɗaya tama rikice, gashi babu ƙarfin yin tsiwar dake cin ranta gareshi.
Sosai ya matsa jikinta har suna jin fita da saukar numfashin juna. Hibbah ta sake maƙurewa a bango dan tsoro da rashin sabo. Shiko tsumammun idanunsa ya zubama fuskarta tare da zaro hannunsa ɗaya daga aljihun wandon ya ɗaura bisa bangon ya tokareta ganin zata zille.
Matse jikinta tayi da sake rumtse idanunta dan har cikin ranta bata fatan ya taɓata kodan tuna ƙazantar da suke aikatawa shi da su Abba da tayi. Shiko fuskarsa ya sake kaiwa gab da tata tamkar zai haɗe bakinsu sai kuma ya waske akan kunnenta. Cikin kaushin muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara magana,
“Babu farauta mafi wahala a duniya sama data *_DAMEESA_*. Da ga yau da ga yanzu ki sani. Master tamkar google yake. A kowane lungu da saƙo yanada ido tamkar google a yanar gizo. Duk wanda ya ce zai hanani barci, shima bazaiyi nasa ba. Ina fatan kin ganee karatun?!!”.
Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga hanunsa jikin bangon cike da tabbatarwa da kaushin murya yana jan jikinsa baya.
Nannauyan numfashi Hibbah ta fisga jin ya matsa a jikinta. Ta buɗe idanunta ta watsama bayansa da ya juya harara. Cikin yunƙurowar tsiwar tata da a yanzu ta samu filin fita tace, “Ni kuma Muhibbat Aliyu Hamza gwarzo sai na karya wannan alwashin naka, ina a cikin gidan nan tare da kai zanyi sanadin da za’a faraucekan cikin sauƙi a kuma kama ka. Idan takamarka haɗa hannu da munafukai kuna zaluntar mutane ku sani ko’ina bazakuje ba. Kuma wlhy ko ƙwarzane ya sami ɗaya da ga cikin yayuna sai kayi nadama da ga kai harsu ƙazamai masu ɓoyayyar manufa suna aikata ƙazanta da fasadi aban ƙasa. Shuraim kuma da ka saci fuskarsa kazo ka wargaza aurenmu a ranar ɗaurasa, idan ma ɓoyesa kai ko halakashi kasani sai na ɗiba fansar jininsa akanka”.
Wani shegen malalacin murmushi ya saki. Tare da fara tafa hannayensa a hankali yana juyowa gareta cikin salo da ƙasaita. “Nice baby girl, ina son irin haka????????.”
Sai kuma ya tamke fuska yana sauke mata razanannen kallon da har cikin ranta takejin hantar cikinta na kaɗawa. Amma tsaurin ido da tsiwa ya sata ƙoƙarin danne hakan tana hararsa harya ƙara takowa inda take.
Gira ɗaya ya ɗage da yin mutsu-mutsun fitina da idanunsa. “Da ni Master kike tunanin yin *_TAKUN SAAƘA?._* Lallai zan baki dama, tabbas kuwa zan baki, amma sharaɗin faɗuwa ko nasara zan zartar da sune a lokacin da ɗaya ta kasance…..”
“Ko ka bani ko karka bani dama damata a hannuna take na tona muku asiri. Satoni da kukayi nan bashine ke nufin nasara ba ko cigaba da rufuwar sirrinku. Ɗaura auren yayyena da ƴaƴansa da kuka ƙulla bashike nufin nasarrku akan ahalina ba. Dan haka ka sani, *_TAKUN SAƘA_* da kai dama a cikinta nake tsundum. Dan koba komai a harin farko na maka TAMBARIN da ya saka gudun ceton rai batare da kayi tsammani ba mai idon google”.
Ƙafa yasa ya taɗeta ta faɗa saman gadon, cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi ya ɗaura ƙafarsa ɗaya akan gadon tare da ranƙwafowa kanta. Ƴar mitsitsiyar bindigar da ya zaro a aljihun bayan wandonsa ya ɗaura mata a kan kunne yana zuba firgitattun idanunsa cikin tsakkiyar nata. “Zan iya kasheki a cikin wannan gidan. Na binne gawarki batare da wani mahaluki ya taɓa tunanin binciko inda na kafa ramin ba”………….✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]