NOVELSUncategorized

TARAYYA 19-20

Page 19
Cikin nutuwarta ta tura qofar palon tashiga da siririyar sallama taga baya palon ta sake hadiye wani yawun tana qoqarin daidaita numfashinta da

nutsuwarta ta nufi qofar bedroom din data gani tayi knocking ahankali sbd sanin bayason hayaniya. +

Jin shiru yasa tasake knocking din amma shiru ganin kar abincin ya huce tayi laifi kuma ga tunanin bayason yin mgn ne yasa ta murda cikin tsoro tsoro ta shiga tareda rufe qofar ta juyo ta tsaya jiran umarni
kanta asunkuye yake jin shiru yasata dagowa taga baya dakin saitayi tunanin qila yana dayan dakin harzata juya sai qofar bathroom ta bude ya fito daure da towel a qugunsa light brown sabo qal murdadden jikinsa da muscles sai glowing yakeyi ruwan wanka na gangara alamar tsantsin fatarsa,
a tsorace ta kalli qofar idanuwanta yashiga cikin nasa da sauri ta juya masa baya duk ilahirin jikinta da muryarta na rawa tace,
Yi,,,ha…kuri ammy tace na..
Tray din hannunta ne ya kufce sbd rawar da jikinta keyi tayi saurin riqewa tana qoqarin saita nutsuwarta sbd jin baice komaiba har lokacin.
Bayanta ya qurawa ido duk da tajuya baya yana iya ganin yanda numfashinta ke fita da qarfi sbd kafadunta dake sama suna sauka baisan da ita akazoba saidai kuma baiyi mamakin ganintaba sbd sanin waye ammynsa idan tanason mutum.
Closet dinsa ya nufa yaciro kaya marasa nauyi,
Wata black transparent  Louis vuitton longsleev yasaka da farin wando na Louis Vuitton sai turarensa na Clive Christian imperial Majesty.
Duk abinda yakeyi ko ajikinsa baburuwansa da tsayuwarta
Zama palo ya nufo batareda yace mata qalaba ganin harya fice baice mata komaiba ta biyo bayansa,
A palon ta tarardashi yazauna yana kunna wayoyinsa daya kashe
Sanin yanda jinin sarauta yake yasa ta matso gabansa a natse ta ajiye tray din kan table din gabansa ta bude masa komai cikin tsoro tsoro sbd gudun laifi.
Fridge ta bude ta dauko ruwa marasa sanyi sosai tazo ta ajiye masa.
Kallonta yayi wannan karon ba ‘Dan mamaki sbd wannan shine karo na farko dazaici abinci agidansa da ruwa ajiye gabansa tun baici abincinba batareda yace akawo masaba,
Koyaushe idan zaici abinci suhailat da mai aikinta Carolina basa kawo masa ruwa kullum saiyace akawo masa bayan yayi nisa dacin abincin. 1
Ficewa tayi tasauko ta nufi kicin suka cigaba da aikinsu.
Bayan mintuna Carolina takoma takwaso kayan.
Saukowa yayi su amah dake fitowa daga dakinsu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa.
Daukar fammah yayi yariqo hannun amah yana cewa,
Heyy daddy’s girls.
Zama yayi kusada sultana yana ajiye fammah kusadashi yace,
Gud morning ammy?
Morning or afternoon maheer look at the time.
Bai kalli agogonba yace,
Nace ina kwana ne ammy sbd bamu haduba tun safiyar yau sai yanxu so…..
Murmushi tasaki tareda dafa hannunsa dake kan nata ta juyo da kyau takallesa cikin kulawa tace,
Yaya suhailat I hope kunsamu shawo kan matsalar?
Shafa kan amah yayi yace,
Amah take your sister and go to your room idan nagama mgn da ammy zanzo okkk?.
Tashi sukayi riqeda hannun juna suka nufi room dinsu da gudu cikin wasa.
