HAUSA NOVELWACECE NI Complete Hausa Novel

WACECE NI Complete Hausa Novel

 

Basu dawoba sai dare sosai lkcn Mu’azzam yayi bacci sukayi sallama da Abuha ta tafi akan cewa zasuzo da Ummuh, suna zuwa gda ya shige dakinsa da Mu’azzam a hannunsa itadai batace masa qalaba itama ta shige nata dakin ta kwanta saboda bacci takeji sosai.
Hakanan sukaci gaba da wata quntatacciyar rayuwa har tsayin watanni biyu kalma bata shiga tsakaninsu ko gaisuwa tayi masa bai amsawa hakanan yakejin bayason ganinta ko motsinta bayason ji a inda yake wannan dalilin yasa sai suyi sati guda basu hadu ba zuwa wannan lkcn ciwo yaci qarfinta sosai kullum cikin zazzabi amai da ciwon kai take gashi Allah ya dora mata wani mugun kwadayi kullum abinda zataji tana sha’awa daban gashi ko tasa an nemo mata bata iyacin na kirki sai taji ta qoshi idan ta cika takurawa kuma ta kama sheqa amai.

 

Kullum Baba Zulai cikin tuhumar ta takeyi meye yake damunta haka amsa daya ce babu komai yau dai abun yaci tura don tunda ta tashi take murqususun ciwon ciki dole Baba Zulai ta kirashi a waya take fada masa budar bakinsa sai cewa yayi “to kiyi mata abinda zaki iya kibarwa Allah sauran” yana ida fadi mata haka ya kashe wayar ta saki baki sororo da tsananin mamaki jikinta yayi mugun sanyi saboda bata taba lura da abin yakai hakaba a matuqar sanyaye ta koma dakin nata ta tarar da ita tadan samu relief ta hada kanta da gadon tanata sharar hawaye ta zauna a gefenta tace “waini meye yake faruwa tsakaninki da mijinki ne yar nan?”
Hawaye ne ya zubo Mata tace “yace bazaizo ba ko?” Kallonta Baba Zulai tayi tayi murmushi me ciwo tace “shiyasa nace kada ki kirashi nasan amsar dazai baki kenan bansan abinda nakeyi masa ba yake daukan wannan matakin akaina ba” kallonta Baba Zulai tayi tace “gsky bazai yuwuba yar nan dole asan abinyi ki fadawa iyayenku asan matakin da zaa dauka bantaba ganin rashin imani irin wannan ba matarka qanwarka batada lfy amma kace babu ruwanka”

 

Girgiza mata kai tayi tace “kada ki fada musu don Allah wlh bana fatan shiga tsakaninsa da iyayensa musamman Ummuh” miqewa Baba Zulai tayi tace “nasan baki da kudi ki tashi ki fito muje a dubaki akwai albashina na wannan watan bantaba ko sisi ba” miqewa tayi suka fita jiri da dibanta Baba Zulai ita ta riqeta Mu’azzam yana bayanta suka fito Jabir drivensu tajasu zuwa wani asibiti dake cikin unguwar suna zuwa babu bata lkc suka bata gado tare dayin gwaje²nsu cikine da ita wata biyu harda sati daya sosai Baba Zulai tayi murna tare da gdy ga Allah bata daddara ba ta sake kiransa ta fada masa yakuwa nuna farin cikinsa harda tambayarsu suna wanne asibiti, ta fada masa yace su jirashi kafin wani dogon lkc sai gashi a asibitin ya shiga dakin da take tana kwance yaje ya rungumeta yanata murmushi yace “na gde sosai everlasting kin gamamin komai” bata iya cewa dashi komai ba likitan ya shigo yace.

 

“Baba jikar nan taki akwai damuwa a ranta don Allah ku rage sanyata damuwa mace me qaramin ciki bata daukar damuwa jininta zai iya hawa” kallon Colonel Marwan tayi shima itan ya kalla ya kawar dakai tare da cewa “me kikeso kici everlasting?” Kawar dakai tayi ji takeyi kamar ta shaqeshi saboda takaici.
Kallon da yaga tanayi masa ne yasashi shiga hankalinsa likitan ya miqa masa takardar magungunan ya fice shima ya tashi ya fita tashi tayi ta dubi Baba Zulai hawaye na zubo mata Allah ya sani batayi farin ciki da samun cikin ba Mota suka shiga Jabir yaja suka tafi gdan suna shiga yayi parking babu kowa a cikin masu gadin gdan su uku sai Ostin shi daya tanata yan waqoqinsu na sojoji bude qofar tayi ta shiga ta haura saman saboda baccin dake idonta.

