Hangen Dala 1HAUSA NOVEL

Hangen Dala 1

©️®️ *SAFIYYA HUGUMA*

????️‍????️????️‍????️ *HANGEN DALA*????️‍????️????️‍????️
_Ba shiga birni ba_

Mallakar

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*_Taqaitaccen labarine wanda ke dauke da kukan kurciya da kuma tsumagiyar kan hanya_*❗

*zaku iya sauraren litattafaina tsofaffi dama sabbabin da zan soma dorawa a dandalin youtube,a tashata ta SAUTIN HIKIMA*

*littafin ALKAWARIN ALLAH yanzu haka yana can nasoma dorashi gamai sha’awar saurare*

 

 

Dai dai lokacin qarfe biyu saura na rana ne,tana zaune cikin madaidaicin falon nata wanda ya wadatu da tsafta,gefe guda kayan yaranta ne data debosu daga kan igiya bayan sun bushe tana ninkesu daya bayan daya tana tarawa a gefanta,gefe daya na zuciyarta cunkushe suke da tunani kala daban daban da taketa qoqarin kauda su.

Idanunta tadaga sanda taji an yaye labulen,maman ummi ce ke shigowa hannunta dauke da qaramar yarinyarta da take goyo,idanu mmn amir(mamallakiyar dakin) tabita dasu tana karantarta,lokaci guda duka ta zabge ta rame tayi firgai firgai,haka taci gaba da kallonta harta samu kan daya daga cikin kujerun tazauna sannan ta aje ummi,wadda tana ajeta ta rarrafa tayi wajen mmn amir,yarinyar na qarasowa ta dauketa tana juyata gami dayi mata wasa yarinyar tasoma dariya
“Yanzu maman amir kina ganin zamanmu a haka yayi dai dai kenan?,munaji muna gani haka baban amir zai sake kawo mana wata cikinmu?,muna zamanmu muda yaranmu cikin kwanciyar hankali zai debo mana matsala?” Ta qarashe maganar wanda kana jin sautin muryarta kasan cewa ba qaramin tashin hankalo bane cikin zuciyarta,daga kai mmn amir tayi daga wasan da takewa ummi ta dubi mmn ummin,ba shakka kishi abune mai ciwo dacin zukata,kuma ita kanta zuciyarta kullu yaumin ba cikin dadi take ba duk da cewa ba wannan ne farau a kanta ba,amma ita kishiya kullum sabuwace a wajen mutum,saidai wannan ba komai bane idan aka kwatanta da sanda xa’a auro mata mmn ummin,banda Allah yasanya ta hadu da iyaye nagari,takuma yi yaqi da zuciyarta da wataqila yanzun hakan ba wannan zancan ake ba,cikin kwantar da murya tace
“To yazamuyi mmn ummi?,baban amir dai bamu muka haifeshi ba bare muce zamu hanashi abinda yayi niyya” kai take kadawa da sauri
“Zamu iya hanashi mmn amir indai zamu hada kai mu duka biyun muyi masa bore kamar yadda nakeyi yanzun,yanxunma abinda yasa haqata ta kasa cimma gaci saboda ni kadai naketa qoqarina kinqi kisa min hannu” qaramin murmushi ya subuce daga fuskar mmn amir tana duban mmn ummin,ta tuna wasu shekaru baya da suka shude,lallai wanzami baison jarfa
“Mmn ummi,abinda nakeso ki gane shine,dukkanmu qarqashin bbn amir muke nida ke gaba daya,duk wani abu da zamuyi don mu tashi hankali komu hanashi aure bamu da riba don Allah ne ya halasta masa,bugu da qari da haka nayi a baya da wala’alla nima bana bigiren da nake kai a yanzu,abinda dai na gayamikin shi zanci gaba da gaya miki,kiyita haquri ki kauda kai,komai yayi farko yana da qarshe,kuma babu wani abu dawwamamme sai ikon Allah,watarana sai labari,hakanan me haquri shike da riba” miqewa mmn ummi tayi cikin fushi da rashin gamsuwa,baki tadan tabe
“Munaji muna gani mmn amir wlh zamu zama ‘yan kallo idan bamuyi da gaske ba,ke kuwa kinsan yadda yarinyarnan ta mallake baban amir?,hala bai taba waya da ita a gabanki bane saini daya raina?” Murmushi ta sake saki
“Ba rainakin da yayi,face ke da kokaqi tsayawa ki fahinci komai…”
“Mmn amir” mmn ummi tayi saurin dakatar da ita
“Wallahi wallahi yarinyar ban labarinta kaf yazomin kunnena,duk cika da batsewar unguwarsu babu tantiriyar yarinya mara kunya irinta,inata boye miki ina miki hannunka mai sanda amma na fuskanci baki gane ba,yana daya daga cikin abinda yasa hankalina yasake tashi kenan,bin malamai take kamar tashin hankali,ki fuskanta mmn amir muyiwa kanmu gata tun batazo ta fiddamu daga cikin yaranmu ba” tsai tayi tana duban yadda mmn ummi ta sake firgicewa,sai data gama sannan tace
“Zauna don Allah mmn ummi muyi magana ta qarshe dake” kaman bazata zauna ba,amma dole tazauna din don neman hadin kai da mafita take,sai data tattara dukka hankalinta akanta sannan tace
“Kin yarda da Allah mmn ummi?” Kaita gyada tana dubanta
“Indai haka ne to ki yarda da cewa babu wata halitta data isa ta cutar dake saoda yardar mahaliccinki,sannan matuqar zuciyarki a wanke take ba wani abu mummuna da xai sameki saidai idan qaddararki ce,duka wannan abun da kikewa baban amir bashi bane zai sanya ya fasa aurensa ba,saima qara nisanta kanki dashi da kike,idan kyautatawa na saka namiji ya qara aure da baban amir bai auroki ba,amma da lokaci yayi hakanan na haqura,na shanye duk abinda yabiyo baya na kama kaina na haqura,wannan abun da kike ba mafita bane,tashin hankali bazai qara miki komai ba sai wani tashin hankalin,ki nutsu don Allah ki sawa ranki haquri da salama” shuru mmn ummin tayi,wanda kafin takai ga cewa wani abu anyi sallama a tsakar gidan nasu,dukansu suka amsa suka zubawa qofa idanu don ganin wanda zai shigo.