Lumshe oily eyes dinsa yayi batareda yajuyo yakalli ammyn ba yace,
Anmata cs babyn bezo da raiba
Sbd wahalar datasha sosai bamason ta farko yanxu saitayi 48 hours.
Kallonsa sultana tasakeyi cikin tausayawa tace,
STORY CONTINUES BELOW
Allah yabata lafiya yakuma tsare gaba amma babyn mace ce ko….
Kasa qarasawa tayi sbd faduwar da gabanta yayi na rashin wace amsa zai bata.
Its a boy.
Kallonsa tayi amatuqar firgice da tsananin mamaki saidai tayi saurin yin istighfar sbd agurin Allah komai mai yiyuwane.
Shiru tayi zuciyarta na wasi wasin abinda takeda niyar yi akan zaman rumanah dashi saidai tsoro yafara shigarta,
Idan dama ‘yaya mata Allah yaqaddaro maheer zai fara haifa kafin yaya maza idan ta tura rumanah gurinsa tasamu ciki yanxu yaya kenan..
Rufe ido tayi Cikin Cikin zuciyarta tace,
Ya Allah kasa ‘Dan nan daya shi maheer zai Haifa harsai sunsamu makarin dazai karye abinda ke bibiyar sarakunan mineelik.
Fitowar rumanah daga kicin zatazo tambayar ko ammyn nason wani tana ganinsa ta juya tun bata qarasoba sultana tabita da kallo tana cewa,Allah yakaremin ke ‘yar amanata.
Tashi yayi yanufi dakin yaransa ya tararda suna drawings ya zauna bakin pink gadon amah yayi crossing legs ya qura musu ido sun saba da dadynsu bamaison magana bane yasa basu damuba presence dinsa kawai nasasu farin ciki.
Saida maraice yaje asibiti ya dudduba reports din suhailat sai bayan magrib yadawo lokacin ammy na bedroom dinta.
Kai tsaye ya wuce sama wanka yafarayi yasako jallabiya fara qal tareda tareda sakin gashinsa dakeda ‘Dan tsawo ya sauko ya nufi gurin ammy.
Yana bude dakin tana budewa ta fito harsaida qirjinsu ya hadu da juna tayi saurin ja da baya tana sauke kai
Shikuwa yi yayi kamar baisan meya faruba ya shigo tayi saurin ficewa.
Dakinta taje tana shiga ta tube tafada wanka.
Tana fitowa tayi sallar ishai ta fesa spray ta saka kayan bacci Riga da wando farare  masu santsi tana cikin daure gashinta  Carolina tashigo tace sultana nakiranta.
Aje daurin gashin tayi ta dauki diguwar riga bai budadden gaba tasa tareda rufe kanta da hular rigar ta fita.
Zaune ta tararda ammyn bakin gado cikin shirin bacci cikeda girmamawa tace,
Ammy gani.
Yauwa rumanah idan kingama shirin bacci kije sama dakin maheer ki kwana can idan zaki kitafi masa da tuffa.
To tace kanta asunkuye tareda juyawa ta fice..
Wannan halin na biyayyar rumanah akan kome akasata yasa take qara qaunarta.
Bata koma dakiba kicin taje ta bude fridge ta dauko apples din guda biyar ta jera a glass bowl da ‘yar qaramar wuqa ta fito ta nufi saman.
Sanin qila baya palo yasa ta bude qofar palon ta shiga ta nufi bedroom dinsa tayi knocking ahankali.
Saidatayi so uku taji shiru tasan bazai amsaba yasa ta bude dakin tashiga.
Zaune yake yana waya da doctor Edward daya kirasa yana fada masa wasu results din suhailat dasuka fito.
Gabansa ta isa ta aje kan table din daya Dora qafafunsa ta juya
Palo taje ta dauko masa ruwa da cup tadawo ta ajiye daidai lokacin ya gama waya ya miqa mata hannu tabasa ruwan yakarba yasha
Kamar bazaiyi magana ba yace bana buqatar apples din yanxu take them back.