 

Bude qofar tayi ta shiga ta fara cire kayanta ya rage daga ita sai under siket da bra taji an bude qofar bathroom din an fito ta kalli qofar da sauri cikin firgici wani gajeran mutum ta gani baqi ya fito dagashi sai boxes ya nufota taja baya da sauri tare da qwallah ihu, a lkcn Marwan ya hauro saman da sauri ya bude qofar ya shigo yaga yanda mutumin ya damqi nononta yana qoqarin cire bra dinta yana cewa haba Baby shekara nawa muna harkar nan da zaki tayarmin da hankali ki gujeni yanzu ki barni na jiyar dake dadi yau har magani nasha saboda kince wannan banzan kodadden mijin naki baya kulaki har yanzu nasan kin tara ruwa sosai tun haduwarmu ta qarshe ana danasha gindinki har yanzu zaqin ruwan durinki nakeji a bakin…”
Wani uban ihu Colonel Marwan ya saki tare kaiwa mutumin damqa amma saiya hankado masa Marwah da tuni ta sume saboda tashin hankali ya tureta yabishi a guje ya bangaje Baba Zulai dake fitowa da tire a hannunta ya fice haka suka keta da gudu yana qoqarin zaro bindigar pistol din dake qugunsa yaji sautin harbin ya tashi mutumin ya fadi riqe da qafarsa Emmah ne yayi harbin ganin yanda uban gdan nasa yakecin uban gudu shida wani qato shikuwa Ostin jikinsa bari yakeyi saboda tashin hankali……..

 

 

More comments????
More typing ????

 

 

*Mrs Dr M.A…✍????*
[3/14, 9:32 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

 

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*FREEDOM WRITTER’S ASSOCIATION.* ????????️
( _Y’anci don cigaban Mata, y’an ci ya d’ara bauta, freedom writters._ )

*( F.W.A)????*

 

*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*

 

_typing✍????_

 

*Mrs Dr M.A…*

 

*50-52*

 

Da gudu ya qarasa gaban mutumin ya sanya hanu ya damqi wuyansa ya miqar dashi ya hada kansa da bishiyar da take gurin ya sake jifa dashi a fusace yace “kasamin shi a waccan dakin horon ka hada masa shocking harsai ya fadi abinda ya kawosa gdana har dakin matata waye ya turoshi.
Juyawa yayi da koma ciki zuciyarsa na wata irin bugawa kamar zata faso qirjinsa ya sake haurawa saman ya taddata kwance inda ya barta wani irin tuquqi zuciyarsa takeyi masa duk yanda yakeso yasa a ransa ba ita ta kawoshi ba ya kasa dubada abinda Ostin ya fada masa cewa “hajiya tayi baqo” inkuwa hakane to tabbas tasan da zuwanshi ga qarin wata hujjar daga kalaman mutumin da yake cewa ta fada masa mijinta baya kusantar ta, idan ba itan ta fada masa ba waye yasan baya kusantarta? Juyawa yayi ya fice zuciyarsa na tafasa ya shiga dakinsa ya zube a tsakar dakin dafe da qirjinsa shi kadai yasan irin zafin da qirjinsa yakeyi masa kwarto a cikin gdansa dakin matarsa da yafiso a duniya diye da kowacce mace hawaye suka zubo masa yana girgiza kansa yanajin wani qunci yana mamaye kowanne kusurwa na jikinsa da gaske ne wannan qazamin mutumin ya kwanta da Zahransa meyesa tayi masa haka meyasa zata ha’inceshi.

 

Miqewa yayi yana layi kamar zai fadi ya shiga dakin nata baba zulai ya tarar tana shafa mata ruwa a fuskarta tana hawaye saboda wannan sharrin ya girmi tunaninta matuqa tayi mamaki tunda suke da Marwah bata tabayin baqo namiji ba ko a Hira bata taba cewa da ita tanada wani namiji data sani ba bayan Colonel Marwan ba ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bakinta yana furta “innanillahi wa innah ilaihirraji’un” hawaye nabin kwarmin idonta, tsallaketa yayi ya shiga cikin dakin ya dauki dansa ya tsaya a kanta yace “kin munafurceni kin ha’inceni bantaba tunanin haka daga gareki ba Zahrah kaico da bamu muka tarbiyyantar dake ba wannan ba tarbiyyarmu bace kina da aurena akanki kike neman wani namijin me kike nema Zahrah meye banayi miki wacce buqata kike da ita da tafi tawa dahar kike neman wani kin cuceni Zahrah Allah ya isa tsakanina dake qato har gidana”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button