AUREN GADO Page 21 to 30

Tunda ya dauki hanya take kuka kasa kasa, ta cusa kanta cikin cinyoyin ta, kukan tausayawa kanta takeyi, domin batasan me zata tarar ba idan ta koma cikin wannan gidan. Yana yi yana waigota baice mata tak ba saida ya shiga cikin tangamemen gate din ya parker, kashe motar yayi tareda kallon ta yace “enough munzo gida”, welcome back, ki sauka zanje insiyo miki kazar Amarci, ga part dinki can a bude ki wuce ciki kawai. dago kai tayi hawaye sharkab, “bazan shiga cikin wancan gidan ba” tunfarko ba aso zamana a ciki ba, yanzu ma bazan shiga ba inda nafara zama tun farko a ciki zan zauna. “Gidanki ne you can choose any place, go ahead sai nadawo. Ya ja baya tareda barinta tsaye takasa koda daga kafarta, sakawa takeyi da warwara ta Ina zata fara, Ina ta nufa can inda yace ko ciki ta tarar da Mommy. Juyawa tayi ta nufi hanyar main house, domin da zama da khaleel gwara zama da Mommy a wurinta yanzu.
Shiru tayi saida mommy ta gama tsab ta gaida ita, “momy Ina wuni”. Munafuka da ban wuni ba zaki ganni ba maras zuciya, yoh Ina zakiyi zuciya kina kwadayin a/c gidan Malam nakan buzu babu. Fauziya ce ta matso gaban ta tana huci “jaka akuya” in banda kina dakikiya ina ke Ina my Khaleel kema kinsan na wuce da Ajinki bare inyi kishi dake baki isa in hada miji dake ba.
Wani irin tafasa zuciyar ta takeyi, don haka saida ta gyara tsayuwar ta tace “Ai Akuya nada rana domin akan yanka naman ta aci haka jaki ma domin yakan dauki kaya ko banza kinga shima yanada rana, Amma mutum mai kwakwalwar kifi shine Wanda baisan darajar dan Adam ba, dake mace ce mai daraja bazaki tsaya kina zagin iyayen wani ba, kuma Alhamdulillahi duk rashi da talaucin mu baki gan mu kofar gidan ku muna barar Abinci ba, sannan mijinki dakike magana dashi da rashin shi duk daya a wurina, ni da zaki taimaka min da kinsa ya maida ni inda ya dauko ni yafimin kwanciyar hankali, kuma dake kin kai mace da kin taimaka tunfarko kin hana Auren nan, da banda masoyiya sama dake.
Wani irin daga hannu tayi zata zabga mata Mari taji anrike hannun ta carab, saurin juyowa tayi idanun ta a rufe ko gani batayi tace ” mommy kibarni in daki Y’ar gidan talakawan nan ba kyajin mugayen kalaman datake fadamin ni sa’arta ce.
Jin an watsar da ita a gefe yasa ta dawo cikin hayyacin ta, ta ganshi tsaye fuskar shi ba fara’a, yace “I know you will react like lunatic, shi yasa na dawo, kuma ki godewa Allah da hannun ki yakai fuskar ta yau da sai kin kwana gidan ubanki, tunda bada kudin gwamnati muka gina gidan mu ba.
“Khaleel banson dibar Albarka agabana kake tarewa wannan yarinyar fada, me kakeson nuna mana ne, tafimu mutunci da daraja kenan, Toh ahir dinka dani wallahi zanyi maganin ka da duk Wanda ya daure ma gindi ka kwaso min wannan yarinyar cikin gidana. “Mommy me tayi daga shigowar ta kuma agaban idanun ki take kokarin marar min mata, wallahi da abakin wanna igiyar da kuka daura mara Amfani yau. Baki dukansu suka saki sunkasa furta komai, ya juya gefen ta” kema bakyaji na nuna miki part dinki inda bamai damunki kin shigo nan, kinga bazan iya tare miki fada kullum ba let go to your part. Matsawa tayi tana tura baki ni anan zan zauna bana son can. “OK as you wish, ya riko hannun ta ya nufi hanyar dakin shi da ita tana kokarin kwacewa, Amma karyarta domin ta riku, har wani hadota yayi da gefen shi ya wuce da ita cikin dakin tareda kulle kofar yabarsu a sume, suna shiga ta fisge tareda nunashi “karka kuma kokarin tabani banaso. “Ni kuma inason tabaki kuma bake zaki yanke wannan hukuncin ba nine zan yanke hakan ko Ina bukatar tabaki ko banayi nine zan zartar da hakan.
