WACECE NI Complete Hausa Novel

Mamaki sosai ya cika Ra’isah na yanda yaketa wani rawar kai akan lamarin yarinyar tsoro ya cika zuciyarta tabbas badan tana shayin ya nada mata na jaki a gaban mutane ba da ta gwada masa hauka amma duk da haka zata gwada masa dan kadan, sunansa ta kira suka dago da sauri ta tako gabansu taje ta kusa dashi tace “nayi maka mgn baka bani amsa ba inada abinyi VIP nayo nazo domin na qure qaryarka da kullum kake cemin wannan yarinyar batada lfy shiyasa baka dawo ba to yau dai alawa taje qasa saboda haka kabani dana kuma anan zaka saketa kazo mu tafi dama babu wanda yasan na dawo kaga asirinmu zai rufu sai muce haihuwarsa mukayi yau dinnan”
Wata uwar harara ya zafga mata yace “banason kina karantamin hauka fah a gidan wanne mahaukatan kika taba ganin anyi haka uwar da tana raye a daukeshi a bawa wata shi watanma wacce batasan ciwonsa ba tobari kiji ki shiga hankalinki nine nace zan baki kuma nafasa dolene dana ya rayu da mahaifiyarsa saboda haka ki qyalemin mata ta huta ki juyaki koma inda kika fito muma muna tahowa gobe”
Wata uwar ashar ta dauko ta sauke masa jikinta na rawa tace “Marwan ni kake fadawa cewa matarka wace matar taka wannan yar kwararon haihuwar tasha itace…” Kafin ta ida abinda takeson fada taji wani irin jiri ya debeta, bata gama dawowa hayyacinta ba ya fuzgeta da qarfi ya watsata wajen dakin ya mayar da qofar ya datse,
Matsawa yayi jikinta a sanyaye ta zubawa fuskar yaron ido tana qare masa kallo hawaye na kwaranyowa a idonta “wannan yar kwararon haihuwar tasha…” Kalaman Ra’isah sunayi mata yawo a kunnenta ta sanya hanu ta rungume dannata a qirjinta ta saki kuka me ciwo, matsowa yayi gabanta sunajin yanda Ra’isah ke dukkan qofar tana ihu tana cewa “wlh qaryane qarya kake Marwan kaci amanata qarya kake ka yaudareni ka munafurceni nayi maka rana kayimin dare Marwan baka isaba dolene ka bani dana kuma dolene ka saki yarinyar nan bana buqatarta cikin rayuwarmu ka bude qofar ka bude nace wlh saika bani dana danane Kaine kace zaka bani…”
Hawayen Marwah na qaruwa tana rintse idonta tana furta “Innanillahi wa Innah ilaihirraji’un wata sabuwar masifa ni Marwanatuh Colonel kaina zai fashe jiri nakeji kayi Mata abinda takeso kada ku kasheni…” rufe Mata baki yayi yace “sanin zamu fuskanci wannan qalubalen ne yasa nace kibani hadinkai wajen tabbatuwar kasancewar mu tare kada kisa haukannan a ranki aurena dake mutuwa ce kawai zata raba kuma wlh everlasting bazan taba rabaki da danki ba duk duniya wa kike dashi bayanni dashi meyasa saboda farin cikin wata zan rabaki da naki? Adalci kenan Marwah? Hmmm! Uhmmm!! Sadaukarwarki gareni tafi gaban wannan butulcin Marwah zanyi komai don farin cikinku dake da Ra’isah amma bazan taba tauye haqqin wani saboda farin cikin wani ba” karbar yaron yayi yace “banso ya farajin kowacce kalma ba a duniya naso ace kalimatusshihada itace ta fara ratsa kunnenka Mu’azzam” shiru yayi yana yiwa yaron huduba a kunnensa.
Gefe kuma Ra’isah tanata haukanta na cewa dole sai an bude Mata ta shigo bayan ya gamane ya dago yace “daga yau na koma Abu Mu’azzam na tashi daga Colonel” lumshe idonta tayi ya sake dora matashi a cinyarta ya miqe ya matso ruwan zafi a dispenser ya fara hada mata tea me kauri ya dawo ya fara bata tanasha saboda ji take cikinta kamar anyi mata sata tasha tea din sosai, ajiye cup din yayi ya sanya hanunsa ya zuge mata zip din rigarta ya zare mata ita ya gyara mata riqon yaron a hannunta ya sanya masa nonon a saitin bakinsa aikuwa ya kama, sosai taji wata a azaba ta ziyarceta tayi wata qaramar qara ya kalleta yayi mata ni’imtaccen murmushi yana shafa dayan nonon nata tare da sawa a bakinsa shima yana taya dan nasa zuqowa saida yaji wani ruwa me maiqo ya fara zuwa a bakinsa sannan ya cire ya juyo da yaron yasa masa wannan din a bakinsa yakuwa fara zuqo ruwan nonon tanajin kamar Mu’azzam din na zuqowa da ranta saboda zafi.