Dauka tayi tamayar fridge din palonsa tadawo ta dauke cup da ruwan dayasha tamayar saita kasa dawowa cikin dakin ta tsaya qofar dakin tana zullumin komawa kuma bazataso taqi bin umarnin sultana ba koda kuwa a mafarkintane.
Tun tana tsaye qofar bedroom din hardai ta zauna bakin qofar dakin ta jingina da qofar ta lufe idanuwanta tana tunanin rayuwarta yanda ta jujjuyawa yau wannan gobe wancen,
Tafaro amatsayin ‘yar bayi,
Tadawo baiwa daga baiwa takoma tamkar sa ‘daka yanxu kuma gata a ‘yantatta kuma matar ‘Dan sarki batasan kuma gobenta meta tanadar mataba.
Da asuba ya tashi yayi alwala yasaka jallabiya da farar qaramar hula yasa ya nufi qofa Dan zuwa masallacin da dake kusa dasu na wani balaraben qasar.
Yana bude qofa yayi tuntube da ita kafin yayi qoqarin hana kansa kaiwa qasa tuni ya fada samanta da sauri suka kalli juna cikeda mamaki yake kallon idanuwanta dake cike taf da tsoro.
Kallonta yakeyi batareda yadagataba kokuma yayi mgn.
Idanuwansa yamaida kan qirjinsu dake hade numfashinta dake fita da qarfi yana qara hade jirjinsu.
Hawayen azabarda hannunta keyine suka gangaro mata kuma bazata iya cewa yadagaba.
Hawayen yabi da kallo kafin yakalli cikin idonta cikin wata irin murya yace,
Inada nauyine? 20
Rufe ido tayi ahankali tareda girgiza kai.
Sake kallon idonta yayi yagano wani Abu yatashi ahankali ya miqe tsaye.
Tashi tayi ta dafa zata miqe takasa sbd azaba Dan taji lokacinda kashin hannunta ya targade.
Hannun yakalla nantake yagane taji ciwone yagane dalilin kukanta kenan.
Hannu ya miqa mata cikeda bin umarni ta kama ya miqar da ita ta juya da sauri zata fice ya riqo hannun tareda dawo da ita harsaida ta fado jikinsa hular kanta ta Zame.
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya zuba mata idanuwansa tareda kamo hannun ya matsa still idanuwansa na kanta
Rintse ido tayi da qarfi sbd zafi
cikin lazy voice yace,
Akwai zafi? 4
Saki jikinta yayi daqyar ta iya girgiza kai.
Mamaki tabasa wani malalacin murmushi ya fito gefen bakinsa ya sake matse hannun sosai sai kawai ganin yayi ta zube jikinsa idanuwanta na rufewa. 1
Shiru yayi yaji tabbas suman azaba tayi ya dago fuskarta yakalleta cikin maqoshinsa yace,
Unbelievable.
‘Daukarta yayi ya kwantar a kujerar palon ya tayarda sallarsa hankali kwance saida yagama tukuna yadauko ruwa a fridge yazuba mata kadan
Ajiyar zuciya tasaki tareda bude idanuwanta ahankali
Kan fuskarsa idanuwanta suka sauka ta lumshe ido tasake budewa sai kawai hawaye suka fara gangaro mata.
Qura mata ido yayi yana mamakin hawayenta sbd dukkanin alama na ciwon datajine abinda baitaba ganiba ga suhailat duk kuwa wuya da azaba yanada wuya suhailat tayi hawaye
Ita kuma wannan hawayen nata na shagwabane tunda daga Dan wannan ciwon sai hawaye.
#mamuhgee
Page 20
Haske writers association???? +
Not edited.
Dagowa tayi takallesa tana qoqarin tsayarda hawayenta
Suna hada ido ya miqe tsaye ya nufi bedroom dinsa batareda yace qalaba ko waiwayenta.
