NOVELSUncategorized

TARAYYA 11-12

Page 11
Haske writers association???? 
Suna isa part din na suhailat dake kallon na yarima itace tayi saurin matsawa ta bude mata qofar tashiga.

Babban parlour ne daya tsaru sosai da uwayen nairorin da aka zuba masa gurin tsarasa,
Royal cushions ne purple and golden komai na palon qyallin adon kalar golden din.
Duk haduwa da tsaruwar part din sultana saidataga wannan ma na suhailat yayi kyau sbd ita atunaninta baza’ataba samun part dinda yakai na sultana tsaruwa da kyauba saigashi na suhailat dinma ya tsaru kamarna sultana duk da tanajin labarin haduwa da tsaruwar part din adama kasancewarta itama ‘yar adoce sosai.
Kuyanginda aka turowa suhailat ‘din sukayi saurin shiga taitayinsu suna mata barka da shigowa.
Hannu kawai ta ‘daga musu tareda kallon rumanah tana nuna mata ‘dakinsu amah tace,
Kije kiyi musu wanka da ruwa marasa sanyi kuma bamasu zafi sosaiba ki shiryasu sai abarsu su huta kafin anjima suci abinci.
Tana gama fadar haka tamiqa mata hannu ta bata handbag dinta ta shige bedroom dinta.
Dakinsu ta nufa dasu tayi musu wanka ta shiryasu harzata fito suka maqale mata takaisu gurin mum dinsu.
Bata saba da yaraba batama ta6a zama da yaraba tun tasowarta
Daqyar tasamu ta lallabasu ta fito.
Tana fitowa part din tasaki ajiyar zuciya sbd gabadaya a takure take sbd tsoro da gudun aikata laifi.
Kodata koma part din sultana a palon farko ta ra6e sbd ganin alamun har lokacin yarima naciki.
Gab da magrib yafito tayi saurin zubewa amma ko lurada akwai mutum shibaiyiba ya wuce yabar part din da qamshinsa.
Sum sum ta nufi palon ciki ta tararda ammyn zaune har lokacin ta durqusa cikin girmamawa tace,
Ammy a table za’a jera abinci kokuwa anan?
Murmushi tayi cikeda farin ciki tace,
Ajera a table kuma ayiwa maheer honey pancakes da sugarless drink sbd bayacin abinci mai nauyi musamman yanxu da daddare
And kihada masa fruitsalad with less apple sai kikai masa part dinsa kisaka a fridge din Palo nasan idan yafito sallar magrib bazai komaba sai dare.
Wani irin yawu ta hadiye na muguwar faduwar data sameta jin inda aka aiketa itadai batason tayi laifi komai qanqantarsa.
Ficewa tayi tafara kawo abinci a second palo tana jerawa a dining jikinta amatuqar sanyaye.
Honey Pancakes din tayi tareda kawowa dining daidai lokacin aka shiga sallar isha takoma tahado fruit salad ta zuba a glassbowl ta ‘daura a tray ta nufi part ‘dinsa qafafuwanta har wani hardewa sukeyi sbd yanda jikinta ke rawa.
Tana isa kallo ‘daya tayiwa guards din qofar ta juya tayi part din suhailat ta saka cikin fridge tareda sanarda kuyangin palon su sanarda suhailat ankawo fruit salad din yarima.
Kodata koma sallah taje tayo tareda komawa part din sultana tana saka kai da sallama dashi idanuwanta suka faracin karo yana cin pancakes din yana yiwa mahaifiyarsa murmushi.
Juyawa tayi da sauri sultana ta lurada ita amma sanin bayi basa zuwa idan yana guri musamman idan abinci yakeci kozaici yasa tabarta takomawarta.
Sai qarfe tara yabar part din sultana yanufi nasa
Yana zuwa ya tu6e yashiga bathroom dinsa da aka cika masa bathtub da ruwa masu matuqar qamshi da ‘dumi ya lumshe fararen oily eyes dinsa tareda kwantawa yana sake jin nutsuwa.
Allah yayisa mutum mai tsananin son rayuwa musamman tajin dadi saidai suhailat bata cika son irin wannan rayuwarba itakuma sbd sunada abubuwan dasuka banbanta ra’ayoyinsu saidai suna qoqarin ganin hakan baitaba rayuwar aurensuba.
STORY CONTINUES BELOW
Sam bayason wanka a shower saidai a bathtub sbd yafison koyaushe yakwanta cikin ruwa tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin kafin yayi wanka,
Itakuma suhailat Sam batason wanka a bathtub saidai shower shiyasa haryau baisamu irin rayuwarda yakesoba sbd basu ta6a wanka atareba
Kwata kwata batama shiga toilet din bedroom ‘dinsa sbd ‘duk girma da fadin toilet dinsa bayason ganin ruwa ko yayane a qasan toilet dinsa itakuma idan tashiga toilet saita gama jiqa koina take fitowa.