Ba jimawa baquwar tayi sallama a qfar dakin mman amir din sannan ta daga labulen tashigo,cikin fara’a maman amir din tayi mata maraba duk da cewa baquwar mmn ummi ce,amma yanayin da mmn ummin ke ciki yasa ta kasa sakin fuska ko tarbarta,gaisawa sukayi sosai cikin mutunci sannan tadubi mmn ummi
“Lafiya kike kuwa maryam?” Baquwar tafada tana duban mmn ummi,shuru mmn amir tayi tana ci gaba da ninke kayanta ba tare data saka musu baki ba,ajiyar zuciya mmn ummi tasaki ba tare data bata amsa ba,saita waiwaya taba duban mmn amir
“Mmn amir lafiya kuwa?” Sai a sannan ta dubi baquwar,tasan cewa qawace sosai ga mmn ummi kuma makusanciyarta,don haka tasan da cewa tasan komai
“Kiwa maryam fada wala’alla keta yarda da zancanki,kan maganar qarin auren bbn amir,gaba daya ta daga hankalinta tafita hayyacinta,ba abinda ban gaya mata ba taqi ji,wai ai tasan halin yarinyar anxo an gaya mata”
“Eh fa,da wannan don wannan,yarinya fa kusan halinta a bayyane yake koni nayi bincike,mara kunyace ta qarshe,sannan ko a gidansu uwarta itake juya ubanta,sai abinda tace,bata ganin kowa da gashi” sosai gaban mmn amir ya fadi,amma saita ambaci sunan Allah ta kuna kauda tsoronta,donta tabbatar idan har hakan ya bayyana to kamar ta baiwa kanta dasu qofa ne
“Idan harka riqe Allah zai isar maka,yakuma tare maka abinda yafi qarfinka”
“Hakane,amma dole ku tashi tsaye,kuyi duk yadda zakuyi wallahi,don nikam ina jiye muku”
“Abinda naketason ta fahimta kenan amma taqi ta gane” mmn ummi tasamu bakin magana a wannan gabar
“Ahto dai” baquwar mai suna rashida tamiqe tana daukan ummi sannan tace
“Bari mu qarasa ciki”
“Toh” kawai mmn amir ta fada,jikinta a sanyaye saidai tana qoqarin qwararawa kanta gwiwa,mmn ummin tabi bayanta suka fice.

