HAUSA NOVELWACECE NI Complete Hausa Novel

WACECE NI Complete Hausa Novel

 

*************************

Bayan dogon lkc al’amura gabadaya sun rikicewa Colonel Marwan Jos ba dadi bukur ba dadi azaba sosai gashin quma Ra’isah takeyi masa yanda takeso haka takeyi dashi babu mece mata qala gashi tunda ta dawo daga Rasha batada cikkakiyar lfy kullum cikin bleeding na jini take kullum da dare bata bacci cikin watanni ukun farko tayi nasara ta cire masa tunanin Marwah da yayanta amma tun bayan shudewar wannan watanni komai ya qara rikicewa Marwan kullum cikin tunanin matarsa yake da inda zai ganta duk inda yake tunanin Ummuh zata kai masa matarsa yaje amma batanan yaje Lebanon yaje Qatar duka batanan tambayar duniya yayima Ummuh da Abuh amma sunqi fada masa duk ya susuce ya rame sai dogon hanci kawai da idanu kullum cikin Kiran wayar ta yake amma ya kasa samunta ko sau daya wannan abu ba qaramin shigar dashi tashin hankali yake ba kuka kam har yagaji dayinsa a gurin kowa amma babu wanda ya taba tausaya masa wannan dalilin yasa yake ganin kamar su Ummuh sun daina qaunarsa.

 

Haka dai wasu watanni suka qara turawa ciwo nacin Ra’isah a tsaye har yakaita ga kwanciya kashirban lkcn data kwanta ciwon shi baya gari yana Lebanon akayi masa waya akace jikin Hajiya yayi tsanani shima ciwon yakeyi a tsaye hakadai ya daure ya taho, ba qaramin kaduwa yayi da yanayin daya tarar da ita a ciki ba baba zulai ce take fada masa da safe tajita shiru bata fito ba har wajen sha biyu shine ta shiga ta tarar da ita male² cikin jini sharkaf har ka babu shiri ta dauki qaramar wayarta takira Innanta budar bakin Innanta tace ai ita ta jima da yafewa duniya ita idan da rabon ta warke Allah ya tashi kafadu idan kuma babu Allah ya hada fuskokinsu da alkhairi tana kashe wayar ta Kira ta Ummah shine fah suka kawota asibitin to tunda sukazo Ummah tace zataje ta daukowa Hajiyan kaya saboda malalar jinin da takeyi bata dawo ba yau har kwanaki uku.
Baiyi mamaki ba tunda yasan irin wulaqanci da qasqancin da Ra’isah takeyiwa iyayenta bata daukesu a bakin komai ba baqin cikinta shine ya kashe ubanta itama uwar dan dai tanada nisan kwanane shiyasa takawo yanzun.

 

 

Binciken likitocin ya tabbatar da Cancer mahaifa ce tayiwa Ra’isah mugun kamu wadda harta taba wasu bangarori masu muhimmanci na jikinta sakamakon magungunan hana daukar ciki da tarinqa amfani dasu zamanin tana barikinta koda yake har lkcn da suke tare da Colonel Marwan tayiyyi amfani dasu daga bayane da likita ya fada mata zasuyi mata illa ta daina kuma ta dawo tanason haihuwar ruwa a jallo ta rasa an riga an kashe mahaifa da planning qarshe ma al’adarta ta dauke gaba daya kusan shekara hudu batayi wannan dalilin yasa ta samu damar sheqe ayarta son ranta idan tace masa ta tafi China ko Rasha neman magani sai ta lafe da wani farkanta susha sha’aninsu shikuma wawan tabarshi gaho idan ta dawo kuma ya nemeta tace bazata iya ba ta gaji ko batada lfy.

 

 

Saida tayi wata daya da sati biyu a asibitin zuwa lkcn wata nadama ce take zuwar mata imani yana ratsa zuciyarta ganin yanda mijinta da iyayensa suketa hidima akanta duk da ta lura hankalin Marwan baa kanta yakeba kwata² takanyi kukan nadamar abubuwa da yawa musamman data samu labarin wacece Marwah a gurinsa ta shiga tsakaninsu ta rabasu ta qarfin tsiya har tayi qoqarin sheganta musu yayansu na sunnah da ita ta kasa nutsuwa ta haifa masa lkcn duniya na buga bata gangarta me zaqi da dadin sauti yanzun gashi tanaji tana gani tayi batan bakatantan babu haihuwar babu soyayyar mijin tunda tasani da zata tona masa abubuwan data rinqa aikatawa da auransa akanta sakin wulaqanci zaiyi mata idanma bai harbeta ba.
Yauma yazo asibitin suna zaune a dakin da take zaman kurame saboda shidai Allah ya sani tunda tayi sanadin rabuwarsa da matarsa yaji ya tsaneta yayi niyyar qarashe mata saki dayan daya rage tsakaninsu sai kuma ta fara ciwon nan to tunanin kada duniya ta zageshi ace dan bata da lfy ne ya saketa shiyasa yaci gabada zama da ita amma Allah Allah yake taji sauqi ya qara mata gudu.
Wayarsa ce tayi ring ya zarota da sauri ganin sunan Abuha mahaifin Marwah yasa gabansa ya fadi ya kara a kunnensa da sauri yayi sallama cikin sarqewar murya, amsawa Abuha yayi yace “banga kaje ganin yarinyarka ba….” katseshi yayi da sauri yace “ta…ta haihu ne Abuha ina take meta haifa dawa yaron yake kama?” Murmushi Abuha yayi yace “ta haihu yau kwana biyar ta haifi Baby girl me kama dakai kana yaro nayi maka shisshigi nayi mata huduba da Sakinah”………………