A bangaren rayuwar aurensu kuwa Sam bata iya kwana a ‘dakinsa sbd komai dare idan suka gama abinda sukeyi a bedroom dinta take kwana sbd daga ita harshi kowa yafison ya kwana shikadai akan gado shiyasa yawanci zata raba dare a bedroom dinsa susha love dinsu kafin tayo dakinta.
Bayan sun jima da aure yazo yasaba baya iya kwana sai ajikinta amma itakuma dukkanin cikin datakeyi bayason kwanciya dashi hakadai yama cirewa ransa kota haihu basa kwana tare saidai su raba dare tare.
Bude idanuwansa yayi ahankali tareda kallon ruwan sbd qamshin dasuke fitarwa yakalli gaban mirror din cikin toilet din yagansu kaloli kusan guda goma masu kalar qamshi dabam dabam.
Saidayayi mintuna kwance cikin ruwan kafin yayi wanka ya fito daureda brown towel sabo qal ya tsaya gaban mirror tareda goge jikinsa ya fesa Hugo black men’s spray tareda gyara sumarsa da lafiyayyar qasumbar dake kwance a farar fatarsa fuskarsa ya fesa mouth spray mint flavour ya nufi closet ya dauko kayan bacci white colour yasaka tareda nufar makeken lafiyayyan royal bed dinsa dayake gyare da komai white da kusan eight pillows masu laushi.
Wayoyinsa ya kashe tareda ajesu a bedside drawer ya kashe wuta yabar bedside lamps masu duhun haske.
Kwashe komai tayi tasake gyare palon tayiwa ammy Saida safe ta nufi gefensu na bayi anatse.
Tana zuwa babu kowa a dakin ta kwanta bayan tacire uniform dinta tasaka tsohon uniform dinta sbd sune tamayar na bacci dama idan akaga uniform dinka sun mutu ana baka wani.
Kodasu mamani suka shigo idonta biyu amma ta lafe tanaji mamani nata fada tana zaginta
Ta share hawayenta tareda rufe ido tana danne kukanta.
Tundaga ranar kusan itace take wahala da suhailat da ‘yaranta sbd kullum ita sultana ke aikawa tana yiwa yaran wanka takuma kaimusu abinci ta Jere a dining safe rana dare saiya zamto ayyuka sunmata yawa danma babu laifi suhailat na sakar mata fuska sosai hakama yaran ba laifi suna yarda da ita ba kamar kowaba sbd kullum ita ake sawa ta daukosu takawo gurin sultana su yini kokuma gurin sarauniya adama.
*
Sati ‘daya da zuwansu yarima yana zaune gaban sultan sbd kiransa dayayi cikeda girmamawa yake sauraren mahaifin nasa.
Cikin iko da umarni sultan yace,
Aure zaka qara maheer ibn abdulshams.
Shiru yarima yayi cikin tsananin mamaki tsawon lokaci harsaida mataimakin sultan yasake maimaita masa kafin ya ‘dago manyan oily eyes dinsa yakalli haris abdallah mahaifin khaleefa kuma mataimakin sultan yace,
Ina bawa sultan da mataimakinsa hkr sbd babu sha’awa ko burin qara aure arayuwata.
Wani shu’umin murmushi sultan yasaki tareda sake maimaita zancensa.
Shima maheer cikin girmamawa yasake maimaita amsarsa.
Kallonsa sultan yayi yasan sarai waye maheer saidai bazai barsaba zaiyi amfani da qarfin ikon mulkinsa dakuma ikonsa na mahaifinsa akansa.
Batareda yakallesaba yace,
Maheer ibn abdulshams zabin farkone nabaka na qarin aurenka.
Rufe idanuwansa yayi ahankali yana danne 6acin ransa yace,
Ina qara bawa sultan hakuri akan wannan buqatar tasa sbd idan nayi auren bansan yaya zan iya kwatanta adalcin kulada mata biyu ba.
Murmushi sultan yasake saki tareda kallon sarkin gida dake tsaye da sauri yafice ya nufi hanyar part din sultana.
Mintuna qalilan akayiwa Jakadiya iso tashigo tareda zubewa qasa tana gaisuwa.