**************

Cikin nishadi da walwala ta kashe wayar,fuskarta washe fes tana jin wani farinciki na gewayata,ji take kaman ta mallako baban amir ta gama
“Gaskiya kina sha’aninki rufaida,kinacin duniyarki da tsinke,kin samu mutumin nan fa a hannu yadda ya kamata” dariya rufaida ta sheqe daita
“Wata abu takazar ubanma saina shiga gidan,kinsan Allah?,gaba daya tausayin matansa nakeji” wata muguwar dariya zahra’u tasaki
“Wallahi harkinsa na hango randa zan shiga gidan auwal,ni kaina matarsa tausaya mata nake” kai kawai rufaida ke kadawa cikin nishadi da gadara,tana hango yadda zata maidasu
“Na rantse da Allah duk saisun raina kansu,sainasa a karan kansu sunji cewa su gidadawane basu iya komai ba,sai baqinciki yakusa hallakasu saboda ganin zallar madarar soyayyar da xa’a dinga zubarwa a gidan,zasu gane kurensu,zasuyi danasanin hada kishi dani”
“Allah yakai damo ga harawa” zahra’u ta fada cikin qyaqyata dariya,sai a sannan fatima dake zaune gefe tayi magana
“Wallahi wallahi zahrau da rufaida kuji tsoron Allah gaba dayanku,haka kawai bayin Allah nazaune da mazajensu da yaransu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali zaku je musu da mugun tanadi da baqin qulli na tarwatsa zaman lafiyarsu?,waishinma ce muku akayi matan nasu gazawa sukayi da yasa zasu aureku?”
“Gazawa sukayi mana!…..idan banda tsabar gazawa ta yaya zaki bari mijinki yaga wata harya aura,wallahi dani yasoma aura ko mace daya bazan bari yaqaro ba bare biyu,da basu gaza ba da basu nemu ba” cewar rufaida tana tafa hannuwa gami da jefawa fatima harara
“Kinga qyale wannan,batasan dawar garinba da Allah,ai babu cinyewa da nuna isarki,ki nunawa mace kurenta,ki kuma nuna mata cewa keba sa’arta bace,wutsuyar raqumi tayi nesa da qasa irin ki shiga ki taddata kiyo waje da ita”
“Shine qarshen magana” rufaida tafada tana tattare katin bikinta daya kawo mata dazun tanason tasoma rabo sati mai zuwa,kallonsu kawai fatima take tana kada kai,lallai wanda yayi nisa baya jin kira,ta tabbatar su rufaida sunyi nisa cikin kuskure
“Tashi don Allah tawan mu wuce,igbo road nakeso mu soma zuwa zan kwaso qananun kaya na tarwatsa zuciyar kishiya ya halakata saboda tsabar kishi,kin gansu nan dubu ashirince cif yakawominsu inje in siya” shewa suka saka bayan sun tafa
“Muje muje muje,mu zabi qarshen magana,amm fatima,don Allah idan kin gama ki gayamin saina sameki a gida” rufaida ta fada tana yada mayafinta cikin sauri,har suka fice fatiman bata iya sake cewa komai ba face binsu da kallo da takeyi.
[9/18, 6:22 AM] UmmDiDi????‍????: ????️‍????️????️‍????️ *HANGEN DALA* ????️‍????️????️‍????️
_Ba shiga birni ba_

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button