WACECE NI Complete Hausa Novel
More comments????
More typing????
*Mrs Dr M.A…✍????*
[3/17, 9:18 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER’S ASSOCIATION.* ????????️
( _Y’anci don cigaban Mata, y’an ci ya d’ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)????*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍????_
*Mrs Dr M.A…*
*59-60*
Numfashi ta sauke tare da qoqarin miqewa yayi saurin kai hanunsa zai dagota ta daga masa hannu da sauri tace “kada ka tabani Marwan bana buqatar kowanne irin taimako daga gareka na roqeka don Allah ka ficemin anan wlh banason ganinka” yanda take mgnr ne cikin zafin rai yayi mugun razana shi bai taba kawowa a ransa itama tana fushi dashi haka ba abinda ya dauka kawai su Ummuh ne suka hanata nemansa.
Bai gama wannan tunanin ba ta kuma cewa “na dade da cireka a cikin rayuwata na dade da mantawa da wata halitta irinka da take rayuwa a doron qasa kuma na dade da fara nadamar rayuwa da mutum mara uzuri mara imani meson kansa irinka kuma kullum cikin fadawa Allah yabimin haqqina ya sakamin qazafin da kayimin na zina bazan taba yafe wannan mugun tabon da kasamin a zuciyata ba don Allah ka fita Marwan ka ficemin daganan banason ganinka bakada wata alaqa da yata yadai tawace kuma na yarda zan nema mata uba bada dadewa ba ubanda bazata taba tuhumata akan kasancewarsa uba a gareta ba”
Kalamanta iyakar lugude haka sukeyiwa zuciyarsa miqewa yayi ya haura gadon ya kamota ta fusge ta miqe da sauri ya biyota yana cewa “tsaya kiji Zahrah…” Bude qofar tayi ta fice daga dakin da sauri ta fada dakin granny ya tsaya sororo yana kallonta harta rufo qofar yayi murmushi tare da cewa “zaki shigo hanunane yarinya dani kike zancen”
Juyawa yayi ya shiga dakin Ummuh yakuwa yi saa tana bathroom ya qarasa da sauri ya dauke yarsa Mu’azzam yana bacci hakan ya bashi damar ficewa da ita ya sauka qasa da sauri ya bude dakin da yake sauka ya shiga ya kunna hasken dakin ya zauna a gefen gadon ya bude fuskar yarinyar ya zuba mata ido yanajin wani farin ciki yana ratsa zuciyarsa qaunar yayan nasa biyu tana qara shiga duk wata kafar qashi na jikinsa ya jima yana kallon Babyn da taketa bacci cikin jin dadi kafin ya kwantar da ita a hankali ya tashi ya rage kayan jikinsa shima ya kwanta yunwa yakeji amma bazai iyacin komai ba saboda ransa a jagule yake gaba daya komai ba dadinsa yakeji ba.
Ummuh tana fitowa daga wanka taga babu Ukteeh dinta ta fita da sauri sai tayi karo da Granny tace “ina little Sakinah?” Qasa ta nuna mata tace “ubanta ya dauketa naga fitarsa har wani fakar idon mutane yakeyi” murmushin takaici tayi ta juya ta dauki wayarta ta kirashi bugu daya biyu ya daga tace “ka kawomin yar mutane nace maka kafin ranka ya baci” kashe wayar tayi ya sauke ajiyar zuciya ya sake gyara kwanciyar sa yace “idan ma kukayi wasa wlh saina debe yayana duka tunda kuma bakujin tausayi na kun kasa fahimtar halin da nake ciki”
Baikai musu jaririyar ba saida safe ya shiga dakin Ummuh ya nufa ya bude tare da sallama tana zaune tana shirya Mu’azzam guri ya samu ya zauna yace “ina kwana Ummuh ya me jiki?” Harararsa tayi batare data amsa ba tace “saboda ka mayar dani granny shine nace ka kawomin Ukteeh ka shareni ko yarinyar daba lfy ce ta isheta ba kazo ka dauke musu ya ka kwantar da ita cikin sanyi” girgiza kai yayi yace “haba Ummuh saikace bansan ciwonta ba zan barta a cikin A.C waima meye yake damunta?” Bata kulashi ba taci gaba da ayyukanta shiru din yaji tayi yawa ya miqe yace “bari naje naga jikin everlasting din…” Katseshi tayi da cewa “aa kada ka sake ka shigar mata daki wlh zaka fuskanci bacin raina ka daina shiga jikinta ba matarka bace tsoronka nakeji da yarinyar nan” juyowa yayi ya kalleta yace.
