TAKUN SAKA 42

Hibbah jitai tamkar ta tsala ihu. Tai azamar wuntsilowa a jikinsa, yana son kamota ta zille da gudu tabar wajen.
Binta da kallo yayi yana sakin murmushi da lumshe idanu.
★★★
Hibbah bata sake jin ɗuriyar Master ba har tai shirin barci ta kwanta, zuciyarta cike da tunani da kwaɗayin ganin ahalinta. Wani gefe kuma na imagine yanda su Ummi zasuji cewar Isma’il shine master ashe, dan ita kam har yanzu zuciyarta ta kasa gaskata hakan, neman wanda zasu tattauna maganar kawai take a ranta. Dan tambayoyine fal bakinsa amma kunyarsa da nauyin daya aza mata yasa ta kasa masa ko guda ɗaya.
Tun tana a tsorace da tunanin zai shigo har barci yay awon gaba da ita bai shigo ɗin ba. Sai kusan ƙarfe ɗaya har tamayi nisa a barci sannan ya shigo a matuƙar gajiye da tsananin bukatar barci. Yaji daɗin ganin tayi barcin, hakan na nufin ta ɗan samu ƴar nutsuwa a zuciya da jikinta daya murza a jiya. Shirin barcin yay shima da dukkan abinda yake na al’adar rayuwarsa sannan ya kwanta a gefenta.
*_Washe gari_* tamkar jiya tare sukai sallar asuba. Hibbah dake ta faman sinne-sinnen kai ma ta gaishesa da tambayar jiinsa. Amsa mata yay da tambayarta nata jikin itama, tace ita dai lafiyarta ƙalau. Murmushi yayi kawai bai sake cewa komai ba harya kammala azkar ɗin dayay zamanyi sannan ya mike ya bita gadon. Harta fara lumshe idanu taji saukar hannunsa a jikinta. Babu shiri ta buɗe tana kai hannu zata ture nashi. Hanawa yay ta hanyar riƙe hanun nata da busa mata numfashinsa cikin kunne.
Zatai magana yay saurin tareta da faɗin, “Shiiii bake kikace lafiyanki ƙalau ba”.
“Da wasafa nake ALLAH akwai ciwo”. Ta faɗa da sauri tana buɗe idanunta sai gasu a cikin nasa. Duk kuma yanda taso janyewa ya sarƙesu ta gagara. Wasu mayatattun halittun fitina take gani suna yawo a cikin idanun nasa. A take nata suka fara tara ƙwallar da shi kuma suka sake ɗaga masa hankali.
“A ina ciwon yake?”.
Yay maganar da wata kasalalliyar muryar dake tabbatar da ɗunbin begenta dake cizonsa. Sake rikicewa Hibbah tai zata fara ja da baya yay mata runfa da jikinsa yana jan sassanyan numfashi da busa mata akan fuska. Sosai ta rikice, dan irin abinda tagani cikin idanunsa a shekaran jiya da rana yanzunma shine tattare da shi. A hankali ya ɗaura hanunsa saman nata yana sake matso da fuskarsa gab da tatan. Kai ta shiga jujjuya masa laɓɓanta na motsawa alamar son roƙonsa.
Yasan bazai iya ɗaga mata ƙafa ba, hakan yasashi lumshe idanun nasa dai-dai yana kai laɓɓansa saman tausasan nata, dan dama dauriya kawai yakeyi harya iya ɗaga mata ƙafa da daddare. Rawar jikinta da kukan da take masa yau har yaso yafi na shekaranjiya dan wahalar data sha kawai take ƙiyastowa. Shiko da idanunsa suka rufe bida ita kawai yake ta salo-salon da baisan yama iyaba sai yanzun.
Kuka take sosai tana lafe a jikinsa, nata jikin na ɗan rawa dan yauma ɗin dai wahalar tasha, duk da dai ta shekaranjiyan tafi ta yau sai dai ta yau ɗin ma babu sauƙi dan famine. Shiko babu abinda yake iya furtawa sai shafa bayanta zuwa gashin kanta.
“ALLAH yay miki albarka”.
Ya faɗa a fusge yana sake turata cikin jikinsa har saida ta ɗan saka masa kuka ya sassauta mata. Sai da yaji kukan nata ya ƙi tsayawane ya mike cike da dauriya ya kaita toilet. Yau ɗin ma dai da taimakonsa ta gyara jikinta tana faman masa raki da roƙon ya kaita wajen Ummi ita dai karya kasheta.
Sosai yaji tausayinta dan shima yasan dai yayi gaggawar koma mata duk da wahalar data sha kwana biyu da suka wuce. “Indai wajen Ummi ne zan kaiki, amma sai kin barmin kuka. Kin yarda?”.
Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh ta yarda. Ya sumbaci kumatunta da faɗin, “Good girl! ko ke fa. Kefa yanzun kin girma harkan yara yawane Hibbaty”.
Da wannan daɗin bakin ya taimaka mata suka fito, koda suka sake komawa suka kwanta lafe masa tai a jiki tana jan ajiyar zuciya har barcin wahala yay awan gaba da ita cikin ƙanƙanin lokaci. Sumbata ya kaima goshinta, a ransa wani nutsuwa da kaunarta na ratsashi. Dan a yau yafi jin matuƙar nutsuwa fiye da shekaranjiya da komai yayisa ba cikin hayyacinsa ba.
Barci sosai sukayi batare da wani ya takura musu ba. Dan su Habib ma tun safe suka bar gidan. Baba Saude kuwa da ba sanin mike faruwa tayi ba ita duk ɗaukarta ma Hibbah bata gidanne. Dan tun randa sukazo bata sake ganinta ba master ya kasa ya tsare.
Kusan a tare suka farka. Sai dai jin motsinsa yasa Hibbah ƙin buɗe nata idon. Idanunsa ya zubama fuskarta yana ƙare mata kallo, yanda yaga idonta naɗan motsawa yasan ta tashi. Baiyi magana ba, sai yatsansa daya ɗora saman rumfar idon yana wasa da shi. Dole ta buɗe idanun da ture hannunsa tana kumbura fuska. Murmushi yayi da saƙalo hanunsa ta bayanta ya matso da fuskokinsu dab da juna yana kai mata sumbata.
“Nifa kwana biyu naga harma kin nutsu autan Ummi”.
Yay maganar cikin raɗa tamkar mai tsoron ajisu.
A ranta tace, (ba dolena ba. kana min wannan muguntar nacika magana kace na maka rashin kunya ka fake da hakan ka maidani machine). A fili kam saita marairaice masa fuska tana mar-mar da idanu. “Dan ALLAH yaushe zaka kaini wajen Ummin?”.
Yasan dama shine matsalarta. Maimakon ya bata amsa sai ya lumshe idanunsa yay shiru tamkar bai jita ba. Idanunta ta buɗe tana kallon fuskarsa har batasan ta shagala ba. Sosai yaji idanu na yawo masa a jiki, amma ya dake harda sauya saukar numfashinsa tamkar mai barci. Tunaninta barcin gaskiyarne ya ɗaukesan. A hankali takai hannu bisa girar idonsa ta ɗan gyara, sai kuma ta murza goshinsa kaɗan duk dan son ta tabbatar ba facemask ya saka ba. Sake kumawa tai kan laɓɓansa nan ma dai taji, ta cigaba da shafa kumatunsa da siririn gashi na saje ke kwance har zuwa kunnensa ta ɗan murza nan ma zuwa bayan kunnen da ƙeyarsa. Yanda take masa gaba ɗaya tsigar jikinsa miƙewa take, ganinfa da gaske neman firgita masa jiki takeyi sai da ya shammaceta ya buɗe idanunsa da suka fara sauya kala. Aiko karaf suka faɗa cikin nata. Saurin janye hannunta tai a fiskarsa amma ya riƙe ya dannesa da nasa. Gaba ɗaya ta daburce, baya ta juya masa murmushi na kufce mata dan taji kunya harga ALLAH.
Shima murmushin ya saki da kwantowa bayanta yana son leƙa fuskarta. “Ki kalli mijinki nakine auta, yanda kike auta a gidanku insha ALLAH kece ta fari kece auta a zuciyar Shuraim ɗinki. Karkiji komai, kiyi komai ba komai baby luv”.
Fuskar ta cusa a cikin filon, duk yanda yaso ya janye taƙi. Dole ya haƙura ya miƙe yana dariya da take mamaki. Tanaji ya shiga toilet ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Jin motsin ruwa ya sata tabbatar da wanka yake dan haka ta miƙe ta fara gyara gadon, fatanta ta fice kafin ya fito. Tana cikin gyaran takardun daya ajiye idanunta ya sauka akan wadda ke sama da tsautsayi yasa file ɗin ya ɗan goce suka zubo. Tsugunnawa tai tana tattarosu sai taga tamkar sunan Abbansu a jiki. Duk yanda taso hana kanta dubawa ta kasa, ɗaya bayan ɗaya ta dinga dubasu sai taga duk takardun kaddarorinsu ne da ta taɓa jin su Yaya Muhammad na maganar suna hannun Halilu. Mamaki ya kamata ta cigaba da dubawa har zuwa na ƙarshe da ke rubuce da dogon bayani. Ƙofar bayin ta ɗan kalla jin har yanzu akwai motsin ruwa yasata zaman dirshan ta fara karantawa a nutse……….✍