Juyawa tayi domin ta fita yayi saurin shan gaban ta ya rufe kofar da key ya cire yayi gaba Abin shi, “kazo ka budeni intafi dakina. “Excuse me? Kinada wani daki ne bayan wannan da kuma gidan da kikaki shiga? “Yes dakin mijina da na saba zama. Dawowa yayi da sauri gaban ta, ta zuba mai ido shima cikin kwayar idanun ta yake kallo tareda dage gira daya, “repeat that”, “say it again, yanzu in nuna miki am your husband and believe me zakisha mamaki na. Ja da baya tayi kadan, “nifa bazan Kwana daki daya dakai ba. “OK zamu gani yau, ni kuma bazan Kwana ni kadai ba as far as you are my wife, muje zuwa inga who will win. Kallon dakin takeyi tana tunanin lokacin da ta shigo cikin shi suka zauna akan gadon yana shayar da ita kalamai masu dadin gaske, namiji Dan soyayya yayi a rayuwa, she is missing him so much waye zai maye mata wannan gurbin? Har wani tsigar jikin ta ke tashi idan tana tuna lokacin da yake taba ta.
Kallon gadon tayi taga ba Wanda ta sani bane, karewa dakin kallo takeyi yanzu take realizing an canja komai new, jin motsin shi yasa tayi saurin juyowa, tagan shi yana kwabe kayan jikin shi tayi saurin bashi baya tareda cewa “ai dama bakajin kunyar yawo tsirara a cikin mutane” ka girma bakasan ka girma ba. Bai tanka taba saida ya cire duk manyan kayan yarage dagashi sai boxer, ya fito ainihin namijin shi, tsarin jikin shi a bayyane kirar shi broad chest din shi murdadden hannun shi irin na ainihin maza naturally, Wanda duk macen da ta kalle shi sai ta afka mai lokaci daya, shiyasa fauziya takasa hakura dashi har gobe tana mafarkin kwanciya a wannan kyakkyawan jikin har safe,
Matsowa yayi tareda dafe west dinshi ya zo har gaban ta, zare idanun ta tayi tareda saurin runtsewa bayan ta mai kallo daya tana girgiza kai “wai kai meye haka kakeyi baka kojin kunya”?
Wani irin mugun murmushi yayi, that’s exactly what he is looking for a wurin mace me kunya, and its going to be so much fun, domin duk namijin da ya Auri mace mai kunya zai mori kuruciya da rayuwa mai cikeda nishadi, “open your eyes or…..
Ja baya tayi tareda girgiza kai “kaga don Allah kasa kaya kuma ni kabarni intafi part din da kace. “You are late, now listing to me, open your eyes ko in cire boxer din and believe me kema sai kinyi necked irin nawa mun tsaya aga Wanda yafi kyau ba kaya. Da mugun gudu ta bude idanun ta tareda kallon shi cikin ido way’enda ba duk mace ke iya resisting kallon cikin suba, but sunfi mata saukin kallo akan jikin shi, ita da Ahmed bai taba mata irin haka ba Amma wannan marar kunyar Hmmm.
“What did you said? Bana girma? Yafada yana matsowa tareda yin murmushin gefen baki, irin na muguntar nan, da kuma enjoying each and every moment with her. Tana ja da baya har ta cimma kofar bathroom dinshi ta manne yana biye. Saida yaje gab ya kalli kofar, “just say it ba sai kin jan yo ni da wayau ba. “What? Tafada tana zare idanun ta domin yafi karfin duk wani tunani da zatayi,