Kallon hannunta tayi dake radadi sosai tasaka ‘dayan hannun ta share hawayenta ta miqe ahankali taja hular rigarta ta rufe kanta ta nufi qofa ta fice.
Tana saukowa ta tararda Carolina a palo tana qoqarin fara aikin gyaran gidan sbd su amah zasu school.
Kallonta Carolina tayi cikeda mamakin ganinta tana saukowa daga saman a wannan time din saidai kuma ba abinda yashafi aikinta bane sai kawai taci gaba da aikinta
Itama rumanah nauyin Carolina din taji yasa takasa yimata magana ta nufi dakinta tashige.
Toilet tashige tayo alwala daqyar sbd ciwon hannunta tafito tayi sallah tana gamawa ta fito ta nufi kicin saidai duk yanda taso tayi aiki kasawa saidai takoma daki ta zauna ta qurawa hannun ido tana tuno yanda ciwon yasamu.
Lumshe ido tayi tuno kalamansa”””inada nauyi ne?”””
Sai a lokacin mamakin maganarsa yake shigarta
Tasake tuno qaqqarfan jikinsa saikuma tayi saurin lumshe idanuwa sbd kunyar ganinsa dataji saikuma taji sanyin qamshin turarensa yashiga hancinta tayi saurin bude ido taga babu kowa zuciyarta ta buga da qarfi.
Mikewa tayi ta nufi jikin window ta tsaya
Wani sabon qamshinsa taji yashiga hancinta har zuciyarta ta rufe fararen idanuwanta ahankali tareda budesu takoma bakin gado tasake zaunawa har lokacin hancinta da idanuwanta sunkasa daina jiyo qamshinsa
Zuciyarta takasa sukuni
Rashin sukunin hakan yasata miqe tafito jiki asanyaye ta nufi kicin.
Duk yanda taso yin aiki a kicin kasawa tayi sbd rashin nutsuwar datake ciki gashi hannun yafara kumbura saidai batajin zafin kamar yanda takejinta cikin rudu da rashin sanin abinda yake damunta.
Kallo Carolina tabitadashi ganin kamar tana cikin damuwa gakuma hannunta daya kumbura cikin tausayawa tace taje daki ta huta tana kwatanta mata da hannu.
Murmushi qarfin hali tayi zatayi magana doorbell yayi qara atare suka kalli agogo da Carolina sukaga qarfe bakwai da minti goma,
Wanke hannu Carolina tayi ta fito cikin din ta nufi qofa ta bude.
Dawowa tayi riqeda leda fara ta kalli rumanah tace taduba mata chips data zuba ta nufi sama.
Knocking tayi ahankali saidai ba amsa hartagaji bail budeba harta aje saidai tadawo qasa dashi takalli rumanah tace magani ne batasaniba ko urgent yake buqatarsa gashi bata shiga bedroom dinsa ta miqawa rumanah tace ta taimaka mata taje gurin sultana tafada mata kozata kirasa awaya tasanar masa.
Qura mata ido rumanah tayi sbd sanin bata tada sultana idan tana bacci ataqaicema lokacinda take tashi bacci baiyiba saidai zuciyarta na fargaba da idan yana buqatar maganin ne a gaggauce.
Karbar maganin tayi ta fito palo ta nufi dakin sultana saidai kuma tasamu kanta da tsayawa cak sbd qila yana cikin wani haline yake jiran maganin.
Juyawa tayi ta nufi saman tana qoqarin danne faduwar gabanta harta isa ta shiga palon ta nufi qofar bedroom din tayi knocking.
Shiru ba amsa tasake yin knocking din still ba amsa
Kasa juyawa tayi ta rabe qofar dakin gabanta na tsananta faduwa hakama takasa tafiya sbd fargaba.