 

 

More comments????
More typing????

 

 

*Mrs Dr M.A…✍????*
[3/16, 11:25 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

 

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*FREEDOM WRITTER’S ASSOCIATION.* ????????️
( _Y’anci don cigaban Mata, y’an ci ya d’ara bauta, freedom writters._ )

*( F.W.A)????*

 

*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*

 

_typing✍????_

 

*Mrs Dr M.A…*

 

*56-58*

 

Cike da tsananin farin ciki yakeyiwa Allah gdy ya miqe da sauri zai fita yaji muryar Ra’isah tana cewa “Sweet Zahrah ta haihu ko?” Juyowa yayi ya kalleta sheqeqe yaja wani uban tsaki ya fice daga dakin ya dauki motarsa ya nufi gdansa, ayau dinnan bazai kwana a 9ja ba sai a Lebanon.
Yana zuwa kayansa ya rinqa hadawa bayan ya gama ya shiga yayi wanka ya sake fitowa yayima Emmah mgnyazo yajashi sai airport, babu bata lkc yayi duk wani abu daya dace Allah ya taimakeshi akwai me tashi lkcn aka bashi set, kasancewar yammace suka tashi shigar dare yayi kai tsaye gdan kakanninsu ya nufa yana shiga yaji me gadin yana masa murna hakan ya tabbatar musu da cewa matar tasa tana gdan kutsawa yayi parlourn ya tadda Grandma a zaune itada autansu Ummuh sai Mu’azzam da yaketa qiriniya da tafiyarsa da bata gama qwari ba.

 

Baiyiwa kowa mgn ba ya qarasa inda dansa yake ya daukeshi ya rungume yana dariya yace “Babana shine ka tafi ka barni cikin mawuyacin hali ina mamanka da qanwarka?” Dariya yaron yakeyi harda rufe fuska irin nasu na yara dukka parlourn sukayi dariya, Ummuh dake fitowa daga dakin da Marwah take ta zuba masa ido cike da mamakin inda yaji lbrn haihuwar fuskar jaririyar dake hannuta ta kalla ta kalli fuskar uban nata yarinyar kamar hotonsa kamar har tayi yawa hatta yatsunta da komai nata irin na ubanta ne, ajiyar zuciya Ummuh tayi ta rabashi zata wucce yayi saurin ajiye Mu’azzam ya matsa yace “sannu da qoqari Ummuh ashe nasamu qaruwa Everlasting ta haihu amma shine baki fadamin ba yanzu da Abuha bai fadamin ba shikenan bazan sani ba saikace ba yata ba”

 

Murmushin takaici tayi ta zauna akan kujera batare da tace mashi komi ba ya matsa yasa hannu zai dauki Babyn ta ture hannusa tace “ubanta bai yarda ka taba masa yaba” dagowa yayi a firgice ya dubeta zaiyi mgn ta nuna masa hanya tace “kada ka fadamin komai Bunayyah jeka banson ganinka fah” miqewa yayi zuciyarsa na mugun radadi ya nufi dakin da yaga Ummuh ta fito ta daka masa tsawa tace “kada ka kuskura ka shiga dakinnan ba hurumin ka bane kaje ka dameta da rawar kanka tana fama da kanta” baiko tsaya yaji abinda zata qarasa fada ba ya tura dakin ya shiga ya mayar da qofar ya rufe.

 

Tana kwance a saman gadon ta zubawa silin idonta da yake cike taf da hawaye cikinta nade da bandeji, matsawa yayi da sauri gabanta ya tsuguna a qasa daidai fuskarta ya dora hanunsa saman cikinta ajiyar zuciya taja me qarfi lkcn data shaqi qamshin turarensa ta juyo da kanta idanunta ya fada cikin nasa ya lumshe idonsa tare da sauke numfashi me qarfi yace “ashe aiki akayi miki everlasting meyasa kika boyemin abinda ya kamata na sani yanzun da Abuha bai fadamin ba da shikenan kema bazaki fadamin ba kin biyewa su Ummuh kina fushi dani akan wannan dan qaramin dalilin ba laifina bane kiyimin adalci Zahrah bakeba duniya ma ta shaida inasonki wlh bacin raine yasa na furta miki abinda na furta please everlasting don Allah ki taimakeni kinji”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button