Cikin mulki da nuna ikonsa yace,
Jakadiya aje yau awanke masa baiwar datafi kowace kyau ‘daya cikin biyar ‘din danace agyara akai masa daga yau aringa kaita kowane dare harsaitayi ciki,
Kuma daga yau an dakatarda matarsa zuwa gurinsa sai baiwarsa tayi ciki
Idan ya kaucewa umarnina Jakadiya ki sanarda sultana zaarah na sauketa daga matsayinta na sultana kiyiwa adama albishir da samun sabon matsayi. 1
Yana fada ya miqe nan dukkanin su haris abdallah suka miqe yashigewarsa palonsa na musamman.
Cikeda girmamawa Jakadiya tace,
Angama sarki mai adalci.
Miqewa tayi da sauri ta fice sbd ganin halinda yarima yashiga sbd tsananin 6acin ransa da baqin cikinsa daya kasa 6oyuwa.
Miqewa yayi yafice kai tsaye part dinsa ya nufa tareda bawa guards din qofar part dinsa gargadin duk Wanda yayi motsi mai qarfinda harzai shigo part dinsa yadamesa arufesa tsawon shekara guda.
Jin haka yasa akayi sanarwa tuni kowa ya nutsu yashiga taitayinsa.
Jakadiya kuwa cikin qanqanin lokaci tasa aka tara dukkanin wata baiwa dake masarautar mai shakatun dabasu wuce sha takwas,sha tara zuwa ashirin da uku da hudu.
Koda aka kira duk suka halarta banda rumanah dake bedroom din sultana tana jera kaya acikin closet.
Duk iya damuwa da rashin mafita sultana naciki sbd tun binciken farko Jakadiya tace bataga wadda ta daceba gashi sultan yace yau.
Zaune kawai take amma hankalinta nakan halinda maheer yake ciki yanxu.
#mamuhgee
Page 12
Akan nuratu jakadiya ta tsayarda idanuwanta tana nazarinta sbd zama da rumanah yasa itama takeda nutsuwa daidai gwargwado…… +
Tsaya to idan zama da rumanah yasa takeda nutsuwa ba kamar mahaifiyarba me zai hana su dauki Mai nutsuwar gabaki daya.
RUMANAH”””shine sunan dayazo ranta atake tasaki murmushi cikin farin ciki sbd tasan sultana idan taji ta inda jikokinta zasu fito bazataji damuwaba.
Sallamarsu tayi tareda juyawa kar tsaye ta nufi hanyar zuwa gurin sultan.
Tana zuwa akai mata iso cikeda girmamawa ta zube gabansa cikin bayyanarda farin cikinta tace,
Allah yataimakeka ansamu baiwa mafi nutsuwa da kyawu acikin bayin masarautar mineelik,
Baiwa ummu-rumanah ‘yar tsohon aminyaccen bawanka bulama.
Shima wani irin murmushi yasaki tareda kallon Jakadiya yace,
Allah yayi saina hada zuria da bawa mafi soyuwa agareni
Aje ashiryata yau za’a fara rakata turakar yarima
Bulama Allah yaji qanka da rahamarsa,
Jakadiya kije idan ta haifi namiji ina miki albishir da akwatin dalolin amurka. 9
Miqewa tayi tana zuba godia da farin ciki tareda adduar asamu biyan buqata.
Lokacinda ta isa gurin sultana ta zube gabanta ta zauna cikin farin ciki tace,
Allah yataimakeki Ansamu wadda nasan zakifi kowa farin cikin fitowar jikokinki ta tsatsonta.
Kallon rashin fahimta sultana tayi mata cikin qoqarin Kore damuwarta sbd jin ansamu mafita.
Baiwa ummu-rumanah ta wajenki itace nakega tafi cancanta da’a za6a sbd ganin nutsuwa dakuma shakuwar dake tsakani.
Wani irin kallo sultana ta jefi Jakadiya dashi cikin mamaki da takaici.
Datasan rainon datakewa rumanah na idan tasamu sanin asalintane daga mamani ta ‘yantata danta koma gida cikin yan uwanta ne.
Dauke kai tayi cikin bada umarni tace,
Kije kinema masa wata banda rumanah.
Kallonta Jakadiya tayi da sauri cikin mamaki tace,
Allah yataimaki sultana naga tafi kowace baiwa cancanta tazamo uwar jikinki koba komai tunda ‘danki ne ba wani akace akaiwaba.
Girgiza kai tayi tareda juyawa takalli qofar bedroom dinta da rumanah ta fito cikin nutsuwa daukeda zanin gadon data cire ta fice tana mamakin kallonda suka biyota dashi kamar ta canza.
Laundry din masarauta ta nufa takai kayan ta karbo wasu sabbin zannuwan gado masu laushi farare qal tana fitowa mamani ta shigo part din laundry din daukeda kayan wankin adama itama takawo.