Jin shiru sosai yasata qara kwankwasawa cikin nutsuwa tana qoqarin sake kwankwasawa aka bude dakin hakan yasa saura kadan ta fada masa tayi saurin daidaita tsayuwarta tareda sauke kanta qasa daqyar ta furta,
Ga saqo aka kawo.
Batareda yakalletaba ya karbi maganin cikin maqoshinsa yace,
Wait.
STORY CONTINUES BELOW
Cak ta tsaya ya bude ledar yaciro maganin yaduba ya miqa mata.
Dagowa tayi suka hada ido danasa dake kafe da ita tasaka hannu takarba hannunta yakalla batareda yaqara cemata komaiba ya rufo qofar.
Hannunta daya kalla yasa ta fahimci mai hakan ke nufi takalli ledar maganin tasaki fuska akaro na farko datayi murmushin daya fito daga zuciyarta tun bayan rasuwar iyayenta.
Saukowa tayi ta nufi dakinta ta ajiye maganin ta zauna duk bayan minti qalilan tana waiwayowa takalli ledar.
Qarfe takwas su amah suka tafi school bayan fitarsu da awa ‘daya ya sauko cikin wasu blue black Balenciaga’s suit dogon gashinsa a daure qamshin turarensa na annick goutal mai sanyi ya ratsa palon sosai wayarsa ce kawai ahannunsa sbd meeting zaije ba ba asibiti ba saiyadawo zaije hospital din.
Itakadaice a palon itama fitowarta kenan cikin doguwar riga ash zata dakin sultana sbd lokacinda ake gyaran dakinta yayi.
Sunkuyar dakai tayi sum sum tashige dakin sultana.
Tana shiga ta tararda ita zaune kan couch tana waya cikin girmamawa ta durqusa tagaida da kai ta daga mata sbd wayar datakeyi. 1
Tashi tayi tafara qoqarin gyaran dakin cikin dauriya sbd tsananin azabar da hannunta ke mata saidai bazata iya barima sultanar tasaniba.
Shigowa dakin yayi da sallamarda shikadai yaji abarsa ya nufi gurin ammyn ya sumbaci hannunta data miqa masa yana cewa,
Saba’ul khair ya ammy.
Murmushi tasakar masa tareda katse kiran ta ajiye wayar tana cewa,
Barka da fitowa yarima maheer.
Kallonta kawai yayi batareda ya amsaba yace,
Zan fita sainada dawo.
Allah yatsare but did you take your breakfast?
Kai kawai ya daga mata ya juya haryakai bakin qofar dakin ya tsaya batareda yajuyo ba cikin husky voice dinsa yace,
Bani fruits din gaban ammy. 1
Yawu ta hadiye cikin faduwar gaba sanin da ita yake saidai bazata iya dauka da hannu dayaba dole sai biyu gashi batason ammy tasanda ciwonta.
Kallonsa ammy tayi cikin mamaki ganin baya tabacin abinda bashi aka kawowaba.
Cikin sanyin jiki ta aje pillon dake hannunta ta je gaban ammy ta dauki dan glass bowl din amma tuni hannunta ya gaza bowl din yafadi qasa ya fashe.
Da sauri ammy takalli fuskar rumanah din
Da sauri ta durqusa zata bada hakuri sultana takalli hannunta cikeda mamaki da kulawa tace,
Rumanah hannunki akumbure,
Ciwo kikaji shine kike aiki?
Numfashi ya sauke a maqoshinsa kafin ya ficewarsa sbd dama abinda yakeson ammyn ta fahimta kenan. 2
Ita kanta tagano dan ammy tasan taji ciwo yasata daukar Abu mai nauyin da bazata iya dauka da hannu dayaba saidai batasan dalilinsa nayin hakanba.
Qura mata ido ammy tayi cikin sigar fada tace,
Meya samu hannunki ya kumbura haka kamar ma karywa ko targade.