Cigaba yayi da matsa dayan breast din nata na hagu da hannunsa yanata zuba mata sannu har saida yaga ta daina ciccijewar sannan ya miqe ya nufi wajen asibitin lkcn Ra’isah ta gaji da haukanta ta fice daga asibitin,
Office din likitan ya koma tayi discharge nasu suka dawo tare yana riqe da ita ita kuma likitan tana rungume da kyakkyawan yaron tanajin kamar tace subata shi yaron balarabe sak.
Kai tsaye wani hotel ya nufa ya fita ya barta a mota bai jima ba ya dawo ya karbi yaron itama ya rungumota jikinsa suka hau hawan farko ya bude wani daki suka shiga ya zaunar da ita ya cire mata mayafinta ya fita bai jimaba ya dawo dauke da kayan abinci ya baje mata a gabanta gasasshen nama ne daya hadu da wata saup sai wani shayi me kauri batajin dadin komai a bakinta haka ya rinqa matsa mata saida taci har saida ya tabbatar ta qoshi sannan ya qyaleta kasancewar dare yayi a lkcn ma bakwai da rabi na dare yasashi gyarawa Babyn kwanciya ya dagata ya dorata a gadon yaja mata blanket ya rufeta yace.
“Kiyi bacci zanje yanzu na tura kayanmu 9ja nanda awa goma sha biyar zasu sauka so zanje na siyo wanda zakuyi amfani dasu zuwa gobe da zamu tafi banason komawa gdan can nasan Ra’isah tanacan tana jirana”
Batayi masa mgn ba ya juya ya fita bayan ya miqa mata wayarta qurawa yaron ido tayi tana kallonsa yanata baccinsa cikin kwanciyar hankali mamaki takeyi wai ta jikinta yaron ya fito, ajiyar zuciya tayi tare da riqe goshinsa tayi masa addu’o’in da suka sawwaqa, wayarta tayi qara ta kai hanunta ta dauka a hankali “Ummuh” taga an rubuta ta kara a kunnenta da sauri kafin tayi mgn tace “barka da arziqi Bintun yanzu Bunayyah yakiramu yake fada mana kin haihu Masha Allah Masha Allah nayi murna da wannan haihuwa Allah ya raya mana Mu’azzam gobe muna jiranku kinji ki shafa min kan dana Allah yayi muku albarka wannan aure shine aure me albarka”
Ajiyar zuciya tayi cike da kunya tace “na gde Ummuh Allah ya qara girma” murmushi tayi ta rinqa fada mata yanda zata kula da kanta sosai sannan sukayi sallama tana ajiye wayar Kiran Helin ya shigo tayi kamar karta dauka sai kuma ta canza shawara ta dauka.
Guda ta rangada tace “am very happy My Marwah kinyi farar haihuwa sai maqiya shabune wannan shine matakin nasararmu ta farko kin haifa ya hana matar gold akwai rikici a gaba amma shima zaizo ya wucce da qafarta saita gudu tabar maki mijinki, inanan Ina jiran dawowarku kada ki yarda ya raba muku gda ya hadaku guri daya tanan ne kawai zata gane kema mace ce kinfi wata macenma ta nanne zata gane yanzu Marwan ba nata bane nakine keda danki tanan ne zata gane tayi wauta kuskure me girma da bazata iya gyarawa ba, mu hadu a next level Marwah Ra’isah kin gama yawo qaramar yar bariki ce ke maci amanar miji………..
~_Rikitata rikita wannan rikicin cikin gida shi ake kira turnuqu fadan ibilisai, ko waye da nasara a hargitsin oho._~
More comments????
More typing????
*Mrs Dr M.A…✍????*
[3/6, 1:09 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER’S ASSOCIATION.* ????????️
( _Y’anci don cigaban Mata, y’an ci ya d’ara bauta, freedom writters._ )