HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Fahimtar yadda suka kalleta ne yasa tayi murmushi tace”ba wani abu bane nima can nake aiki kuma gsky Yusuf sai kayi hkr don zan rubuta report akanta sbda ta kiyaye ko don gaba tunda irin sune ko ba kishiya ba ahada kai dasu ayi ha’inci acikin aiki yakamata adauki matakin irin waddan nan miyagun ma’ikatan don su shiga taitayinsu sbd aikin jinya ba wasa bane aiki ne na taimakon yan uwa gaba daya.don haka karku damu duk da abun na family ne ba issue bane na waje amma yakamata tasan aikinta.”wannan gsky ne tun lkcn uwar yaron nan ta nemi haka amma muka tausheta sbd gida ne amma tunda yanzu har ankai ga haka kuma gashi Allah ya kawo wani rabon ai bama yi shiru ba.ko yaya kace Umaru??”gsky ne Granny hakan shine daidai.Nabila kam kamar ta rungume matar taji aranta matar tayi mata kuma ko ba komi Jamila zata shiga taitayinta sbd daga ganin matar she is very smart.ita ko Hawwa taso ace da anbar maganar shikam Yusuf bai damu ba da duk hukuncin da Jamila zata fuskanta.nan dai tabasu shawarwari masu kyau kuma tace insha Allahu zata nemesu idan ta koma aiki katsina don yanzu hutu takeyi haka suka bata number’s dinsu tare da gdy sannan kuma tace ma Granny don Allah taba Yusuf matar shi su tafi babu wani abu in Allah yaso, sallama tayi masu ta tafi cikin farin ciki samun mutane masu karamci tunda dama tana ganin girman Kaka acikin uguwarsu.

Haka Umar ya fadima Granny komi game da abunda Mummy sukayi da ita da Jamila wanda shi kanshi Yusuf sai aranar yasani kuma yayi mamakin da Hawwa bata sanar masa ba tabar wannan matsalar ita kadai acikin ranta gsky Hawwa tayi arayuwa yana kuma jinjina ma hakurinta shi kanshi Umar da Nabila babu abunda zai ce masu sai gdy tsakaninsu amma fa Jamila shu’umace ta gske.nan dai Kaka tace duk da haka ba zama za’ayi ba kamar yadda kasa ana rokon Allah to ba fasawa zamuyi ba Umaru acigaba nima nan zan sanya asata a Addu’a kuma ku cigaba da gaya ma Allah Allah yayi maku Albarka ya kara hada kanku yasa zumuncin ku ya zama sanadin shaga Aljannarku.Amin Amin suka amsa gaba dayan su.to ranar dai basu koma ba nan suka kwana kuma sukace kada Granny ta fadi ma kowa so sukeyi su shammaci Umma haka da kyar ta yarda da tsarinsu sannan tunda tayi ma Hawwa kwadon zogale taga ta cinye shi tasa masu aikinta suka nemo mata mai yawa don su tafi da shi da kuli.

*******************
Washegari da basu wani dade ba suka shirya suka kama hanyar katsina Kaka tana tayi masu ftn Alkairi.haka suka isa katsina basu zame ko ina ba sai gidan Umma tana zaune falo ita da Asabe suna fira sai suka tsayuwar mota Asabe ce tace”badai sy Alh Karami bane tun yanzu?”ai kinsan tafiyarsu yanzu haka sun sha rigima da Hjy ne suka rugungunto suka taho, bata gama magana ba sai gasu sun shigo da sallama dariya Asabe takeyi tana amsa sallamar tana cewa”badai matar taku ta koro ku haka ba zama kowa yayi sai Hawwa data je jikin Umma ta zauna dama ita ta kosa ta sauka a motar dariya kowa keyi tare da gaisuwa Umar ne yace “haba Baba Asabe ai ko da mun bata redcard dinta a hannu.Yusuf ne yace Baba Asabe don Allah kije mota abude take akwai tsarabarku nan ki kwasota.” To Ranka shidade tashi tayi ta nufi kofar fita har zata fita “Hawwa tace ki duba gaban mota zakiga wata roba ki dauko mani ita Baba Asabe ” to uwar dakina ta amsa tare da fita wajen Nabilace ta kumshe dariyarta ta tashi ta nufi part dinta ita ko Hawwa bata ma san sunayi ba suma Yusuf da Umar kallon kallo sukeyi suna sunne kai ita ko Umma bata ma san komi ba dawowar Baba Asabe tana mika mata robar da ita kanta bata san kominene ba aciki tayi amsa tayi tabude da sauri tasa hannu zata fara ci Umma kallon mamaki ta bita dashi rike mata hannu Umma tayi tace “Hawwa yaushe kika zama kazama da zaki sanya hannu kici abu ba tare da kin wanke hannu ba??bata fuska tayi kamar zatayi kuka tace” plss Umma kibarni inci tana kokarin kwace hannunta takai baki kamar wata tsohuwar mayya hhhhhh”su ciki manya.kallon Asabe Umma tayi tace kamata kuje kitchen ta wanke hannu sannan”to uwar dakina tashi muje wanda ita tuni Asabe ta gano jirgin itama Umma hakan amma tana son jin ta bakin su tukunna.bayan sun shigene, Umma ta kalli Yusuf da Umar wanda kowa sosa keya yakeyi yana sunne kai tace”kai!!!kusanar dani komi…dagowa sukayi gaba dayansu suna hada baki wurin tambayar Umma kamar me fa???