“Amma Ummuh koma mene aike kika janyo tun kafin ta haihu na fada muku inason ku dawomin da matata kukaqi kuma ni Zahrah bata haramta a gurina ba matatace idan ke baki sani ba Abuh da Abuha sun sani na dawo da ita qarqashin igiyar aure na dama qaddara ce ta ratsa har hakan ta faru”
Dagowa tayi ta kalleshi da sauri amma kafin tayi mgn ya fice tabi bayansa da kallo tana mamakin yanda akayi Abuh ya boye mata cewa Marwan ya mayar da Zahrah a ranta tace “aikuwa da sauran kallo wlh saiya gwaru kafin ta koma gdansa ai itama tanada haqqi wannan zalumcin yayi yawa”
Shikam yana fita dakin Marwah ya nufa a zaune ya taddata ita da granny granny na bata wani abu a bakinta tanaci tanata zuba mata sannu, zuba mata ido yayi gabadaya ta canza masa tayi wani haske tayi qiba ga wani kyau data qara na kwanciyar hankali daganinta kasan hankalinta a kwance yake kuma tana samun kulawar da take buqata.
Numfashi yaja ta dago a kasalance ta kalleshi shima ita yake kallo granny ta miqe tace “yawwa dama na gaji Ina bata tanaqin karba zo maza kayi aikinka dama amfaninka kenan” miqewa tayi zata fita itama ta miqe zatabi bayanta ya damqo hannunta da sauri ya mayar da qofar ya datse da key ya zare key din ya janyota yana qoqarin hadata da jikinsa, batada qarfi saboda ba qaramin galabaita tayi ba a haihuwar Ukteeh wannan yasa yayi nasarar hadata da jikinsa ya matseta yana sauke ajiyar zuciya ya dago fuskarta ta rintse idonta bakinta yana rawa ya dora dan qaramin bakinsa akan nata yana tsotsa tare da lumshe ido yana qara shigar da ita jikinsa yana tura harshensa cikin bakinta daqyar ya samu ta buda masa ya shigar da harshensa cikin nata yana danna nata dashi yanajin wata nutsuwa na saukar masa rabonsa da samun wannan nutsuwar tun ranar da zaiyi mata cikin Uktee sai yau.
Lumshe manyan idanunsa yayi tare da sanya hannunsa cikin gashinta yanajan wani rikitaccen numfashi, janye bakinta tayi ta fara qoqarin qwacewa ya sake riqeta idanunsa har sun lada sunyi jawur yace “don Allah kada ki hanani samun nutsuwa dake everlasting ni nakine ke tawace kada ki bari shaidan ya sake shiga tsakanin mu ki dauka qaddara ce ta ratsa har abinda ya faru ya faru Allah everlasting nasan sanda na ganki da wannan tsinannen mutumin amma bansan komai daya faru ba bansan sanda na dauki wayata na rubuta sakon sakin na turawa Ummuh ba bansan sanda na furta duk wata kalma dana fada ba everlasting meyasa su Ummuh sukeson nunamin yayana biyu da Allah ya azurtani dasu ba nawa bane harma suna iqirarin ni da kaina nace banason cikin jikinki wai dakaina na sheganta halattaciyar yata? Meyasa kema kika kasa fahimtata kinsan halin dana shiga saboda rashinki kinsan wahalar da nasha saboda rashinku a kusa dani everlasting nasha wahala sosai inama kansha indai baki tausayamin kin daina guduna ba ban cancanci hakaba daga gareki Zahrah tun bangama sanin kaina ba sonki yake wahalar dani nan gaba kadan zai kasheni wlh muddin kikaqi yarda dani”………………
More comments????
More typing????
*Mrs Dr M.A…✍????*
[3/17, 7:51 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER’S ASSOCIATION.* ????????️
( _Y’anci don cigaban Mata, y’an ci ya d’ara bauta, freedom writters._ )