Saurin matsawa tayi tana cewa,
Mamani sannu da aiki.
Tsayawa mamanin tayi tareda kasa danne baqin cikinta da takaicinta akan rumanah din sbd ko yauma dai ba’a zabi nuratu ba sbd ko wanka batayiba.
Cikin takaici tace,
Rumanah tunda kika zuga nuratu Dan karmu samu farin ciki kema bazaki ta6a farin cikiba arayuwa,
Keda iyayenki kunzamarmin muguwar qaddara sun mutu sunbarmana masifa gashinan kin shiga tsakanina da yata kin shiga tsakaninmu da farin cikinmu….
Rintse idanuwanta dasukai jajir tayi Cikin dannewa tace,
Kiyi hkr mamani bawa baya wuce qaddararsa ko…….
Shaqota tayi cikin tsananin baqin ciki jitakeyi kamar ta cire takaicin iyayenta na shekara da shekaru akanta ta huta.
Hawayen wahala rumanah ke fitarwa sosai batareda tayi yunqurin kwatar kantaba.
STORY CONTINUES BELOW
Motsi yasa mamani sakinta ta kwashi kayanta ta wuce zuciyarta na tafarfasa.
Kukan datake riqewa tana shiga bedroom din sultana tasakesa zuciyarta na quna,
Sosai take kuka tana shesheka sbd yanxune take ‘dandana maraici da quncin dake cikinsa,
Wannan karon harcikin ranta takejin qunci da radadin abinda mamani ke mata shiyasa takasa danne kukanta duk yanda taso.
Sheshekar kukane yadauki hankalin sultana da jakadiya cikin sanyin jiki suka dubi qofar cikeda tausayawa Jakadiya tace,
Sultana amincewa kibada rumanah shine zai sanyaya mata qunci da damuwar datake ciki na  uwar riqonta sbd natabbarda shine zai nesantata daga uquba da tsangwamarta.,
Koba komai wannan itace iya mafi girman soyayyar dazakiyi mata ta amince mata ta zama mai kawarwa da ‘danki sha’awarsa.,
Har abada rumanah bazata ta6a wulaqantaba idan ta hada shimfida da yarima koda kuwa bata haihuba,
Ki qara dubawa sultana.
Shiru tayi tareda rintse idanuwanta cikin rashin madafa da shawara sbd bata fatar rumanah tazama baiwarda za’a riqa kwana da ita tana haihuwa ana kar6e ‘yayan daga qarshe kuma asallameta tayi nesa da qasar bazata qara kusanto ‘yayantaba.
Wani 6angaren kuma batada wata mafita ko ba6in daya wuce rumanah din Dan itace taga tafi cancanta da jikokinta su fito daga gareta koba namiji bane itadai gwara ace rumanah ‘dince ta haifar matasu ba wata baiwarba
Saidai zuciyarta na ganin kamar bata yiwa asma’unta adalcin zaman amincin dasukayiba
Hakama zuciyarta na hango mata wani irin rikici da tashin hankali agaba akan hakan.
Miqewa tayi cikeda damuwa da fargabar rashin madafa,
Masarautarsu has been cursed tun shekara da shekarun dasuka shude,
Duk wani abin alkhairi baya ‘dorewa a masarautar,
Sarakunansu hankalinsu da tausayinsu tareda imaninsu yana gushewa daga lokacinda suka hau kujerar mulkin basa da hukunci saina yankewa duk Wanda yayi laifi kisa,
Hannuwa da qafafun sarakunansu na jiqene da jinin mutane,
Sarakunansu are posses,
Duk Wanda ya alaqantu da kujerar mulkin mineelik sai cursed din yashafesa sbd mugun abin daga kujerar yake.,
Jakadiya kinsan me zamantowa uwa ga magajin masarautar nan yake nufi,
Maheer yaqi karbar sunan magajin sarkine sbd kubutardani daga zamtowa cikin makusanta kujerar mulkin,
Yaqi karbar sunan ne sbd kubutarda kansa daga jiqa likkafaninsa da kabarinsa da jinin bayin Allah, 5
Kinfi kowa sanin tarihin masarautar nan da abinda ke bibiyarta shine zamu ‘dauko yarinyar da batada hakkin komai musakata da abinda zata Haifa?
