HAUSA NOVELWACECE NI Complete Hausa Novel

WACECE NI Complete Hausa Novel

 

 

Tsaki yaja ya fice a fusace ya nufi cikin barreck din gdansa na barreck din ya shiga ya fada kan gado ya dafe kansa yace “oh God everlasting damuwa ce ke gabadayanki” wayarsa ce ta fara ruri ya dauka yaga number Ummuh ya daga da sauri yace “Ummuh ina cikin farin ciki everlasting ciki gareta Ummuh nima nakusa naga dana ki tayani murna Ummuh na kasa boye farin cikina yanzu zan kira Ra’isah na fada mata…” da sauri ta katseshi da cewa “kul Bunayyah banason shirme cikin da baikai ya kawo ba zaka fara yamadidi dashi bakasan cewa wasu daga cikin makusantanka basa burin ganin yayanka ba kai meyasa kullum baka hankali ne?” Murmushi yayi yace “Ummuh kenan ai kinsan ko duniya zataqi zuri’a ta Sweet bazataqi ba saboda haka bazan iya boye mata ba” murmushin takaici tayi cikin tausayin dan nata ta kashe wayar batare da tunanin komai ba ya kira wayar Ra’isah tana dagawa tace “wata guda kenan rabon da ka nemeni sai yau” murmushi yayi yace “yau dinma albishir na kira nayi miki mun kusa samu qaruwa Everlasting ciki gareta wata biyu da sati uku yau Ina cikin farin cikin da bantaba yiba” gabanta taji yayi wata muguwar faduwa bawai lbrn cikin ne ya girgiza ta ba aa sunan daya ambaci yarinyar dashi wai everlasting “Everlasting?” Ta tambayeshi batare da tunanin komai ba yace “eh wlh Sweet amma fah cikin yana wahalar da ita tafi wata biyu tana amai Allah sarki na tausaya mata cikin ya cire mata sha’awata bata iya daukeni kamar dai har dukanta nasha yi ashe nine nayi laifin matsalar daga gareni ne wlh inajin tausayin yarinyar bakiji yanda nake sonta ba bazan iya rayuwa babu itaba…” “dakata Marwan banason shirme me kakeso kacemin? Kanasonta? Ya akayi ka fara sonta ina alqawarin da kayimin na bazaka taba hada matsayina da wata mace ba a zuciyarka me kake nufi da sunan da kake kiranta nifa har yanzu matsayina na alewa ne kawai a suna a bakinka amma wannan qazamar yarinyar mara asali har ta samu matsayin ka kirata da everlasting me kake nufi….”

 

 

Daka mata tsawa yayi yace “ya isheki haka Sweet na fada everlasting kin isa ki hanani fadin abinda ke rainane ko cewa nayi dake zan karya alqawarinki dane idan ta haifa zan karba in baki nikuma naci gaba da hutawa da matata”
Kit ya kashe wayar ya miqe ya fita ransa a mugun bace ya nufi clinic din mutane sai barka sukeyi masa take yaji duk wani quncinsa ya yaye ya shiga ya tarar da ita a kwance lkcn ta gama waya da Helin take fada mata halin da ake ciki tayi mata fada sosai akan sakacinta na daukar ciki yanzu daga qarshe tace “babu damuwa tunda kici gaba da kula da kanki mijinki na tabbatar a yanzu yana sonki so na gaske kiyi hqrn jure masa kada ki sanya aranki kina da ciki bazaki iya da mijinki ba wlh aikine ja a gabanki kiyi yaqi da karuwan mijinki sannan kiyi yaqi da shadiyar matarsa da take rura wutar komai ki dawo da hankalinki jikinki ki saki jiki dashi tunda har zuri’a tashiga tsakanin ku ki barmin sauran aikin”

 

 

Wannan dalilin yasa ta kwantar da hankalinta yanda yaganta yasashi farin ciki ya matsa jikinta da sauri ya riqota ya miqar da ita ya hadata da jikinsa ya dora hanunsa a cikinta yace “inasonki Everlasting kinga dai ikon Allah ko da tuni kishi yasa kin kashe uban yayanki” qasa tayi da kanta tana qoqarin janyewa ya sake riqota yace “kice kinasona kinji don Allah zanji dadi wlh” sake janyewa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ni…ni banason…” Saurin rufe mata baki yayi idanunsa ya ciko da qwallah jikinsa na rawar data bata tsori tace “bafa kaine banaso ba turarenka ne banaso amai yake sani”
Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi yace “na daina sawa amma kice kinasona” lumshe idonta tayi kalmar tanayi mata nauyi kafin tayi mgn taji yayi qasa ta bude idonta da sauri ganin yayi knilling yasata itama tayi qasa tace “ in…Ina…son…ka…” Wata uwar runguma yayi mata yana dariyar da bata taba sanin ya iyaba yace “wayyoh dadi Everlasting da gaske kina Sona?”