Kallon qofar daya fita tayi asace kafin ta sunkuyar dakai cikin sanyi tace,
‘Yar buguwace nayi.
Yanayinta sultana takalla taga alamun ba gskia tafada mataba sbd tasan rumanah tun tana jaririya saidai tasan bata taba yimata qaryaba.
Qofar itama takalla sbd taga lokacinda rumanah tasaci kallon qofar lokacinda maheer yafita kenan yana sane da ciwon,
Kodai dama da gangan yasata daukar Abun?
Maida kallonta kan rumanar tayi cikin kulawa tace,
Menene kika bugu dashi?
Qofa.
Sake kallonta ammy tayi tasan tabbas ba abinda tafada din bane taji tausayinta yakamata tace,
Tashi kije zansa maheer yaduba miki hannun idan yadawo.
Miqawa tayi ba musu ta fice sbd zata iya cewa tunda take arayuwarta batasanma ya ake musuba a alamari duk abinda aka sata shitakeyi sbd suma basu taba sata abinda yakaucewa addininta ko lafiyartaba.
Abinci taci kadan tasha magani dakuma shafa ta kwanta nan take bacci yayi gaba da ita.
Ranar Carolina ce tayi aikin komai ita kadai.
Suhailat ta farfado saidai ko motsin kirki da magana bata iyayi komai sai anyi mata koda su amah suka dawo school da yamma tareda sultana suka nufi hospital dubo mum dinsu.
Kodata tashi bacci hannun ya sauka gabaki daya babu wani zafi sosai ta sauko gado ta tube tashiga toilet tayo wanka da ruwan zafi sosai hannun da jikinta dayaso kamuwa da zazzabi suka saki tayi sallah ta fito taci abinci nan takama aikin dinner babu bata dogon lokaci suka gama home made pizza sai boiled vegetables da kuma fruits salad din yarima.
Itace ke jera abinci a dining din suka shigo
Shine agaba hannunsa riqeda riqar suit dinsa ta sama farar long sleeve dinsa kamar yanxune yasata
Kallo daya tayiwa hanyar shigowar ta sauke kai tana aje cups din hannun ta.
Shi ko kallon inda take baiyiba duk da acikin idon juna suka fara cikin karo ya wucewarsa sama.
Dagowa tayi tabi bayansa dakallo yana kaiwa qofa zai shiga ya tsaya cak
Tayi saurin dauke kanta shima baijuyoba sai yashige.
Ajiyar zuciya tasaki cikin ranta tana qoqarin daidaita numfashi.
Ammy dake kallonsu tun shigowarta tasaki numfashi tareda nufar hanyar bedroom dinta tashiga.
Wanka yayi yayi sallar magrib yana zaune kan sallayar akayi ishai yafito yaje masallaci dagacan yana dawowa ko shigowa baiyiba hospital yakoma.
Kwance take idanuwanta a rufe amma hawayen daya gani yasashi sanin idonta biyu yakalli nurses din dake tareda shi da sauri suka fice.
Shafa fuskarta yayi ta bude idanuwanta dasuke jajir ta qura masa ido zatai magana ya girgiza mata batareda yabude bakiba.
Share hawayenta tayi daqyar sbd nauyin jikinta cikin tsanani sanyin murya tace,
I love you…i love you and pls always remember it even in the future.
Lumshe ido yayi batareda yace komaiba ya sunkuya yayi kissing forehead dinta murya daqyar yace,
Time to sleep,Gud night.
Lumshe ido tayi tareda gyara lullubinta ya sake kissing dinta yafice bayan yaduba file dinta.
Koda ya isa gida babu kowa a palo sai sultana itama dan tanason ganinsa ne.
Yana ganinta yasan dawowarsa take jira yayi kissing hannunta yace,
Gud night ammy jeki kwanta nadawo.