Hhhhhhh kaji yan rainin wayo…..masha Allah masoyan Tun Ina Karama Ina maku ftn Alkairi kuma Walhi ina ganin sakonninku ngd ngd irin sosai din nan Iluv u all my fans…..

Jinjina agareki Aunty nah ta kaina!ASEEY BEAUTY Allah yabar kauna????????????????????

TUN INA KARAMA????????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!

PAGE 35

……….kallonsu takeyi tana nazarinsu, Umar tashi yayi ya fita yana sunne kai kasa kafin yakai kofar fita shima Yusuf ya tashi ya bi bayansa, murmushin su na manya tayi cikin ranta kuma hamdala kawai takeyi ma Allah.batace masu komi ba itama tashi tayi ta shiga wurin Nabila don itace kawai zata fayyace mata komi, tana shiga tasamu Nabila ta fito daga bathroom.kallon Nabila tayi tace”wai meke faruwa ne da Hawwa Nabila?cikin kulawa da farin ciki ta karaso inda umma take tsaye ta kama hannuwanta tace”Umma ai saidai mu gode ma Allah don Hawwa Allah ya tsareta daga sharrin Mummy da Aunty Jamila.bata boye mata komi ba tun zuwansu kankiya kuma tace tayi mamakin yanda suka hana Granny fadi ma Umma komi amma su kuma sun kasa tunda harda zancen da rigimar Granny tayi mata akan abar mata Hawwa.murmushi Umma tayi tace”Alhamdulillah Allah kai ka iya Allah ka iya mana kada wadan nan bayin naka su kara cutar da baiwar nan taka…..Amin Umma Nabila tace”Insha Allahu Allah zai tsareta.sun dau lkc mai tsawo suna magana da Nabila kafin Umma ta fito cike da murna ta nufi kitchen don ganin me sukeyi ita da Asabe, tana isa ta iske Asabe kadai na sakin dan wake.dariya tayi tace “Asabe yau kuma dan wake zamuci agidan ne?” Walhi hjy uwar dakina ce ke son cin dan wake gashi nan inayi mata so nakeyi kafin ta tashi bacci in hada mata komi.dariya Umma tayi tace”wai Asabe kin fahimci komi ko??”eh hjy ai ina kallonta nasan Allah ya bamu rabun mu “Asabe ina cikin farin ciki kuma ina gode ma Allah yanzu ya kikaga zamu bullo ma Al’amarin game da zaman gidansu kindai san komi akan gidan” gsky ne to hjy me zai hana in koma wurinta in zauna kafin ta warware sosai??”gsky kin kawo shawara haka ya kamata ayi kuma na tabbatar zata samu kulawa sosai kamar gabana take to badamuwa bari kawai inyi ma Yusuf din magana sai ku wuce tare idan sun tashi tafiya ki gama sai ki kimtsa kawai ngd Allah ya bar zumunci.”haba hjy nima fa diyata ce don haka wannan ai yima kaine ba komi.

Koda Hawwa ta tashi baccinta shiga tayi tayi wanka tayi sallah sannan ta tasa dan wakenta daya ji kayan lambu ga kwai ta zabga uban mangyada da yaji tana ci tana jin wani dadi aranta don ita kawai duk abunda taji tana son ci batayi masa da wasa, tana tsakar ci ne Yusuf ya shigo gidan don shi Umar ya wuce gida domin ya huta.hankalinta kwance yanda Yusuf ya hangota saida taba shi dariya yana matsowa kusa da ita yaga uban yajin datake sha ya zaro ido!!!ita kadaice a palo don Nabila ma tana daki tana bacci Umma kuma tana part dinta suna waya da Abba akan abunda ya kamata suyi akan wannan abun farin cikin daya samesu Asabe kuwa na can na shirin tafiya.yana isa ya janye kwanon danwaken gabanta cikin damuwa yace “wannan wane irin shan yaji ne Hawwa kin san ke bamai lfy bace ba ko??kwabe fuska tayi kamar zatayu kuka tace “Don Allah kabani Hubbynah yunwa nakeji cikin shagwaba take magana.” Amma honey ulcer fa kin san kina shan wahala fa idan ta tashi plss ki canza wani mana yana kokarin tashi da kwanon yaji muryar Umma tana cewa”kabar mata abunta ai ba yin kanta bane babu abunda zai faru wannan shine zaman lfyr ta kasan masu yaron ciki anso abasu abunda suke so zuwa wani lkc zasu bari ta karashe magana tana amsar kwanon daga hannun shi tana mika ma Hawwa.amsa tayi ta cigaba da ci tana gode ma Allah da yasa Umma ta fito ta hana shi rabata da abincinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button