 

 

Daga masa kai tayi yayi murmushi yace “na gde Allah yayi miki albarka ya rabaku da babyna lfy kinsan meye sunan babe idan kika haifi mace?” Tayi qasa da kanta cike da kunya yayi murmushi yace “Sakinah shine sunanta sunan qanwar Ummuh ce data rasu shekaru sha uku da suka wucce Marwah asalinmu ba mutanen 9ja bane mu larabawan Lebanon ne Ukteeh shine sunan da Muke kiran Sakinah tare muka taso a gurin kakannin mu nida ita a Lebanon Ukteeh tabani shekara biyar saboda haka ita taci gaba da kula dani bayan Ummuh da Abuh sun dawo 9jah saboda karatuna yasa aka barni acan shekaru sunata tafiya har Ukteeh ta isa aure aka aurar da ita ga wani dan gasar Qatar suka haifi yarsu daya tak me kama da babanta amma ita bata da irin haskenmu tanada dan duhu duhu a cikin fatarta nine na zaba mata suna Fadimatu muna kiranta da Zahrah Everlasting na shaqu da Baby Zahrah sosai tun muna tana qarama na fara nuna mata qauna lkcn idana shekara goma sha bakwai a duniya na gama karatuna,
Tun Ina qarami na taso daso da burin zama Sojah hakan yasa mahaifina ya yarjemin naje nayi training yasani a makarantar sojoji ranar dazan tafi yini nayi Ina kuka ba iyayena nakewa kuka ba rabuwa da Baby Zahrah shine nakewa kuka saboda yarinyar shekarunta biyu amma tayi mugun sabo dani, hakadai ranar dazan tafi daqyar aka rabamu tana kuka ina kuka Ukteeh na kukan tausayin mu”

 

 

Jan fasali yayi ya qara matseta a jikinsa yana shassheqar kuka yace “ashe bansani ba rabuwar qarshe mukayi da Baby Zahrah da mahaifiyarta Marwah rabuwar data zamemin masomin lalacewata Marwah tunda na tafi na kasa samun nutsuwar zuciya kullum saina bata lkcna wajen Kiran wayar Ukteeh kawai dan na zauna nayi hira da Baby Zahrah nayita dariya, ko a makaranta abokai na sun karanceni idan sukaga ina dariya ina walwala to da Baby Zahrah nake waya yarinya qarama me shiga rai duk abokaina sai suka canza min suna kawai suka koma kirana da Baby Zahrah kuma ko hira sukeyi indai ba sunanta suka kiramin ba bana kulasu Marwah munada wata al’ada ta larabawan Lebanon muna iya aurar da yarinya tun tana jaririya ma idan ta samu wanda takeso”

 

Sake share hawaye yayi yaci gaba da cewa “munada wata biyar a training abin ya isheni na kasa jurewa abinda nakeji game da Baby Zahrah saboda haka na shirya nabi jirgi naje 9ja na sanar da Abuh cewa nifa inason Baby Zahrah kuma ita nakeson aure, ba qaramin mamaki da dadi iyayena sukaji ba babu bata lkc Abuh ya shirya muka juyo Lebanon dashi ya sanar da Anwar mahaifin Baby Zahrah yayi murna sosai akace to tunda duka abin na gdane na bari Zahrah ta qara girma sai ayi mana aure, nakuwa qeqashe qasa nace ni saidai a dauramin aure da ita haka aka daura aurena da Baby Zahrah tanada shekara biyu da rabi inada shekara goma sha tara ranar nayi hotuna da yar qaramar matata kamar wata babba haka na rinqa rungume kayata ke ranar a dakina ta kwana na kwana ina kallonta kwanaki uku hankalina ya kwanta Baby na ta zama tawa na koma makaranta.
Satina guda da tafiya aka kira aka sanar da Ukteeh Ummuh batada lfy tana asibiti ashe qaddarar mutuwar matata ne da mahaifiyarta qawata, qin fadamin Ukteeh tayi suka shirya suka tafi 9ja…”

 

Muryarsa ce ta qara rauni kuka yacita sosai yaci gaba da cewa “daren ranar kamar nasan wani abu zai faru dani ban iya bacci ba gashi inata kiran wayar su Abuh da wayoyin su Ukteeh harma data kakanni na na kasa samu ashe a wannan daren qaddarar da rabuwata da Baby Zahrah ta fado Marwah jirginsu ne yayi hatsari a cikin 9ja ya dagargaje a duk wani mutum dake cikin jirgin ya mutu ciki harda Ukteeh da Baby Zahrah har garama Ukteeh su Abuh da mijinta sunga gawarta amma Baby Zahrah ta qone qurmus banganta ba Marwah ta mutu ta barni da ciwo a zuciyata.
Bansamu lbrn mutuwar ba sai bayan wata biyu kullum naje gdansu Baby Zahrah Abuha cemin yakeyi suna 9ja dana gaji na shirya na tafi 9ja na tarar basanan haka sukayita yimin yawo da hankali hardai na gaji naje nasa kakanmu a gaba nace saiya fitomin da matata ina kuka wannan ya tashe hankalinsu suka fito suka fadamin gsky”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button