Murmushi tayi tareda miqewa ta fuskanci qofar bedroom dinta harzata wuce tace,
Gobe inason kayi mana booking flight zamu wuce Libya nida rumanah zuwa jibi,
Kuma inason kafin natafi da ita tasan matsayin aurenta sbd idan munje ba dawowa zamuyiba acan inason tasamu sabuwar rayuwa dan haka kanada zabin iya sauwaqe mata kafin jibi muwuce.
Tana gama fada bata juyoba ta shige dakinta.
Cak ya tsaya bakin stairs din tun lokacinda tafara magana harta gama yana waiwayowa tana shigewa.
STORY CONTINUES BELOW
Qofar dakinta yakalla kafin ya haye yana isa daki ya kashe wayarsa data damesa da ringing batareda yaduba mai kiranba.
Tubewa yayi yafada toilet yayo wanka yana fitowa yagama shirin kwanciya ya kwanta.
Gari na wayewa ya qarfe tara saura ya sauko cikin shirinsa sbd yanada tiyata har biyu yau.
Motsi yaji dakinsu amah yasa ya tsaya tareda waiwayo qofar tareda tunanin meyasa basu tafi school ba har time din.
Tura qofar dakin yayi daidai zata fito saura kadan suyi karo tayi sauri matsawa gefe cikeda jin nauyin rigar dake jikinta ta bacci sbd ganin Carolina taje kaisu amah school tareda driver yasa take gyaran koina kafin caro din tadawo ta rage aiki.
Qura mata ido yayi tsawon mintuna kafin yakalli hannunta ya dauke kai yafice ko gaisuwarta bai tsaya amsawaba. 1
Saidata tabbatarda ya fice ta dago kai tareda kallon qofar ta daga hannu daqyar taci gaba da aikinta.
Bayan tagama gyaran dakin sultana harzata fita cikin kulawa takira sunanta.
Dawowa tayi ta zauna gabanta cikin ladabi ta amsa.
ki shirya gobe insha Allah zamu wuce Libya,
Rumanah duk Wanda qaddara da jarabawar ubangiji tasama ya rungumeta da imani Allah baya taba bari ya wulaqanta shiyasa nake miki kyakkywan zato sbd ke mai hkr da yarda da qaddarace dan haka ki yarda da qaddarar dazatazo miki dangane da aurenki insha Allah zaki samu kwanciyar hankali da kwakykyawar rayuwa Libya.
Gyada kai tai jiki asanyaye sbd dama tasan aurenta bamai dorewa bane.
Miqewa tayi ta fice.
Tausayinta sultana taji saidai tasan raba auren shine yafi a rayuwar rumanah din sbd maheer bazai taba daukarta amatsayin mataba dan haka gwara ya sauwaqe mata su tafi can ko karatu tasamu tayi har Allah yakawo Wanda zaisota sbd tasan sunyiwa rayuwar rumanah illar da har abada basa fatan tasan sune sukayi mata wannan illar dan kuwa qiyayyarsuce zata ture girmansu a idonta shiyasa takeson ta nesantata ma kwata kwata da mineelik idan tana tareda maheer batai nesa da mineelik ba kuma shikansa idan yagano wannan sirrin saiya tsani sultan da ita kanta mahaifiyarsa.
Rumanah na fitowa tacigaba da ayyukanta jiki asanyaye harsuka gama ta nufi daki tayi sallah azahar tananan zaune Shiru akai la’asar tayi ta fito suka hau aikin abincin dare.
Suna gamawa Carolina ta nufi dakin suhailat tafara aikin gyara sbd washe gari da safe akace za’a sallamota tadawo gida.
Itadai rumanah Suna gama girki ta nufi dakinta tayi alwala tayi sallar magrib tana idarwa tafara hada dukkanin kayanta ta shiryasu a akwatinanta biyu tana gamawa ana kiran sallar ishai tasako wata alwala tazo tayi sallah.
Bayan tagama abinci tafito taci daqyar sbd ko yunwa ba bataji ta dauki apple daya takoma daki.