Rumanah kwaqwalwarta bazata iya daukar masifun dazasu biyo bayan zamtowarta mahaifiyar magajin masarautar nanba,
Idan muka sakata cikin wannan masifar muka jiqa hannuwanta da jinin mutane bamuyi mata adalciba,
‘Dana yakubatardani da kansa daga wannan masifar shine zamu saka yarinya aciki bayan batasan me hakan ke nufiba.,
Sultan alamarin yariga ya dade shigarsa ayanxu koda ‘Dan cikinsa baya tunani biyu kafin ya yanke musu hukuncin kisa,
Masifar tariga tashiga jikinsa bayaji baya gani rashin bin kowane irin umarninsa daidai yakeda fitar ranka….
Cikeda sanyin jiki Jakadiya tace,
Hakan zaki tuna kiyi hkr kibada rumanah idan ta haihu mu tseratarda ita ta hanyar turata nesa inda har abada bazata sake kawo kanta nanba wannan shixai mata Katanga daga zamowa MINEELIK-ASSULTANAH TA BIYU.
Shiru sultana tayi cikeda tsananin tsoro da fargabar abinda suke shirin yi,.
Fitowar rumanah daga bedroom dinta yasasu juyawa qofar.
Sunkuyar dakanta tayi sbd fuskarta datayi jajir sbd kukandatayi.
Wani irin mugun sabon tausayinta yashiga sultana batasan lokacinda tajawota jikinta ta rumgumeba cikin wata irin sanyin murya tace,
Asma’u ki yafemin.
Rumanah kema karki qullaceni.
Batamaji abinda ammyn kefadaba sbd kukanta daya dawo sabo tuntuni take Neman Wanda zai rarrasheta koda tsuntsune sbd mawuyacin halinda take ciki.
Jakadiya ma cikin tsananin tausayin rumanah din can qasan maqoshi tace,
Ki gafarceni rumanah amma rayuwarki ta birkice daga lokacinda kika haifi ‘da namiji sbd qaunar danake yimiki ina miki fatar samun ‘ya mace sbd kubuta daga muguwar tsinuwar dakebin makusanta kujerar masarautar mineelik.
Saida rumanah tayi kuka sosai Wanda hakanan yake zuwa takasa tsaidasa saidatayisa sosai kafin sultana ta ‘dagota tareda kallon fuskarta tana maida hawayenta takalli jakadiya tareda ‘daga mata kai ahankali.
Tasaki rumanah tayi bedroom dinta tanaji ajikinta haqqin rumanah bazai taba barinsuba.
Jiki amatuqar sanyaye ta juya ta fice Jakadiya tabita da kallon tausayi.
Tana zuwa dakinsu ta zauna bakin katifarta tareda rafka tagumi ta fada tunani.
Nuratu ce tashigo dakin tayi saurin isa gurin rumanah din kawai ta rungumeta Tana cewa,
Rumanah karki karaya kisake jajircewa kina haquri da mamani zata daina wata rana ko ance tayi bazatayiba. 1
Murmushi mai ciwo tasaki tareda kallon nuratu tace,
Mamani uwace banta6a riqeta arainaba.
Zuciyarki nada kyau rumanah Allah yabarki ahaka.
Murmushi tayi tace,
Ummana,abbanah da ammy bayansu kece mutum ‘daya dana sani mai zuciya mai kyau Dan haka keda ammy Allah kuma yabarku ahaka.
Dariya sukayi suna qoqarin manta damuwar abinda yafaru.
Ahankali nuratu takalleta tace,
Rumanah kintuna lokacinda muke wasar riqe riqen gudu da ruwa a cup a dakin nan?
Murmushi tayi tareda kallon nuratu sbd wannan wasar itace abinda bazata ta6a mantawaba a quriciyarta,
Itace abinda nuratu ke tuna mata tasakata nishadi amma yau saitaji jikinta yayi sanyi tace,
Meyasa kika tuna wannan yanxu?
Haka kawai na tuna sbd bansaniba kobazamu sake samun damar tunawaba irin haka cikin jindadi.
Qurawa nuratu ido tayi zatayi magana aka shigo dakin.
Kallon qofa sukayi sukaga bayi kusan biyar atsaye saiga Jakadiya tashigo fuskarta a tamke babu alamar wasa takalli rumanah ta ‘dauke kai ta juya Tana cewa,
Ku taho da ita zuwa part din gyara yanxunan.
Tana fada ta fice sbd kar tausayin rumanah yashigeta.
Kallon juna sukayi itada nuratu irin kallon da nuratu ke mata na tsananin tausayi yasa tayi saurin kallon qofar da jakadiya ta fita tayi kafin tasake kallon nuratu da tuni hawayen rabuwarsu ya gangaro mata.
Matsowa sukayi suka kama hannunta ko qwaqwaran motsi bata iyayi suka fice da ita.
#mamuhgee

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button