Uncategorized

TAYI MIN KANKANTA 31

Ad

_____

 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *TAYI MIN ƘANƘANTA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*To sabon sauyi acikin tafiya,😊akwai sabon novels ɗina dazan saki wata me kamawa in muna da rai da lafiya,sunan shi SHIMFIƊAR AURENA na kuɗi ne duk meso ze iya turo kuɗinsa tun yanzu naira 500 kacal,update biyu arana,safe da dare,insha Allahu, ku biya ku karanta daga jin sunan kunsan zaa ɓata hankalin dare,ga wanda yasan hannun surbajo yasan bazata bashi kunya ba karku bari abaku labari,SHIMFIƊAR AURENA,littafine daze kerewa kowanne,novel nawa,akwai tarin sirrika da magunguna acikinsa,dazasu fito da kimarki ta mace,sannan ga sirrin riƙe miji da ƴan uwansa,an baje kolin basira acikinsa,kisiya ki biya ki karanta,wannan soyayyar da akewa surbajo to afito a nuna ta akan SHIMFIƊAR AURENA,500 ne kacal*

*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*Whatsapp 07044600044 aturo shaidar biyan ta nan*

*Note bana adding a group kuma bana turo book pc in zaki shekara kina tambayar ɗaya daga ciki ba wanda zaki samu daga gareni,na jima ina faɗin banayi amma anki a fahimta,in baayiba kuce anyi wulakanci,*

*31*

Yau ma kamar kullum,zahra ta dawo da makaranta,dan haka kitchen ta nufa kai tsaye ta fara nema musu abinda zasu ci da dare.

Duk komai cikin hanzari take yinshi,dan bataso ya dawo ya sameta a kitchen ɗin.

Ad

Hammad har wata rama yayi ta musamman sabida gaba ɗaya zahra ta gama kwance masa lissafi, wata muguwar shaawarta ce ke ɗawainiya da shi amma ita yanzu ta bari su haɗu ma ko taɓata ne yayi taƙi amincewa,ya rasa me ke damun ta,duk ta sauya masa.

Koda ya shigo gidan magriba akeyi,ganin motar da zahran driver ke kaita makaranta a fake ne ya gane ta dawo.

Jiki ba ƙwari ya shiga falon,ga mamakinsa,tana tsaye gurin center table tana gogewa.jikinshi har rawa yake ya ƙarasa gunta,a ɗan tsorace ta waigo,sosai ta firgita da ganin ramar da yayi.

Ƙureta yayi da ido,yama rasa abinda zece mata,gaba ɗaya zahran yanzu kwarjini take masa ta cika masa ido.

“sannu da zuwa”ta faɗi tana ƙoƙarin kaucewa a gurin.da zafin nama ya kamota,ya maƙureta a bango,yace “nace kidena hukuntani ta haka,pls ki faɗamin abinda nai miki zan baki haƙuri,amma banaso kina wulaƙantani,duk a ina kika koyo wannan halin”yayi tambayar cikin rashin wasa,dan ta fara kaishi bango.

Zahra da tsoro ya fara kamata cikin dauriya tace”ka sakeni da zafi fa,”ta faɗi rai a ɓace.”anƙi a sake kin,ki kasheni ne se ki samu sanyi aranki.”hammad ya faɗi azafafe.

Tsaki zahra tayi,wanda hakan sosai ya harzuƙa hammad ƙara matseta yayi da kyau ranshi a ɓace yace yana huci”bana ɗaukar reni agurin babba ma bare ke,ki iya takunki ki tsaya matsayinki,son ki da nake ba ticket bane daze baki damar wulaƙantani,kina jina”ya faɗi cikin daka tsawa.sannan ya  saketa,luuu tayi kamar zata faɗi sannan ta dawo daidai.

Kuka tasa be tsaya sauraronta ba ya juya ya nufi ɗakinshi,ranshi in yayi dubu ya ɓaci sabida ko iyayenshi basa masa tsaki bare zahra,wato reni ya shiga tsakaninsu kenan.

Kulle kanshi yayi a ɗaki yana ta safa da marwa,yana dukan iska,yama rasa mezeyi mata yaji daɗi aransa.

Zahra ma ganin be tsaya rarrashinta ba kamar yadda tai tsammani sum sum tayi ta miƙe ta wuce ɗakinta.

Hawaye takeyi wannan na bin wannan.

Tabbas ba ƙaramin ɓata masa rai tayi ba amma tasan yayanta baya fushi da ita duk abinda zatai masa,ita tsakin bata san ma ya fito ba.kuka taci ta godewa Allah,sannan ta nemo husna a waya,dan ta faɗa mata abinda ya faru.

“zahra wulaƙanci daban jan aji daban,babu wani namiji dazakiyiwa hala ranshi be ɓaci ba,ni ba haka na koyar dake ba,kidinga dan kama kanki agabanshi,ba ki saki kanki kamar sakarya ba haka nace,amma fisabilillahi taya zakima mijinki tsaki,zahra kisa ran zaku wanye lafiya,to wlh kiyi gaggawar zuwa ki bashi haƙuri”cewar husna cikin faɗa sannan ta kashe wayarta.

Zahra wani kukan ne ya sake kubce mata,tabbas bata kyauta ba itama tasan haka,ganin kukan baze kaita bane yasa ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala,ta fito tayi sallah sannan ta caɓa ado cikin wata doguwar riga wacce ba abinda ta ɓoye ajikinta,hatta ɗan pant ɗinta ana ganin shi,suko nipples dama dede inda suke na rigar net ne ba abinda ya ɓoye.

Feshe jikinta tayi da turaruka masu kwantar da zuciya sannan ta nufe ɗakinshi,cikin takun ta me ɗaukar hankali.

Tura ƙofar ɗakin tayi,ta shiga,zaune yake kan abun sallah ya haɗe kanshi da guiwarshi yayi nisa cikin tunani,jin turo ƙofar ne yasa ya waigo da sauri.

Zahra ce tsaye fam dubunta tsirara tana kallonshi cikin wani salo na natuba.

Kallonta yakeyi,dan be tsammaci zuwanta gunshi ba, besan dalili ba baya iya fushi me tsayi da ita,sonta ya gama nakasa zuciyarshi.

Miƙewa yayi ya koma kan gadon ya zauna ya miƙar da ƙafafunsa ya harɗe hannayensa a ƙeyarsa,ya lumshe ido.

Zahta jikinta duk ya mace,dan haka kasa ƙarasowa tayi,ta tsaya a bakin ƙofar tana kallonshi.

Sun kwashe fin minti talatin a haka,shi lumshe idon da yayi dan ya kalleta da kyau ne cikin sirri ba tare da tasan yana yi ba,ganin duk ta takure ne yasa ya buɗe idon ya saukesu anata,yace cikin dakewa”in kin gama tsayuwar kin fita ki ɗan kullemin ƙofar”

Sosai zahra ta jima da karantar halayen yayan nata,dan haka cikin sassarfa ta tako ta iso gareshi,gefen gadon ta durƙusa tana wasa da hannunta,tace murya a sanyaye,kamar me shirin kuka,”yaya kayi haƙuri don Allah nasan ban kyauta ba,kuskurene bazan kuma ba ka yafeni”ra faɗi a daburce sabida kallon da yake mata.

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button