Tana shigowa ta tube tashige toilet tayo wanka ta zauna sanyaye gaban mirror spray na Prada tadaure dogon gashinta ta zauna zugum.
Qarfe takwas su amah sukai dinner Carolina tashige dasu tayi musu wanka sukai shirin bacci kafin suka fara karatu da tab dinsu daganan kowannensu bacci yayi gaba dashi.
Sultana sai qarfe tara da rabi tayi dinner sbd ganin maheer baidawo da wuriba.
Tana zaune palon tana kallon news qarfe goma da rabi yashigo yana waya.
Ganinta zaune yasashi dakatarda wayar ya kashe gaba daya ya zauna gefenta yana gaidata.
Ciro komai na tafiyarsu yayi ya miqa mata sosai gabanta ya fadi da ganin itada rumanah nedai zasu tafi,
Duk da wani sashe tanason raba auren amma batayi zaton zai barsu su tafi tareba tayi zaton itakadai zai siyowa ticket din.
Karba tayi tareda ajewa gefenta tace,
Wane time ne flight din?
9:00am””””yafada yana miqewa.
Abiyoka da dinner dinka?
Girgiza kai yayi batareda yajuyo ba  yace,
Abani fruits kawai.
Ajiyar zuciya tasauke sbd zancen dazata fada amma ta daure tace,
Idan takawo ka rubuto mata sallamarta sbd nunawa sultan sheda nan gaba.
Juyowa yayi yakalleta kafin ya juya ya wuce.
Yana shiga dakinsa tubewa yayi yafada wanka.
Dakanta ta isa kofar dakin rumanah din ta tura ahankali tashiga da sallama.
Miqewa tayi da sauri ganin sultana dakanta tazo kiranta cikeda kunya dajin nauyi ta durqusa sbd rigar bacci kawai ajikinta.
Ganin tanajin nauyi yasata dauke kai tace,
Kije ki kaiwa maheer fruit.
To ammy'””””tace ahankali cikin nutsuwa.
Idan kin kai kindawo inajiranki adakina.
Sake gyada kai tayi.
Saida ammyn ta fice ta miqe ahankali tareda daukar doguwar riga mai ma6alli biyu agaba da hula tasaka tafito ta nufi kicin.
A qaramin tray ta zuba ta dauki qaramar wuqa ta nufi saman.
Sanin baya palo yasa ta murda tashiga ta isa qofar bedroom dinsa ta daga hannunta dake rawa tayi knocking ahankali.
Jin shiru harso uku yasata murda tashiga
Duhune sosai adakin shiyasa ta tsaya cak tsakiyar dakin.
Ba zato taji anriqo hannunta tayi saurin rintse ido numfashinta na fita da sauri.
Bedside lamp ya kunna tagansa tsaye gabanta cikin sanyeda dogon wandon bacci fari qal amma baisaka rigaba murdadden jikinsa a bayyane ya kafeta da lazy eyes dinsa tuni jikinta yasake daukar rawa ta aje tray din kan table din tsakiyar dakin ganin zai kufce mata.
Yana ajewa ta Juya taji hannunsa yariqo nata ta tsaya cak.
Dawo da ita yayi ta baya ahankali bayanta yahadu da qirjinsa.
Rintse ido tayi numfashinta na tsananta fita ya zura hannunsa daya ya balle botins din rigarta lokaci daya ta zame qasa ta fadi
Sake rintse idonta tayi da qarfi amma ko hannu daya bata daga.
Juyo da ita yayi suka fuskanci juna yana kallon fuskarta yasa hannu ya zame rigar baccinta
Rigar na barin jikinta tasaki kuka ahankali ya jawota yasaka cikin jikinsa lokacin kukanta ya tsananta
Sai kawai ya dauketa ya nufi gadonsa da ita akaro na farko ya hada bakinsa da nata.
#mamuhgee

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button