BudurwaKanjamauLabarai

Na Goga Wa Maza 120 Cutar Kanjamau – Wata Budurwa

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafa wa cutar kanjamau bayan ta gano tana da cuta mai karya garkuwar jiki a shekarar 2016.

Ta yi wannan bayanin ne a Twitter bayan wata ma’abociyar amfani da Twitter ta sanar da yadda take rayuwa da cutar tsawon shekaru uku bayan ta same ta.

Ta bayyana cewa ta samu cuta mai karya garkuwar jikin yayin da take da shekaru 21 a duniya kuma yanzu shekarunta 24.

“Na samu cutar kanjamau inda da shekaru 21 kuma yanzu shekaru na 24 sannan ina rayuwata lafiya.”

A yayin martani kan wallafar, wata budurwa ‘yar Najeriya mai amfani da suna @the_afropolite ta ayyana cewa ta samu cutar ne ta wurin abokin yayanta a 2016 lokacin da take da shekaru 18 a duniya.

Ta kara da cewa a shekarar 2017 ta gane tana da cutar kuma ta sha alwashin gogawa wasu abinda aka bata ba tare da kwaroron roba ba.

Budurwar ta kara da ikirarin cewa ta gogawa maza 115 cutar tare da mata 19 a halin yanzu kuma ba ta gama ba.

“Na samu cutar ta wurin babban abokin yayana a 2016 lokacin da nake da shekaru 18 kacal. Shi ne namiji na farko da na fara sani har zuwa lokacin da na cika shekaru ashirin a duniya.

A watan Disamban 2017 na gane ina dauke da cutar. Daga nan na sha alwashin rabawa mutane. A yanzu na sanya wa maza 115 da mata 19 kuma ban gama ba.

Daga Muryaryanci

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button